Kanin Ajali
Chapter 34 of 34
aka ce mai ya samu matsala zai wawayo shi ya duba lafiyan shi.
Balle dan mutum mai rai ka tuna ni marainiya ce banda uwa banda uba sai Allah da yan uwana dakai.
Saukin abin Duk abinda mutum yayi Allah na ganin sa kuna can matan duniya suna rudin zuciyar ku ka jefar damu nan ka manta damu.
Ina gamawa na tura masa bai bani amsa ba run ina duba wayata har na daina don bai turo min da amsa ba bai kuma kirani ba.
Ni na dauka ba zai amsa min ba sai can dare misalin goma da rabi ya kirani sai Amira ta dauka tana gaida shi.
Yake tambayan ina maman ku tace gata nan tana tambayan shi baba yaushe zaka zo yace yana nan tafe ki ba maman ku wayan.
Ta miko min na karba da yi mashi sallama bai karba ba sai cewan da yayi kece kika turo min da sako ?
Shiru nayi ban bashi amsa ba yace maman Amira kina jina nace eh yace na sake ki ma,ana sauran saki daya dake tsakani mu na yanke shi yau.
Yana fadin haka ya kashe wayan shi ya barni a gurin sandare zuciyana tana famtsama da al,amarin shi ba abinda yazo min a rai sai maganan anty da tasha fada muna akan mazajen mu shine.
Kuyi hankali da mazajen nan naku wallahi watarana zaku wayi gari sun baku baya indai namiji ne kun dauki rayuwan ku gaba daya kun ba mazajen ku amna kun manta da kowa naku.
Kun maida su sune uwa sune uban ku duk kokarin da dangin mahaifan ku ke maku baku gani sai gani kuke kowa makiyin ku ne yanzu.
Zasu iya sakin ku a lokacin da komai naku ya kare ko su kara aure abokiyar rayuwan jin dadi nan gaba bayan kun gaba batar da komai naku a kansu .
Don haka wallahi ku gyara tun abu bai lalace maku ba gaba don mazan yanzu basu da tabbas a rayuwa wanan lokaci na ba maza amana gaba daya ya wuce ko.
Idan anty tana wanan maganan mukan ji zafin ta ko muga tana muna baki ne sai muje gefe mu zage ta muce bakin da take muna ya koma kan diyan ta ba mu ba.
Yau sai gashi maganan ta ya zama gaskiya a gare ni a lokaci guda nayi tunane kala kala a raina banda abokin kuka a dakin kuma hawaye bai zo min ba ko zan samu sauki a zuciyana.
Murya yata amira ne ya dawo dani ga tunanen da nake a gurin tana fadin yanzu mama baba ya sakeki ina zamu koma ke nan kuma ?
Sai lokacin hawayen da nake nema yazo min a lokaci daya na fara sakesu a fuskana nan muka taru dani dasu muna kuka a dakin ba mai bamu hakkuri.
Don yanzu yara wayon su yafi shekarun su don sun fahinci abinda kalman sakin dayace yayi min yake nufi har suna tayani yin kukan da nakeyi.
Na rasa yadda zanyi da raina kuma wa zan tunkara in fara fadawa sai gashi ya sake kiran wayan sai amira ce ta dauka tana fadin baba ka saki maman mu ne ?
Yace Amira ba maman ki waya yarinyar tazo ta kara min wayan a kunne yake fadin sorry fa na saki karamin zawarci ko kiyi hakkuri yana gama fadin haka ya kashe wayan shi.
Sai wani haushi shi na kara jin ya shigo min a zuciyana wai karag min zawarci ya manta da dinbin matsalon dake gabana wanda ban san da wanda zan fara ba a ciki yanzu.
Don nasan na sabawa dangina da yan uwan mahaifan, dama duk wani wanda ke tare dani ada muna amfana da juna a can baya.
Ba wanda yazo min a rai sai Baffa kanina a lokacin don haka na daga waya na kirashi a cikin daren lokacin sha daya da rabi na dare yayi.
Yana dauka na fara mai kuka a kidimay yake tambayana abinda ke faruwa dani.
Cikin muryan kuka nake fadin Baffa Jamil ya sake ni yanzu yace a cikin kidima shima yazo garin ne nace a a ta waya mukai magana dashi yace ya sakeni .
Ya sake fadin garin yaya haka ya faru daku kuma nace wallahi daga magana ya furta ya sakeni sai cewa baffa din yayi to ai shike nan ya kashe waya.
Na sake kiran shi duk da haushin kalamin shi da nake ji din a lokacin cewa da yayi ai shike nan nace zaka zo ne yanzu ?
Yace ba inda zan zo yanzu dare yayi ki bari sai da safe zan shigo da Allah ya kaimu ya kashe wayan shi.
Ranan a yadda naga dare haka naga rana a rayuwana in sakawa ina kwancewa ni kadai a dakina don yaran sun gaji da sharholiyan su sunyi barci abinsu ko.
Kiran asuba nayi sallah ga batan basirana sai yafawa nayi zuwa gidan wanan dan uwan nasa da mukaci kudina a tare dasu nayi.
Kafin inje shiya kirasu ya fada masu karya da gaskiya sun hau sai cewa sukayi ainina ja wa kaina da nayi hakkuri yadda kowa ke hakkuri aida ba haka ba.
Na rasa abinda zance sabofa na fahinci bayan nasu suke haka na kwaso kafa na dawo gidana inda na samu kanina baffa yazo yana wanke ma yarana baki.
Ina shiga ya kalleni fuska a murtuke yana fadin ke kuma ina kika fito tun da safen nan daga massalci na nufo gidan ki ban samay ki ba sai yara dake barci.
Nace unguwa na tafi wani kallo ya watso min tare da fadin gidan malam kika tafi ke nan ko ?
Cewa mahaifin jamil din kai tsaye na kyale shi tunda ya gano ni yanzu ni ba wanan ne a gabana ba nan dai na fara kawar da zancen tare da fadin wallahi baban Amira ya cuceni.
Yace ya cuci kanshi don Allah zai saka maki dama mu ya samu wuri ya zauna tare da tambayana yadda abin ya faru haka.
Ban boye mai komai ba na kwashe na fada mai duk yadda mukayi har sakin ya shiga tsakanin mu yace min takardun shi fa na karatu nace suna nan.
Ok kin gane duk wani abu da kika san nasa ne ki hado min su ki bani wallahi idan bai ban kudina ba ba zan bashi ko allura ba a cikin su.
Nan dai bayan mun gama magana na hado mai komai nasa harda yan tsumakaran shi na bashi na yadauka ya fita dasu akn cewa zamu hadu a gidan baba kabiru ansan yadda za a yi.
A haka muka aje shawara dashi bayan fitan shi naji ba zan iya tsayawa yin wani abin karyawa ba can nasa yarana a gaba muka nufi gidan gaba daya.
Sai ganin mu mutanen gidan sukayi da safe haka suna fadin ina muka fito haka ne da sassafen nan kuma ban iya masu magana ba na shige dakin anty.
Na kasa magana sai da Baffa yaji muryana ya fito daga dakin su na samaein gidan yazo shike fada masu abinda ya faru dani .
Sai duk suka saka salati a lokaci daya hankalin kowa ya tashi balle ma da na ce masu saki uku ne a tsakanin mu sai mamaki ya kamasu a lokacin .
Suke tambayana garin yaya haka ya faru basu sani ba ko a lokaci daya yai min saki uku gaba daya haka ?
Nan kowa ya shiga fadin abinda yazo mai a baki wanda a lokacin nake jin maganganun nasu kamar kari a jikina.
Nadama ya fara zo min tare da dinbin dana sani a rayuwana wanda yanzu keya ce gareni don aikin gama ya gama ko wasu daga cikin su har da kuka sukayi don bacin rai.
Anty ta nisa ta fara bani magana cikin kwanciyan hankali tare da jefa min kalaman da suka fara kwantar min da hankalina.
Lokacin baba ya fita tace inje in rufe dakina in dawo lokacin baba din ya dawo gida sai a yanke shawaran abinda ya dace dani.
Nace banda kwadon da zan kule dakina dashi tace ikon Allah ta mike ta dauko min kwason daki ta bani na tafi .
Tun da na dawo gidan na rasa wani abin kwarai da zan dauka a dakin nawa don babu wani abin kwarai da zan iya tafiya dashi gida lokacin.
Hakan dai na dan tsintsinto tsumakaran yarana don in sunyi wanka su samu na canzawa a gida kafin a yanke shawara akan mu a san yadda za ayi damu.
Haka dai na rufo kofan na juya zuwa gida hankali a tashe dani don ko maganan karyawa ban da shi a lokacin don tsanin damuwan dake tare dani.
A can gida kuma bayan fitana ne baba ya shigo ake fada mai abinda ke faruwa ashe a cikin dare a ciki ikon Allah baba ya samu wata dama na bada mutum biyu a nursing school .
Sai ya kira layin Jamil din don yaji inda da hali sai jn tafi sai jamil di ke fada mai hali da muke ciki dashi sai dai bai fada mai ko saki nawa bane don baba ya kashe wayan tunda ya fada mai cewa ai mun rabu dashi.
********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.
Visit > https://www.aihausanovels.com.ng
Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.
Email > aihausabooks@gmail.com
******* FOLLOW US ******
Facebook: Ai Hausa Novels
Twitter: Ai Hausa Novels
Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels
WhatsApp Number: 09017242889
Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU