Murucin Kan Dutse

Chapter 7 of 146

ba da kikeyi yanzu.
Nan dai nai ta bata hakkuri har na samu ta sauko naga ta dan sake jikin ta muryan mama ce ke cewa ina mai sharan nan take ne kin bar shara iska zai kwashe.
Sai ji nayi Inna na fadi aiki take min a daki a sa wasu su share ba ita kadai bace ai a gidan.
Nace a raina taufa ance mai hakkuri dama bai iya fushi ba mama zata kai inna ga bango ke nan.
Muna nan zaune wani dabara ya fado min a raina na saurin daukan hijjab dina nace wa Inna ta ina zuwa na fice daga gidan.
Kofan gida na koma na tsaya ban dade ba naga baba ya fito gaidashi nayi yana kallona yace Rahama may kike a wanan gurin da sanyin safiyan nan haka ?
Nace baba kai nake dako kafito akwai maganan da nake son muyi dakai ne.
Kallon mamaki ne yai min nakai durkushe a gaban shi nace don Allah baba alfarma nake nemawa inna ta akan zaman su da mama a gidan nan.
Duk zaman da suke na kishi a tsakanin su baba ba wai lalai bane sai ka saka bakin ka a ciki tunda kai ba mazauni gida bane baka san waina da ake toyawa ba a bayan fitan ka.
Kallona yake cikin mamaki yace Rahama har ankai lokacin da za ki tari gabana akan maganan uwayen ki.
Nai saurin cewa baba ba hakana bane yaune naga inna har ta shirya wai zata bar gidan bata iyawa ta gaji da abinda ake mata shine nace bari nai magana.
Yanzun haka wallahi inna batasan zan yi wanan maganan da kai ba ma hakkuri dai nake baka baba ko dan darajan mu a tsakanin ku ka rangwanta ma rayuwan ta hakana.
Shiru yayi kamar mai nazarina can yace naji amma ita Asiya ne yau har tai niyar yaji ?
Nace kwarai kuwa baba Allah ya gyara ni kadaine a waje na tare ta data fice daga gidan.
Yace to jeki naji Allah yai maki albarka idan nadawo zanga ita innar taki zamuyi magana da ita na fahinta nace baba nagode Allah ya kara rufa asiri.
Ya wuce na juya na shiga gida zuciyana fes na san ko ba komai killa Allah ya kusa kawo muna saukin al, amarin mu ne a gidan.

****** ********* ******
Tun daga wanan lokacin da mukai magana da babana ta fahinta naga al, amura sunyi wa inna sauki sosai ba inna kawai ba har ma diyan ta da akewa kahonzuka a gidan mun dan samu saida sosai.
Ya zuwa yanzu ba karamin alheri Garbati yake kawowa ba gidan mu wani naci wani kuma dangin tufafi ne duk ba, a tabawa sai gurin mama altine ake boyewa.
Cikin hakane na roke shi yai hakkuri har na zana jerabawa na na karshe kafin ayi bukina dashi.
Da kyat na samu ya amince min wanda zuwa lokacin har labarin zancen aure na dashi yabi gari wanda mama ce da diyan ta suke yada zancen a gari.
Don mama har iyalin shi sai da ta fada masu irin alherin da yake kawo muna gidan mu .
Wai yanzu duk neman shi a kaina yake karewa komai kawo muna yake dani da uwata idan anga yadda muka koma wasu bulbul damu don mun samu ya rike muna kan maciji muna wasa da bindin shi.
Haka yasa matan shi suka tayar da hankalin su su basu yarda ba ya dauko masu yar jikan su a matsayin kishiyar su mafarin nazo ina masu rashin kunya a cikin gida.
Yace shi ra, ayin shi ke nan mai zama ta zauna wacce bata iyawa hanya a bude yake mata.
GNin da gaske yakeyi yasa suka kama kan su bayan ya saka masu waigi ga zancen da cewa.
Kada yaji wani ko wata yaiwa yarinyar nan ko iyayyen ta wani sheri zai dauki mumunan mataki akan ko waye a gidan.
Dole suka saka mai ido ba yadda zasuyi namiji idan yaso abu kunya fice mai yake a idon shi.

Mama altine ta tafi birni ganin anty da tadawo daga waje ganin likita akan matsalan ciwon ta.
Sai washe gari bayan ta huta anty ke tambayan ta wai mama ina Rama na take tana nan tana karatun ko ?
Mama tace wani karatu Sa, ade Raman ki kan aure zatayi bada dadewan nan ba.
Haba mama wani aure yarinya kamar Rama kuma ?
To ai sai kiyi Rahama kan har an kawo sadakin ta itace ma ta hudu a gidan mijin ta.
Anty dake kwance tace what ?
Mama wai da gake kike ko wasa tace ina wasa dake ne balle na fada maki wasa.
Uban ta yaba da ita ga wani tsohon maikudi na garin mu aure yanzu haka karatun data kwallafawa raine ya hana ayi bukin kin san ta samu sa, a don kokarin ta an kaita gaba yanzu bana zata fita daga makarantan ma.
Ran anty yai matukar baci dajin wanan labarin da tayi na zancen aure na nan dai mama ta koro mata komai akan zancen.
Na bata matukar tausayi tace mama in ba abin kauye ba ko mu da mukai aure da girman mu yaya muka kwashe da kaidin kishiya balle yarinya karama akaita cikin guzamay mata haka ?
Mama tace mu a kauye ai hakan ba komai bane gare mu amma duk da haka Rahama tayi kankanta kwarai agidan nan.
Da mama zata dawo sakon zannuwan gado da sauran kayan aiki dasu kudi anty ta bayar akawo na shagalin buki na wanda baifi wata biyu ba ayi yanzu.
Harda yan din kuna kala biyar da sauran abubuwa duk ta hado min tace aba Inna hakkuri saboda jikin ta bata samun zuwa bukin .
Amma idan ta samu lafiya zata zo taga dakina daga baya insha Allahu.
Mama tace kice wanan tafiyan na Rahama ne nayi ai taso ta biyoni sosai amma nasan mahaifinta ba zai yarda ba shiyasa na bata hakkuri.
Da mama ta dawo daga birni sai washe gari muka shiga taron ta don da dare ta iso garin.
Ai nan ta baje muna sakon anty na muna kallo wani abin ma ni ban san yadda za, ai amfani dashi ba agidan.
Ban san lokacin da na dunkule na fara kuka ba da kyat mama ta lalashe ni na wanke fuska na.
Sai da naje gida nake labartawa Inna ta abinda ya faru ta rike baki cikin mamaki tana cewa kai wanan boyar Allah ni ban san abinda zan saka mata dashi ba a duniyan nan ?
Mama ko sai gori take sake muna da habaici wai rana bata karya sai dai uwar diya tai kunya.
Daga uwar har uban sai kudi ake ci amma ko roba ba asai wa yarinya ba na aure .
Su dai gasu gani wai an bizzine tsohuwa da ranta suga yadda za afita kunya duk tallan da nayi Inna ta kasa saye min wani abin kwarai.
Dama tayi haka ne don ta kure inna don tasan ba, a aje min komai na aure ba a yanzu tunda mun sakakance cewa ni
boko zanyi ba aure ba yanzu.
To yanzu ga aure ya taso suga ta tsiya tasan dai gidan su Inna ba wata tsiya zasu barkata min ba don suma nema sukeyi.
Magana duk yabi gari inna bata aje min komai ba ga aure ya taso ba abin kaiwa gidan miji.
Lokaci ko kamar jira yake sai kara matsowa yake niko sai karatun jerabawa na dake gabana nakeyi kawai.
Ba abinda yai min tsinanen zafi akan maganan mama da diyan ta a gidan mu.
Garbati yasa aka gina min daki mai girma da fadi yadda zai isheni aka kewaye shiyan daban cikin na iyalin shi can gefe daya an shafa farar kasa yaji sai kyali yakeyi.
Haka ya kara bankantawa iyalin shi rai sosai har suka so tayar da hankalin su.
Amma da ya basu dan wani abu suma suyi gyara sai baki ya mutu murus kowa ta shiga sha, anin gaban ta da diyan ta amma kishin yana nan daram a ran su.
Duk inda yabi sai ba, a ake mai na ya fado gari ya zarta maza zai bare yarinyar dalleliya a ledan ta sai ya washe baki cikin jin dadi yana dariya.
Mama ko sai auki fadawa mutane karya da gaskiya takeyi akan zancen bukin tana zunden inna ta.
Inna ta duk tabi ta ramay sai dan wuya daga ita sai uwar dakin ta mama altine suke shirin bukin sai yan uwan su tsiraru da sukaji suka gani.
Ko su ba wai sun san shirin da Inna da mama altine sukayi min bane haka ake tafiyan a dunkule.
Gaba daya daga inna har baba babu wani mai kwanciyan hankali dama ma inna dake nuna halin ko in kula da bukin.
Idan ka cire mama da yaran ta wanda su ko a kwalar rigan su bai shafe su ba.
Ta dai zuga shi ya zugu yanzu kuma ta saka mai ido yaji kunya dan kudin sadakina da aka kawo dashi ne yake kokarin sayen komai.
Na dan gadon katakon da za, a sai min ma ya gagara daga karshe ganin haka tasa inna dabaran cewa yaba mama altine kudin ta shiga birni ko na hannu ne ta sayo min.
Tayi hakane don idan kudin ya shiga hannun su sai su san dabara mama altine ne ce ta koya mata wannan dabaran.
Baiki shawaran Inna ba tamika masu dan abinda ya saura takaiwa mama altine ta shirya sai birni da kudin daga karshe anty ce ta cika aka sayi min saitin gado da dan wardrove da katifa har da karin tarkace.
Wanan matar ba abinda zamuce mata sai dai Allah ya bata lafiya ya shirya mata zurian ta da albarkan sa kawai.
Ganin babu komai a dakin inna ta yasa mama ta samu baba da zancen da yamma bayan ya dawo gida take cewa.
Yanzu malam kana ganin haka zaku kai yarinyar na aure babban gida irin haka babu komai da uwarta ta tana da mata na fita kunya kaima sai nake ganin a furin ka hakan ne ?
Baba da yanzu ya fahinci mama so take taga wallen shi kuma tasan sirin abin sai ya boye mata ba su mama kudin sadakin da yayi yace anyi auren ne ko kikaga uwarta ta kaita hakana ?
Haka yasa taji haushi taja bakin ta ta tsuke ta bar zancen sai ido tana cewa ni dama taimakon ku naso nayi ko mu tafi gida tumba dillaliya adan samu abinda aka tsintar mata gurin ta in yaso bayan bukin abinda aka samu sai abata kudin ta.
Baba yace ko tabarma Allah ya hore mata daga gare ni sai na kaita dashi .
Yafice abin shi gidan ya barta nan tana mashi dariyar mumuke ta baya tana an daiji kunya wallahi anyi shigewa ai ciki amma ba, a iya fitar da yarinya kunya.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE NA FADA IDAN BAKI BIYA BA KIKA KARANTA MIN NOVEL NA BARKI GA ALLAH.

IDAN KIN BIYA KIKA TURA MIN NOVEL WANI GROUP KO KIKA BA WA WANDA BAI BIYA BA KE MA NA BARKI GA ALLAH DON KINCI AMANATA ALLAH ZAI SAKA MIN A KAN INSHA ALLAHU WACE TASAN BAZATA IYA RIKE AMANA BA DON ALLAH TAI MAGANA NA BATA KUDIN TA TAFITA MIN GROUP DON AMANA NAUYI GARE SHI ABINDA KA RAINA SAI YA HANAKA KETARE SIRADI GOBE KIYAMA ALLAH YA BAMU IKON RIKON AMANA A TSAKANIN MU.
DON NAGA NOVEL DINA A WANI GROUP KUMA NASAN WACE TA FITAR DON BATAI MAGANA BA NA BARTA GA ALLAH DON ALLAH SHEDA NE GA ALKAWARIN MU DA KU, ,

6
Ranan da na zana jerabawan karshe na na secondarya rana ce da ya kamata nai mafarin ciki a raina don kowa ka gani a cikin mu yana cikin farin ciki da jin dadi a ran shi.
Sai dai ni a gareni sabanin hakane don ya kasance min kamar rana na bakin ciki a gare ni.
Lokaci daya yanayi na ya sauya min naji duniya tai min kunci a raina komai ganin sa nake yai min baki a raina a dalilin tunawan da nayi wanan jin dadin rayuwan ya kusa yanke min.
Don wanan auren jarabtan da na tsinci rayuwana dashi na auren tsoho da mahaifina zai min a lokaci daya haka, batare da yai la, akari da irin rayuwan da zanje gidan miji na tarar.
Wanda yau baifi saura kwana goma ba naje gidan Alhaji garbati a matsayin matar auren shi nima a gidan.
Juyawa nayi zuwa staff room don nai sallama da malam mutumin da yai tsaye a kaina har nakai wanan matsayin na yau a gare ni.
Malam yana ganina yace a, a Rahama an kanmala ko ?
Maimakon na nuna farin ciki na sai na kai durkushe a gaban shi na fara kuka yace subbahanallahi Rahama lafiya dai ko ?
Cikin kuka nafara cewa malam nazo ne nai maku godiya akan tsaya min da kukayi har na kai ga wanan ranan ga karatuna.
Sai dai kuma gashi guri na ba zai kai na zama likitan da nake son zama ba na taimakawa yan garin mu kamar yadda nake da gurin haka a rayuwana.
Mahaifina ya yanke min wanan gurin nawa ta bayar dani aure ga wanda yaso yau saura kwana goma ayi bikina akaini.
Subbahanallahi inji malam yace yaushe haka ya faru kuma Rahama waye kuma miji ?
Sai na dan kakaro murmushi a fuskana nakw cewa malam an kwana biyu da hakan ba kuma kowa bane mijin sai Alhaji Garbati dan bida na garin nan.
Shi da sauran malamai da suke saurare na cikin tausayi sukace garbati dai garbati wanan tsohon mutumin da muka sani ?
Nace shi malam ,
Malamai suka ce kai amma mahaifin ki ya cuce rayuwan ki Rahama ga wanan tsohonbzai bada ke dan kwadayi ko don may ?
A hankali nace nima ban sani ba malam na mike ina masu godiya na ke masu sallama na tafi,
Nan na barsu da mamaki kowa na fadin albarkacin bakin shi a kaina na nufi gida.
Na shiga gida da sallama na na gaida da su mama da na samu tana raba abinci a tsakar gida.
Nan na shige dakin inna na kwabe uniform din jikina fita nayi na debi ruwa don na watsa naji dadi jikina.
Mama ta bini da harara wai dan ruwan da zasuyi aiki dashine kuma zan kwashe nai wanka don ni nafi kowa tsabta ko may ?
Ina ban daki na fara watsa ruwa ne naji mama tana rafka salati haka yasa nasan ba lafiya ba ke nan.
Nai saurin watsa sauran ruwan a jikina na fito da sauri nan na samay su tsaye cirko cirko sai fada mama takeyi ita kadai Inna ta tana tsaye a bakin kofan ta itama fuskan ta a cikin damuwa yake.
Na karaso inda take ina fadin Inna lafiya ko may ya faru kuma ?
Kafin mama ta bani amsa take cewa dani wai angon ki ne ba lafiya gashi can an kwashe shi zuwa asibitin birni yanzu.
Gabana ne naji ya yanke ya fadi min ras ras nace shi Alhaji garbatin ne da kan shi baida lafiya ?
Mama tace idan bashi ba da uban ki ko bakiji may nace bane ni.
Allah ya sauwa nace na watsa ruwa a kafana dana rage a sauran roban da na fito dashi ban daki da nai wanka.
Nashige dakin mu kawai na fara sallah bayan na idar ina jin mama tana karasa aikin ta sai faman mita takeyi akan zancen ita kadai a tsakar gida.
Na juya inda inna take zaune cikin damuwa nace inna may ya samay shi ne ?
Take cewa dani yanzu nima nake jin zancen a gurin yaya wai ya kwana biyu yana irin wanan ciwon dama.
Allah ya sauwaka nace, naci gaba da kwalliya na ba abinda ya damu raina ko kadan.
Sai bayan dawowan babane muka samu labari wai ashe ya kwana biyu yana irin wanan lalurar .
Fitsari ne ke mai wahalan fita idan zaiyi sai kuma yanzu da suka tafi asibiti ake cewa harda hawan jini yana da shi.
Mama sai cewa tayi Allah ya cece mu ga farar kafa mu kan ?
Kamar yaya farar kafa kuma baba ya tambaye ta hakanan ?
Tace to yau saura sati a saka lalle haka ya kasance dashi ai sai ace yar mu ce zata shiga da farar kafa gidan shi .
Ki kadai fadi yanzu inji baba lalurar da kowa yasan ashe yana dashi dama shine zaki fadi haka ?
Tace ai idan ni ban fada ba iyalinshi su fada tunda koda yake dashi duniya basu sani ba sai yanzu .
Lauratu wai may yasa baki son a zauna lafiya ne ke duk abinda zai kawo fitina a tsakani kin san yadda zaki jawo shi.
Idan da yar cikin ki ce za, a kai gidan ai baza, ki fadi haka ba akan ta.
Allah ma ya tsare ya ta da wanan rayuwan gaskiya ne baka son a fadi kuma in ni ban fada ba duniya zasu fada ai.
Baba yace yanzu na gane may kike nufi akan yarinyar nan mutane suna fada min ban yarda ba amma yau na yarda da hakan.
Nan dai suka fara halin nasu na sa in sa a tsakanin su wanda ba mai shiga don ko mutum ya shiga sai yai kunya don ajima kadan zakaga sun shirya ne.
Bayan an sallamo Alhaji garbati ne daga asibiti ya turo kiran babana yana son magana dashi.
Baba baiyi nauyin kafa ba ya tafi amsa kiran da Alhaji Garbati yake mai a kofan gidan shi inda akai mai shimfida mutane suna zuwa gaida shi da jiki baba ya samay shi.
Bayan sun gaisa yai mashi yaya jikin shi da sauran iyalin shi ?
Ya bukaci da sauran mutanen dake gurin yana son ganawa da babana akan wani magana sun san alakal dake a tsakanin su don haka suka basu guri.
Alhaji garbati ya sake gaida babana yake cewa ya aika a kira shi ne don su yi magana akan

Download complete TXT · Novel page