Murucin Kan Dutse

Chapter 24 of 146

a gajiye nake banga anty a falon ta ba yadda na saba samun ta tana dan zama ana hira.
Sai da na shiga gurin mu na aje kayana nafito zuwa dakin ta a kwance na samay ta nace anty lafiya dai ko ?
Tace da sauki yau ina dan jin jikin ne Rama amma ba wai wani can ba da yamman nan ne ai na, dan ji ba daidai ba.
Na dan tsaya tsaye ina nazarinta a gurin sai dai ban fahinci komai ba na juya na fita zuwa kitchen.
Abinci na hada muna don baci akeyi ba sai nayi dan kadan nagama na shige dakina wanka nayi na fito zuwa gurin anty na samu ta tashi tayi sallah tana zaune a gurin ta ishishire kafata tana ganin na shigo ta mayar da hankalinta gare ni tana fadin har kin kammala ne Rama ?
Eh anty na bata amsa ina nufin gadon dakin dake yamutse a lokacin na fara gyarawa tace ai dama kin barshi har da safe ki gyara nace bari dai a gyara kiji dadin kwanci ai.
Fira muke ina dan kawar da kayan da nagani barbaje a dakin take cewa dani ya kamata fa idan kunyi hutu ki dan leko gida hakana.
Kada muyu rashin hankali yau fa kin kai wata biyar a garin nan babu wani labarin gida kada ace ko an sace ki ne ai.
Dariya nayi nace haba dai ina zasu zaci haka tunda sun san da mama muke nan din ai bazata bar dukiyanta can ba ta gudu.
Innan ki nake tunane wallahi nakan so a dan aika mata da dan wani abu sai dai gurin nakune da wuyan zuwa wallahi sai in mutum zan tayar yatafi can din.
Anty ai zan tafi da zaran anyi hutu na dubo su nima hankalina yana gurin inna wallahi ga rayuwa yanzu kowa kan shi ya sani.
Amira ce ta shigo dakin tana kwala min kira wai nazo ga Nasir zai bata min waya na ya dauka yana game dashi.
Amira bari ya gama sai na baki ke ma kiyi game din dashi a, a Rama jeki karbi wayan ki bana so ana ba yaro waya ni.
Ba wasa a fuskanta don haka na bar abinda nakeyi naje gurin yaran a cikin hikima na karbi waya na zauna muna game din dasu har zuwa dare sukayi barci.
Bayan na gyara wa kowan su kwanciya ne na rufo kofan dakin zuwa dakin anty ta canza yanayin zaman ta yanzu zuwa jingina jikin ta da bakin gadon ta.
Anty baki kwanta ba ashe tace har na kwanta naji kwanciyan ba dadi ido na tsura mata ina nazarin yanayinta na dan lokaci.
Tace nasan yaran ne suka tsayar dake a daki ko nace cikin murmushi sunyi barci ai yanzu.
Ko zakisha ruwan zafi ne a hada maki naga baki ci abinci ba yau tace a kasalance hada min nagani ko zan iya sha.
Najuya zuwa hada mata tea din mama na falo zaune tana kallo don akwaita da son kallon wasan hausa.
Duk wanan yanayin da Anty ke ciki bata san da shi ba har na hado nakai mata shayin ta.
Tasha sosai ina zaune da wayana ina karatu a ciki daga gefen ta tace na bata ruwa mai dan sanyi kadan na mike zuwa kitchen na dauko ruwan.
Sai bayan na koma na zauna nake kallon agogon wayana dare ya soma yi lokacin dan goma da rabi ya kusa.
A gefen gado ta dan sada kanta kamar mai barci sai naci gaba da karatuna don ina zaton ta samu barci ne a lokacin.
Can take cewa dani Rama dan kamani na kewaya gaba na ne ya fadi don ban son jin kalma kamani daga bakinta don tuna ranan da tai wanan ciwon ba dadi.
Na kamata zuwa bandakin nafito har na zauna naji ta kwalla min kira da karfi da sauri na karaso har cikin ban dakin da take.
Gurfane take a kasan ban dakin nata sai dai duk yanayinta ya sauya idanuwan ta sun firfito waje kaman ba ita bace muke zaune da ita lafiya yanzu ba.
Tace yi sauri kizo ki kamani don Allah da sauri na kara ida take duke, a kasa cikin ban dakin nata duk da baida wani datti don kullun ina wanke shi kusan sau biyu ko uku idan ina gida.
Irin rikon da tai min sai da kasusuwan jikina suka amsa a lokaci daya naji tana wani irin nishi mai karfi.
Duk tsoro da fargaba ya kamani a lokaci daya kara karfin rikon da taimin tayi tai wani irin nisawa da karfi sai ga yaro ya fado kasa yana ta cilla ihu irin na jarirai.
Jikina ya dauki rawa sosai yaron da uwar tafiya kusan a tare suka fito lokaci guda sai jikinta yasake rikon da tai min ta sassauta tana fadin Allah nagode ma Allah nagode ma.
Jikina sai rawa yakeyi wa zan kama ne uwar ko yar zan kama ban bi ta kan yaron dake ta ihu ba akasa ita na rike da kyau na jinginata da abin wanka, tare da gyara mata zama.
Sannan na koma daki da sauri na jawo zanin data cire na dora yaron sama ina faman yi mata sannu sannu anty.
Nace bari na kira mama falo kai ta gyada min inajin wayan ta dake saman gado yana ta faman ringing a lokacin ban bi ta kanshi ba na fice daga dakin.
Mama dake zaune ita kadai tana magana da tv nace a razane mama kizo anty ta haihu .
Wani kallo ne ta watso min tace ke kan akwaiki da shirmay wallahi wazaki ruda ana zaune kalau .
Nace wallahi mama ba wasa nakeyi ba na juya da sauri na koma dakin inda take har lokacin tana zaune yadda na barta bata motsa ba ta kurawa yaron dake ta kuka ido.
Mama tunda ta sayo kai a dakin kukan yaron ya tare ta tace ikon Allah ashe yar nan da gaske kikeyi Allah mungode ma.
Cikin kidima nace mama a kama yaron sai ni na gyara anty ta fito ko duk mama ta rude tana cewa ni mai ma nasan zanyi.
Na tuna da Inna ta ta haihu reza akace na aheka na sayo shagon uguwar mu take nace mama akawo reza ne tace yauwa keda wallahi duk ma na rude wallahi.
Inda take aje reza na dauko sabon reza na kawo mata da sauri tai yadda akeyi ta yanke cibin yaron.
Tayo waje dashi sai lokacin na dabaran kama anty na sake ruwan zafi da dama already akwai shi a tank da taimakona ta gyara jikinta nakamata zuwa cikin daki.
Nakoma na tsabtace ba dakin da kyau tare da zuba kayan kamshi ko ina sannan na fita da sauri na dauko wani katon roba a store din mu na wanke na dawo dashi dakin.
Nace wa mama ta shiga bari na dauko masu abin zama ta zauna akai komai sai dana tanadar mata shi a gurin.
Nace mama na tuna ranan na sayo bakin sabulu da majigi da sauri na dauko inda na aje don wanan ranan.
Saboda a training center an fada muna anfi son da an haifi yaro ai mai wanka da bakin sabulu da majigi shiyasa da naga mai sayarwa na sayo mata shi gashi ko yayi rana yau.
Na koma furin anty na bata kaya ta saka takoma saman gadon da na gyara da yamma ta kwanta a hankali.
Gurin mama na koma ina kallon yadda take wanke yaron ina zuba mata ruwa tana darza mai sabulun sallo da majigi a jikin shi tana wanke mai daudan ciki dayazo dashi har tagama na koma da sauri inda anty ta aje kayan baby na dauko showel a cikin su.
Wayan anty dake ta ringing yasa na bar mama ta karasa abinda takeyi wa yaron a lokacin .
Daddy ne ke ta kiranta ashe har four miscalled yai mata ba, a daga ba jin an daga wayan yafara cewa heart beat ina kika shiga waya nata kuka haka baki daga ba ?
Nace a sanyaye Daddy ba anty bace ga anty nan ta haihu ne a razane naji yace da karfi what ?
Ta haihufa ki kace ?
Nace eh daddy ta haihu.
Kuna asibiti ke nan yanzu ?
A, a daddy muna gida a gida ne ta haihu ai.
Innalillahi naji ya ambata da karfi, yace tana ina yanzu bata wayan naji nace rana kwance tukun bazata iya waya ba tace.
Yace subbahanallahi kina jina ina mama nace gata nan tana wa baby wanka ne amma tagama zata fito.
Yace ok yanzu nasan an rufe gida kada ki kwanta bari na buga waya yanzu za, azo a duba su don haka kije ki bude gida kafin maishi yazo.
Nace to daddy yasake cewa lafiya da ita antyn naki take dai ko ?
Nace to daddy lafiya ke nan amma dazun dai kafinta haihu bata jin dadi yace bari na turo yanzu a dubata dai ya kashe wayan na jira mama tazo na bata kayan shafan yaro da sauran abubuwa na fita daga dakin zuwa bude gidan.
Na dan jima a gurin kafin mutumin da daddy yace zaizo din yazo tare muka shiga naga yar aikin Zulfa a tsaye tana kallon mu har muka shige ciki.
Nai mai iso har dakin ya shigo inda take likitane ya gaida mama dake zaune ishishire a kasa tana shafawa yaron man Alaiyadi da hulba a jikin shi yana kuka.
Yace tare da kallon inda anty take kwance yace madam yaya akayi haka kuma mu dake expecting din kizo asibiti kika haihu a gida kuma ?
Murmushi tayi mashi yai mata yan tambayoyi tare da duba idonta har harshenta saida yace ta bude baki ya gani.
Ta bude ya duba yana cewa ok da sauki sosai sai dai yanzu bari ai maki allurai mu gani zuwa safe idan Allah ya kaimu.
Nan dai yai mata allurai tare da bata yan maganunuwa na sha yai muna sai da safe nabi bayan shi na rufe part din mu.
Na dawo nabata maganin da aka bata tasha takoma ta kwanta na gyara rufa mata jikin ta da kyau.
Nan mama ta bani yaron ta koma bandaki don ta gyara uwar tafiyan dake cikin wani leda aje.
Yaron na kurawa ido duk da jariri ne amma uban shi ne sak wallahi yai matukar kama dashi sosai.
Can gefen uwan na shimfide shi a hankali na koma na dan kara gyara kayan da ke baje da akai amfani dasu.
Sai lokacin na tuna dasu Amira na fita zuwa na leka su a dakin mu inda muke kwana tare dasu.
Suna kwance suna barcin su hankali kwance sai suka bani tausayi ga uwar su a cikin wani hali amma kurciya bai sa su sani ba su.
Da ace wani abu ya samayta ne yanzu bazasu sani ba suna barcin su hankalinsu a kwance abinsu.
Na rufo kofan na dawo dakin anty na samu ta samu barci sosai na kura mata ido tare da hamdala ga ubangiji.
Juyawa nayi zan fita mama tace dani amma anan zaki kwanta ko Rahama ?
Nace wani abin ne kuma mama tace cikin damuwa a fuskan ta tau wai dare ko ni yanzu ma ai kin fini karfin hali wallahi.
Nai dariya nace kai wallahi mama tace ai gaskiya ne keda har karban haihuwa kin iya haka ai kin fi gaban mamaki.
Nace mama daurowa ne fa amma ni ina na taba karban haihuwa a rayuwana.
Tace zaman ki gidan garbati ai yasaka maki halin manya kin koyo zama cikin manyan mata.
Ranan nan na kwana a dakin tare dasu mama na barcinta sai nice ke fama da yaron da yaki barci yana kuka da tandan baki.

********* ********* *********
Babu ko sallama suka ganta ta fado masu gida duk ta jemay tayi baki kamar ba Lawisa ba uwar tsiwa da miskilanci.
Daga mama har su Rukaiyya sai tabayanta sukeyi ko lafiya amma ta kasa basu amsa.
Gurin da mama ke aje abinci ta nufa tafara bude kwanukan abinci nan taga wani busasshen tuwo da miyan dayai sanyi na kuka ta hauci kamar mayunwaci.
Rukaiyya na ganin haka ta dauko mata sauran kunun da suka rage ta surka mata da ruwa taba tasha sai da tai kat da ita.
Sai bayan tagama ne take labarta masu abinda yafaru da ita a gidan da kishiyar ta.
Aiko mama ta hau fada da zage zage tana fadin babu inda zata koma akashe mata ya da yunwa da duka haka.
Da wani ake son mutum yaji ga yunwa ga duka kuma kamar nakai masu jaka a gida don kishin tsiya har dadin may sukaji ne wai.
Budan bakin Lawisa da asiri ke aikin a kanta sai cewa tayi a, a mama tunda na samu abinda naci bari kawai na koma ai zamuyi daidai dasu.
Ko yanzu don naga zan kwana da yunwane yasa na zo nan don na samu abinda naci kawai.
Salati suka saka mama baki bude take cewa Lawisa kima da hankali kuwa ai maki wanan tsinanen duka haka kice kuma zaki koma gidan tun baizo ba anji ba, asi ai mashi kaahedi akai.
Ta sake cewa a, a mama bari dai na koma dakina taimako guda zakiyi min shi a dan dinga kai min dan abinda zanci kawai.
Rukaiyya tace Lawisa yaushe kika koma hakane kardai kice min son Jatau kikeyi wai ?
Tace kada naso shi ba mijina bane nidai ku bari na koma dakina kawai tunda na koshi.
Suna kallo ta mike tsaye tana gyara wuyan hijjabinta tare da kokarin ficewa daga dakin tana masu saida safe.
Kallon mamaki tabarsu suna mata tafice da sauri daga gidan tabarsu man a cikin mamakin ta.
Mama anya kan Lawisa daya kuwa uwar tace nima dai shinagani wallahi yarinyar takoma kamar wata zautatta da ita haka.
Akwai dai inji mama don Jatau mugun mutum ne tsafi da sheri ba wanda bai iyaba indai jatau ne a garin nan.
Inko har wani abin ne yai mata zamu hade dashi wallahi don ba yarda zanyi ba gaskiya a illanta mi ua ina gani haka.
Tafiya take da sauri takoma dakinta donji take dan zaman da tayi a gida kamar ana tsakaranta tabar gidan ne.
Tana zuwa ta samu Jatau a tsakar gida yana ma matan shi tujara kan an wullakanta mai abincin da yai wahalan kawowa.
Sai ga lawisa tashigo ko sallama babu hanne tabita da kallon mamaki tana cewa au mara mutunci dawowa gidan kikayi har muna murnan bako ya tafi ashe bakona kofan gida.
Lawisa tace ban tafi ba yar bakin ciki nadawo babu inda zani kuma sai dai ki mutu zamana da Jatau a gidan nan daram wallahi.
Murmushin mugunta yayi yasan aikin daya shukane ke aiki a kanta inba haka ba yasan mama ba zata kyaleta ba ta dawo gidan haka kai tsaye sai anyi fitina.
Ta shige dakinta yabi ta daidai tana cire hijjabin dake a kanta yace yanzu yarinyar abincin da nakawo ne kukai wa wullakanci haka ?
Tacs o kai abinci ne gaban ka ba dukan da aka taru uwa da diyan ta.
Yace aike kika ja may yakaiki zubar mata da girkin ta da tayi don baki da mutunci na sani.
Lawisa tace ko gobe sukace baza, zasu banj abinci naci na koshi ba haka zan masu wallahi.
Nan dai yai ta masifan shi bata kula shiba sai shirin kwanciyan ta takeyi ita.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, ,

IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA AMANA AKANKI YAR UWA DON KIN CI AMANAN NA, , , ,
20

Mu kan bayan fitan shi muka barbaje kayan bukin mu nan muka shiga ci bayan na cire wa Anty da mama nasu.
Zaune muke a tangamaymay falon anty muma kallo tunda ranan ba karatun addini sai ga hindatu buguja buguja tana zuwa tai tsaye kerere a kofan falon tana cewa Sa,ade man yana kiranki a falo, daga haka tajuya ta wuce .
Anty dake zaune a kasa tana kallo tai tsaki tare da cewa Allah yasa dai lafiya wanan kira da dare haka.
Da kyat ta mike zuwa falo inda suke a zaune su biyun har sun hallara a falon kowan su na zaune tana jin iko da mulki tare da ita fuskan ko wace na fuskan wani gurin sai dan jijiga kafan da sukeyi.
Da sallama a bakinta ta shigo falon tana saye cikin katon hijjab da ya rufe mata jikinra lif har kasa.
Babu wanda ya amsa mata sallaman nata sai shi maigidan da ya dan dago kai ga abinda yakeyi ya amsa mata.
Sai ta samu guri saman daya daga cikin kujerun ta zauna a kai tana sauraren shi.
Bayan kamar minti uku da shigowan ta gurin na tsit babu wanda yai magana a cikin su sai zuwa can ya dan dago kai tare da barin abinda yake yi yana cewa uhumm kun shigo ko ?
Yace bissimillah Zulfau ina son ki fada min abinda kika kirani ga waya dazun kina fada min cikin hasala don ban fahince ki ba a lokacin .
Wani dan harare harare take yi tana kada kafa cikin hasala yace sai kin fadi abinda kikace dazun a cikin waya .
Shiru tayi bata da niyan yin magana ya sake harzuka yana cewa a hasale, sai kin fada min abinda wani ya tsare maki a gidan nan ko abinda kike ganin nai wa wani banyi maki ba ke ?
Tace ni ba ai min komai ba kawai dai yadda kai min cin fuska dan ka dauko yar aikin Saade a gaban motar ka ka share ni cikin mutane haka kamar wata mara daraja dani.
Ke may yasa da kika ganni baki taso ba zuwa inda nake koni kike son cikin mutane na nuna masu kin fi karfi na a gida.
To tunda naga bakya son zancen a yanzu na yi shiru zan bar shi idan halinki ne zaki koma ai.
Wanan yarinya ai samun gurin ta yayi yawa a gidan nan don tana takama a gurin matar gida take zaune muko su agola ne

Download complete TXT · Novel page