About this Novel

 

Story Preview

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM GODIYA YA TABBATA GA ALLAH DA YA BANI IKON FARA WANAN NOVEL DIN A CIKIN KOSHIN LAFIYA YADDA MUKA FARA SHI LAFIYA UBANGIJI YA BAMU IKON GAMAWA LAFIYA.

DA FATAN SAKON DAKE CIKINSA ZAI ISA GA INDA YA KE BUKATAN ZUWA GURIN MATA YAN UWANA ALLAH UBANGIJI YASA MU ANFANA DASHI

WANAN PAGE DIN FREE PAGE NE DAGA SHIMFIDAR LABARIN MAI SO ZATA IYA TUNTUBANA DON YIN REGISTER SHIGA GROUP DIN

NAGODE TAKU HAR KULLUN ZAINABUN KU


Hasken farin watan daya haski taurarin da suka zagaye shi masu fitar da kyalli daga ganin su,
Wanda hakan yasa sun kayata gari matuka hadi da sanya zukatan bayin Allah a nishadi
Wanda mafi yawan zukata mutane musan man na kauye inda babu wutan lantarki a garesu cikin jin dadi da walwala.
Ga iska mai dadi da yake dan kadawa lokaci lokaci gami da kamshin kasa dake tashi gwanin dadin shaka.
Ga yara dake jin dadin yanayi duk da dare yayi amma suna waje suna wasan su don babu duhu da zai sa ashige gida a lokacin
Tafe take da sauri iskana dan kada ta hannuta rike da farar roba mai marfi da ta dauko nikan awara da zasu soya da safe kafin ta tafi makarantan boko.
Tafe take cike da nishadi a zuciyar ta wanda yanayin yake saka ta jin dadi har tana lumshe idunuwan ta.
Tana tafe cikin sauri bata da wani guri daya wuce taga ta isa gida ta tatace markaden wanken da ta dauko daga gurin nika.
Wasu mutane ne zaune wanda magidanta ne dabian su shine duk dare a shimfida katon tabar kofan wani gida su dinga yan ciye ciye kafin su shiga gida gurin iyalinsu da aka bari da tuwo da miyar kuka bakifi ko nama a cikin

Continue reading →

Reader Reviews

Login to leave a review.

No reviews yet — be the first.

Hausa Authors Forum

More Novels You May Like