Murucin Kan Dutse

Chapter 85 of 146

na samay ta muka gaisa na tambaye ta duk mutanen gida tace suna lafiya Rukaiyya ma ta haihu na biyu.
Naji dadi sosai muna cikin hira jinior na kwance a jikina yana wasan shi Nasir na gefe na a kwance sai ga uwar ta fito daga dakin ta.
Na gaida ita irin yadda ta karba min yasa mama ta kalle ni yaran ta kalla tace dasu ban hanaku zama jikin mutum ba ashe ?
Cikin rashin sanin may ke wakana mama tace cikin dariya kai amma Saade akwaiki da wani magana kuma .
Rahama da yaran nan ai sai Allah shifa yaro kamar dabba yake inda yaga ido a nan yake ko yaushe, da basu tafi gurin wani sun mamay shi ba fuska suka gani.
Sai cewa anty tayi a, a mama bana son irin haka yanzu kowa ya tsaya matsayin shi yara dai nawa ne aiko ?
Gyara dai zancen ki Saade yara naki ne kin haife su ne kawai amma aida Rahama suka bude idanuwan su ko ?
Kai mama don Allah ki bar wanan zancen idan ta samu nata zata bude ido da su ai.
Ikon Allah inji mama Altine tace kanki daya kuwa yau Saade nifa tun zuwa na naga canji sosai a yanayin ki.
Muna murnan kin samu lafiya kuma sai sabon yanayi ya shigo gaskiya banji dadin jin wanan zancen ba dakika yi yanzu.
Ina yarinyar nan tun bata san duniya ba Allah ya hada ku tare har talai kin sadaukar da sonta a kan ki.
Anty tace ada ke nan mama ni yanzu ai an shani na warke ko na fahinci waye dan adam ka gan shi a rana kakai shi innuwa yanzu ba may kara yaudara na kuma.
To Allah ya kyauta da magana ke nan a gidan naku don naga alaman haka tun zuwa ban ga Gajiye a nan ba tun da tazo taimin sannu da zuwa sai wanan bakar matan nake gani tundazu gata bata da ko marmari kamar muguwa.
Mikewa nayi nace mama a huta gajiya zan koma sai da safe ina mikewa yaran ma suka mike wai zasu bini amma fafir uwar ta rufe ido ta hana su a gaban mama dani.
Bayan fita na mama take mata magana take cewa haba Saade ban san ki da wanan mugun rayuwan ba.
Tace mama ai dole ne ya kawo hakan nan dai takawo wa mama dalilin ta mama dai tana sauraren ta har ta gama maganan ta.
Tace amma kinyi kuskure wallahi Saade yau ina kwakwalwanki ya shiga da tunanen ki da har kike wa yarinyar da kika raina da hannun ki kika bata tarbiyan da kike so tayi koda a bayan ranki ne ?
Wanan bakin tuhumar da zargi ai wahalal da kanki kikeyi da zubarwa kanki daraja a gun yar kankanuwar yarinyar da take jin ki fiye da kowa a duniya.
Dake nan mama yanzu ai Rama ta wuce sani na don ta samu wanda suka fini ke kike daukan ta a yarinya mama.
Yarinya ce zatai kokatin rabani da mijina ta na kokarin ganin sai na koma baya gun mijina daga taimako sai abu ya koma tsiya kuma ?
Eh lalai kin ko samu matsala babba don dai ni ko ga wani ban taba tunanen haka ba a gareki balle wanan yarinyar Rahama.
Duk yadda mama taso ta kwantar mata da hankali anty taku fahinta hakan sai dai ta nuna mata bacin ran yadda take saka har da yara a cikin kishin mu .
Ganin bata da niyar yarda yasa mama tace da safe zata bar gidan idan Allah ya kaimu don bazata zauna tana ganin wanan irin cin fuskan ba haka da anty ke min.
Daddy ya shigo gaida mama ya samu mama na fada da anty din, yake cewa mama gaya mata dai na rasa inda halin Saade ya boye har ta amince wanan yarinyar ta kai ta ga wanan zubar da mutunci.
Da sauri anty ta dakatar dashi tace kaga idan zakai maganan ka kayi amma ka daina sako Falmata a zancen ka kadai hanata shigo maka gida kan matarka ko kuma ta bari ba sai ka barta hakana ba.
Nan suka fara sa insa a gaban mama din dashi hankalin mama yai matukar tashi tana jin yadda anty ke mugun aiban ta ni abin ba dadi ko kadan.
Da kyat anty ta samu ta sashi ya fita tun fitan shi bara sake magana da anty ba ta mike zuwa dakin da take sauka a ciki.
Ina shiga daki na kuka na zauna nayi sai da na gaji na share hawaye na ni kadai a dakin don nasan tunda har mama tai magana anty bataji ba abin yayi nisa ke nan.
Tun da safe sai ga mama har part dina inda ta samu na shirya zan fita ina saye da lapcoat a jikina da cup din tea ina dan kurbawa Gajiye da Fatima suna zaune suna kallo don har sun gama duk abinda zasuyi ko.
Muna ganin ta shigo ne duk muka mike muna gaida ita ta zauna sai mukai shiru na dan wani lokaci.
Can ta ambaci sunana tace Rahama abinda nake so dake shine kici gaba da hakkuri don shi ramin karya kurare ne bai dorewa don na fahinci an riga da an zuga Saade don haka ni yanzu sai dai ke da kuke tare a nan na kara baki hakkuri kawai.
Nace mama babu komai dama haka zama ya gada zo mu zauna zo mu saba watarana kai da mai shi.
Tace jiya abinda tayi a gaban minin ku banji dadin shi ba ko kadan ni tsorona kada wanan shuumar ta cuta mata ta inda ba a sani ba.
Gashi ta kawo mata wanan munafukar ta zauna da ita a gidgida Allah kadai yasan irin abinda suke gunguma mata a tsakanin su.
Gajiye tace nima abinda nake tsoro ke nan wallahi amma ita hajiya taki ganewa nace insha Allahu zan saka ido don ni ba zan yarda na biye mata ba haka.
Nan dai mukai sallama da mama din bata kara kwana ba ta bargarin ko anty din ta saduda amma ko a jikin ta don ta shiga tarko ko .

********* ********* *********
Falmata tagama duk shirin da take son yi a kan anty don haka ta shirya fara aiwatar da nufin ta gareta.
Ina dawowa daga school da yamma don yau ban tsaya an karasa dani ba don bana jin dadi tun safe .
A daidai kofan mu naga mai Napep ya sauke yar aikin anty tafito da wani irin katon jarka irin na mangyada ko manja din nan.
Da kyat ta ciciba zuwa cikin gidan ina mamaki ko may ye a cikin jarkan haka ta dauko mai nauyi ta dai shige dashi wurin su kai tsaye.
Ban shiga ba don na rage shiga yanzu sai da dare bayan na gama magariba kafin ishai na dan lekata don jikina ya dan sake min lokacin.
Ina shiga na samu matar ta tsiya wanan abinda ta shigo gidan dashi da yamma ta mikawa anty shi.
Ta amsa zata fara sha na shigo falon nakai kallo na ga abin bakikirin da shi haka ta kurba tana bata fuska na gaida ita naga bata ji dadin shigowa na ba na gan ta a hakan.
Ni dai na gaida ita na juya abina ina mamaki ko may ye wanan abin da anty ke kinkima ma cikin ta oho ?
Muna samun hutu daddy yai tafiya dani sai da mukai wata daya da sati biyu muka dawo nayi kyau sosai gashi da mun dawo bukin Gajiye da Fatima za, ayi shi.
A lokaci duk wanda yasan ciki zai gane ina dauke da ciki a jikina sai dai su matan gidan gaba daya idon su ya rufe basu gane ba.
Sai ranan da mama Laraba ta shigo ta zo akan maganan auren son shi ya kirata tazo maigidan don bai abu har yanzu bada ita ba.
A falin na samay su zaune suna hira na shigo gaida ita tana ganina tace a, a ikon Allah abu ko yayi kyau sosai wallahi ashe na dade rabon da na ganki sarakuwa na ashe abin arziki ya samu haka har ya nuna ban sani ba ?
Da sauri gaba dayan su suka mayar da hankalin su a kaina cikine zaune a jikina kuwa dagwas dashi dan wata shidda da kwana ki har ya dan turo dayake na farko ne a gare ni baiyi wani girma ba sosai.
Gaba daya falon yai shiru na durkusa har kasa ina gaida mama tace a, a haba tashi tashi kina wanan matsayin inake ina durkusa kada ki haiho min da igiya a wuya.
Daddy yai murmushi yace fada mata dai mama don Rama bata jin magana wallahi haka nake fama da ita kan kula da kan ta.
Nai dan murmushi na dago na dan sakar mai harara irin na masoya nace kai daddy duk wanan kokarin da nake kuma sai an kai kara na gun mama kuma ?
Yace wani kokari kin dai ji abinda mama tace don Allah ki kula Rahama ni ina maganin hutu zan daukar maki ki daina shiga asibiti har ki haihu.
Humm, umm inji Hindatu lalai abu yazo ga masuyi ke nan shi cikin ma har wani abin ado ne dashi kuma ashe.
Zulfa tace ai ba ayi ba yanzu za, ayi ashe mugani ashe an samu karuwa ake faman boyon shi gare mu to Allah ya ingata.
Amin inji daddy da mama ni dai kaina yana kasa Anty na daki a nade don jikin ta ya dawo ba dadi yanzu amma haka take nukurkusa dashi.
Daga bakin yar aikin ta da sukai gulma da hanne ta samu labarin cikin jikina sai ga mama kuma da zata tafi ta shigo tana mata murna ashe an samu alheri ne Allah ya raba mu lafiya.
Amin kawai tace wa mama din don jin maganan take kamar zata shude a lokacin ranta ta rasa may ke mata dadi.
Ranan kan gidan kamar an aiki masu da mugin labari ko wani part zancen cikin suke suna mamakin yadda basu gane ba sai da mama tazo sukaji a bakin ta.
Bukin saura sati uku ayi shi jikin anty ya tsanan ta mata ina shiga gaida ita duk da ba fuska a gareta amma haka nake shiga gaida ita na dan zauna na dan lokaci.
Gashi ina son na taimaka mata amma babu daman yin haka a gare ni ganin bata da lafiya yasa mai aikinta yin abinda taga dama sosai ta fito da kalar ta a fili.
Yaran basu da shakat ko su walla su da gidan uban su yakai har ta fara dukan yaran da sun danyi ba daidai ba.
Haka yasa na rufe ido ranan da na samu ta daki Amira uwar na kwance babu daman magana nan na rufe ido nai mata tas nace idan ba zaki iya hakkuri dasu ba sai ki tafi.
Har nagama na zaci anty zatace don may nai mata haka amma sai banji tace dani komai ba naja yaran nai masu wanka nabasu abinci a part dina sukaci sai barci.
Zakaji tana kiran saliha saliha amma sai ta kyale ta hakana har tagaji ta barta tace bata zuwa ita tagaji wallahi.
Haka muka wuce muka barta a cikin matsala muka nufi kauye wurin buki satin mu daya amma ina buga mata waya akai akai naji lafiyan jikin ta.
Na samu na shawo kan mama Altine taje ta duba anty bata ki ba ta shirya muka zo tare yadda muka barta daga ita har yaran mun samu abin ma karuwa yayi sosai.
Sai da nai kuka yadda na samu yaran sun lalace na samo wata yar aiki diyar lami kawar mama altine da Innata.
Gajiye a cikin gidan zata zauna a boys quarters inda akaba su tace basai na dauko mai aiki ba zata kula dani haka na amma dole na nemo wata da zamu zauna dindindin a part din tare dani.
Mama Altine sai kuka take cikin tashin hankali dole aka je asibiti da ita ba laifi ta dan samu sauki kwana biyu.
Yanzu muna dan samun saukin a zaman mu gashi cikina ya gama fitowa fili sosai kowa kuma yasan da akwai shi.
Bayan kaman sati uku har na walwale ga jigilan bukin da nasha ina barci cikin dare naji ana buga kofan mu sosai da karfi.
Na yunkura na tashi da kyat kaina babu ko dan kwali na fito dasauri muka hade da Aisha da na dauko take cewa anty tun dazun ake buga muna kofa da karfi haka.
Sai da na tambaya da waye naji muryan mama Altine ne na bude da sauri nace mama lafiya dai ko ?
Tace ina fa lafiya Rahama jikin antyn naki ne ya tashi wallahi abin ba dadi ita kuma wanan shedaniyar nayi ta da ita tace wai bazata fito ba dare yayi gashi ni kadai ne a shiyan sai ita.
Da sauri na kwasa sai dakin yadda na samu anty zaka dauka ma ta mutu ne wallahi na fashe da kukan tashin hankali sosai.
Na kamo ta ban ko damu da nauyin da nayi ba na fara bata taimakon gagawa wanda ko asibiti muka tafi shi za, a fara bata a can din.
Allah ya taimake ni ta nisa da karfi na rugomay ta ajikina ina wani irin kuka mai tsuma rai sosai.
Can dabara ya fado min nace mama ta miko min wayan anty dake aje gefe na kira maigidan yana ganin kiran karfe biyu da mintuna ya dauka a cikin tashin hankali nake fada mai halinda take ciki.
Ai ko minti biyu bai dauka ba sai gashi dakin yana ganin ta yace yaushe abin yai tsanani haka mama tace wallahi lafiya muka kwanta da ita don har ta sha magananin ta fa kafin mu kwanta din.
Asibiti aka nufa cikin daren nan dole da ita take aka bata gado naso na bisu amma daddy ya rufe idon shi ya hana ni yaran na tayar muka nufi dakin mu da su hakana.
Na rufe dakin anty na wuce da keys din wuri na ranan dai haka gari ya waye muna tunda safe har na shirya da abin karyawa na nufi asibitin da take.
A cikin tashin hankali muka samay su sai bincike ake a kanta daga karshe zuwa karfe daya likitocin suka gano wani magani take sha yai mata wanan illar haka ajikin ta sosai don har ya fara bata mata kayan cikin ta ko.
Maganin da take sha likitoci ke son suyi bincike akai an kwaso sin duba amma duk basu da wani illa sai abin ya daurewa mutane kai sosai.
Can anata magana mama tace akwai wani wanda naga wanan yar aikin natsiyaya mata safe da yamma koshi za, a duba a gani ne.
Cikin mamaki daddy yace wani irin magani ne wanan nace lalai nima naga tana yawan shan shi don nasha ganin ta dashi da dadewa.
Daddu yace a je a dauko tare muka tafi mun samu Saliha tana kwance ta kure volume din tv tana kallon raye raye.
Cikin fada daddy yace what noses is this a gida na wanan abin ke faruwa haka kuma mai shiya na kwance rai a hannun Allah ke kina nan kina holewar ki.
Part din na shiga dubawa inda Allah ya taimakeni na hango jarkan maganin can an boye shi cikin wani lungu na tsiyaya a wani gora Saliha na kallo na zamu fita take cewa dani Rahama bani key din dakin hajiya zan gyara ne.
Nace abar gyaran sai ta dawo ayi amma ba yanzu ba kan muka fice daga gidan da maganin muna hanya daddy sai kallon maganin yake yana mamaki shi.
Yace yaya ma za, ayi mutum mai hankali ya dirkawa cikin shi wanan mugun abin haka ne wai ?
Nace ni kwata kwata ban yarda da wanan maganin ba ma daddy wallahi amma dai bari a bincika a gani kawai.
Sun shiga dashi a cikin dakin bincike mun kuma samu taji dama numfashin ta ya dawo normal yanzu ko.
Nan dai muka zauna likitoci na shigowa duba ta akai akai bayan fitan babban likita ne nace mama kinji waban matar wai na bata dan makulin dakin anty zatai gyara a ciki .
Mama tace injin baki bata ba dai nace gasu a jakkana ai nifa mama ban yarda da mutanen na ba don zasu iya cuta mata gaskiya tace Allah dai ya kyauta ke dai Rahama.
Doctors suka taru inda suka kira maigidan tare ya shiga dani mun samay su a zaune bayan gaisawa ne suke tambayan wanan maganin da aka kawo daga ina aka bata shi ne wai ?
Yace bai sani ba sai babban likita yace to a gaskiya masu binciken mu sun yi bincike sosai a kan shi sun gano cewa an hada sanadarai ne masu matukar cutar da dan adam a cikin sa..
Don haka maganin ya cutar da ita fiye da tsanmanin kowa don ma anyi mamakin yadda mutum zai sha shi ya kai har war hakan nan bai mutum ba.
Dole sai an binciko mai hada shi kafin ya cutawa sauran al,umma daga baya don yanzu Allah kadai yasan wanda aka cutawa dashi hakana.
An bar maganan ga sai an nemo wanda ya bata shi dole kafin ai wani abu akai da haka aka mike kowa ya fice office din.
Muna fita nace daddy Saliha itace ta farko da zamu fara tuhuma don ita ce ke daukowa tasan inda ake karbo shi dole.
Nasan kuma zata iya gudu idan ta fahinci akwai matsala da sauri yace bari ya bugawa maigadi waya ya tsare ta karta gudu.
Sunyi magana da mai gadi yace yanzu kuwa yaga wanan matar da ka hana zuwa tazo sunyi magana ta shiga gida sai ya hango ta tafe da sauri yace gata nan zata fito da kaya Alhaji yace tsare ta har in zo yanzu.
Bamu bata loiaci ba ya dauke ni police station ya tsaya yai reporting aka bashi yan sanda da mota muka nufi gidan.
Kafin saliha ta karaso get din yasa sakata da key ya rufe ya kada aljihun shi tana zuwa tace dashi bude

Download complete TXT · Novel page