Ajiya A Duhu Book 2

Chapter 9 of 24

ya ce, “Ɗan baƙin ciki, idan fa bamuyi da gaske ba guy ɗin nan sai ya kankane komai ta yanda ko kallonmu bazata ringa yi ba balle ta tuna munrayi tare anan matsayin abokan aikinta. ALLAH dai yasa ta manta da abinda ya faru baya. Ni damuwata ma randa ta kamamu muna gulmarta ni da Teemo da Hafiz”.
       Caaa kowa yay yana faɗar albarkacin bakinsa. Sai dai duk suna cikin fatan ALLAH yasa Maanal ta yafe musu sudai. Daga haka suka ɗora da gulmar ashe Maanal ɗin tasan abinda ta taka akwai alaƙa tsakaninta da boss shiyyasa take musu girman kai. Gashi nan cikin ƙanƙanin lokaci tazo ta samesu ta kuma shallake abinta matsayin ogarsu. Kai kai wannan al'amari da taɓa zuciya yake..........✍️



_😀 ALLAH ya shirya yan gulma a duk inda suke🤣😂_

      

*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. 🙏_*

*09032345899*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
[22/04, 3:30 pm] Leematu: *_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣3️⃣


______________


......A office ɗin Maanal kuwa sai da taima Yaqub magana sannan ya ɗan saki jiki suka ƙarasa aikin a ɗan gurguje saboda lokacin meeting ɗinsu yayi. A tare da shi suka fita a office ɗin. Hakan yay dai-dai kuma da sakkowar AA daga sama, da'alama daga office ya fito. Bayansa CFO ce da Bussines Director. Da alama suma wani abun zasuyi mai muhimmanci, dan elevator suke ƙoƙarin nufa. Wani irin zuba musu ido AA yayi ɗan guntun sakewar dake fuskarsa na ɓacewa. A ransa ko ayyanawa yake, (Yarinyar nan bazata fita sabgar yaron nan ba ko?). A zahiri kam yanda ya wani ɗauke kai sai ka rantse baima gansu ba. Amma ita Maanal tana gannin kallon banzar daya watsa mata na fisha ta ƙasan idon. Amma itama sai ta wani basar kamar bata gansu ba ta nufi hanyar conference room tana cigaba da wayarta. Dan magana take da Amrah data kirata suna fitowa.
     Shi dai Yaqub ɗan matsawa yay ya gaishesu. CFO ce kawai ta amsa da Bussines Director. Boss yi yay kamar baiji ba ta shige elevator. Kasancewar shi Yaqub ba kallonsu yake ba bai san yaya boss ɗin yake ba. Sai da suka shige ƙofar ta rufe sannan shima ya nufi conference room ɗin.....
 
_________★

       Rafeeq na zaune Nuwaira a jikinsa tana masa hira amma shi hankalinsa na wani tunani daban. Maganar zuwan Najma Abuja ce keta masa kai-kawo a rai. Kodai zai yi amfani da wannan damar ya sata tai masa wani aiki. Wani gefe na zuciyarsa kuma na farin ciki da fatan tabbatuwar abinda yake hasashe a tsakanin Najma ɗin da Fawzan. Dan auren wani ƙarin GARKUWA ne ga aunty Babba bayan na AA da Maanal. Tun jiya yake son yin waya da Maanal, dan yana son su tattauna wasu abubuwa masu muhimmanci sai dai bai san a yanda zata kalli al'amarin ba. Sannan alaƙarsa da ita kafin aure zai iya saka AA yaji wani abu a ransa idan yaga kiran duk da yasan har abada Ajwaad bazai kawo mummunan abu a garesu ba, amma yana da ƙyau ya kiyaye. To amma a yanzu batun Najma sai ya zaburar da shi, a ganinsa hakan wata hanya ce mai sauƙi da saƙon da yake so zai isa ga Maanal ɗin dan ita kawai yake so a wannan gaɓar tasan hakan saboda ya yarda da ita ɗari bisa ɗari, ya kuma gamsu da tarbiyyarta da soyayyar da takema ƴar uwarsa, soyayya ce irin ta ɗa da mahaifi.....
       “Babie!”.
  Nuwaira ta kirashi a cikin kunne cike da shagwaɓa. Kallonta yay da sauri, sai kuma ya sauke ajiyar zuciya tare da sakar mata murmushi ya sake jawota jikinsa. Hancinta ya kama ya ɗan ja. “Kefa yarinyar nan shagwaɓaɓɓiya ce. Minene kuma?”.
     Baki ta ɗan tura masa. “Bakai ne ka tafi tunani ba inata kiranka bama ka jina. Minene ke damunka wai? Ina lure da kai tun jiya baka da sukuni”.
       Sake lakace mata hanci yayi. Tare da faɗin, “Tunaninki nake fa”.
   Tai murmushi mai ƙayatarwa. Duk da tasan ba hakan bane cike da farin ciki tace, “Godiya nake Babie. ALLAH ya ƙara mana farin ciki da kwanciyar hankali”.
      “Amin my angel, harma da soyayyar juna”. Ya faɗa yana ƙanƙameta a cikin jikinsa. Wata irin soyayyarta na ratsa jini da ɓargonsa. A tabbas har randa aka ɗaura masa aure da ita zuciyarsa Maanal take so, amma ganin halin da suka samu AA ya sake sakashi ɗaukar ɗamarar yaƙi da zuciyarsa akan sadaukarwarsa. Dan ya sake tabbatar da AA ya fisa buƙatar Maanal. Shine kuma ya cancanci samunta ɗin. Koda ya shigo ya samu Nuwaira a ɗakinsa matsayin mallakinsa baiyi wani yunƙuri ko tunanin zasu sami juna ta sauƙi ba, sai dai kuma labarin ya canja saboda karfin tasirin nasihar iyayensu a garesu, gashi shi kuma yana a cikin wani hali na buƙatar abokiyar rayuwa. Cikin ƙudirin samawa kansa sauƙi kawai ya yarda ya tunkareta, sai dai a lokacin da komai ya kankama sai labarin ya canja, dan tamkar ya shiga sabuwar duniya ne da zazzafar soyayyarta. Na biyu haƙurinta da biyayyarta, Nuwaira bata da kwaramniya, ga sauƙin kai da kyakkyawar fahimta. A ɗan kwanakin da suka samu tare ya fahimci hakan sai soyayyarta ta ƙara tasirantuwa a zuciyarsa. Dan haka yake baje kolin amarcinsa yanda ya kamata, itako tana nuna juriya da dattako..
     Ɗaukarta yay cak ya nufi bedroom. Zizzilewa ta farayi cikin dariya tana faɗin, “My R please Aunty Rufaidah fa zanje na taya aiki a kitchen”.
        “A nan ma ai aikin zakiyi, yama fi na Aunty Rufaidah lada”. Ya faɗa yana tura kai cikin ɗakin da sumbatar goshinta......

__________★

       Tattaunawa ce sosai ta kasance a zaman meeting ɗin na su Maanal. Domin abubuwane masu muhimmanci da suke son kawowa na gyara a matsayinsu na artists ɗin companyn. Daga ƙarshe Director Mustapha ya sanar dasu batun da za'aje ƙasar Chaina a kansa. Wadda tun kwanaki CEO ya gabatar, ya kuma bada damar kowanne ɓangare su bada mutane biyu da zasu samu horaswar ta kwanaki goma kacal in sha ALLAHU. To zuwa yanzu kowane department na ƙoƙarin kai nasu, dan haka suma ya kamata sukai nasu ɗin. Dan haka aɗan nazari da su manyan sukayi cikin satin daya gabata, da ayyukan kowa da suka duba da ƙwazonsa sun yanke waɗanda suke ganin sun cancanci zuwa.
      Aifa nan kowa ya shiga gyara zama da fatan ya kasance shine. Duk da kuwa wasu a cikinsu an taɓa zuwa dasu wasu ƙasashen akan irin hakan. Dan ba sabon abu bane duk bayan wata shida Company na irin wannan zuwa ƙaro sanin kai da kai ɗin dan ƙaruwar ilimi ga ma'aikatansu. Director Steven ne ya miƙe yay bayanin waɗanda suka samu wannan dama. Wato Maanal Habib Giro da Yaqub Nuhu. Tuni fuskokin su Zaharadeen sun canja, ko tafin da akayi ma da ƙyar suka tafa. Maanal da Yaqub suka nuna farin cikinsu. Duk da ita dai Maanal bata so haka ba. Musamman data tuna maganar da AA ya taɓa mata akan tafiyar. Sai dai tana fatan ALLAH yasa bada shi za'ai ba.
     Suna tasowa a meeting ɗin yay dai-dai da lokacin break. Ransu Zaharadeen a ɓace suka wuce. Kowa naji a ransa akwai makirci a wannan tsarin. Dan a ganinsu kawai an zaɓi Maanal ne dan tana matar boss a yanzu, ita kuma ta zaɓi Yaqub saboda suna tare. To aiko lallai zasusha mamaki, dan ko zasuyi amfani da wannan damar akan Yaqub game da alaƙarsa da Maanal ɗin sai yabar Companyn nan da ƙafafunsa. Ai sun san dai boss ba mahaukaci bane ba zuciyarsa ba dutse bace zaiji kishi...

       Salla kowa yay ƙoƙarin zuwa gabatarwa. Bayan an idar masu tafiya cin abinci suka tafi, masu komawa office suka koma. Harda Maanal kuwa a masu komawar, duk da yau batazo da abincin nata ba. Hankalinta kwance ta fito daga elevator tana danna waya fuskarta da murmushi dan kuwa charting take da su Aneesa. Dai-dai ta danna zata ma Zeezah vn aka zare wayar a hannunta, da sauri ta ɗago idanunta, sai ko cikin na AA dake kallon wayar alamar karanta charting ɗin yake. Hannu takai zata amshe wayar, ya janye jikinsa batare daya daina karanta hirar tasu ba.
     Kamar zata saki kuka ta ce, “Amma dai haka babu ƙyau ALLAH”.
   Bai tanka mata ba bai kuma daina karantawar ba, sai ma fara tafiya da yayi, binsa tayi tana jinta duk a ruɗe, dan tsokanarta su Aneesan keyi a kansa. Acewarsu har an gama cin amarcin ne ta dawo aiki. Amasar data tura musu cewar (Ai ba sai an gama a gida ba zasu cigaba da ci a office) yasa suka tasata gaba da shaƙiyanci irin na ƙawaye. Itako tana bama kowa amsa dai-dai shi. Dan tafi sakewa tai musu surutu a charting fiye da zahiri. Son amsar wayar yasa Maanal bata ankara ba har sun shigo office ɗinsa. Sai da yakai zaune a rukunin kujerun ta ƙara kai hannu zata fige wayar batare daya daina abinda yake ba ya saka mata ƙafa ta faɗo jikinsa sannan. Da sauri ta kalla inda take, aiko dai a cinyarsa take ɗare-ɗare babu ƙarya. Miƙewa tai yunƙurin yi, yasa hannunsa ya sake rungumota da ƙyau, tare da saka idanunsa cikin tsakkiyar nata da wani salon ɗage gira sama.
        “Bake kika ce za'aci amarcin a office ba! Miye na pretending kuma amarsu ta ango?”. Yanda yay maganar kamar mai raɗa ya saka tsigar jikinta tashi, ga kunya na neman halakata tamkar ba tana tare da Bestyn ta dake goyata a bayansa ba ko bayan kekensa, wanda suke cin abinci a kwano ɗaya. Wanda yasha yimata wanka da mata tsarki, wanda yasha wanke mata underwears harda masu jini a jiki batare da ƙyanƙyami ba. Wanda y.....”
      Knocking ƙofar da akai ne ya katse mata tunani, bama tasan ta daka tsalle ta miƙe daga jikin nasa ba gaba ɗaya. Bai hanata ba, amma ya kamo hannunta ya zaunar a gefensa gab, kafin ya danna remote ƙofar ta buɗe a hankali ta hanyar rabewa biyu. Kallo ɗaya AS yay musu ya duƙar da kansa. A haka ya ƙaraso gabansu ya ajiye basket ɗin hannunsa yana faɗin, “Sir gashi in ji driver”. Bai jira amsarsa ba ya juya ya fice, ƙofar ta koma a hankali ta rufe kanta. Ajiyar zuciya Maanal da kanta ke ƙasa ta saki. Kallonta yayi, ganin ta kauda kai gefe ya ɗan laɓe baki, sai kuma ya gyara zama ya fara fiddo kulolin da ke cikin basket ɗin wanda babu tantama yasan na gidansu ne, kuma tabbas daga Oum suke. Sai da ya gama buɗe komai ƙamshin abincin ya bulale office ɗin sannan ya juya yana kallon Maanal dake satar kallon sa shi da abincin ta gefen ido.
         “Mrs Darma aikin kine wannan! Tashi ki bani abinci”.
      Kallonsa ta juyo tayi, ya ɗage mata gira ɗaya. Cike da neman magana ya furta, “Kin san dai anan babu Aban naki ai balle kice bazaki yi ba”.
     Sosai ta tura baki gaba. Batare da tace komai ba ta matsa kaɗan bakin kujerar ta ɗauka plate ta fara haɗa masa abincin. Idanu kawai ya zuba mata, ransa fes da kasancewarsu a hakan. Sai yanayin ke tuna masa wani lokaci acan baya daya shuɗe. Murmushi ne ya shiga ƙawata fuskarsa dan tamkar a yanzu ne komai ke faruwa. Harta kammala bai farga ba, sai da ta ɗan bubbuga spoon a plate ɗin sannan. Cike da basarwa ya haɗiye murmushinsa, batare daya ce komai ba ya gyara zama abinsa ya hau cin abincin bayan ya ɗauka wani spoon ɗin ya ƙara alamar nata.
        “Nifa na ƙoshi”.
    “Ɗura kike so kenan? Garama kici da arziƙi”.
Tasan zai aikata kuwa. Dan haka ta ɗauka spoon ɗin kawai itama. Jujjuya abincin kawai take amma ta gagara kai lauma ko ɗaya, baice mata komai ba, face ɗibowa ya nufi bakinta da shi. Yanda yay wani kicin-kicin da fuska babu alamar wasa yasa ta amsa ɗin.
       “Gulmammiya dama abinda kike so kenan”. Ya faɗa yana dungure mata kai tamkar ba shine yay maganar ba.
        Ita sai abin ma ya bata dariya, amma bata dara ɗin ba ta dai yi murmushi dan ya tuna mata baya. Idan ya lallaɓata taƙi cin abinci musamman in tana fushi da shi sai ya ɗiba ya bata a baki tare da dungure mata kai sannan yace mata gulmammiya. Murmushin nata ba ƙaramin ɗaukar hankalinsa yay ba, amma yasan yana yin magana zata birkice masa, dan haka yay shiru ya cigaba da cin abinsa yana ɗiba yana bata kuma. A mamakinsu sai gashi su ci sosai abinsu. Sun kammala kenan tana gyara wajen kiran waya ya shigo masa, AS ne ya sanar masa ma'aikata fa sun taru domin masa murnar aure. Amsa ya basa da cewar suna zuwa. Daga haka ya yanke kiran.
         “Oya let's go mutane na jiranmu”.
Da mamaki Maanal ta bishi da kallo dan ya nufi inda rigar suit ɗinsa take, “Wai mi?”. Ta faɗa cikin sigar tambaya.
      Batare daya kalleta ba yace, “Zasu tayamu murnar aure ne”.
    Kasa sake cemasa komai tayi, ta ƙarasa tattare komai kawai ta maida a basket ɗin sannan ta miƙe, veil ɗinta ta gyagygyara tare da ɗaukar wayarta a inda ya ajiye sannan ta nufi ƙofa inda yake tsaye yana jiranta.........✍️
          


*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. 🙏_*

*09032345899*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
[22/04, 3:30 pm] Leematu: *_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣4️⃣


______________


.........HUZNAH

        Sosai gaɓɓan jikinta ke mata ciwo, duk yanda take tunanin iya daurewa hakan ya gagara. Kuka kam taci harta godema UBANGIJI. Zagi babu kalar wanda Sageer bai sha ba a wajenta. Gashi bata sake jin motsinsa ba a gidan sai bayan magrib. Tana zaune wujiga-wujiga har yanzu bata gyara jikinta balle sauke nauyin sallolon dake a kanta ya shigo ɗakin. Kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa, batare da damuwa da hararar da take binsa da shi ba ya wuce bathroom ɗin ɗakin. Ruwa mai ɗumi ya tanada sannan ya fito, batare da Huznah data cusa kanta a ƙafafunta tana sabon kuka na takaicin ganinsa ta ankara ba taji kawai an cicciɓeta. Mutsu-mutsu ta farayi na son sauka, amma da yake ƙarfi ba ɗaya ba ko gezau ya shige bayin da ita. Tana kai masa duka da komai da fisge-fisge ya taimaka mata. Sai da ya tabbatar ruwan ya ratsa mata jiki ta samu ƴar nutsuwar da yake buƙatar ganinta a ciki sannan ya fito a binsa muryarsa babu alamar wasa ya bata umarnin yin wanka tare da gargaɗinta mintuna biyar ya bata tazo tai sallolin data tarama kanta. Idan kuma ba hakaba zata sha mamaki.
      Haka kawai taji wata masifaffiyar shakkarsa, babu ɓata lokaci ta gabatar da duk abinda ya sanyata ta fito tana ɗingisa ƙafa ɗaure da towel. Duk da ta bashi dariya da tausayi duk sai ya danne, fuskarsa babu fara'a ya miƙa mata riga da hijjab, komai batace ba ta ɗauka ta sanya ta fara gabatar da salla. Sai da yaga har tayi raka'a biyun farko sannan ya fita domin zuwa massallaci shima......

______★

      Ƙarfe biyar Abah ya kirata yace ta fito su wuce. Lokacin tashi yayi, amma akwai aikin da take yi, sai dai bazata iya cema Aban haka ba, sai kawai ta tattara aikin da abinda duk zata buƙata ta tafi da su bayan ta kashe wutar office ɗin ta fice. Kai tsaye inda AS ya nuna mata zata dinga ajiye key dan masu shara da safe su gani ta ajiye. Batare da tabi takan AA ba ta fice abinta ta samu su Abah. Cike da girmamawa ta gaisheshi sannan ta shiga driver ya maida ƙofar da dama shine ya buɗe mata ya rufe. Fuskar Abah da murmushi ya danƙa mata tsarabar da yayo mata, dan shi fa har yanzu kallonta yake tamkar su Naufal a gabansa. Cike da jin daɗi tai godiya ranta fal farin ciki...
  
      Sam AA bai san da tafiyar Maanal ba. Aiki ya masa yawa harya shiga over time ɗin nasa na tsiya. Kiran magrib ya sashi kallon ƙawataccen agogon dake a office ɗin. Ɗan tsai yay cikin tunanin Maanal data faɗo masa a rai. Sai kuma ya ɗauka waya yay kiran AS dan yasan tunda bai shigo masa sallama ba shima yana nan bai wuce ba. Ilai kuwa hakanne. Yana ɗauka daga can AA ɗin ya furta, “Zo mana”. Ya yanke kiran. Babu jimawa sosai AS ya shigo, sai da ya masa sannu da aiki kafin yace, “Gani sir”.
      Batare da AA ya ɗago daga abinda yake ba ya ce, “Besty fa?”.
    Sam AS bai gane kan zancen ba, dan haka ya ce, “Sir Besty kuma?”.
Karan farko AA ya ɗago ido ya kallesa, sai kuma ya dafe goshi ya ɗan murza. Cike da basar da suɓutar bakin nasa ya furta, “Maanal”.
         “Oh I'm sorry Sir, ai inaga tun five ta tashi”.
    Jimmm AA ɗin yayi, sai kuma ya jinjina kansa batare da ya sake cewa komai ba yay masa nuni yaje. AS na gama fita AA yaja numfashi ya fesar, sai dai a zahiri baice komai ba. Saima miƙewa da yay ya nufi bedroom yay alwala. Koda ya fito tattara dukkan abinda zai buƙata yay a cikin briefcase ɗinsa, dan dolensa yay aiki a gida kam daren yau. Yana fitowa AS ya amshi kayan hannun nasa ya haɗa da nashi shima, a tare suka sauka ƙasa. Sai da suka fara salla a massallaci su ƴan tsiraru dan akwai irinsa ƴan over time

Download complete TXT · Novel page