Showing 273001 words to 276000 words out of 452169 words

Chapter 92 - Mayrah Complete By Khaleesat Haydar

wanda yake nufi tace "Wai Musharraf? Dubiya kawai ya zo yi yallabai" Abba ya wani hade rai yace "What for? Sannan wa ya gaya masa bata da lafiya har ya zo Dubiya?" Ammi da jikinta yayi sanyi ta kasa cewa komai, a fusace Abba yace "Am asking wa ya gaya masa bata da lafiya har ya zo asibitin" A hankali Ammi tace "Maheer ne ya kirasa saboda hankalinta ya kwanta, dazu da safe ta dinga cewa a kira mata shi ta nemi yafiya, kasan in mutum na jin jiki babu abinda bazai zo ransa ba...." Abba ya dakatar da ita yace "Can u hear ur self speaking? For what reason za ku yanke hukunci ba tare da sanina ba, shi bashi da hankali ne Maheer din da zai kirasa? ko ya manta rashin mutunci da tijaran da suka yi mana a police station ne?" Ammi tace "Aa yallabai ku ka yi ma juna dai, kar ka manta mu fa musulmai ne, meye amfanin keeping grudges, ai ba haka addininmu ya koyar da mu ba, beside don ya zo dubata naga ba laifi bane sannan tare ma da mahaifiyarsa suka zo wallahi har ta ba Mimi 50k, to meye laifinsu? Kar fa ka manta ku kuka fara saka yan sanda suyi arresting yaron, to tunda har suka iya mance hakan su zo har Abuja dubiya daga kano don me mu ma baza mu manta ba?" Cikin fada Abba yace "Ohh haka kike gani ko? To wallahi idan wani abu ya kara billowa ke zan yi blaming, shi kuma Maheer banda bashi da tunani sam ko ita tace a kira mata yaron sai ya kira, inda Usman ya fi sa kenan don nasan da shi ne bazai kirasa ba wallahi, ana ƙoƙarin yarinya ta mance sa completely a rayuwarta shine ku ke kara gayyato mata shi, iyayen yaron nan su ne root din duk abinda ke faruwa da ita a yanzu" Ammi tace "To dai wannan MDn dake tsaye kanta ba dare ba rana yayan Musharraf din ne, uwarsu daya ubansu daya, sai mu yi yaya kenan?" Kallonta Abba ya tsaya yi baya ko kiftawa, bayan few seconds yace "Yayan Musharraf kuma? How?" Ammi tace "Mu ma duk haka muka yi mamaki kamar yanda ka yi, yayansa ne uwarsu daya ubansu daya" Shiru Abba yayi alamar he is completely speechless, Ammi tace "Atoh, kuma kai kanka ka fadi kirkinsa, dubi fa duk da matsayinsa na MD yanda yake mana a asibitin nan, yanzu ma bai dade da fita ba ma ka shigo, wai CEO dinsu na son magana da kai, kilan maganar Bill dinsu ne...." Abba ya sauke ajiyar zuciya bai sake cewa komai ba, Ammi ta juya ta koma cikin ward din, Office din Dr Khalil Abba ya tafi, Dr Khalil dake shirin zai tafi gida don ba shi da night shift ya gaida Abba da ladabi, Bayan Abba ya amsa yace "Pls Dr kayi min magana da MD wai yana nemana" Dr Khalil yace "Ohk to bari in duba ko yana office" Fita Dr Khalil yayi ya tafi office din MD, zaune ya gansa a kan office chair dinsa da cup din coffee a gabansa ya jinginar da kansa da kujeran idonsa a lumshe, yana jin an bude kofa ya bude ido a hankali, Dr Khalil ya karasa yace "Wai lafiyarka kuwa duk na ganka wani iri, in dai Mayraah ce naga fa har magana ta fara bawan Allah" MD yace "Ban gane ba" Dr Khalil yayi wani dariya yace "Dama ina ta son sai ta samu sauki in maka tambayoyin nan dake cunkushe a raina sun hanani sukuni....." MD yace "Tambayar me?" Dr Khalil na murmushi yace "Ko da yake da sauran time, ba yanzu ya kamata in maka tambayar ba" Ko kallonsa MD bai sake yi ba, ya matsar da coffee din gabansa, Dr Khalil yace "Dad dinta ne ya zo office dina wai kace kana nemansa" MD yace "Yea, bari in fara ma Ceo magana, ita ce ke nemansa" Daga haka ya mike yana tafiya a hankali Dr Khalil dai ya bi sa da kallo. Abba na zaune office din Dr Khalil MD ya shigo bayan ya gaishesa yace "Tana office dinta zaka sameta a can Sir" Abba ya mike yace "Ohk then" MD yayi leading dinsa har zuwa office din Ceo, bayan yayi knocking ya bude masa kofa, Abba ya shiga MD ya kullo kofar sannan ya bar wajen, Zaunawa Abba yayi saman kujera yana gaisheta, a hankali ta amsa, Abba yace "Ya kokari kuma? Dazu da safe nake Allah Allah in tambayi Bill dinmu sai kuma wani uzurin ya taso min naje kano, dawowata kenan aka sanar kina nemana" Ceo ta gyada kai, bata bari sun hada ido da shi ba duk da dai glass na idonta speaking calmly tace "Pls birth certificate din daughter din ka nake tambaya da garin da aka haifeta...." Abba yayi shiru yana kallonta ita dai bata bari ta hada ido da shi ba, ta dinga kauda takardun kan table dinta, Abba yace "Ai ranki shi dade wannan sai dai in tambayi me dakina, don na mance ko an mata ko ba ayi ba gaskiya...." Ceo tace "To ko zaka tambayeta sai ka dawo yanzu ina jiran ka" Abba yace "Sure, right away" Mikewa yayi ya nufi kofa ta bi sa da kallo kafin ya fita a hankali tace "Ko da ba a mata Birth certificate ba ina bukatar garin da aka haifeta, da ranan da aka haifeta, da kuma lokaci" Abba ya juya ya kalleta, shiru yayi na ɗan dakikai, sai kuma da sauri yace "Toh zan tambaye ta" Daga haka ya fita ya kulle mata kofa, mamaki ne ya cika Abba, don ya kai second talatin a tsaye bayan ya fito daga office dinta, to me kuma zata yi da birth certificate din Mayraah, ai it's something that is not necessary shi dai a tunaninsa, to ko saboda a saka a file dinta ne take tambaya, amma gaskiya shi kam bai taɓa jin asibiti sun bukaci birth certificate ba in ba dai kilan shi ne bai sani ba, a haka dai har ya isa dakin da su Mayraah suke.... Zaunawa yayi yana kallon Ammi dake lallaba Mayraah ta ci abincin da Aunty Mariya ta girka mata, yace "She is asking for her birth certificate" Ammi ta juya ta kallesa tace "Birth certificate kuma? What for?" Abba yace "Ni ma dai shine na kasa ganewa, dama idan an kwantar da mutum a asibiti ana tambayar Birth certificate dinsa ne? Ina ce iya shekarunsa ake tambaya" Mayraah dai kallonsu kawai take, Ammi ta ajiye plate din abincin hannunta bata sake cewa komai ba, Abba dake kallonta yace "Ya naga mood dinki ya canza, lafiya kuwa? is there anything wrong?" A hankali Ammi tace "To ai ban taba jin haka bane, why is she asking for her birth certificate, ita dai ba iyaka ta fadi bill dinsu mu biya su kudinsu su sallamemu mu wuce gida ba, ai jikin nata ya ma yi sauki tun da yamma kawai a sallamemu gaskiya..." Abba zai yi magana Usman ya shigo da sallama, Ammi na kallonsa da sauri tace "Usman ka taɓa jin inda aka tambayi patient birth certificate a asibiti? ba iyaka shekarunsa ake tambaya ba ko date of birth dinsa? Then why the certificate gaba daya?" Usman yace "Birth certificate kuma? Me za ayi da shi" Abba yace "To haka dai tace, har cewa tayi in ma babu birth certificate din to tana bukatar garin da aka haifeta, ranan da aka haifeta da kuma lokaci, amma bari dai Maheer ya shigo sai mu tambaye sa ko haka ake yi" Ammi tace "Aa kawai kace mata ba a taɓa mata certificate din haihuwa ba, kuma a kano aka haifeta a gida ba a asibiti ba...." Abba dai bai sake cewa komai ba. Ana kiran isha shi da Usman suka tafi masallaci, Ammi dake ta zaune ta kasa motsawa daga inda take tun maganar da Abba ya kawo mata ta juya a hankali ta kalli Mayraah, cikin sanyin murya tace "Ina ke maki ciwo yanzu kuma Mimi?" Mayraah ta ɗan yi murmushi tace "Yanzu dai babu ko ina Ammi, kawai dai jikina ba kwari ne har yanzu" Ammi tace "Kin gaji da zaman asibiti ko?" A hankali Mayraah ta gyada mata kai tace "Na gaji Ammi" Ammi ta bude handbag dinta ta ciro dubu biyar sannan ta mayar da jakar ta ajiye ta mike tsaye tace "Mu tafi gida kawai nasan baza su yarda su sallamemu ba sai suce sai nan da wasu kwanaki..." Daga haka ta kama hannun Mayraah ta sauko da ita daga kan gadon dama an riga an cire mata drip tun dazu da ya kare kuma ba a sake saka mata wani ba, Ammi ta dauko mata takalmanta ta ajiye mata, Tana rike da ita ta saka takalmin, sai da Mayraah ta ga wani jiri bayan ta tsaya, Ammi bata damu da hakan ba tana rike da hannunta suka nufi kofa suka fita daga ward din, suna shigowa reception ta ki kallon ko wace nurse ta nufi kofar fita, daya daga nurses din ta mike tace "Ma'am... Za ku ina?" Sai a sannan Ammi ta kalleta da sauri ta kirkiro murmushi tace "Aa za mu ɗan zaga premises din asibitin ne tayi exercise ko zata ji kwarin jikinta" Nurse din ta koma ta zauna tace "Ohk Ma" Daga haka Ammi ta fita rike da Mayraah, direct gate suka nufa Ammi na waige waige har suka fita daga asibitin gaba daya, da kyar Mayraah ke tafiya don har strength dinta ya kare, Ammi dai na rungume da ita a jikinta har suka iso bakin titi ta tsayar masu da adaidaita sahu suka shiga ta gaya masa inda zai kai su.

Mayraah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence via 07087865788

Ina iyaye, yayye da Anties din yaran suke ne If you're looking for an exclusive Baby clothing boutique then visit us at Kids Collection & Fabrics
Shop No BB3, Palm Height Plaza. Opposite Padofec Estate, VON / Trade more road Abuja Nigeria.

Muna da Kayan yara masu kyau da inganchi directly from Bangladesh, Turkey and Dubai
Kuma masu sauqin kudi da rahusa very unique & affordable. Muna delivering zuwa ko wace jaha a kowane Lokaci
For more beautiful pictures and videos check our Instagram page @kids_collection_nfabrics
https://www.instagram.com/kids_collection_nfabrics?igsh=YzljYTk1ODg3Zg==
In
For enquiries and order
Contact 08035943474

You'll never regret buying from us.

84
Mikewa Aunty Mariya dake zaune parlor tayi da mamaki tana kallon Ammi da suka shigo parlon tana rungume da Mayraah, ta karasa kusa da su da sauri tace "An sallameku ne Ammi?" Ammi bata amsan tambayarta ba, hakan yasa Aunty Mariya ta taimaka mata wajen rike Mayraah da ko tsayuwan kirki ta kasa suka wuce sama zuwa Bedroom din Ammi, Ammi ta kwantar da ita a hankali saman gadon sannan ta rufa mata duvet tana kallonta cikin sanyin murya tace "Sannu" Mayraah dai ta kasa cewa komai don ji take kamar an kara mata ciwon da take ji a kirjinta tun da suka fito asibitin, ga wani sabon ciwon kai, Aunty Mariya dai na tsaye ita ma sai sannu take mata ganin yanda take sauke numfashi, Mayraah ta lumshe ido don baza ma ta iya amsawa ba, mikewa Ammi tayi ta fita daga dakin, Aunty Mariya ta bi bayanta ta sameta zaune parlor tayi tagumi, Aunty Mariya tace "Wai an sallameku ne Ammi? naji jikin nata da zafi fa, numfashin ma kamar da kyar take yi" Ammi ta kalleta a fusace tace "To ya bazan dawo da ita gida ba Mariya? Ban san me matar take nufi da ita ba...." Kasa ci gaba tayi ta fashe da kuka, Aunty Mariya that is confuse ta zauna kusa da Ammi tace "Ban gane ba Ammi, me ke faruwa? wace mata?" Cikin rawan murya Ammi tace "Tun fara aikinta a asibitin dama hankalina bai kwanta ba Mariya, har cikin raina naji ban yarda da CEO din asibitin ba, in baki manta ba ai har kiranki nayi na gaya maki tafiyar da ta sa aka yi da ita zuwa UK, ban san meye manufarta akan Mayraah ba, yanzu kuma ana zaune kalau kawai ta kira Abbansu wai tana bukatar birth certificate, to me zata yi da birth certificate din Mayraah? Dama ana haka a asibiti ne? Me yasa tun kwantar da mu ba a bukata ba sai yanzu?" Da damuwa Aunty Mariya tace "Kai Ammi, shine zaki fito da yarinya babu izininsu bayan kin san halin da ta tsinci kanta a kwanakin baya da kyar kuma aka samo kanta, what if jikin nata ya kara rikicewa Ammi? Sannan meye a ciki don an tambayi Birth certificate dinta? This is not enough reason na dawo da ita gida Ammi, ni damuwata kar ciwon nan ya dawo sabo mu shiga uku" Ammi na hawaye tana girgiza kai tace "In sha Allahu hakan bazai faru ba, kawai Alhaji ya dawo a canza mana wani asibitin gaskiya don bani da kwanciyar hankali a asibitin nan, ban san meye manufarta akan yarinya ta ba, wa ya sani ma ko er Cult ce, wallahi duk fargaban da nake kenan" Aunty Mariya dai ta kasa cewa komai tayi tagumi tana kallon yayar tata, Ammi dai hawaye sai sauka idonta yake, bude kofar Parlon aka yi duk suka juya, Abba ya shigo Usman na biye da shi a baya, Abba sai kallon Ammi da ta wani hade rai yake, sai kuma ya kalli Aunty Mariya yace "Ina Mayraahn take?" A hankali Aunty Mariya tace "Tana daki" Wucesu yayi ya shiga dakin, Usman ya karaso kusa da Ammi ya duka yana kallonta yace "Ammi meyasa za ki taho da ita gida a halin nan da take ciki?" Ammi ta fashe da kuka tace "Wallahi Usman ban yarda da Ceo din nan ba, da kyar in ba er shan jini bace" Usman ya ma rasa abinda zai ce mata sai kallonta yake, Abba na shiga Bedroom din yaga wani sabon zazzabi ya rufe Mayraah, sai sauke numfashi take da kyar, ya fito parlor a fusace yana kallon Aunty Mariya yace "Kin dai ga karamin tunani irin na yayarki ko? Ina ce kin dai gani? Yarinyar da dakyar aka samo kanta shine saboda rashin tunani baiwar Allahn nan zata fito da ita asibiti bata duba halin da take ciki ba? Wani me hankalin ne zai yi wannan abun da tayi?" Aunty Mariya ta mike da sauri bata bar sa ya ci gaba ba ta dinga basa hakuri, Ammi dai ko kallonsa bata yi ba hawaye na sauka idonta, Abba da ransa yayi mugun baci yace "Zan maida ita asibitin kuma wallahi bana son ganin kafarta a can, gwara ke Mariya ki je ki ci gaba da jinyarta" Ammi ta mike tace "Wallahi bazaka maida min yarinya asibitin matar nan ba, ai asibitoci kala kala ne a Abuja kuma masu kyau, wanda ma suka fi wancan kyau, me yasa baza a canza wani asibitin ba..." Ko kallonta Abba bai yi ba ya shige dakin Aunty Mariya ta bi bayansa, Usman ya kama hannun Ammi da ke kuka suka fita parlorn ya maidata wani parlor yayi kasa da murya yace "Ammi bai kamata ki fito da ita asibitin ba, har yanzu fa ba wai samun sauki tayi ba kuma kema kin sani..." Katse sa tayi tana kuka tace "Me yasa baza ku fahimce ni ba ne wai Usman??" Usman ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yace "Na fahimce ki Ammi, birth certificate dinta da ta bukata ka'idar asibitinsu ne za ayi photocopy a saka cikin file din patient, kinsan ko wani asibiti da rules din su, so baki tsaya kin fahimci dalilin tambayar certificate din da tayi ba kika yi saurin yanke hukunci" Ammi dai bata fasa kukan da take ba, Usman ya dinga kokarin kwantar mata da hankali. Aunty Mariya na rike da Mayraah suka sauka downstairs Abba na biye da su a baya, gaba daya jikin Aunty Mariya yayi mugun sanyi, bata san sanda Abba ya dawo mafadaci haka ba cikin kankanin lokaci, da da ne a yanda ta san sa uffan bazai ce ma Ammi ba sai dai kawai ya maida Mayraah asibiti, amma yanzu sam ba haka ba, ya daina mata uzuri kwata kwata, Mayraah na rungume jikin Aunty Mariya har suka isa asibitin a motar Abba, zuwa sannan kam gaba daya jikinta ya rikice don sai sarkewa numfashinta yake, hakan ya sa aka shiga Emergency da ita. Duk yanda Ammi ta so zata koma asibitin bayan tafiyar su Aunty Mariya Usman bai yarda ya bar ta ta koma ba ganin yanda ran Abbansu ya baci, cikin kwantar da murya yace "Ammi pls ki bari gobe da safe sai ki je tunda tare suka koma da Aunty Mariya kuma kinsan zata kula da ita sosai, don Allah kiyi hakuri ki bari gobe, nima yanzu bazan koma ba, idan ya so gobe da sassafe sai mu je" a haka dai ya dinga kwantar mata da hankali har ta hakura da komawa asibitin amma ba can cikin ranta ba, su Hajja da Mama Ladi suna can dakin visitors basu ma san me ke faruwa ba a gidan. Karfe sha biyu saura aka cire ma Mayraah oxygen da aka sa mata bayan numfashinta ya dawo dai dai, MD da Dr Hamid ne tsaye Emergency ward din watching her closely, MD ya karasa kusa da ita ganin kamar magana take son yi, dukawa yayi yana kallonta bai dai ce komai ba, da kyar tace "Ina son zan sha ruwa pls" Yayi shiru bai ce komai ba kuma bai fasa kallonta ba, hakan yasa ta dauke kanta tana kallon direction din Dr Hamid kilan shi zai taimaketa, shi ma da yaga magana take son masa ya isa kusa da ita ya duka yace "Ya aka yi?" Murya can kasa tace "Dr ruwa nake son zan sha" Calmly Dr Hamid yace "Za ki sha zuwa anjima, be patient" Ta marairaice tace "I'm very thirsty" Yace "I know, za ki sha anjima kadan" Daga haka ya juya ya fita ward din, Abba dake bakin Emergency din a zaune tun dazu ya mike yana kallon Dr Hamid, Dr Hamid

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login