Babu So

Chapter 8 of 58

ya shafa yana murmushi. “Dole ki dage ki koya hausa a zaman nan Mamana, dan rashin iyawan ya taka rawar gani cikin accident ɗin nan”.
      “A'a Abba dan ALLAH ni zan koma  Malaysia”.
    “Tsit gurin yay babu wanda ya iya cemata komai. Sai Shareff ne ya wani taɓe baki da barin wajen ko uffan baicema kowaba balle bayanin yanda ya samota dan a matuƙar gajiye yake ga ciwon kan nasama zazzaɓi yake neman komawa. Daddy ya kashe shirun wajen da faɗin, “Kuje ciki tai wanka taci abinci dan tana buƙatar kwanciya da wuri. Mamana mayi magana da safe”.
    Badan tasoba tabi Mom dan bata iya musu ba kuma. Duk da yanda Aysha ke tsoron faɗan Mom haka tabi Anam sashen Mom da ƙudirin su kwana tare, dan jitake kamar kafin safiya za'a ƙara cemusu ba'a gantaba ta sake ɓata.
  
   Washe gari tunkan ma Anam ta kira Abie ɗinta ta sanar masa Daddy ya kirasa sukai magana. Yayma Shareff kuma faɗa sosai kamar zai ari baki. Daga ƙarshe ya kafa masa dokar hukuncinsa shine kai Anam wajen aiki kullum ya kuma ɗakkota. Idan ko wata matsala ta sake shigowa akan Anam to lallai ya kuka da kansa dan sai ya matuƙar ɓata masa rai a gidan.
      Shi dai Shareff ɗin baice komai ba akan hukuncin. Sai Mommy ce tace sam bata yardaba ɗanta ba driver bane ba. Ko kallonta Daddy baiba, ya dai tabbatar mata idan Shareff ya isa yaƙi bin umarninsa.
       Ai wannan magana ta dagula ran Mommy a safiyarnan. Dan tata masifa ita da Gwaggo data fito tana goya mata baya. Daga Daddy har Abba babu wanda ya sake tofa tasa dan sukam dai yanzu sai dai su kalla Gwaggo kawai tunda sun fahimci bata ƙaunar zaman lafiyarsu da ɗan uwansu, Halima ce kawai ta kasa fahimta sun kuma barta wataran zata gane da kanta musamman da suka san idan akai auren nan na Fadwa da Shareff.

        ★★★★

  Duk yanda Mommy taso hana Shareff ɗaukar Anam hakan bai yuwuba. Dan shi dai haƙuri kawai ya bata da nuna mata illar fushin mahaifinsa a garesa. Ya roƙeta ta kwantar da hankalinta a hankali zai janye jikinsa ya samama Anam ɗin driver kowa ma ya huta. Wannan magana tashi ce taɗan kwantar mata da hankali ta maida kanta ga hidimar shirye-shiryen bikinsa.
      Daga ɓangaren Anam ma taci uban borinta akan malaysia zata koma ta fasa hidimar ƙasar su Mamie suka lallasheta da tabbatar mata cewar idan sukazo bikin Shareff zasu san abinyi. Hakanne yaɗan kwantar mata da hankali ta zauna zaman jiran lissafin kwanakin bikin. Yayinda ta cigaba dabin Shareff ɗin a takure. Shike kaita shike ɗakkota, daga gaisuwa babu abinda ke haɗasu sai harara. Ita kuma tata tura baki kenan da ɗaure fuska ita a dole haushinsa takeji duk da bata da riƙo sam wannan karon dai ta riƙe.

           Yau a gurguje yay shirin tun 7 ma batai ba ya fito saboda wani babban uzirin dake gabansa a office ɗin. Ga baƙi zaiyi akan wani babban project da suke saran samu insha ALLAH. A tsaitsaye ya shiga sashen Mommy suka gaisa koma shayin bai zaman shaba yau dan yaran kansu duk suna ɗaki basu gama shiri ba. Baije sashen Gwaggo ba dan ya gaji da mitarta akan ɗaukar Anam da yake yasan zata ɓata masa lokaci. Aunty Amarya ma a tsaitsaye suka gaisa ya nufi sashen Mom. Bayan sun gaisa da Mom ɗin cikin raba ido da kallon ko'ina na falon yace, “Mom tana ina zan makara?”.
      Da mamaki Mom ɗin ke kallonsa. “Wai kana nufin Anam?”.
    Kansa ya jinjina mata. “Eh Mom, yau zan fita da wuri inada uziri shiyyasa na sanar mata tun ɗazun ta shirya da wuri”.
      “Tab ɗi, to aiko banama zaton ta tashi a barci Babana. Ni kuma ban saniba ai da na tadata ta shirya”.
        Cikin ɓacin rai ya ɗan sake duban agogonsa da rumtse idanunsa. Ganin Mom ta nufi ɗakin yaja ɗan siririn tsoki. “Mom bara naje idan Khalel zai fita su taho tare inada meeting ne mai muhimmanci”.
      “To bara na tasheta dan nasan shima ɗin gab yake da fitowa kuwa”.
   Komai baice ba ya juya ya fita.
         Ba ƙaramin jan ido Mom taima Anam ba kafin ta tashi. A gurguje tai shiri saboda Khalel daya leƙo ya mata gargaɗi. Tasan halinsa shima ba mutunci ya cikaba shiyyasa tai ƙoƙarin shiryawa aɗan gurguje tanata kunƙuni dan barcin bai ishetaba. Tsaf ta shirya cikin kayan NYSE kamar koyaushe, sun mata cif kamar ka saceta ka gudu, ƙaramin baby hijjab tasa yau. Tayi ƙyau sosai sai zuba ƙamshi take mai daɗi. Khalel da gaba ɗaya yake ƙage da fitowar tata hanata zaman shan tea ɗin da Mom ta haɗa mata yayi.
     “Mom Please ki barta tasha a hanya ko a office ɗin, ALLAH idan na makara Yaya zaimin faɗa duk da shine yace na ɗauketa, gashi meeting ɗin nan inada alaƙa dashi nima.”
      “Amma Khalel ta fita bata karyaba? Bayan kasan bako wane abinci take iyaci ba. Kai da Shareff ɗin duk wutar ciki tamuku yawane kawai, amma duka ƙarfe nawane yanzu ɗin? An faɗa muku kowane zai dinga iya uban sakkonku da aiki kamar matching?”.
    “Mom bazaki ganeba wlhy. Please ki barta nidai”.
   Kafinma Mom ta sake magana Anam tace, “Kibari zansha a can ɗin Mom kinsan masifar wancan mutumin tafi ta Yah Khaleel”. Murmushi kawai Mom din tayi yayinda Khaleel ke hararta.

       Sosai Khalel ya zumbuɗa gudu a hanya, lokacin da suka isa wajen aikin nata har bakwai da rabi ta kusa gotawa. Sai dai sauƙinsa ma babu nisa mai yawa da company ɗinsu dan duk titi ɗaya ne. Baki ta taɓe ganin yanda duk Khalel yabi ya damu kansa tunda suka taho yake mata masifa a mota wai idan tace lalaci zatai to zata dinga hawo motar kasuwa kuwa shi dai baza'a dinga sashi ya jirata ba. Ita dai komai batace ba sai faman ɓata fuska dai takeyi tana cin inibi ɗinta data taho da shi daga gida da buga game a waya har suka iso.
      “Kije idan an fita break zan kawo miki abinci”.
     Sosai ta waro idanu waje. “Har ƙarfe nawa kenan Yah Khaleel?”.
       Harararta yay yana ƙoƙarin jan murfin data riƙe zai rufe. “Lokacin zuhur mana”.
    “Haba Yah Khaleel one fa kenan? Kaga ƙilama yunwa ya halakani kawai”.
    Dariya ta bashi amma sai baiyiba. “Naji zan roƙa Ya Shareff idan an tashi meeting zanyi squeezing time na kawo miki”. Kafia tace komai yaja motarsa yay gaba. Tabi motar da kallo tana tura baki gaba.

         Kamarko yanda yay alƙawarin ya cika. Dan wajen sha ɗaya aka kawo mata saƙo. Koda ta buɗe sai taci karo da takeaway na abincin da take tsananin so. Daɗin da taji ya sata tura masa text message na godiya, dan hakan tamkar tarbiyyar su Mamie ne a gareta, indai an mata alkairi komin ƙanƙantarsa sai tayi godiya harma da addu'a.
        Saƙonta ya shigo wayar Khaleel ne a dai-dai sanda wayar ke a hanun Shareff. Yazo nuna masa hoton wani zane da aka turo masa daga lagos sai kira ya shigo masa a ɗaya wayarsa, bazai iya ɗaukar wayar a gaban Shareff ba shine ya fita. Baiyi niyyar buɗe saƙonba, amma ganin sunan daya turo saƙon ya sashi buɗewa. Shiru yay na wasu sakkani yana kallon saƙon tamkar mai bitar karatunsa, sai faman cizar lip yake, sallamar Khaleel ta sashi danne saƙon ya aunashi a delete gaba ɗaya. Wayar ya miƙama Khaleel batare daya kallesa ba. “Kaje da shi zamuyi magana daga baya kawai”.
        Ɗan jimm Khaleel yay yana kallonsa, dan sanin maganar tasu muhimmiyace, hasalima shine ya damesa da kira tun ɗazun akan yazo duk da yasan suna meeting ne. Amma kuma sai bai kawo komai a ransaba yace, “Okay Yaya. To koma dai na tura maka shi kawai saika sake nazari kafin?”.
         “Okay yayi”.
Ya faɗa a taƙaice kawai. Kasancewar shima Khaleel ɗin miskilin kansa ne sai bai sake tofa komaiba ya miƙe ya fita abinsa. Haka kawai ya samu kansa da binsa da harara harya fice. Tsaki yaja da rumtse ido kamar irin mai takaicin kansa ɗin nan. Ya sake jan tsaki ya miƙe gaba ɗaya yabar table ɗin. Can jikin ƙaton window da aka ƙawata office ɗin da shi wanda ake hango har titi da cikin compound ɗin company ɗin kasancewar a saman upstairs office ɗinsa yake yaje ya tsaya. Ya jima wajen a tsaye hannayensa duka a aljihu yana kallon kaikawon mutane daga titi zuwa cikin company ɗin...

       Da lokacin tashi yay addu'a tai tayi ALLAH yasa Khaleel zai dawo ɗaukarta, har kiransa tayi dan taji sai dai bata samesaba network ya hana. Tun shigowar motarsa wajen tasan addu'arta bataci ba. Ɗan duban Yaseer abokin aikinta kuma shima ɗan hidimar ƙasa ne dake gefenta tai a sanyaye. Ya sakar mata murmushi dabinta da ƙyaƙyawan kallon da yake hanata sakewa da shi. “Ga Yayana yazo bye”.
     Manyan idanunsa ya lumshe da sake buɗewa a kanta. Shima ya miƙe har lokacin idonsa a kanta. “Haba dai Friend haka ake Friendship ɗin anama juna rowan dangi? Kamata yay kice muje na gaida Yayanmu ai ko? Kullum sai dai naga yazo ɗaukarki baki taɓa gayyata ta na gaisar da shi ba”.
      Murmushi kawai tai batare da tace komaiba. Ganin tayi gaba yay saurin bin bayanta har sai da tafiyarsu ta dai-daita. Kasancewar tinted glass ne yasa Yaseer knocking duk da sarai yasan wanda yake ciki ya gansu. Shiru babu alamar za'a sauke ya ƙara knocking fuskarsa faɗaɗe da murmushi. Zai ƙara na uku Anam ta girgiza masa kai a hankali, dama abinda ta gudar masa kenan shiyyasa taso hanashi tun farko. Tana ƙoƙarin buɗe baki ta bashi haƙuri aka sauke glass ɗin a hankali.
          Kallon daya watsa mata ya sata kauda kanta tana taɓe baki, Ƙara ɗaure fuska yay da duban Yaseer daketa faman shafar ƙeya yana murmushi.... Kafinma yace wani abu Yaseer ɗin yay saurin faɗin, “Good afternoon Yayanmu”.
       Kamar bazai amsaba sai kuma ya miƙa masa hannu alamar suyi musabaha, babu musu shima Yaseer ɗin ya basa suka gaisa, a mamakin Anam harda cema Yaseer ɗin, “Yaya aiki?”. Yaseer ya amsa fuskarsa na sake washewa ga sinne kai yana famanyi kamar wanda ke agaban surukai. Anam ta ɗan taɓe baki tana jinjina kanta, a ranta kuwa gulmarsa take. Tana son ɗagama Yaseer dake ɗago mata hannu nata hanun tanajin shakka, sai da taɗan faki idonsa ta ɗaga sau ɗaya ta fuske. Sai dai batasan yama rigada ya gantaba. Bai daiyi maganaba ya tada motar suka wuce.
       Shiru babu wanda ke magana tsakanin shi da ita sai redion motar daketa karaɗi, ganin inda suka shiga saɓanin gida daya kamata su nufa ya sata kallonsa a sace tana muy-muy da baki alamar akwai magana a bakinta sai dai babu damar faɗa. Sai da ta karanta symbol ɗin wajen ta gane Saloon sukazo, mamaki ya sata dubansa dan batasan mi sukazo yi wajen ba. Ido suka haɗa yana ƙoƙarin kai waya kunensa tai saurin ɗauke nata. Shima janye nasa yay da cire wayar daga kunensa hango Fadwa na fitowa a wajen tamkar tarwaɗa. Tayi ƙyau sosai cikin doguwar rigar atamfa, sai veil siriri data yafa iya kanta ta naɗesa a kafaɗa, ga wani uban glasess daya cinye rabin fuskarta sai dai ya mata matuƙar ƙyau kasancewarta fara ƙyaƙyƙyawa. Gefe da gefenta ƴammata biyune suma ƙyawawa kamarta farare tas da su. Yanda suke dariya zai tabbatar maka wata maganar sukeyi dan har ita Fadwan fuskarta cike take da murmushi. A hankali Anam taja siririn tsaki daya sashi ɗan waigowa ya dubeta, sai dai ta wani kauda kai gefe kamar wadda taga kashi. Sarai ya fahimci dasu Fadwa take, amma sai baice komaiba ya buɗe murfin motar ya fita fuskarsa sam babu walwala dan ya tsani taron ƙawayen Fadwa da suka zame mata kamar jela. Idan ka ganta da wannan yau gobe da waccan zaka ganta, na jibima daban ne...........✍

*_Haɗuwar iliya da wargaji😂 kunsan dai ba sauƙi😹😹, ku faɗama yarinyar nan taku yau sai mun rama marinmu ko shi Yayan nata bai isa dakatar damu ba ehe😜🤭._*


_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻
[10/26, 7:15 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*




*_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*. *_Typing📲_*




*_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*



*_09_*


.........Murmushi Fadwa ta sakar masa, cikin narke murya taima hannunta kiss da hura masa .
      “I miss you my Soulmate”.
   Kansa kawai ya jinjina da wani ɗan guntun murmushinsa iya laɓɓa. Cikin iyayi da feleƙe ƙawayen nata ke gaishesa idanunsu kamar zasu faɗo a kallonsa. Ɗan tsuke fuska yay yana amsa musu sama-sama.
        “Baby am sorry na saka wahala”.
Fadwa ta sake faɗa tana sake narke masa har tana saka tsigar jikinsa tashi. Nanma murmushi kawai yay mata da kauda kansa daga gareta dan shi kaɗai yasan halin da dama yake ciki ita kuma tana son sake kunnashi da wani. Cikin motar yay ƙoƙarin komawa da nufin ɗakko mata saƙonta, ita kuma batare da tunanin tare yake da kowaba ta nufi ɗayan side ɗin a zatonta anan ya ajiye saƙon nata ne, tana kuma son ƙara birge ƙawayenta da akaikaice tasa ake musu hoto acan gefe batare daya sani ba....
        Sosai Anam ta cika tayi fam da takaici, tayi yunƙurin buɗe motar ta fita taji ya sakata a lock dan yasan dama abinda zata iyayi kenan tace zata fita kamar wancan ranar. Ya ɗakko ledar dake a back sit ɗin Fadwa ta buɗe ita kuma. Ido huɗu sukai da Anam, ta watsa mata wani kallon banza ta ɗauke kai dajan siririn tsaki da faɗin “Ballagaza” a hankali....
        A yau kam tayi laƙawarin bazata ƙyale ƴar iskar yarinyar nan ba. Cikin jin ɗacin (ballagaza) data kirata dashi tace, “Kin yima ubanki dan uwarki.”
    Duk da Anam bajin hausa take da ƙyau ba tasan zagi, amma sai tayi kamarma bataji Fadwa ɗin ba, taciro Bluetooth daga bag ɗinta ta fara ƙoƙarin maƙalawa a kunne Fadwa ta buge hanun Bluetooth ɗin ya faɗi ƙasa. Ƙafa tasa ta takesa da shegen takalminta mai tsananin tsini......
       “Fadwa!”.
    Shareff ya faɗa a ɗan kausashe.....
“......Amma dai Soulmate kanajin tsakin da taimin ai, ranar na ƙyaleta daboda darajarka, amma yau gaskiya bazan iyaba, ban son raini..!”
    Itama ta faɗa da sauri cikin tarar numfashinsa.
          Anam data sake cika tai fam tai yunƙurin hanɓarata baya ta futa. (Yo dama a gayama kura gayyar cin nama bayan bidirin nasu ne🤣. Ba'a takali Anam ba ma yaya aka ƙare balle anzo har gida da goron gayyata😂).
      “Idan kika fita a motarnan sai ranki ya ɓaci!!”. Yay maganar a tsawace da fisgota ya maida ya zaunar. Kuka ta fashe masa da shi dan zuciyarta tazo wuya. Baibi takantaba yay yunƙurin fita a motar sai ya hango Fadwa can ta nufi motarta a fusace ƙawayenta na take mata baya. Idonsa ya rimtse da taune hakwaransa, sai kuma ya furzar da huci mai zafi yaja murfin a fusace ya rufe, na side ɗinta ma shine ya rufosa ya tada motar suka bar wajen dan tuni su Fadwa ma sun fice a wajen har tana bulama mutane ƙura.

         Cikin sake tunzurasa da kukanta keyi yaja birki da ƙarfi, firgita tai ta ɗago da sauri tana kallonsa. Harara ya watsa mata tare da gangarawa gefen titi ya kashe motar. “Nidai ka kaini gida, kuma saina sanarma Daddy mata na maka kiss a titi da rungumek....”
     Bamm ya bige bakin nata, kukan ƙarya ta sake fashe masa da shi dan ko hawaye babu yanzu sai dai taji zafi sosai. “Har Abba ma saina faɗawa da Abie da Mamie da Mom da aunty Amarya”. Ta sake faɗa da ɓalle murfin motar zata fice. Riƙota yay ya maida murfin ya rufe yasa lock. Takaicinsa da haushin abinda Fadwa ta masa yasa takejin zafinsa batare data san dalili ba, cizo tai ƙoƙarin kaima hanunsa dake riƙe da nata....
       “What!! Ni zaki ciza?”.
   Bata kulashi ba ta sake kaima hanun cizo. Babu shiri tilas ya saketa, yana mai girgiza kansa. A hankali yakai kwance jikin kujera bayan ya kwantar da ita, hannayensa duka harɗe a ƙirjinsa ya lumshe idanu yana mata kallon ƙasan ido. Tunba yanzuba yasan Anam fitinanniya ce dama, sai dai yayi zaton tabar tsiwa zuwa yanzu, amma tun tana ƴar ƙaramarta boss ce daman. Yasha zuwa hutu ya samu an kawo ƙarar Anam daga school ta naɗi ƴaƴan mutane babu dalili, idan kuma gidansu akazo nanma ta jibga, idan gidansu taje yaran ba tsira sukeba. Ƴaƴan aunty Mimi ba ƙaranar wahalar Anam sukaci ba duk da wasu sun girmeta bata ɗaga musu ƙafa........
       “Nidai ka buɗemin, bazan sake shiga wannan motar ba da akeyin wannan abun....”
      Duk yanda yaso danne murmushin dake son fita ya gaza hakan, gefe ya maida kansa yay murmushin kafin ya tashi zaune sosai fuska a haɗe ya riƙo hanunta dake jikin handle ɗin ƙofar, baki ta buɗe zata saƙi ƙara dan matse hanun yayi yasa yatsunsa biyu ya riƙe lips ɗin nata fuskarsa a tsananin haɗe. Sosai idanunta suka sake firfitowa, ga tsoro ga tsiwa......
       “Haɗiyemin wannan kukan, ki kuma faɗi miye abunda akeyin kona tattakaki”.
    Tsaf ta haɗiye kukan zuciyarta na bugawa da sauri dan kusancinsu yayi matuƙar yawa, kanta ta fara jujjuya masa a hankali. Idanu ya zare mata da sakin lips ɗin nata, “Ai saikin faɗa mara kunya”. A tsorace take amma bakin yaƙi mutuwa. Taja jikinta baya da maƙurewa a jikin ƙofa, “To ka bari muje gaban su Daddy ɗin basai na faɗa ɗin ba....”
     Bakin ya sake kaima ɗalli tai saurin duƙewa da cusa kanta a tsakanin cinyoyinta. Ƙwafa yay da komawa jikin kujerar ya lafe yana kallon waje,  kusan mintuna huɗu suna a haka ring ɗin wayarsa ya katse shirun nasu. Iska ya ɗan furzar da kallon wayar, ganin Daddy ya sashi ɗagawa yakai kunne a ladabce yay sallama.
       “Shareff kuna ina?”.
  Ɗan jimm yay saboda jin muryar

Download complete TXT · Novel page