About this Novel
An old man, who looked to be around fifty years old, was sitting on a bench, holding a small radio and listening to it.
Suddenly, a fancy car, an Annoconda model, sped down the road, creating a small wind because of its fast speed.
The car stopped suddenly at the gate of a big house, and the driver started honking the horn loudly, almost like there was a fight going on.
Startled, the old man dropped his radio, stood up quickly, and rushed to open the gate.
As soon as he opened it, the car drove inside, heading towards a part of the house.
A young woman stepped out of the car. She looked so thin that it seemed like she didn’t eat much. If not for her body shape and the clothes she wore, one might not even think she was a woman. However, her smooth skin showed that she came from a comfortable life. She wore a long dress made of fine material, a hat on her head, and high-heeled shoes that were extremely sharp.
Story Preview
Page1
Cool ce!
Free book ne, Comment kawai nake buƙata please, if not zanyi abunda bakwa so 🌝
Typing ba kullum ba, sai an ganni kawai.
Ƙirƙirarraren labari ne, ban yi shi dan cin zarafin wani ko wata ba.
Wannan rubutun mallakina ne, ban yadda a juya shi ta kowacce siga ba sai da izinina, kuma ban yarda a sɗora mini shi a kowane website ba sai da izinina.
BISMILLAHIRAHMANNIRAHIM
Dattijo ne wanda a ƙalla zai kai shekaru hamsin, zaune akan benci hannunsa riƙe da 'yar ƙaramar radio, yana saurara.
Wata Haɗaɗɗiyar mota ce ƙirar Annoconda, aka kwararo dogon layin da Ita, wanda gudun da motar take ta haddasa tashin wata 'yar ƙaramar guguwa.
A ƙofar wani makeken gate motar tayi birki, aka fara wani irin horn, sai kace yaƙi.
A gigice ya yasar da radiyon da ke hannunsa, ya miƙe a zabure ya nufi gate ɗin, yana gaganiyar buɗe shi.
Yana buɗe gate ɗin, aka turo hancin motar, zuwa wani sashi na gidan.
Wata matashiyar budurwa ce ta fito daga Motar, gata nan dai kamar bata cin abinci, ban da yanayin jikin ta da kuma kayan da suke sanye jikinta, ba ka ce mace bace, saboda tsabar rama, sai dai fatar jikinta za ka kalla ka gane 'yar hutu ce, da ga ita sai doguwar rigar material, da hula a kanta tana sanye da wani uban takalmi me shegen tsini.
Ta nufo gurin da dattijon nan yake kokawar maida gate ɗin ya rufe tsigil- tsigil, tana zuwa ta ƙare masa kallo sannan tace "wai kai dan Allah wani irin mutum ne? Kai ta abu kamar mara jini a jiki ko wanda baya cin Abinci? Duk Abincin da kake ci kamar gara amma ba ka da wani Amfani
Reader Reviews
Login to leave a review.
No reviews yet — be the first.