Ajiya A Duhu Book 2

Chapter 10 of 24

sannan suka nufi gida shi da drivern sa, AS ma tashi motar ya shiga ya nufi nasu gidan.....
      Lokacin da AA ya isa gida tuni Maanal ta jima da hutawa. Dan har taya Oum girki tayi kasancewar rigimar Abah ta tilasta mata komawa kan duty. Bayan sun kammala ne suka nufi ɗaki yin salla. Ana idarwa tai zaman yin karatun Alkur'ani Oum kuma na lazimi har akai isha'i sannan suka fito. Sashen Abah Oum ta tafi, hakan yasa Maanal zama ta shiga duniyar tunanin nata na fama.
        Gaba ɗaya kwanakin nan hankalinta ba'a jikinta yake ba. Dan al'amarin su Mamy yayi matuƙar jijjiga mata zuciya. Dauriya kawai take tana danne komai dan kar kowa ya fahimta musamman AA da Oum. Hatta a office yau dauriya kawai take da ƙarfin hali. Dan tasan idan kowa bai fahimci halin da take ciki ba shi zai fahimta. Shiyyasa ma ta toshe duk wata hanyar kasantuwarsu a waje guda a gidan kafin yau, yayinda shi kuma ta fahimci yana fushi da ita akan hakan duk da dai yanda suka kasance yau a office kamar ya huce...
        Bayan wucewar Oum zaman shurun ya isheta, gashi tana son yin waya da Didi Shahidah. Tasan kuma dole ta nemi inda zata kawaice idanun mutane kodan abinda zasu tattauna. Fitar Oum zuwa sashen Abahn ya bata damar ɗaukar novel ɗinta da glasses ta yafa ƙaramin veil a kanta batare data ɗaura ɗan kwalin atafar doguwar rigarta ba ta ɗauka ruwa da popcorn dake ajiye a dining. Compound ta fito, sai da ta gama bin ko'ina dake ƙwanyar da hasken security light da kallo sannan ta nufi hanyar inda AA ya taɓa kaita kwanaki dake da swimming pool, dan tasan can ɗin ma sharr ne da hasken tamkar rana. Shigarta wajen ya sakata lumshe idanu saboda busowar wata ni'imtacciyar iska mai ƙanshin furanni a cikin hancinta, murmushi tayi, zuciyarta na sake zumuɗin ƙarasawa gaban ruwan. Sai dai me tana ɗaga ƙafa dole ta koma ta tsaya cak, sakamakon saukar muryar Mamy cikin kunneta. Magana take a kausashe, cike kuma da bada umarni. Kai kawai Maanal ta girgiza cike da takaici zata juya dan bama ta buƙatar jin baƙaƙen maganganun da Mamyn ke faɗa akan Oum, amma mi sai taji Muryar AA a bazata yana faɗin, “Amma Mamy yanzu baƙya ganin hakan zai zama wani abu daban idan nace yarinyar nan ta dakata da zuwa Company na. A yanzu fa Maanal matata ce, a ganina ta wuce dukkan wata alfarma kuma sai iko ma da take da shi akan komai na. Kema fa gashi faɗa kike kullum akan Abah, dan na tabbata da ace baku haɗa miji da Oum ba amintarku har abada bazata taɓa rawa balle har kukai ga wannan matakin. Duk da dai daga ɓangarenki ne aka samu rashin fahimtar, dan har zuciya wlhy Mamy kina a zuciyar Oum da girma da daraja. Ni dai Mamy bazan gaji da baki haƙuri da faɗa miki gaskiya akan wannan al'amarin ba. Dan ALLAH ki ajiye makamanki akan Oum, bana son lokaci yakai ƙurewar da wani a gidan nan zai ji wani abu akan hakan, musamman sauran ƴan uwana da Abah. Sannan batun aurena da Maanal kiyi haƙuri, hakan wani hukuncine na UBANGIJI dake rubutacce a ƙaddararmu, kodan yanda abubuwa suka faru a baya, da yanda suke a yanzu yakamata mu fahimci al'amarin nan fa mai girma ne.....”
         “Hakane ubana”.
     Mamy ta faɗa cike da hasala da gatse kuma. Murmushi AA yayi na tsantsar damuwa. Sai kuma ya ɗan kalleta da idanunsa da suka kaɗe sosai. “Kiyi haƙuri idan kalamaina sunyi nauyi da yawa Mamy, har abada ni mai biyayya ne a gareku ku duka ukun nan. Sannan zan bama kowanneku kariya daga cutarwar ɗan uwansa.....”
      “Kai ka sani kuma wannan. Na baka kafin nan kafin fara azumi kazo min da cikakken bayani akan ma'anar Maawad kamar yanda na faɗa maka, tare da dukkanin takardun kadarorin ka...”
          “Mamy ki gafarceni, wlhy ban san yanda zan iya tunkarar Oum na amshi abubuwan nan a hannunta ba”.
      “Okay haka kace? Toni zan tunkareta na amsa tunda ba uwata bace ba ai”. 
     “Mamy Please....”
Ko kallonsa batai ba ta wuce fuuu. Ja baya Maanal tai ta laɓe a ɗan lungun da akai adon wajen. Dan bata buƙatar Mamyn ta ganta. Zuciyarta kuwa wani irin zafi take mata, matuƙar tausayin AA na ratsa mata ɓargon jiki. Kenan shi Mamy ta bayyana masa ainhinta, tana kuma amfani da damar tana tursasa masa yin abubuwa dan tasan yanda Oum keda muhimmanci a garesa. Murmushi ta saki mai matuƙar ciwo, sai kuma da sauri ta share hawayenta ta bar jikin bangon tamkar yanzu ne take shigowa saboda jin ƙarar taku alamar shine zai fito. Bayyanarta ya sashi tsayawa cak, itama sai ta tsaya ɗin tana kallonsa, dan duk yanda taso basarwa ta kasa hakan. Tausayinsa ne ke neman fin ƙarfin zuciyarta.
       AA da ganin Maanal ɗin ya sashi jin shock wani irin tsinkewa zuciyarsa tayi, addu'a yake ALLAH yasa yarinyar nan bataji tattaunawarsa da Mamy ba. Dan bazai taɓa son hakan ta kasance ba sam. Cikin son basarwa ya shiga haɗiye nannauyan abinda ke tsaye a maƙoshinsa ya daidaita fuskarsa. Sai kuma ya cigaba da takowa a hankali har zuwa gabanta. Kayan hannunta ya ɗan zubama ido, kafin ya janye ya maida kan fuskarta. Cikin tausasa murya da ƙanƙanceta ya furta, “Daga ina?”.
       “Sama”.
   Ta bashi amsa.
Murmushi yayi a karo na farko, tare da lumshe idanunsa ya sake buɗewa a kanta. “Bakin nan dai bazai daina ma mutane baƙar magana ba ashe?”.
       Samun kanta tai da ɗan sakar masa murmushin itama sai kuma ta kauda kanta gefe tana mai laɓe bakin kaɗan. Shima murmushin ya sake saki dan nata murmushin wani sanyi ya saukar masa a zuciya. A hankali kuwa ya saki ajiyar zuciyar tare da matsowa gab da ita. Matsawa tayi baya tana mai waro masa idanun kaɗan, irin na (lafiya dai?) shima sai ya bita. Danganewa tayi da bango, hakan sai ya bashi damar dafe bangon da hannu ɗaya ya mata rumfa da jikinsa. Gaba ɗaya ta jita kamar a keji, ga wani irin watsal-watsal da zuciyarta ke mata, sassanyan ƙamshin turarensa kuwa na saukar mata da kasalar jiki da gaɓɓai. Shima ɗin wani irin haurawa yaji jininsa nayi a saman kai, a hankali muryarsa cike da taushi da nauyi ya furta, “Bestie, please give me a hug mana”.
         Sosai zuciyarta ta harba, duk yanda taso daurewa ta kasa, idannunta ta ɗago slowly ta sauke akansa, shima kallon nata yake, sai taga kamar idanunsa na ƙyallin hawaye, duk da tasan wannan normal ne a garesa, dan in har ma yana cikin farin ciki sosai idanun na fari tas-tas zakaga tamkar kuma an bisu da mai ne. Amma na wannan yanayin babu abinda take hangowa a cikinsu sai tsagwaron damuwa da ɓacin rai........✍️


_To bazawarin Huznah dai kazo da bidia, runguma kuma? Gaskiya wannan salon cin amanar Abah ne kawai 😂_




*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. 🙏_*

*09032345899*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
[23/04, 4:14 pm] Leematu: *_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣5️⃣


______________

........Samun kanta tai da sakar masa sassanyan murmushi, tare da buɗe hannayenta a hankali alamar bashi damar daya buƙata.
        Idan yace zuciyarsa bata nema tarwatsewa ba a wannan gaɓar yayi ƙarya, amma wannan ba lokacin tunani ko nazari bane. Duk da ya mata tsaho sosai cike da jin illahirin jinin jikinsa na narkewa ya wani irin shigewa jikin nata ya rungumeta tsam har sai da ta ɗan rumtse idannunta. Sosai tausayinsa ya shiga marmashe mata illahirin zuciya, dan kasancewar kanta kwance a ƙirjinsa tana iya jin yanda zuciyarsa ke bugawa da sauri-sauri, ga hucin numfashinsa na sauka a kunnenta da zafi-zafi. Sun kai tsahon mintuna biyar a haka, ita harma ta fara jin ƙafafunta sun mata nauyi. Sai taji shima kamar ya mata nauyin. Muryarta na wani irin komawa sanyi ƙalau ta ce, “You're sleepy?”.
         Maimakon bata amsa sai ya girgiza mata kai kawai. Sai kuma ya miƙe tsaye sosai ya ɗagota itama daga ƙirjin nashi ta tsaya da ƙafafunta. Fuskarta ya kafe da sassanyan kallo, ita sai ma ya bata kunya. A hankali ta risinar da idanunta ta koma kallon yatsun ƙafarsa dake fes-fes cikin tattaunsan baƙin takalmin daya sanya. Hannu yasa ya ɗago fuskar tata ta hanyar kamo haɓarta cikin hannunsa. Maimakon ta kallesan kamar yanda yake buƙata sai ta lumshe idanun nata. Murmushi ya saki kaɗan, cike da son tsokanarta ya ɗan ranƙwafo ya dai-daita fuskar tasu numfashinsu na sauka a fuskokin juna. Cike da shauƙin yanayin nasu ya  furta, “Besty!”.
          Kasa amsawa tayi, dan gaba ɗaya jinta take kamar ta nutse a cikin ƙasa. Shima fahimtar bazata amsa ɗin ba sai ya sake sakin murmushi irin mai maƙalewa a gefen bakin nan. Cikin maida muryar tasa ƙasa-ƙasa sosai tamkar mai raɗa ya ce, “An bani Hug saura kis....”
      Ai baima kai ga ƙarasawa ba ta waro idanunta gaba ɗaya warrr a kansa. Sai dai kasancewarsu gab da juna ya sata maidawa kuma da sauri ta lumshe tare da janye jikinta baya tabar wajen da sauri. Dariya sosai ta bashi, amma sai baiyi ba ya saki ɗan murmushi yana miƙewa tsaye da ƙyau ya zuba duka hannayensa a cikin aljihun farin jeans ɗin wandonsa ya bita da kallo. Sai da ta zauna batare da ko waiwayensa tayi ba ta buɗe novel ɗinta ta sanya eyeglasses a idonta sannan ya shiga takawa a hankali zuwa inda taken..

     ★ Ya jima tsaye a inda ta barshi yana kallonta, kafin ya tako shima a inda taken. Kujerar dake facing ɗinta ya zauna, batare da yace mata komai ba ya zuba mata idanunsa kawai hannayensa duka harɗe a ƙirjinsa. Yanda ya zuba mata idanun nasa masu kaifi ya sakata daburcewa ta daina fahimtar abinda ma ta fara karantawa. Amma a zahiri bazaka taɓa tunanin a rikicen take ba dan ta maze ƙwarai da gaske kamar bata san da shi a wajen ba. Dai-dai nan kiran Oum ya shigo wayarsa. Kasancewar ringing ɗinta na musamman ne ya saka shi dakatawa daga faɗar abinda yay niyya ma Maanal. Wayar ya ciro daga aljihu yana gyara zamansa da ƙyau. Sai dai idanun nasa har yanzu a kanta tamkar ya samu television ɗin kallo.
    Cike da tsokana ya furta, “Assalamu alaikum uwargidan Abah har a ALJANNA”.
     Murmushi Oum tayi daga can. Cike da jin shauƙin ƙaunar Autan nata tace, “ALLAH to ya tabbatar Autan Oum ɗinsa, sannan tare da ku Bestyn bestynsa.”
     Murmushi AA yayi mai faɗi, sai kuma ya ɗan saci kallon Maanal a miskilensa ya furta, “Shike nan dai Oumna kin rama 1-1 kawai.”
    Dariya sosai Oum tayi, sai kuma ta ce, “Dama zance kazo kaci abinci gamu nan zuwa tare da Abahn ku zaici abincin tare damu”.
         “I'm so happy, Oum! gamu nan”. Daga haka ya yanke batare da Oum ta fahimci inda (gamu nan) ɗinsa ta dosa ba. Yana ajiye wayar ya zare book ɗin Maanal tare da ɗaukar kwalin popcorn ɗin nata da goran ruwan ya ce, “Oya let's go Oum na kira”.
     Komai bata kawo a ranta ba ta miƙe kawai. A jere suka fito duk da ba wata hira suke ba. Sai da sukazo fitowa ne cike da neman magana ya gwargwaɗa mata magana a kunne. Da sauri tai gaba zata barsa saboda kunya, yayinda murmushi ya ɗan ƙawata fuskarta batare data shirya hakan ba. Shima murmushin yake yi dan haka kawai murmushin nata ya saka shi jin nishaɗi. Ai cak Abah da Oum dake fitowa daga sashensa suka tsaya. Galala Abah ya saki baki yana binsu da kallo, yayinda Oum ta gimtse dariyar dake neman suɓuce mata da ƙyar. Suna tsaye kamar gumaka AA da Maanal suka shige sashen Oum batare da su sun ma farga da su ba. Gyaran murya Oum tayi kaɗan, hakan ne yasa Abah maido da idanunsa kanta, harrarta yayi. Daƙyar ya iya gimtse dariyar tayi gaba tana faɗin, “let's go tunda gasu can.” bata jira cewarsa ba tai gaba tana murmushin data kasa riƙewa. Suna zuwa ƙofar sashen Oum Maanal ta zame tai hanyar baya ta kitchen ita adole bata son a gansu tare da AA. Bata san wanda take gudun su gansun ba sun riga sun gansu. Samun su Inte na haɗa abincin da zasu kai dining sai kawai ta shiga tayasu.
         AA kam daya shige shi kaɗai dariya ma ta bashi. A ransa yace (Magulmaciya, kina so kina kaiwa kasuwa). Fawzan kawai ya samu a falon yana kallo. Zama yay kusa da shi. Fawzan ya dubesa da ƙyau, sai kuma ya ɗan matsa da fuskarsa yana shinshina shi. Harararsa AA ɗin yayi, ciki-ciki ya ce, “Miye?”. Da ƙyar Fawzan ya gimtse dariyar dake cinsa, cikin ɗaure fuska shima kamar yanda AA ɗin yayi ya ce, “Yada tsarguwa haka Malam, ka bari na gama tantancewa mana. Naji ne kana ƙamshi kamar na turaren Lilly.”
      Irin ɗan waro idon nan AA ɗin yayi, ya ce, “Kai yaya Fawzan ido ka koma samin?”.
     “Oh da mikake tunani? Kasan dai bazan bari aci amanar Abah ba. Kuma zanma ƙanwata garkuwa”.
    Rasa ma abin cewa AA yay, sai kawai ya zubama Ya Fawzan ɗin ƙasaitattun idanunsa. Sosai Fawzan ya kwashe da dariya, dan yasan ya gama kaishi maƙura kenan. Ai idan kaga Auta ya rasa abin faɗa to yakai maƙura kenan...
     A haka Oum da Abah suka shigo suka samesu. Gaishesu sukayi, suka amsa Oum na faɗin, “A'a ina Baby na kuma?”.
     Fawzan ne ya bata amsa da, “Ai tunda na shigo ban gantaba Oum, maybe tana sama ko?”.
    Kai Oum ta jinjina tana jiran AA ya bada amsa, amma ya basar abinsa tamkarma baijisu ba. Sosai shima Abah ke satar kallon AA ta gefen ido ransa fal mamakin, dai-dai nan Maanal da su Inte suka fito a kitchen. Dariya taso kama Oum, amma ta danne da ƙyar idonta akan Maanal ta ce, “Oh ashe kina kitchen Auta”.
      Kai Maanal ɗin ta jinjina tana murmushi da satar kallon AA daketa latsa waya kanshi kwance a kafaɗar Fawzan hankalinsa kwance like baima san mike faruwa ba. Juyawa tai tana gaida Abah dayay Zuru yana kallonsu su duka. A ransa ko faɗi yake (Aiko zakuci ƙaniyarku ku duka) a zahiri kam amsawa yay cike da kulawa. Daga haka suka ɗunguma dining cin abinci.....
      
        A nutse suke cin abincin, yayinda Oum da Abah ke ɗan hira Fawzan kuma da Maanal. AA kam hankalinsa nakan waya komi yake oho masa. Abincin ma bawani ya maida hankali bane a cinsa. Wayar Oum ta zare daga hannun nasa, yako kalleta a shagwaɓe. Harararsa tayi tare da nuna masa abinci tana faɗin, “Ni tunda ka tashi ciwon nan kake neman maida abinci abokin gabarka Auta. Oya maza yanzu naga plate ɗin nan, in ba haka ba ɗura zan maka”.
       Dariya Fawzan yayi, Maanal ma ta kasa riƙe nata murmushin saboda ganin yanda AA ɗin yay da fuska. A dai-dai nan Mamy ta shigo sashen da sallama. Gaisheta Fawzan yayi bayan duk sun amsa mata sallama, tare da faɗin, “Naje sashen yaran nan sukace kina wanka”.
     Cikin danne takaici Mamy ta ce, “Eh sun faɗa min”. Ledar hannunta ta ajiye a gaban AA da tunda ta shigo ya maida hankalinsa ga cin abincinsa. Maanal kam sai satar kallon Mamyn take bayan ta gaisheta itama. Ajiye ledar ya saka AA ɗagowa ya kalleta a karo na farko, hakama su Abah kallon ledar suke. Murmushi ta ƙawata fuskarta da shi, tare da juyawa tana kallon Oum. “Bara na aiki ɗanki gidan Aunty tunda dai yaji sauƙi, na manta shaf har drivers ɗin gidan sun tafi gashi da sassafe zasu wuce lagos”.
       Fuskar Oum babu wani damuwa ta ce, “Eh ya kamata kam a kai mata su a daren nan. Auta sai ka maida hankali ka gama ko kar dare yayi, duk da dai kai ba tsoron fitar daren kake ba”.
     Kansa kawai ya jinjina batare da yayi magana ba. Dan shi yasan babu wani saƙo. Mamyn ce ta kafa masa sharaɗin zuwa yaga Nuratu ya kuma bata kayan da zata bashi yace inji shi wai Ramadan basket. Zama Mamyn tayi suka cigaba da hira da Oum da Abah, sai kawai AA ɗin ya miƙe badan ya kammala cin abincin ba, dan zuciyarsa gaba ɗaya jinta yake a ƙuntace, amma miƙewar da zai yi suka haɗa ido da Maanal sai wata dabara ta faɗo masa. Guntun murmushin iya shege yayi, cike da shagwaɓa ya dubi Abah. “Abah dan ALLAH ka bani aron ƴarka ta rakani tsoro nake ji”.
      Atare gaba ɗayansu suka ɗago suna kallonsa, ya sake narke fuska kamar zai yi kuka. “ALLAH Abah da gaske nake”. Ai kasa daurewa Fawzan da Oum sukai suka sanya dariya. Abah kansa da ƙyar yake iya danne tasa dake neman kufcewa. Maanal kam baki da hanci tama saki tana kallonsa, yayinda Mamy ta cika tayi fam fa takaici har hakan ya kasa ɓoyuwa a fuskarta. Cikin dariya Oum ta ce, “Please Abansu a taimaka mana, ai bazasu daɗe ba yanzu zasu dawo”. Fawzan ma yace, “Abah ayi haƙuri ta rakashi kada yay mana kuka ko kura ta cinyeshi a hanya dan tsoro. Kasan Besty da Besty duk tsanani tare suke zuwa aika”.
     Kai Abah ya girgiza, tare da faɗin, “ALLAH ya shiryeka Ajwaad. Jiba yanda ka wani ɓata fuska like zakama mutane kuka. Shike nan kuje, amma ina nan ina jiran dawowarku, idan kuka daɗe kwanakin zan ƙara”.
         “Thanks You sweet Abah”.
     AA ya faɗa a hankali. Nan ma kan Aban ya girgiza kawai, yayinda Oum ke faɗin, “Baby tashi ku tafi kinji”.
Ji Maanal tayi kamar ta nutse dan kunya. Duk da kuwa a shekarun baya hakan ba komai bane a tsakaninsu. Dan ko tana gidansu aka aikesa zaije yace tazo ta rakashi kida cikin anguwa ne. Haka

Download complete TXT · Novel page