SO DA BURI BOOK 2

Chapter 38 of 39

shiga cikin parlourn suka zauna tukunna Dad yace mata
“Ummi sai kin yi hak’uri da Abba a yanzu.
Kar ki damu
In sha Allah zai sauk’o.
Kin ji.
Ki tashi kije d’akinki ki huta.
Ya gyara abunda ya b’ata d’azu.
Ki kwantar da hankalinki
Naki biyayyane, kin ji?”

A hankali take jan numfashi tana share hawayenta
tana jin wani farin ciki yana ratsa ta.

“Tam Dad mun gode”
Tace.
Sannan ta fara k’ok’arin mik’ewa dai dai nan
su Sudais da Shuraim da Aslam suka shigo!
Suna ganinta suka yi kanta da gudu suna Ihun murna
Shuraim harda y’ar kwallar shi
Itama sai da tayi kwallar murnar ganin gudan jininta.
Daga nan suka gaisa da Aslam ta wuce tayi sama ita da su Sudais.
Tun a hanya Sudais ya fara zuba surutu yana bata labarin event d’in, da kalar hotunan da suka yi da kuma yanda Ya Aslam ya zauna a kusa da Huda….


Gaisawa kawai Aslam yayi da su Dad daga nan suka fice gaba d’ayansu..
Basu yi mishi zancen event ba
shima daman hakan yake so..
Iya kar abunda suka sani shine Arshaad bai yi attending ba!.

Shi da Dad suka yi gida Daddy kuma yayi side d’inshi.



Sai dare Jalila ta farfad’o!
Ba kowa a d’akin sai ita kad’ai.
Jiri da ciwo a mararta
take ji ba na wasa ba!
Tana so ma ta mik’e ta d’an zauna amman ta kasa…
A hankali kwakwalwarta ta shiga tariyo mata abunda ya faru da ita d’azu.
Da sauri ta zabura ta dafa cikinta, dai dai nan nurse ta shigo.
Cikin kulawa ta hau gwada ta tana mai tambayarta “ina da Ina ne suke yi mata ciwo?”

A hankali Jalilan tace mata
“Mai ya sameni?
Marata tana yi min ciwo.”

Cikin kulawa nurse d’in tace
“I’m sorry ma’am, kin yi loosing baby d’inki ne”

“L lo Loosing, me?”
Cewar Jalila.

Ganin kamar bata fahimceta ba ya sanya tace
mata
“Kin yi miscarriage!
Cikin jikinki ya fita.”

Da mugun k’arfi ta mik’e ta zauna sai kuma ta fashe da kuka!
Dai dai nan Mom ta shigo.
Tana ganin tana kuka tayi sauri ta k’arasa ta fara bata hak’uri
sai kuma ta juya ta rufe nurse d’in da fad’a, tana cewa
“Ba ance jinin ta ya hau sosai kar a d’aga mata hankali ba?
Shine amma lokaci guda zaki zo ki fara zuba mata wannan mugun labarin?
Asibitin gwamnati ya kamata ki koma ba private ba!
Tunda baki iya tausar patient ba.
Ai inda kin bari da mu da kan mu za mu gaya mata idan mun koma gida....”
Hakanan dai Mom ta wanke nurse d’in tass!! Ta inda take shiga bata nan take fita ba
dag nan tayi signing discharge papers taja Jalila suka nufi mota driver ya jasu…..

Ita dai Jalila in banda kuka ba abunda take yi…
har ga Allah bata son cikin nan ba taso ta haihu amma
kuma yanzu da cikin ya fita ta san tabbas ba abunda zai shiga tsakaninta da komawa gandun albasa!!
Sannan ta daina samun kud’i daga Mom da Auwal kenan har abada!
Amman kuma yadda Mom take lallab’ata sai ta d’an ji zuciyarta ta d’an yi sauk’i!
Maybe tausayinta take ji amma duk da haka ta san ba zai wuce na sati ba zata tarkatata!
Dan haka a take ta yanke shawarar nemawa kanta mafita..
Zata lallab’a Mom ta bata hak’urin abubuwan da ta dinga yi mata
Idan ta kama ma sai tayi k’aryar aljanune da ita tace mata su ne suke sakata yiwa mutane rashin kunya.
Ta samu dai Mom d’in ta ara mata ko da sati uku ne
daga nan ita kuma da ita had’a y’an kud’ad’en hannunta ta sake turawa Umma
a san abunyi ta auri Arshaad ko ta halin yaya ne da wurwuri cikin gaggawa!
Itafa wallahi yadda ta d’and’ana daular nan
to kuwa batajin zata iya minti uku a cikin gidan Baba!….

Tanata sak’e sak’e a ranta a haka suka iso gida!
Sai wani nonnok’ewa take yi gudun abunda Mom zata yi mata, amman suna shiga sai taji Mom d’in tace mata “ta tafi d’akinta ta huta
Coook zata kawo mata abinci yanzu.”

A hankali tace
“Na gode Mom”

Wani kalan murmushi Mom d’in tayi wanda Jalilan ta kasa ganewa.’Daganan Mom d’in ta juya ta nufi hanyar kitchen a ranta tace
“Yarinya kenan!
Sarai na san zaki iya yi mana bori, kice ba zaki tafi ba ki tada mana hankali
Kuma ko yanzu na san idan akai test a jikinki positive za a gani..
Ki jira nan da kwana uku
In sha Allah za ki san wacece Adama.”


GANDUN ALBASA
Tun da garin Allah ya waye Huda take kuka
Idan zaka titsiyeta ka tambayeta ba zata tab’a iya gaya maka menene tak’amemen abinda ya sanya ta kukan ba!
Ita dai ta san bata da nutsuwa
sannan a mugun tsorace take
amman tabbas ba wai shariyar Arshaad kad’ai ne dalilin tashin hankalinta ba.

Sakina da Khadija sun yi lallashin sun yi har sun gaji sun rabu da ita.

Hankalinta bai sake tashi ba
sai da k’awayenta suka zo
sannan mai makeup itama ta zo ta fara shiryata!

Tayi alk’awarin ba zata sake kiran Arshaad ba amman haka ta daure ta kirashi
wannan karan kam a kashe ma taji wayar tashi gaba d’aya
dan haka hankalinta ya sake tashi!
Ba abunda yafi d’aga mata hankali irin kar azo d’aurin aure yace ya fasa!
Ita gara ya fito ya fad’a mata gaskiya
akan yayi mata hakan...

Nasarawa gra.
A b’angaren Arshaad kuwa jiya ya gama shirya plan d’inshi
amman ga mamakinshi kamar wani ya gayawa Mammy bayan Magrib nayi ta shigo d’akin nashi ta kafa ta tsare!
K’arshema a d’akin a kan couch ta kwana tsabar bala’i.

Tun jiyan da ta shigo har yanzu k’arfe 10 bata fita ba!
Ko wanka ko brush bata yi ba, har gara ma shi yanata watsa ruwa saboda zazzab’in da yake jikinshi..
Yana lura da ita ko mik’ewa yayi ya shiga shiga toilet zai yi wanka ko alwalla sai taje bakin k’ofar ta lab’e mishi har sai ya fito sai kace wani wanda akace mata zai b’ace!
Dagashi har ita ba wanda ya samu bacci jiya
Idan ka gansu duk a gigice.
Ko da Aaima ta kawo musu breakfast ma ba wanda ya tab’a har yanzunnan
Tun jiyan da ta shigo har yanzu ba wanda ya cewa wani uffan a tsakaninsu.
Amman duk wani motsinshi idanunta na akanshi.
Ba abunda yafi d’aga mishi hankali kuma ya bashi mamaki irin yanda ta kasa tashi ko sallah tayi
Yanzu haka yana lura da yadda ta kasa zama mai kyau sai faman mutsu mutsu take yi
wanda ya tabbatar fitsari take ji amman gudun kar ta shiga ya gudu ta gwammace ta zauna a haka!.

Suna a haka Dad ya shigo cikin d’akin.
Yayi mamamkin ganinta a zaune amman sai ya d’auke kai kawai ya maida hankalinshi ga Arshaad, ransa a d’an b’ace yace
“Ka san fa k’arfe 11:30pm ne d’aurin auren, uban me kake yi a zaune a haka?”

A hankali yace
“Ina kwana Dad”

“Lafiya” kawai yace masa, daga nan ya nemi waje ya zauna kafin yace
“Mik’e maza, yanzun nan Aslam zai kawo maka kayanka”

A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya yanayin k’asa k’asa yana kallon Mammy wadda ta d’auke kai tana kallon gefe.
Mik’ewa yayi jikinshi ba kwari ya fad’a band’aki!
Ya kai kusan 20 minutes tukunna ya fito sanye da bathrobe a d’akin ya tarar da Aslam sanye cikin sky blue d’in rantsattsiyar shadda aikin gaban rigar white da d’an ratsin blue ya murza farar hula mai asalin kyau da tsada sai kyalli take yi da farin takalmi
hatta agogon hannunshi white ne. Yana rik’e da babbar rigarshi a hannu wadda take a ninke, k’amshinsa gaba d’aya ya cika ilahirin d’akin….
Suna had’a ido
ya sakar mishi murmushi
a hankali yace
“Ango”

Murmushi shima Arshaad d’in yayi sannan ya wuce jikin wardrobe d’inshi ya na mamakin ta yanda zai shirya a gaban waennnan body guards d’in!
Inner wears d’inshi ya kwasa
ya d’auki jakar kayan da yaga an ajjiye akan gadon ya juya ya wuce toilet.

Bai yi minti biyar cikakku ba ya fito!

Murmushi Dad yayi yana kallon shi yana mai jin wani sanyi a ranshi!
Kana ganinshi kaga Ango..
A hankali jikinshi a mugun sanyaye ya k’arasa gaban mirror ya d’an shafa mai sama sama a hannu da fuskar shi sannan da k’afa, ya fesa perfumes ya d’auko takalmin da ya fito da shi a jakar kayan nashi ya sanya…
Farar shadda ce k’all! Mai babbar riga sai bak’in takalmi hula da agogo..
Yana gyara d’aurin agogon suka ji knocking
Aslam ne ya juya ya d’an bud’e k’ofar dake a kusanta yake.
Da mamaki yake kallon Abba da Daddy
da Auwal a bayansu.
Dad Abba da Daddy duk ankon shadda ruwan goro light suka yi, aikin rigar ciki da babbar rigarsu kuma na kalar kayan amman dark sosai
Sai hulunansu zannah bukar
d’in da suka amsa sunansu ZANNAH bukar! Amman kowa da design d’inshi, takalmansu
kuma na fata kalar ruwan goro masu mugun kyau da tsada iri d’aya.
Yayinda Auwal ke sanye da maroon shadda shima ya murza zannah bukar d’inshi mai asalin kyau da tsada.

Cikin girmamawa Aslam ya gaida su Abba
Daddy ne yayi dariya yace
“Kaga yau har da mu a y’an sneaking a shigo estate ko?”
Murmushi kawai Aslam d’in yayi. Kallonshi kawai Abba yake yi…
Ya manta when last da ya ganshi da manya kaya,
ba k’aramin kyau yayi ba,
har ga Allah Aslam ba wai favorite d’in Granpa bane kad’ai Har da shima Aslam ne favorite d’inshi!
Kawai dai shi d’in baya nunawa ne
Yaron akwai hankali da nutsuwa da sanin ya kamata
“Ina ma inama!
How i wish......”
Ya fad’i hakan a ranshi
sai kuma yayi saurin kawar da tunanin ya juya suka fara gaisawa da Dad.
Daga shi har Daddy ba wanda ya kalli ko inda Mammy take
Kuma sarai sun ganta dan har had’a ido suka yi da Abba!
Hakan kuwa ba k’aramin sake ingizata yayi ba
Tabbas yau sai ta nuna musu ta isa wallahi!

Chap!! Arshaad ya shirya dan haka suma duk suka mik’e
dan har an fara jera musu kira
Abokanan su sun fara zxuwa venue d’in..

Ba tare da Mammy ta motsa ba tace
“Arshaad!”

Sai da ya sauk’e ajiyar zuciya ya lumshe idanunsa ya bud’e tukunna ya juyo yace
“Na’am Mammy”

Mik’ewa tayi tsaye tace
“Koma ka zauna”

Sannan ta dubi su Dad waenda suke kallonta gaba d’ayansu tace
“Kuna iya wucewa
ku tafi!
D’a dai ni na haifa ko?
To wallahi tallahi ba wanda ya isa ya yi mini iko da shi!
Da kuka shigo kuka wani banzatar dani kamar baku ga mutum ba saboda ban kai ba
har kai Abba! Kalla Auwal shima
Aslam ne kawai ya gaidani ya kulani a kaff d’inku
saboda ka riga ka nuna musu bani da mutunci bani da daraja a idanunka!
To
Yanzu ni kuma zan nuna muku na isa dan wallahi ba za a d’aura auren nan ba kaji dai na rantse!”

Murmushin takaici Dad yayi
kafin yace
“Dole ba wanda zai kulaki mana Rukayya!
Saboda kema baki kula wanda ya kamata ki kula ba,
ko kin gaida ni tunda na shigo?”
Ganin ta kauda kanta gefe ya sanya kawai ya girgiza kai kafin yace
“Kaga Arshaad wuce mu tafi!
Zan ga wanda zai hanaka fita yau”

Mammy ya kalla, suna had’a ido tace
“In dai kana neman albarka a auren nan to ka sani ba zan tab’a saka maka ita ba!
Kuma wallahi Arshaad in dai ka fita a d’akin nan
to ban yafe maka ba!”

Da k’arfi ya runtse idanuwanshi yana ji kanshi na mugun sara mishi.

A zafafe
Dad ya yunk’ura zai yi magana

da sauri Daddy ya katseshi ta hanyar cewa
“Dan Allah dan Annabi ka kyaleta,
Uwa ba abar wasa bace ba!
Dole Arshaad da Huda suna buk’atar albarka ta
Dole.”
Yana gama fad’in haka ya juya ga Mammyn yace
“Mammy mu tsaya mu fahimci juna, wannan maganar bata tasoba.
Ki duba shi kanshi Yaron naki mana za fa ki cutar dashi saboda son zuciyarki
sannan da ita kanta Hudan,
babufa abu mafi gorantawa a rayuwar y’a mace
kamar azo aurenta a fasa!..”

Cikin katseshi Mammy
tace
“Yi mini shiru Yusuf!”
Sai da Daddy da Auwal suka d’an zabura jin yanda ta kirashi .
Bata damuba taci gaba
“Babu maganar sulhu fa a tsakaninmu!
Maganace na riga na yita na gama, babu kuma uban wanda ya isa ya sanya ni in chanja wallahi!”
Cikin tsiwa da masifa tace
“Kuma kar ka wani ce mini In duba rayuwar wata Huda dan babu abunda ya shafeni da ita!
Allah Ubangiji yasa a yi ta mata gori a had’a har da kyama da hantara daganan har k’arshen rayuwarta wannan ba damuwa ta bace ba.”

A hankali Aslam ya lumshe idanuwanshi.
Ba tare da Abba ya kula kowa a cikin su ba kawai ya juya ya fita, da sauri Aslam ya bi bayanshi.

Takawa Dad yayi ya tsaya a gabanta sannan yace
“Rukayya bani da ishashshen lokaci!
Ki nutsu ki shiga hankalinki kiyi abunda ya dace, for the last time ina mai shawartarki
ki ajjiye wannan haukar ki bari a d’aurawa Yaron nan aure.”

Cikin katseshi ido cikin ido ta kalleshi kafin tace
“Yahaya! Ko da ace ka bar nan ka tafi kai kad’ai ba tare da Arshaad ba
Wallahi muddin ka d’aura mishi aure da Huda wallahi tallahi billahilazim sai na tsine mishi!”

Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauk’e kawai ba tare da yace mata uffan ba ya juya, har ya kai bakin k’ofa
sai kuma ya juyo yana kallon Arshaad wanda shima shi d’in yake kallo
Wani mugun tausayinshi ne ya lullub’e shi lokaci guda, a hankali yace masa
“ka zauna, kar kaje koina bara muje mu dawo .”
Yana gama fad’in haka ya juya ya fita, su Daddy ma suka bishi a baya.
Abba ko Aslam bai tsaya jira ba ya shiga motarshi suka yi gaba tare da su Shuraim, dama suna ciki anan suka barsu.
Aslam na shrin shiga motar shi shima yabi bayan Abba su Dad suka fito
“Wuce mu tafi masallacin”
Haka kawai Dad yace mishi daganan kowa ya shiga motarshi sukai gaba.

Aslam ya dad’e a tsaye so yayi ace ya bi bayan Abba
dan ya san definately gida ya koma, saboda yaga yadda ranshi yake a b’ace!
Ga shi daman shima so yake ya zille maybe he can use this as an opportunity.

Har zai bishi sai kuma kawai ya yanke shawarar bin bayan su Dad d’in.
Da kyar ya iya tada motar dan yafi minti goma a ciki a zaune bayan ya shiga d’in, daga
k’arshe dai ya tada motar ya fice daga estate d’in…..
A hankali yake driving, babu
nisa sosai dan haka mintuna k’alilan ne suka kaishi masallacin.

Da mamaki yake kallon motar Abba a parke a harabar masallacin!
Kokwanto ya hau yi akan anya kuwa motar tashi ce?
Sudais da ya gani ya nufo shi ne ya tabbatar mishi da Abban nan ya yo..
Chan kuma ya hango suna gaisawa shi da su Madu
cikin tsananin farin ciki da nishad’i.
Auwal ne ya dafa shi dan haka yayi saurin juyowa
Kwata kwata in banda k’unci da firgici ba abunda ya hango a shimfid’e kan fuskar Auwal d’in!
Yana mamakin abunda ya sanyashi a wannan yanayin yaji yace
“Aslam dan Allah idan sun zo kace......”
“Ku wuce muje mana!
Ya naga kun tsaya anan?”
Muryar Dad ta katsesu.

Kallon Auwal d’in yayi ya kalli Dad sannan yace
“Ok”
Kawai, ya juya ya yi gaba….
Duk taku d’aya ji yake kamar yana kusanta kanshi da kabarinshine!
Tabbas badaban Mommy ta rok’e shi akan ya zauna a garin nan ba to da tuni baya nan!
Babu yadda bai yi da ita ba d’azu amman nan ma
furr! Ta ki yarda, ta nace
ta tilastamishi dole sai da yazo wajen nan!
He might look calm
but tabbas ya san ba lalle k’afafuwan shi su iya fitar dashi daga masallacin nan ba!
Wannan wacce iriyar k’addara ce?
Mai yasa yake jin hakan har yanzu?
Mai yasa yake jin haka?
Garin yaya ya bari hakan take faruwa da shi…..?
A hankali yaji Abba yace
“Aslam”
Firgigit! Haka yayi
hankalinshi ya dawo daga duniyar tunanin daya tafi, sai
a sannan ne ya ga yana daff da yin karo da bango ashe,
da sauri ya ja burki!
Sannan ya juyo da kanshi yana kallon Abba wanda yake matsowa daff da shi sosai.

A hankali ya kama hannunshi ya d’an jashi gefe..

Da d’an murmushi akan fuskarshi yana mai kallonshi sannan ya fara magana
“Watak’il yau in yi maka laifi!
Amman dan Allah Aslam ko menene ya faru karka bad’a mini k’asa a ido”

Da mamaki yake kallonshi
zuciyarshi tana dukan uku uku!
Dan a take a yanzun tunani d’aya ne kawai ya fad’o mishi
daga jin furucin Abba na yanzun!
Da mugun sauri ya fara kokawa da zuciyar shi yana k’ok’arin kawar da tunanin
dan jiya ma ba k’aramin artabu ya sha ba! Ko rintsawa bai yi ba
ata dalilin false hope d’in da Mommy ta sa ya d’aurawa kanshi.

Dafa shi Abba yayi sannan yace “mu shiga”
Yana gama fad’in haka ya wuce ciki.
Da kyar Aslam ya iya jan k’afafuwan shi, ya shiga ya nemi waje ya zauna kusa da Abba daff da liman da su Daddy Opposite Auwal.

Kana ganin Auwal tashi d’aya zaka gane bashi da nutsuwa kwata kwata!
Ko zaman kirki ya kasa yi a wajen, sai zaro waya yake da alamun kira yake yi
amman kuma ba a d’auka!
A fili sannan da k’arfi
yace “damn it!!”
Sannan yayi jifa da wayar tashi
wanda hakan ya janyo hankulan mutane kanshi….
Suna had’a ido da Daddy ya zabga mishi harara.
A hankali ya sunkuyar da kanshi ya d’au wayar sannan yace
“Sorry”.
Hannu Dad ya mik’a mishi alamun ya bashi wayar!.
Ba musu ya mik’a mishi
shi kuma ya sa hannun ya karb’a ya saka ta a aljihu
daga nan aka fara gabatar da d’aurin aure……..

Auwal k’ok’ari

Download complete TXT · Novel page