About this Novel

 

Story Preview

[10/2, 12:27 PM] Zeenaran🫶🏻: *_Typing📲_*




*_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_01_*


*_MALAYSIA (SABAH)_*

..........A hankali sautin kukan ke tashi tamkar mai rairashi da gayya. Sai dai daga jin yanda salonsa ke fita kasan tsabar daɗewar da maiyin nasa ya ɗauka yana yine ya kaisa ga galabaita. Kasa jurewa nai na kutsa kaina cikin gidan madai-daici da ke ɗauke da dukkan kayan more rayuwa najin daɗi. Falo ne babba masha ALLAH, sai dai duk girmansa banci karo da kowa a cikinsa ba. Shiru nai alamar tunani, (to ta ina kenan sautin kukan da yaja hankalina ke fita?) rashin mai bani amsa ya sani fara waige-waige a falon. Tabbas ba'a nan ɗin bane, hakan ya sani kutsa kaina dan zuciyata ta banni tabbacin a window da naji kukan ɗakine.
            Takun sakkowa da stairs ɗin da'aka kawata adon falon da shi ya sani maida hankali can. Hamshaƙiyar mace kamila mai yanayi da fulanin ƙasar Nigeria ce ke taku cike da nutsuwa da kamala tamkar yanda shigarta ta kamala ta ƙawata mutuncinta ga mai kallo. Sam banyi zaton ko (zo na kasheki) ta sani da yaren hausa ba, amma a mamakina saina tsinkayi kamilar muryarta na ƙwala kiran sunan *_Anam!_* a ɗan kausashe. Ƙara kausasa muryarta tayi ganin babu alamar wadda take buƙatar ganin data kira da suna Anam ɗin ta fito.
         “Anam! Idan har kika bari na shigo inda kike ki tabbatar sai jikinki yayi tsami kafin kibar ƙasar nan. Shashasha kawai wadda bata kishin kanta. To banda mara kishin kai wake ƙin tushensa? Ba kukan hawayeba kiyi na jini ma babu fa

Continue reading →

Reader Reviews

Login to leave a review.

No reviews yet — be the first.

Zafafa Writers

More Novels You May Like