Showing 27001 words to 30000 words out of 252835 words
a lokacin Baba yayi sallama ya shigo gidan, ya tsaya yana kallon Hajar.......✍️
💛 HAJAR 💛
by ~Feenerh_feeche~
{15....}
Wani ihu Sa'adatu ta kurma tace "Hajar kashe ne za kiyi?, nifa ƴar uwarki ce", Hajar ta kasa cewa komai sbd kallon da Baba yake mata, Sa'adatu ta miƙe tana dafe bayanta, Baba baice komai ba ya wuce cikin gida, Umma ce tayo hanyar soro sbd ihun da ta jiyo, kaciɓus sukay da Baba tace "sannu da zuwa Malam", Baba yace "yawwa", ya wuce ƙofar ɗakinsa, ya ciro keys a aljihunsa, ya buɗe padlock ɗin ya shiga, Sa'adatu ta cafki wuyar Hajar tana ƙunduma mata ashar, Hajar tace "wllh badai nawa ba, dalla malama sakeni niba jaka bace da zan haɗa ƙashi dake", Sa'adatu tace "keee anƙi a sake kin, kiyi abinda za kiyi", zainab dai sai raba idanu take tana cewa Hajar kyaleta dan Allah, Umma tana zuwa ta tarar da Sa'adatu ta cakumi Hajar, Umma ta fara ƙoƙarin ɓanɓare hannun Sa'adatu dake wuyan Hajar tace "meya haɗaku?", Sa'adatu ta cakumo Umma sannan ta danna ihu da ƙarfi tace "Maama ku fito, gasu nan sunyi min rubdugu zasu hallakani", Nabilah ce ta fito tana wuwwurga idanu sai kuma ta riƙe baki tace "Maama fito ki gani", Maama tana fitowa ta ɗauki takalmin roba ta rufe Umma da duka, Nabilah da Maimuna kuma suka taru akan Hajar, Sa'adatu kam har lokacin tana riƙe da Umma gam, Hajar ta kufce daga riƙon da Maimuna tayi mata ta gantsawara Sa'adatu cizo a hannun, Sa'adatu ta saki Umma tana lailayo ashar, Zainab dai jikinta sai rawa yake tana kallon ikon Allah, Sabra ta shigo da ɗan gudunta jikinta sanye da Kayan islamiyya, gefe ta koma ta rushe da kuka, hayaniyar da taƙi tsayawa ce tasa Baba ya fito, tsaye yayi yana kallonsu zuciyarsa na tafarfasa, Maimuna da Nabilah suna ganinsa suka saki Hajar suna huci, Baba ya rumgume hannu yana kallon yadda Maama ke laftawa Umma takalmi, Maama tana ankara da Baba ta wurgar da takalmin tace "mal baka ga yadda muka fito muka tarar da faɗima da ƴarta sun rufarwa Sa'adatu ba", Umma ta juya ta tsinkawa Hajar marii, Hajar ta riƙe kuncinta ta fashe da kuka, Umma ta daka mata tsawa tace "wuce ɗaki", da sauri Hajar ta shiga ɗaki tana shessheƙa, Sabra tabi bayanta itama tana kukan, Zainab dai ta ɗauki jakarta ta fita daga gidan. Umma ta shiga ɗakinta zuciyarta na tafarfasa, har lokacin Hajar bata dena kuka ba, Umma bata ce mata uffan ba sai haushinta da take ji. kiran sallar magrib akai Hajar ta miƙe da lulu eyes ɗinta da sukay jajur, ta fita tsakar gida tayi alwala ta dawo tayi sallah, bayan ta idar da sallar ta jingina da jikin wardrobe, Umma na zaune kan darduna bayan ta idar da sallah, Mu'azzam yayi sallama ya shigo, ya durƙusa a gaban Umma yace "Umma ina yini", Umma tace "lafiya, an taso lafiya", yace "eh lafiya alhmdllh", tace "toh Allah ya temaka", yace "Ameen", Hajar da dasasshiyar muryarta tace "yaya sannu da dawowa", ya ringa kallonta snn yace "yawwa", ya ciro biscuits daga pocket ɗinsa ya bawa Sabra da take homework, Umma ta kallesa tace "idan ka fita Sallahr isha'i ka tahomin da Gana most go", yace "tohm, wane size?", Umma tace "medium", yace "tom" ya tashi ya fita. ƙarfe takwas da rabi Mu'azzam ya dawo da Gana most go a hannunsa, ya miƙawa Umma yace "wnn tayi?", Umma ta karɓa tace "Eh, ga abincinka", ya ɗauki medium warmern abincinsa ya fita, Umma ta ɗauki Gana most go ɗin ta wurgawa Hajar tace "haɗa kayanki", Hajar ta ringa kallonta bata dai ɗauki Gana most gon ba, a hasale Umma tace "ba kiji me nace miki ba?", Hajar ta janyo Gana most gon tace "Umma kayan me zan haɗa?", Umma tace "kayan sawarki zaki haɗa", a sanyaye Hajar tace "tom", ta tashi ta buɗe wardrobe side ɗin da kayanta yake, ta ringa ciro kayan tana ɗorawa akan gado, sai kuma ta dawo ta zuba su a Gana most go, tana gama zubawa ta zuge zip ɗin, Umma ta taso ta kalli wardrobe din tace "waɗan nan kuma fa?", Hajar ta kwaso su ta zuge zip ta zuba, Umma duk tana kallonta, Sabra tace "Umma ina Adda zata?", Umma tace "ba kin gama homewark ɗinki ba, maza hau gado ki kwanta, karna sake jin bakinki", Sabra ta haye gado bata sake magana ba. Hajar dai tayi ta sa ran kiran Baba amma har bacci ɓarawo ya ɗauketa bai kirata ba. ƙarfe bakwai na safe Hajar ta fita tsakar gida tayi brush, tana so ta shiga ta gaishe da Baba amma kuma shakkar hakan take, ɗaki ta koma taga Umma tana shafawa Sabra Vaseline, tana gama shafa mata ta saka uniform ɗinta, Umma tace "ki shiga ki gaishe da Baba kafin ki tafi makarantar", Sabra ta goya jakarta tace "tom" ta fita, sai kuma gata ta dawo tace "Baban bacci yake", Umma dai tayi mamaki sbd da wuya ne kaga Baba yana baccin safe, Umma tace "toh maza ki tafi karki makara". Sabra tayi tafiyarta makaranta, Hajar tace "Umma ina wake yake zan tsince", Umma tace "A'a ba tsintar wake za kiyi ba, zoki shirya fita za muyi", Hajar dai zuciyarta bata yarda da fitar nan ba, haka ta shirya a sanyaye, Umma ta zauna gefen gado bayan ta saka Hijab dinta tace "kiyi sauri kar ki ɓatamin lokaci", Umma ta ɗauki wayarta tayi kira, wayar kare a kunnenta tace "Jamila insha Allah gani nan zuwa gidanki", bayan few seconds Umma ta katse kiran tana kallon Hajar da ta taƙune fuska, Umma ta miƙe ta ɗauki ƴar purse ɗinta tace "wuce muje", Hajar tace "tom" ta wuce zata fita, Umma ta dakatar da ita tace "zo ki ɗauki kayanki da kika haɗa", Hajar ta kalli Umma ganin babu sauƙi a fuskarta ta fara jan Gana most go ɗin data fi ƙarfinta, Umma ta rufe ɗakin da padlock, ruwa ya cicciko idanun Hajar, Umma na ankare da ita tace "muje mana", Hajar ta goge hawayen da ya zubo mata tace "Umma ban gaisa da Baba ba", Umma tace "bacci yake, ko baki ji abinda Sabra ta faɗa ba, ki ɗauki kayanki ki wuce malama, kina ɓatamin lokaci", Hajar ta fara kuka a hankali tace "bazan iya ɗauka ba", Umma ta haɗe rai tace "ƙoƙarta ki kaisu soro", Hajar ta fara jan kayan a hankali, Nabilah da ta fito bayi ta bita da harara tana taɓe baki. bayan Hajar ta kai kayan soro Umma ta saka almajiri ya ɗauka ya fitar musu dasu bakin titi, Umma ta tari Napep, ta kalli Hajar tace "shiga", bayan me napep ya saka Gana most gon a boot Umma ma ta shiga, few minutes suka isa gidan Anty Jamila, Hajar ta ɗan ji relief ganin inda suka zo, Bayan sun shiga gidan, Hajar ta ajiye kayanta a ƙofar palour, Umma ta zauna akan kujera suna gaisawa da Anty Jamila, Hajar ta zauna kan carpet tace "Anty ina kwana", Anty Jamila tace "lafiya lou Hajar", Umma tace "yara sun tafi makaranta ko?", Anty tace "Eh suna makaranta", Umma tace "Jamila dan Allah wata alfarma nake nema a wajenki", Anty tace "tom Adda", Umma tace "dan Allah ina son Hajara ta zauna a wajenki na ɗan lokaci", Anty tace "Adda wnn ai ba damuwa bace ni me riƙe Hajara ce", Hajar dai duk tana jinsu, Anty ta kalli Hajar tace "tashi ki shigo da kayanki ki kai ɗakinsu Hafsa", Hajar ta miƙe a sanyaye wani kuka yana taho mata, yanzu anan Umma zata barta knn, tasan dai Anty bata da wata damuwa, amma ita tanada kwakwar Uwa, ko kaɗan bata so tayi nesa da Umma shiyasa ma babu inda take zuwa. Anty tabi Hajar da kallo, Umma tace "tashin hankali akai jiya a gidan, kuma Hajar ce a gaba gaba wajen assasa hakan", Anty tace "garin yaya?", Umma ta taɓe baki ta gaya ma Anty iya abinda ta sani, Anty tace "Subhanallah, gaskiya Adda haƙurin ki yayi yawa, shine kika tsaya kishiya ta ringa dukanki da takalmi", Umma tayi ajiyar zuciya tace "duk Hajara ce ta jawo, nayi nayi da ita ta dena shiga harkar yaran can amma taƙi ji", Anty tace "toh ai baki san me ya haɗasu ba da har ta biye mata, kika sani cutar da ita tazo yi ita kuma tayi ƙoƙarin kare kanta", Umma ta miƙe tace "da tayi haƙuri ai da yafi, ba zama zanyi ba, daman cewa nai bari na kawota da kaina", Anty ta raka Umma har ƙofar gida, Hajar na fitowa daga ɗakinsu Hafsa taga babu kowa a palour, ai kam ta fita waje da Sauri, har Umma ta tsare nepep tana shirin shiga, Hajar ta riƙe ƙarfen Napep ɗin tace "Umma dan girman Allah kiyi haƙuri..", Umma ta harɗe rai sai kace bata jin zafin rabuwa da ƴar tata tace "ai bakya son zama dani Hajara", Umma na faɗin haka ta shige napep ɗin, mai nepep ya burgi babur ɗinsa, Hajar ta rufe fuskarta da hijab tana kuka ta koma gida, Anty da take bakin gate ta bata hanya ta wuce snn ta rufe ƙofa. Anty dai bata ce mata komai ba, Hajar taci kukanta ta more snn tayi shiru, Anty ta fito daga ɗakinta tace "kinci abinci ma kuwa?", Hajar ta girgiza kai tace "na ƙoshi", Anty tace "shknn" ta shiga kitchen. Umma tana komawa gida ta leƙa ɗakin Baba, a kwance ta ganshi har lokacin, ta tsaya tana kallonsa na 5second snn ta juya, keys ta ciro daga ƴar purse ɗinta ta buɗe ɗakinta, Hijab kawai ta cire ta fito tsakar gida ta fara aikace-aikace, da Hajar tana nan da tuni ta gama, Umma ta dasa kujera a tsakar gida ta zauna tana tsince wake, Maama ta fito da ɗaurin ƙirji da doya guda ɗaya hannunta, zama tayi ta fara yanka doyar, tana yankawa taga doyar gaba ɗayanta ta ruɓe, ta ja wani dogon tsaki ta tashi ta shiga ɗaki ta ɗakko wata, itama dai tana yankawa ta ganta ta ruɓe, Maama tayi wurgi da wuƙar hannunta ta miƙe ta shiga ɗaki, Umma dai tabi ruɓaɓɓiyar doyar da ke zube anan tsakar gida da kallo ta girgiza kai, Umma tana ta kallon ɗakin Baba taga ya fito amma shiru, a hankali tace "A'a wai yau malam lfy yake wnn baccin", ta janyo latsinetarta ta duba lokaci taga har tara da rabi ta gota, miƙewa tayi ta shiga ɗakin Baba, tayi sallama yafi sau uku amma shiru, ta ƙarasa inda yake kwance, sai taga nunfashinsa ya canza, ta taɓa goshin taji kamar tasa akan wuta sbd zafi, ta ɗan jijjigasa tace "malam!!, malam!, malam".............✍️
💛 HAJAR 💛
by Feenerh_feeche
{16...}
Umma ganin Baba bai amsa ba, ga kuma yadda numfashinsa yake fita sama sama yasa ta fita tsakar gida da sauri, salati da sallallami ta zabga snn tace "Rabi ku fito malam ba lafiya", Maama tana ɗaki tana jinta amma tayi mursisi, ita baƙin cikin doyarta da ta ruɓe ne ya turnuƙeta, ƴaƴanta kam suna kwance suna baccin asara, Nabilah ce kawai tayi sallar asuba itama da rana gatsal-gatsal, Umma ta matsa bakin ƙofar ɗakin Maama tace "ku fito mu kai malam asibiti, bashi da lfy", Maama ta gyara ɗaurin ƙirjinta ta fito ta yiwa Umma kallon hadarin kaji tace "Malama lfy kike mana ihu sai kace daga dawanau", Umma dai a rikice take tace "malam nefa ba lafiya", Maama ta tafa hannaye tace "innalillah wa'inna ilayhirraji'un, kika ce kin kashe malam", sai kuma ta rushe da kuka, Umma da take a rikice saida tayi sak jin abinda Maama ta faɗa, Maama ta koma ɗaki cikin sauri ta shiga ɗalawa ƴaƴanta duka a cinya, faɗi take "ƴaƴan nan ku tashi, faɗima ta kashe muku uba", Nabilah da ita baccin nata beyi nauyi ba ta miƙe tana zabga hamma, Maama tace "tashi ƴan uwanki, faɗima ta kashe malam", Nabilah ta zaro ido ta dafe ƙirji tace "Baba". Umma dai tinda taga haukan da Maama take shirin ƙullawa bata sake bi takanta ba, wayarta ta ɗauka ta kira Mu'azzam, tana fara ringing ya ɗauka, Umma tace "Mu'azzam kana ina?", yace "ina wajen mai shayi", tace "taho gida yanzun nan", yace "Tom", Umma ta katse wayar ta ɗauki hijab ɗinta ta fita, Umma ta dawo tare da Munkaila makwabcinsu, Umma ta nuna ɗakin Baba tace "Bismillah". Munkaila ya shiga ɗakin Umma tabi bayansa. Maama da ƴaƴanta sun rufa akan Baba sai kuka suke, Nabilah tace "wllh ai na gansu da sassafe da wata ƙatuwar bakko zasu gudu", Maama ta fyace majina tace "Ta kashe min miji", Umma ta harɗe rai tace "kiga mutuwa akanki, ni ba ce miki nayi ya mutu ba, dan Allah ku fita kun cika masa kunne da haushi, karku ƙara masa zafin ciwo", Maama ta wangale baki tace "haushi fa kika ce faɗi", Umma ta bawa shara ajiyarta ta dubi Munkaila tace "dan Allah Munkaila temaka min mu fita dashi", Munkaila da Umma suka fito da Baba tsakar gida, a lokacin kuma Mu'azzam ya shigo, Umma tace masa ya taro napep, Ta uwa ta uba Maama ta ringa zage Umma tamkar zogale, Umma dai bata biye mata ba, da taimakon Munkaila aka fita da Baba aka sakasa a Napep ɗinda Mu'azzam ya taro, Munkaila da Mu'azzam ne riƙe da Baba, Umma ta tari wani Napep din tabi bayansu zuwa asibiti, da yake ranar Monday ne akwai doctors, Emergency aka wuce da Baba, doctor yana dubasa ya rubuta allurai da za a masa a takarda, Mu'azzam ya amshi takardar yaje ya siyo da ƴan kuɗin da suke aljihunsa, Saida Baba ya zama stable snn aka basa gado sbd kwantar dashi akai, blood pressure dinsa ne yayi mugun high gashi kuma akwai slight heart attack da ake zargin ya samu, Umma dai bata kira kowa daga dangin Baba ba sbd ba ƴan Kano bane, ainahin garinsu Baba Yola, Umma tana zaune gefen gadon Baba da yake bacci sbd alluran da akay masa Mu'azzam ya matso kusa da ita da takarda a hannunsa, a hankali yace "Umma kinga likita ya rubuta tests da drugs da kuma allurai, kuɗin hannuna bazasu isa ba", Umma tace "tom, ka kira Naseer ka gaya masa", Mu'azzam yace "bari na kira saina baki wayar kiyi masa magana", Umma ta gyaɗa kai, Mu'azzam ya ciro wayarsa daga aljihu ya kira Naseer, Naseer na ɗagawa Mu'azzam yace "Yaya ga Umma za kuyi magana", Umma ta karɓi wayar ta kara a kunne, Naseer yace "ina kwana Umma", Umma tace "lafiya lou, ya aiki?", Naseer yace "alhmdllh", Umma tace "toh Allah ya temaka, Baba ne aka kawosa asibiti ba lfy, toh kuɗin hannun mu sun yanke, gashi kuma ba a gama siyan drugs ba", Naseer yace "me yake damunsa", Umma tace "jininsa ne ya hau", Naseer yace "toh Allah ya basa lafiya, Inshallah gobe zan dawo, yanzu dai Mu'azzam ya turomin da account number ɗinsa saina turo muku kuɗi", Umma tace "toh shknn". Mu'azzam ya turowa Naseer account number ɗinsa, babu jimawa saiga alert ya shigo wayar Mu'azzam na kudin da Naseer ya turo. Munkaila ne ya shigo ward ɗin ya yiwa Umma sallama, Umma tayi masa godiya Sosai.
★Through out the day Hajar was so Moody, har saida su Hafsa suka dawo daga schl snn ta ɗan sake, Hafsa ta fige hijab ɗin jikinta na uniform tana kallon Hajar tace "yau sai ga ki a gidan nan", Hajar tace "Eh mna", Hafsa tace "kice ƴan ziyarar sun motsa ta kanmu", Hajar ta nasa mata harara tace "kya ji dashi, naga kema ba zumuncin kike ba", Hafsa tace "Tahfeez", Hajar tace "Tahfeez ɗin ce ta hanaki fita knn?", Hafsa tace "yesso, bari na cire uniform" da haka ta shiga ɗakinsu, Hafsa saida tayi wanka snn ta fito, Hajar ta ɗaga kai ta kalleta, Hafsa tace "ina Anty ne?", Hajar tace "tana ɗakinta", Hafsa tace "kinci abinci?", Hajar ta girgiza mata kai, Hafsa ta wuce hanyar kitchen tace "bari na zubo mana", Hafsa ta zubo musu abincin a plate ɗaya, ta kawo ta ajiye akan carpet ta koma kitchen ta ɗakko musu pure water da gaseous drink, Hafsa ta zauna ta janyo plate ɗin abincin ta saka spoon tace "toh sakko hajiya ta", Hajar ta zamo daga kan kujerar da take ta ɗauki spoon ta fara cin abincin, Anty ce ta fito daga corridorn ɗakinta, zama tayi a palourn tace "yanzu kinga damar cin abincin knn?", Hajar tace "daman Hafsa nake jira". suna gama cin abincin Hajar ta ɗauki plate ɗin ta kai kitchen ta dawo ta zauna tana shan drink. da yamma Anty ta shiga room ɗinsu Hafsa, Hafsa na latsa wayarta, Hajar kuma na durƙushe gaban Gana most go ɗin kayanta, Anty tace "Hafsa ki bata space a press ɗinku ta jera kayanta", Hafsa tace "tom, wai daman da gaske kwana za tay", Anty tace "kun shigo ɗaki kunyi gurgumi sai kace wasu ƴan matan Amarya, wa zai girka muku abincin dare", Hafsa tace "wai da sai daren sai muyi jollof spaghetti", Anty tace "A'a tuwo zaku yi, Hajar tayi tuwo ke kiyi dry okra soup", Hafsa tace "tom, semovita ko?", Anty tace "Eh" ta fita ɗakin. Hajar ce ta haɗa duka tayi, da tuwan da miyar duk ita tayi su, kuma kafin a kira Sallahr magrib ta gama, Hafsa aikin fito mata da ingredients da jajjage kawai tayi, bayan sun idar da sallahr magrib sukay zamansu a palour, Abdallah ne ya shigo palourn first born ɗin Anty, ya kalli Hafsa da take bawa Hajar lbri yace "an gama dinner", Hafsa tace "Eh", ya shiga kitchen, sai kuma ya fito empty hand, ya haɗe rai yace "wai tuwo aka dafa?", Hafsa tace "Eh", yayi slight hiss ya ɗauki remote ya canza channel daga American zuwa channel ɗin da ake ball, ya zauna kan kujera, Hafsa ta kallesa tace "ka turo min 2GB, yanzu na tashi na dafa maka indomie sharp sharp", yace "toh sleep thief, saidai 1GB", Hafsa tace "Eh naji, turo min naga dahir", ya ciro wayarsa ya tura mata Data 1GB, Hafsa ta kalli wayarta da ke hannun kujera tace "yawwa sun shigo, Hajar ina zuwa", Hafsa ta miƙe ta shiga kitchen da wayarta a hannu,