SO DA BURI BOOK 2
Chapter 17 of 39
rintsa dan ni ba anan zan kwana ba Baba nake jira yazo ya d’auke ni sai gobe tukun zan dawo. Amman na san yau rikici zata yi tayi, Mama ta zama mai fad’a sosai!.
Maganar da zan fad’a mata kuwa, gaskiya ce zan fad’a kawai ba wani abun ba.”
Rau rau Huda tayi da idanu.
A hankali Sakina tayi murmushi tace
“Kije ku tafi, tabbas Mama za taji ba dad’i amman kije kawai kin ji?”
A hankali ta share hawayenta ta matso ta rungume Sakina,
dai dai nan Baban su Sakina shima ya k’araso wajen.
Abba ma haka wanda tun fitowarta ya gansu ganin da yayi kamar bata ganshiba ne yasa ya fito ya k’araso inda suke tsaye.
Kusan a tare suka k’araso wajen, Baban su Sakina yana ganinshi ya gane shi ne baban Hudan dan haka yayi saurin mik’a masa hannu
(wani aiki ya tab’a had’ashi da Abban kuma ya samu alkhairi sosai!
Har gidansa ma sukaje suka yi mishi godiya. Yanata yaba alkhairin mutumin, shiyasa
da Arshaad ya rok’esa akan ‘ya rufa mishi asiri kar ya fad’awa kowa daga family d’in daya fito yet saboda gudun matsala’
Shi kuma ya yarda yayi shiru bai fad’a d’in ba
Don yaga sun san mutunci
kuma shi kanshi yana so Hudan ta had’u da Mahaifinta a samu a dedeta komai!
Amma Arshaad yace
baya nan yanzu ya tafi wani aiki kuma akwai issue har yanzu a k’asa, but a hankali a hankali za suyi settling in shaa Allah, komai ya dawo normal .
Shi kanshi a lokacin ya yarda da hakan saboda ya san wani part na case d’in su Madu da family d’in Abban…
To kuma suna k’ok’arin ganin komai ya koma normal d’in
tukun
a samu a daidai sai shi kuma
Aslam yazo yayi musu mai gaba d’aya!)....
Shima Abban kallon sani yake yi masa, sai da Baban su Sakinan ya tuna mishi ‘ya tab’a basu wani contract kwanakin baya’ Tukunna Abba ya tuna shi, Hudan kuma ta gabatar masa dashi a matsayin Baban su Sakina mijin anty d’inta.
Sake gaisawa suka yi sakina itama ta gaidashi cikin girmamawa… kallon Abban take yi tana sake maimaitawa!
Tanaji Ummu tana cewa ‘Baba kishi yake da Abba shiyasa yake yin wasu abubuwan’ tabbas kam dole Baba yayi kishi da wannan mutumin!
Dukda cewa shima Baban ba mummuna bane kuma fari ne shima amman ko makaho In ya shafa yaji ya san babu had’i kwata kwata tsakanin Abba da Baba, Abba ya tsere mishi a komai da komai..
Gashi wani abun mamaki ba zaka tab’a cewa ma ya haifi Hudan ba dan kamar wani d’an 33 haka yake, jikinsa san bai
nuna tsufa ba kamar dai Mama,
Ita kam tunda take a rayuwarta bata tab’a ganin perfect match irin na Abba da Mama ba……
Da kulawa ya amsa gaisuwar tata yana tambayarta “ya school” a hankali tace “muna jiran results ne har yanzu”.
Sun d’an tab’a hira da Baban Sakina daga nan sukayi exchanging numbers suka yiwa juna sallama.
Abba ya lura da yadda Huda ta shak’u sosai da Sakina dan
har suka isa mota tana waigawa tana waving d’inta kamar wata Yarinya
itama Sakinan haka dan ita kam har sai da taga fitarsu tukunna suka shige ciki don su d’auko kayanta.
Tun kafin Mama ta gama gaisawa da Babansu Sakinan ta san yanda tayi ta zulle ta gudu, daman itama k’arfin haline kawai zata yi wajen yiwa Maman bayani
kuma yanzu ga mafita Allah ya kawo mata.
Tunda suka kama hanya Hudan take tunanin abunda tayi sam bata kyauta ba! But ya kamata shima Mahaifinta ta d’an kwantar mishi da hankali tunda ga halin da yake ciki da family d’inshi….
Ya lura da ita sosai, don k’arshema har da y’ar kwalla yaga tana gogewa. Shiru yayi mata kawai…..har sun kama hanyar gida sai kuma ya juya yayi hanyar dominos.
Suna zuwa yayi parking ya shiga bai dad’e ba ya fito da Ledoji nik’i nik’i
dangin su ice cream da milk shake da pizza…..
A baya ya saka ya zagayo ya zauna yace “gashi ita da su Shuraim, in kuma sun yi bacci by the time da suka gidan sai ta sa musu nasu a fridge.”
Godiya tayi masa, daga nan
suka kama hanya, yana ta d’an
janta da hira kad’an kad’an, yace if “she’s bored gobe ta shirya Arshaad ya kaisu munjibir park”
Kamat zata ce masa a’a sai kuma tace “to” kawai.
A haka suka karasa gida.
Shi ya taya ta d’aukar kayan sai da suka isa chan sama tukunna ya ajjiye a parlour yayi hanyar d’akin shi bayan ya rarrage fitulu yana ce mata “ta duba su ta shafa musu addua idan sun yi baccin, itama tayi kafin ta kwanta.”
Kamar yanda tayi tunani, ko da taje su Shuraim d’in har sun yi bacci dan haka tasa a fridge d’in sama dan ita tsoro take ji ba zata iya sauk’a k’asa ba, a
Iyaka saman ma itakam duk a tsorace take!.
Tana jera kayan tana mamakin uban yawansu….
Ice cream d’aya ta Iya d’auka, dan gaba d’aya bata da laka a jikinta tunanin Mama take tayi..duk jikinta a sanyaye yake, ta san tayi laifi babba a Mama, bata san ma ta ya zata sake facing d’inta ba!
Cokali biyu kawai ta iya yiwa ice cream d’in duk dad’in shi amman sai ta kasa sha, da kyar ma ta iya had’iye biyun a mak’oshinta
don haka ta rufe ta saka a d’an mitsitsin fridge d’in gefen gadonta ta mik’e tayi wanka.
Tana fitowa ta rarumo waya ta danna kiran Sakina
Ita kuwa Sakina tunda suka fita tana zama a mota ta kashe wayarta ma gaba d’aya
dan wallahi ta gaji dayawa tana buk’atar isheshen bacci, in yaso duk fad’an da za ayi mata ayishi gobe!.
Shiyasa Hudan tayita kiranta amma taji a kashe…. daga k’arshe ta hak’ura tayi cilli da wayar, ta kwanta, gaba d’aya ranta ba dad’i, bata san ya Mama zata kwana ba yau! Kuka ta fara yi, ta dad’e tanayi kuma daga baya ta share hawayenta….
Wayarta taji tana k’ara dan haka ta lallab’a ta d’auka, gabanta ne yayi wani irin mugun fad’uwa ganin sunan Ummu, sai da wayar ta kusan tsinkewa tukunna ta iya d’auka
tana karawa a kunnenta Ummu tace “kina gida ne?”
“Eh” ta bata amsa.
“Waye ya mayar da ke?”
“Abba” ta sake bata amsa.
“Daman tare kuka zo?”
“Eh!”
“Tam! Sai da safe.”
Hudan tana shirin yin magana taji kit!! A yanke kiran.
A daren ta kira layin Ummu yafi sau ashirin amman bata d’aga ba!
K’arshema dena shiga tayi.
Gaba d’aya hankalinta sai ya sake tashi, sai wajajen 2 tukunna ta samu tayi d’an baccin ta rabi da rabi,
kiran sallar farko ta farka.
Tashi tayi tayi Nafila ta jira aka kira tayi sallar Asubah…
Bata kwantaba sai da tayi azkar d’inta ta fara karatu.
Sai bayan gari ya d’anyi haske tukunnna ta d’an iya yin bacci shima nisanshi iya awa d’aya!
Wayar Sakina ta sake gwadawa tana tashi but still a kashe.
Tana zaune taji kamar ana knocking chan waje k’ofar
falo, mik’ewa tayi ta fita taje ta bud’e…
Tana bud’ewa taga ashe ragowar kayantane na jiya
aka kawo/
Cikin girmamawa maid d’in ta gaidata sanann ta hau shigo mata da kayan leda leda.
Godiya Huda tayi mata bayan ta gama, ta juya ta fita.
Ita kuma ta tura k’ofar taja kayan zuwa bedroom.
Tana gama ajjiyewa a closet
ta fito kenan ta zauna akan gado Abba ya shigo cikin jallabiya mai k’aramin hannu rik’e da hannun Sudais wanda shima yake sanye cikin kayan bacci.
Da sauri Sudais d’in yazo ya rungumeta sannan yace
“Abba just told us that you are our big sister, i’m so glad that we’ve a big sister” Ya k’arashe maganar yana sake hugging d’inta.
Murmushi tayi itama tayi hugging nashi back kafin tace
“I’m so glad to have cute brothers too.”
Da sauri ya d’ago yace “Monday idan anje school zan gayawa Ashraf da Sultan da Kareem nima nayi big sister, dariya suke yi min kullum suna tsokanata!
Yanzu kema kice Abba ya kaiki school d’inmu a sakaki a ss2 dan Allah so that i can come and see you during break time just like they do, and also....”
Abba ne ya dafa kanshi yana dariya, kafin yace
“Sudais wai har yanzu baka san ka girma ba?
Ya kamata fa ace ka daina wannan shirmen
And
Big sis ta gama secondary ai,,kar kayi mata adduar komawa baya mana. School d’in su Aaima zata tafi, ko?”
Yayi maganar yana kallonta yana murmushi.
D’an zamowa tayi ta gaidashi,
a hankali ya amsa yana mai dafa kanta yana kallon idonta da tashi d’aya ya fahimci taci kuka.
A kan Kujerar gefen gadon ya zauna yana kallonta kafin yace
“Me ya saki kuka? Mama kike son sake gani?”.
A hankali ta sunkuyar da kanta k’asa kafin tace “ina jin ba dad’i ne akan abunda nayi mata jiya, Ummu ta kirani nace mata mun dawo, inaga haushi suka ji dan I’ve been calling them since last night amman ba wanda ya amsa.”
Ta k’arashe maganar tana sakin kuka.
Ajiyar zuciya Abba ya sauk’e kafin yace “A kawo miki Sakina? Ku zauna tare?”
Da sauri ta d’ago tana kallonshi, sai kuma ta hau d’aga kai tana share hawayenta.
Murmushi yayi kafin yace
“Ok, but no more crying, in ba haka ba in fasa.”
Da sauri ta cigaba da goge hawayenta, da kyar kuwa ta samu suka tsaya….
Abba bai kira Baban Sakina ba sai da ya sakata tayi murmushi kala uku! Sudais yana tayashi da yi mata cakulkuli.
Bayan sun gaisa ya tambayeshi akan “Dan Allah ya bar Sakina ta zo ta d’anyi kwana biyu da su tunda basu fara school ba yanzun, maybe Hudan ta d’an sake in ta ganta.”
Nauyi da kunyar Abban ne suka hanashi yi masa musu
dan haka yace “yanzu an sallami Mama ne suna kwashe kaya, amma zuwa anjima in shaa Allah zai kawota.
Ya tura mishi adress kawai.”
Godiya yayi sannan ya kashe wayar, ya tura mishi da adress d’in.
Yaji dad’in yadda ta saki ranta sosai.
Cikin murna ta tanbayeshi “me zata dafa?”
Murmushi kawai yayi yace mata “koma me ne in ta dafa yayi”
Kafin ya tambayeta adress d’in su Sakina, tayi mishi kwatance,
daga nan suka fita shi da Sudais........
Wanka tayi ta sa wani silk gown, A shape, colour d’in emerald green, an d’anyi kwalliya ta k’asan k’irjin da igiya mai stones ya zagaye, daga gefe ta gaban an tufkeshi yayi kmr ribbon babba. Bai matsetaba kuma bai yi mata ruwa ba dai dai jikinta, tayi
masifar yin kyau, ta gyara gashinta ta tufke a k’eyarta
sannan ta d’auko d’ankwali kayan ta nad’a wanda kasancewarshi k’arami, yasa ta d’anyi normal d’aurin kai dashi ta kuma bi da edges d’in dankwalin ta kan gashin data tufke ta sake zagayewa da shi d’ankwalin.
Sannan ta d’auki turare ta fesa
duk a cikin kayan da tayi order jiya.
Tayi kyau sosai kuwa abunta.
Wayarta ta d’auko ta kira Ummu still bata d’auka ba, Sakina kuma a kashe.
Jiki a mace haka ta sauk’a ta shiga kitchen.
Ga mamakinta har an gama breakfast, maid d’in jiya da wani shima da uniform a jikinsa irin nata (maid d’in),
Sun gama hada komai, kuloli wajen uku, kitchen d’in sai tashin k’amshi yake yi.
Sai da ta k’araso tsakiyar kitchen d’in tukunna suka lura da ita, kamar zasu kifa haka suka hau gaidata cikin girmamawa..
Itakam kunya da mamaki ma da kyar suka barta ta amsa.
Ta riga tayi niyyar yiwa Abba girki shiyasa ta tambayesu me suka dafa?
To dai d’ayan abincin itakam ba ma ta sanshi ba kuma bata tab’a ganinshi ba ma, sai
shawarma a d’ayan kulan, farfesun kayan ciki kuma a d’ayan, sai ruwan zafi a flask ga mai buk’ata.
A hankali cikin nutsuwarta ta k’arasa ta bud’e inda suka nuna mata a matsayin store d’in ta shiga..
Babu abinda babu a ciki, dan haka ta d’auko, dankali kad’an da kwai da Mayonnais da su albasa sai su green beans da
macaroni.
Sun so su tayata aikin amman tak’i, da kanta ta had’a mishi potatoe salad mai d’ankaran dad’i da kyau!
A dining d’in taje ta ajjiye bayan ta juye a cooler.
Tana shirin barin wajen Auwal ya shigo…
Suna had’a ido da shi ya b’ata rai! Fuskarnan tamau haka
ya nufo dinning d’in.
ita dai Huda ta lura kwata kwata wannan baya
k’aunarta ya tsaneta!
A hankali ta gaidashi amman kamar wanda take magana da dutse ko kallon inda take bai yi ba! Kujera kawai yaja ya zauna ya hau had’a tea.
D’aga sagaggun k’afafunta tayi ta fara takawa don barin wajen dai dai Abba yana sauk’owa, bata ma lura dashi ba sai da ta kusan tsakiyan falon suka yi kicib’is!
Murmushi yayi ya dafa kanta sannan yace
“har an gama girkin?”
Itama murmushin ta mayar mishi tace
“Eh”
“Ok, muje.”
Yace sannan ya kama hannunta suka juya.
Suna zuwa Auwal ya mik’e ya gaidashi, cikin kulawa Abban ya amsa mishi sannan ya cewa
Huda “kun gaisa da yayan naki?”
A hankali ta d’aga kai alamar ‘eh’
Harararta yayi sannan yace
“Daddy ne yace kuzo muyi breakfast.”
“Ok”
Abban yace sannan ya cewa Huda taje taga ko su Shuraim sun gama shiryawa. Har ta juya taji yace
“Ina abincin da kika dafa?”
Da sauri taje ta d’auko kular ta mik’a mishi, karb’a yayi sannan
ya mik’awa Auwal yace masa
“fara yin gaba da wannan, gamu nan zuwa.”
A k’afar bene ta had’u da Yaran dan haka suka juya tare.
Suna k’arasowa parlourn suma suka wuce side d’in Daddy.
Ita dai tana mamakin tou wanchan uban abincin, da aka dafa musu waye zai ci!?
Kasa hak’ura tayi ta cewa Abban
“Ko ta koma ta d’auko kulolin chan, masu aikin fa sun yi girki”.
Murmushi yayi yace mata “Karta damu anjima da yamma idan anyi na sadaka za a had’a a kai tare da wanchan d’in.”
BULAMA ✍️
So da Buri
Free Book
42
Yadda side d’insu yake, haka na Daddy shima yake, komai da komai iri d’aya, kawai de akwai k’ofofi da corridors d’in da suke a nasu wanda babu a na Daddyn.
A parlourn suka tarar da Daddy d’in da alamun su yake jira.
Abba ne ya fara gaidashi tukun su Huda.
Yana jin Yarinyar a jikinshi matuk’a dan haka bayan ya amsa ya hau tambayarta “ya take? Tana jin dad’in zaman? Akwai abunda take buk’ata?”
A hankali tace
“komai
Alhamdulillah.
“Ma shaa Allah” yace sannan suka k’arasa…..
Nan d’in ma abinci wajen kala hud’u akayi.
Cikin nutsuwa da nishad’i sukayi serving kansu suka fara having breakfast d’in.
Basu dad’e da fara cin abincin ba, Hudan taji yanayin bugun zuciyarta ya chanza!
A hankali ta runtse idanunta tana k’ok’arin saita kanta, da kyar ta samu ta bud’e idanunta tana mai jin wata nutsuwa tana sauk’ar mata sakamokon k’amshin turaren da ya sakarmata da kasala lokaci guda!
Basuma lura da shigowar tasa ba, sai da ya matsosu sosai da k’amshin turarenshi ya yi musu sallama, tukunna suka lura da shi.
A hankali yace
“AsSalama alaikom”
“Wa’alaikassalam, d’an albarka!”
Daddy yace yana mai ja mishi kujerar kusa dashi.
Zama yayi, a lokaci guda kuma yana mai amsa gaisuwar su Shuraim sannan yace Daddy Ina kwana”
Da kulawa Daddy ya amsa haka shima Abba bayan ya gaidashi.
Sannan ya juya ya mik’awa Auwal hannu, sukayi musabaha.
A hankali Hudan ta gaidashi ba tare da ta yarda sun had’a ido ba!
Juyowa yayi ya kalli inda take, sai kuma da sauri ya kauda kanshi, a hankali yace “lafiya”
Hira suka d’an fara sama sama, kusan rabin hirar akan maganan company d’in da Aslam da Abba za su bud’e ne.
Ita dai Hudan kasa ci gaba da cin abincinta tayi, tun lokacin daya shigo! Bata san daliliba amma in dai yana waje to sai ta dinga jin kanta uncomfortable, ga yadda k’irjinta yake yi mata shima, wanda ta rasa dalili.
Abba ne ya cewa Aslam
“Ina Arshaad ne? Ban ganku tare ba.”
“Ya tafi d’aurin auren wani Abokin su, and wai za su kai amarya Kaduna, around 2 haka.”
Aslam d’in ya bashi amsa.
“Ok” Abba yace kafin ya kalli Huda yace
“Ko a bari sai gobe kuje park d’in ko? Tunda yau Arshaad d’in yana busy.”
Kafin ya rufe bakin shi Auwal yace “Bani da aiki sosai yau, zan kaisu.”
Hudan ta d’anji sauk’i saboda daman ba zata so su fita itada Arshaad ba, kuma ba zata so ace Aslam ya kaita ba! Amman kuma ba ita kad’ai ba hatta su Daddy sai da suka fahimci akwai wani abun da Auwal ya shirya duba da yadda baya son ta yanzu kuma lokaci guda yace
‘Zai kai ta’
Daddy wanda ya san halin kayanshine yace “a’a! Ka barshi goben Arshaad d’in ya kaisu”
“Daddy i volunteered fa.”
Auwal d’in ya fad’a yana kallonshi.
Cikin d’an fad’a Daddyn yace
“And i insist akan ka barshi Arshaad ya kaisu.”
Murmushi Abba yayi kafin yace “Daddy tunda ya nuna zai kaisun a barshi mana ko? Please.”
Baya son jan magana dan haka yace “ok” kawai
….dukda ya san Auwal bai Isa yayi mata komai ba tunda tare za su tafi ita da su Shuraim amma baya so suje Auwal d’in yayi mata wani kalar rashin mutuncin da zai ja yaji kunya ne.
Murmushi Auwal d’in yayi ya kalli Hudan kafin yace
“Ki shirya around 2:30pm haka”
Yana gama fad’an haka ya mik’e yayi hanyar sama, da alama ma ko “to” d’in data ce mishi bai ji ba.
Shuraim ne ya mik’e, yace “Abba zanje in yi assignment d’ina kafin mu fita”
Da sauri itama ta mik’e daman hanya take nema saboda sam bata k’aunar zamanta waje d’aya da Aslam kwata kwata, gashi ta lura sai faman kallonta yake tayi, sannan anyi rashin sa a ya zauna a kujerar da take opposite d’in tata ne….a hankali cikin nutsuwarta tace “Abba nima bara inje” sannan ta juya ta yiwa Daddy sai anjima. Sudais shima binsu yayi, suka fice a tare….
Da murmushi Abban ya bisu da kallo yana jin wani tsananin farin