Showing 168001 words to 171000 words out of 252835 words
ƙofa ta fita, tana zuwa room dinta ta saka kayan bacci tabi lafiyar gado, uhmm saidai tinda ta kwanta ta kasa baccin juyi kawai take tana naɗewa waje ɗaya tamkar ƙadondoniya, lokaci zuwa lokaci take turo baki ta juya lulu eyes dinta. Ranar Thursday da yamma Nurain ya isa gidansu, yana shiga main palour ya tarar da baƙi, both his paternal and maternal Aunties na zaune palourn da kuma close friends din Maminsa, da ladabi Nurain ya gaishe da mutanen palourn, Mama Mardiyya ƙanwar Abba tace "Uthman ya iyali...?", yace "Alhmdllh" yana shafa kansa, da haka ya tashi ya wuce part din Mami, Sakeena ya tarar a palour tana sealing envelope da aka cika da sabbin kuɗi, Nurain ya ƙarasa palourn yace "wani abun ake ne naga ƴan uwa..?", Sakeena tace "kai komai baka sani ba, yau fa za a kawo lefen Noory", ya waro ido yace "Oh right... Mami ta gayamin", Mami ta fito daga bedroom dinta da 2 notes na kudi a hannunta ta miƙawa Sakeena tace "suma kisa a envelope", Sakeena ta amshi kuɗin tace "Ohk", bayan Nurain sun gaisa da Mami yace "Abba na nan...?", Mami tace "Nope yaje Abuja sai 7 nake jin zai dawo", Nurain yace "Alright". wajen ƙarfe biyar masu kawo lefen Noor suka iso, aka tarbesu da girmamawa snn aka musu shimfiɗa ta fuska da kuma ta tabarma, da suka tashi tafiya ma aka bisu da abin arziƙi. Da daddare wajen ƙarfe takwas Mami na zaune main palour tare da Sakeena, ga uban kayan lefen da aka kawo zube kan Carpet, Sakeena tace "Our Mami baki ga kayan ba kona ɗaɗɗaga miki...?", Mami tace "No dear zan duba later", Sakeena tace "Tom" ta cigaba da duba box din kayan shafa, Nurain ya fito daga great room din Abba, paper din hannunsa ya miƙawa Mami snn ya zauna kan Sofa, Mami ta kalli papern sai kuma tace "i don't understand, wane calculation ne wnn..?", Nurain yace "kayan da nace miki zasu zo to nasu ne...", Mami tace "Masha Allah, Allah yasa rabo ne yasa albarka", yace "Ameen", Mami ta miƙawa Sakeena papern ta tashi ta shiga great room din Abba don daman so take suyi mgana dashi akan bikin, buɗe baki Sakeena tayi tace "Brother wane irin houses zaka siyamin a Villa..?", ya waro ido yace "irin wnda kike so", Sakeena tayi murmushi tace "Toh wai me kake a hospital?", straight forward yace "Help", Sakeena ta ajiye papern kan kujera tace "saidai hakan", ta cigaba da duba kayan da take, can after few minutes tace "Yauwa bani kuɗin kayan Hajar ma", Nurain ya dubeta ya ɗage gira yace "kayan me?", tace "Outfits da zata saka a biki mna", yace "Outfits kuma is she the bride?", tace "yeah she's your bride wcca kake ma favor" ta ƙarashe tana galla masa harara tace "kaga babu enough time saura 2weeks", yace "2week sukay fixing..?", tace "yeah", yace "ohh account digit", ta gaya masa account digit dinta, bayan ya tura mata ya ajiye wayar yace "done", wayarta ta duba bayan alert din ya shigo, ganin kuɗin daya turo tace "bafa 20set za a dinka ba", yace "sunyi kaɗan ne..?", tace "No sunyi yawa sosai zan maka refunding half", yace "no need", a lokacin Mami ta fito tana kallon Nurain tace "Abba yace zaka wuce China..?", Nurain yace "yeah..", Mami tace "when..?", yace "insha Allah on Monday", Mami tace "hope ba zaka daɗe ba", yace "Sure 10days zanyi", Mami tace "Alright... sai ka kawo Hajar nan..", yace "Tom". Before 10 Nurain ya koma gida, sharp sharp yayi wanka ya saka white pajamas don so yake ya sauka downstairs ya zuba abinci, a gidansu yana ganin ana ci yaƙi ci don ynxu sosai taste din abincinta ya kama masa baki, yana buttoning rigar jikinsa ya sauko downstairs ya shiga kitchen, tini ya ɗauki plate ya fara zuba abincin da yau kwana uku knn sai ya tarar a ajiye, yana gama zuba snow rice ya buɗe warmer din stew, yana fara zuba stew din aka buɗe ƙofa, daskarewa yayi a yacca yake da serving spoon a hannu, Hajar tafi seconds biyar tana kallonsa sai kuma ta taɓe baki ta wuce ta ɗauki ruwa, har ta nufi door zata fita sai kuma ta juyo, wata shegiyar dariya ce ta taho mata ganin ya kasa cigaba da zuba abincin sai jujjuya serving spoon din hannunsa yake, tayi gyaran murya tace "kai ma kana tayasu ci knn...?", haɗe gira yayi yace "what are you talking about...?", Hajar ta fashe da dariya tace "Aljanun kitchen fa na ajiyewa shine ka cinye musu..", Nurain bai san lokacin da ya ajiye serving spoon din ba yace "yah... i was only helping them sai an zuba a plate suke ci ai idan a warmer ne baza....", shiru yayi jin ta tuntsire da dariya, ita za a yiwa wayo bayan ita take wanke plate din da yaci, kallonta yake without blinking har tana riƙe ciki, Nurain yayi blushing ya shafa kansa, ya harɗe hannu yana kallonta, saida ta more dariyarta snn ta ɗago tace "wayyoh Allahna", ganin yana tahowa kusa da ita tayi sauri ta buɗe ƙofar kitchen din ta fita, saidai dariyar da take tayi weakening dinta tasa kafin ta hau stairs yayi nasarar fixgota, ta tsala ihu tace "i know your were just helping them, daman su suke cin jagwalgwalo kai baka ci", sakinta yayi ta haura sama da sauri, yabi bayanta da kallo sai kuma ya juya ya koma kitchen yana blushing, stew din ya ƙarasa zubawa ya ɗauki ruwa da lemo ya fita, a palour ma yayi zamansa yaci abincin, sha biyu da rabi na dare Nurain ya rufe laptop din da yake operating, ya tashi daga kan gadon bayan ya zura room slippers ya fita palour, yayi sliding door ya fita daga ɓangaren nasa, a hankali ya murɗa ƙofar ɗakinta ya shiga walking gently without making any sound, kwance ya ganta kan gado ta rufe da duvet, hasken ɗakin ya rage yabar dim, ya matsa gaban gadon yana kallonta da ɗan hasken ɗakin, a hankali ya kwanta daga bayanta ya ɗora kansa a pillow dinta, yana ɗaga duvet Hajar ta farka don daman baccin nata beyi nisa ba, ganin zata miƙe yayi saurin rumgumota ta baya, scent dinsa da ta shaƙa ne yasa taji relief amma kuma saita fara ƙoƙarin fixge kanta, da taga dai bazata iya kwacewa ba ta marairaice tace "please let go off me this is not proper fa..", ya sake haɗata da ƙirjinsa har tana jin bugun zuciyarsa, lumshe idonta tayi jin saukar numfashinsa a gefen wuyanta tace "dan Allah let me go..", murya can ƙasa yace "No.. sai kin faɗi wa kike yima dariya ɗaxu", turo baki tayi tace "nifa ba da kai nake ba, Aljanun ne suke bani dariya..", tummy dinta ya riƙe ya mirginasu suka koma suna fuskantar juna yace "really.. Aljanun kike yima dariya..?", da sauri ta runtse idonta ta gyaɗa kai don idan tace zata buɗe baki tayi mgana toh tabbas dariya ce zata biyo baya, a bazata taji ya haɗe goshinsu waje guda sai kuma yayi brushing lips dinsu, yace "lokacin da kike dariya ai buɗe baki kikay so now answer me bana son nodding talk Silly girl", tini zuciyarta ya fara racing, ta daddage tana matsawa baya don ta raba goshinta da nasa, da sauri ya tallafo kanta ya hanata raba goshin nasu, tana buɗe baki da shirin tsala masa ihu ya rufe bakin da nasa, this time around ba iya brushing lips dinsu yayi ba he sucked her small lips deeply, tini Hajar ta fashe da kuka jikinta har na rawa tace "Ummana wayyo Ummana...", Nurain yayi murmushi mai sauti yana kallon lips din nata da bai gaji da sucking ba, yace "Shhh in ana dariya ba a kuka fa", ba tasan lokacin da ta shiga banka masa harara ba tace "Ni ka sakeni dan Allah, ni fa ba kai nake yiwa dariya ba", yace "Ohh really su Aljanun da kike jin tsoro kike ma dariya knn..?", da sauri ta gyaɗa masa kai, ehen ai kam da kiss din da ya matuƙar firgitata ya gigitata ya mata tinin ba nodding saidai tayi mgana, yana sakar mata lips ta fashe masa da kuka harda shessheƙa, garin riƙeta sbd fincikewar da take ne ya kasa controlling kansa, abu daga tsokana sai kuma ya fita daga sahun tsokana har ya wuce gejin kiss, firgitar da tayi yafi na ranar nan, don wnn karon anje inda ba'a aje ba ranar nan, da kyar ta samu chance din da ta kwala uban ihu sai kuma ta ja numfashi tamkar zata shiɗe tana kiran Ummanta, sai a lokacin Nurain ya sarara mata, gefenta ya kwanta yana sauke nannauyan ajiyar zuciya, Hajar ta ja rigar baccinta data koma wuya tana shessheƙa, daman ba a maganar bra don ita cilli akay da ita may be ma ta kai gaban mirror, gaba ɗaya jikinta rawa yake tamkar an jona mata shoking, yau ita taga jalala da ƙarshen tashin hankali, hantsilowa tayi daga gadon ta kwanta kan carpet ta ringa rusa kuka kamar ranta zai fita, Nurain ya lumshe idonsa yana jinta, idan yace zai rarrasheta to tabbas ba rarrashi zai yi ba wani kukan zai sakata ko kuma ma ya sumar da ita tinda ya lura matsoraciya ce, after 30mins yaji ta dena kukan saidai shessheƙa time to time, da kyar ya tashi zaune snn yayi buttoning rigarsa, a hankali ya sauka daga gadon ya duƙa gabanta, ya rage murya yace "Hajar... Hajar... Hajar", jin shiru bata amsa ba ya ɗauketa ya mayar da ita gado ya rufa mata duvet, daga haka ya fice walking slowly don ya kunnowa kansa ruwa. Washe gari Hajar tayi gurgumi a ɗaki taƙi fita ko ina, daga taji motsi saita kyalla bathroom, tsoron encounter dashi take har cikin zuciyarta, gashi tana so ta sauka kitchen don yunwa take ji amma kuma bazata taɓa iya fita ba, tin safe ruwa kawai ta ringa ɗurawa kanta, wajen ƙarfe biyu na rana ta miƙe a hankali ta matsa gaban window, curtain din ta yaye ta leƙa waje tana kallon compound, parking space ta kalla taga babu motarsa guda ɗaya, hakan ne ya bata hope din baya gidan knn, ai da sauri ta nufi door ta buɗe ta fita, sharp sharp tayi frying egg ta tafasa black tea, jikinta har wani ɓari yake don tayi sauri ta gama ta fita, haka ta shanye shayin da zafinsa yana ƙona mata baki, tana gamawa ta buɗe ƙofa ta fita, a lokacin shima ya shigo palourn da leda a hannunsa, sanye yake da manyan kaya farare tass sbd yau Friday kuma daga mosque ya dawo, Hajar ji tayi kamar zuciyarta ta koma ciki ganinsa, da sauri ta koma kitchen don hawa saman ma ya mata nisa, ta yarfe hannu kamar zata fashe da kuka tace "na shiga uku", jin an murɗa handle ta koma da baya tana zaro ido, sai taji dama ta iya irin magic din nan na cikin films din da Noor take kallo, da babu abinda zai hana ynxu tayi applying dinsa a wnn taƙin ta ɓace ɓat ta huta, sulalewa tayi ƙasa after realizing tabbas shine ta haɗe kanta da guiwa, Nurain ya ajiye ledan fruit da ya shigo dashi, ya ringa kallonta kafin ya fara tafiya gently towards her, ya duƙa gabanta yace "yau ba gaisuwa?"......✍️
💛 HAJAR 💛
{71..}
Hajar dai taƙi tace masa komai kanta na bisa guiwarta, after a while yace "ko nima na zama masquerade ne...?", turo baki tayi ta gyaɗa kai, Nurain ya waro ido yace "why...? me yasa na zama masquerade all of a sudden..?", ta masa shiru ba amsa, yasa hannu ya ɗago kanta, suna haɗa ido tayi sauri ta mayar da kanta, Nurain yayi blushing ya shafa kansa ya miƙe yace "Alright i know daga yesterday's night na zama masquerade din nan", ta sake takure kanta tana jin dama ƙasa ta tsage ta shige kawai, wai daman yana sane da abun be manta ba, yace "Hajar", ba ta ɗago kanta ba amma kuma ta amsa a hankali, yace "i bought some fruit, make a fruit salad", ta gyaɗa masa kai, after few seconds Nurain ya fita daga kitchen din, saida Hajar ta tabbatar ya fita snn ta iya ɗago kanta ta tashi tsaye, ledan da ya ajiye kan Island ta buɗe ta ringa kallon fresh fruit dake ciki, gaba daya fruit din ta wanke snn ta zuba a fridge bayan ta ɗebi wnda za tayi salad din dasu, within few minutes ta gama haɗa yummy fruit salad din wnda ta jefa guda gudan green and purple grapes a ciki, a tsadadden transparent bowl ta juye ta saka a fridge, daga haka ta bar kitchen din ta koma room dinta, nail cutter ta ɗauka ta zauna tana yanke farcenta da bai wani fito sosai ba, tana gama yanke farcen ta tashi ta shiga bathroom ta wanke hannunta ta dawo ta zauna gefen gado, tana zama aka buɗe door, ta san dole shine don haka ta saukar da kanta taƙi kallon door din, ga kuma pure men scent dinsa da already ya cika room din shima ya tabbatar mata da shi din ne, daga bakin door ya tsaya yana kallonta yace "kin gama making fruit salad din ne...?", a hankali ta gyaɗa kai tana wasa da slim fingers dinta, yace "Ohk then bring it to my room" bai jira amsarta ba ya juya ya fita, Hajar ta ɗago kanta ta kalli ƙofar sai kuma ta turo baki, bata gane ta kai masa room dinsa ba, saida ta gama muhawara da zuciyarta snn ta tashi walking gently ta fita, downstairs ta sauka ta shiga kitchen, a tray ta ɗauro bowl din fruit salad din wnda yayi sanyi ƙau, ta saka spoon kan trayn bayan ta rufe bowl din da marufinsa, walking gently ta fita daga kitchen ta haura sama, tsaye tayi bakin door din part dinsa without making any move, da kyar tayi shahadar knocking a hankali, muryarsa taji yace "Come in", tayi ajiyar zuciya ta shiga kanta a ƙasa, zaune yake kan one of the exclusive Sofas dake palourn, yana kallon monitor din laptop dinsa da ya haska hoton posterior view of the heart, kallo ɗaya Hajar ta masa tayi saurin ɗauke kanta tayi sallama, Nurain ya ɗago daga kallon monitor ya dubeta ya amsa sallamar da tayi, ta ƙaraso ta ajiye trayn saman Centre table dake gabansa ta juya zata fita, da sauri ya riƙo hannunta ya janyota ta zauna kan kujerar daga gefensa, yace "are you eager to leave..?", da sauri ta gyaɗa kai, slight smirk yayi yace "Ke!! sai kin jama kanki ciwo ko..? kina ta wani nodding head sai kace lizard.. ko sai na maimaita abinda na masa last night zai buɗe..?" ya ƙarashe yana kallon lips dinta, da sauri ta girgiza kai tana turo baki tace "Ni fa aiki nake a kitchen", yace "Oh i thought sai na buɗesa za kiyi mgana ai", ɓamɓare hannunta da ya riƙe tayi ta miƙe ta nufi door, Nurain yabi body figure dinta da kallo har ta fice, ya dauki fruit salad din ya fara sha, har wani lumshe ido yake sbd yadda dadin ya shigesa. Kitchen Hajar ta koma ta shiga dafa abinci, before 4 ta gama girkin ta ɗebi nata ta bar masa nasa a warmers ta fita. Washe gari wajen ƙarfe sha ɗaya Nurain ya dawo daga unguwar da yaje, thick eyebrows dinsa a haɗe alamar dai ransa ya ɗan ɓaci, tafiyar da zaiyi ranar Monday ashe jirgin ba ta Kano zai tashi ba tacan Abuja ne, don haka yau Saturday ya kamata ya wuce Abuja ranar Sunday yayi clearing komai a can Abujan kafin ranar Monday da jirginsu zai ɗaga zuwa China, kafin ma ya dawo gida yayi booking flight ticket zuwa Abujan, sama ya haura ya murɗa ƙofar room dinta, surveying ɗakin yayi da ido yaga bata nan, rufe kofar yayi ya wuce part dinsa kawai, after like 20mins ya fito in a hurry ya sauka ƙasa, zai buɗe kofar kitchen knn aka rigasa ta ciki, da sauri ta fito ta basa hanya sai kuma ta dan yi bowing tace "ina kwana..", bata taɓa tsammanin zai amsa mata ba sai gashi ya amsa, wucewa tayi zata haura sama yace "Hajar", ta juyo tare da amsawa a hankali, yana kallonta da kyau yace "kije ki haɗa kayanki zamu wuce gidan Mami", ba tace komai ba ta ɗan kallesa, yace "belongings naki da za kiyi amfani dashi na two weeks", tace "tom" da haka ta juya ta fara hawa stairs, Nurain ya lumshe ido yana sauke ajiyar zuciya sai kuma ya shiga kitchen. haka nan Hajar ta haɗa duk wani abu da tasan zata buƙata a box, kayan sawa har cikin tsarabar Hajiya da ta Mami ta kwashi wasu, tana cikin zuge box din ya shigo, ganin tana fama da zip ya ƙaraso ya zuge mata yace "kin gama packing komai da zaki buƙata..?", tace "Eh", yace "Alright ki fita compound" da haka ya ɗauki box din nata ya fita, Hajar ta ɗauki handbag data saka waya da wasu ƴan tarkacen nata, bayan ta saka well ironed hijab da ta fitar ta nufi ƙofa, saida Nurain ya kashe duk wasu electric appliances na gidan ya rufe ko ina snn ya fito compound hannunsa riƙe da car key, wajen mai gadi ya wuce, da sauri Inuwa ya miƙe ya russuna yana gaishesa, Nurain yace "yawwa mal Inuwa yaushe zaka tafi gidan...?", Inuwa yace "insha Allah gobe da sassafe zan ɗau hanya", Nurain yace "Okay" ya ciro kuɗi masu kauri sosai daga aljihunsa ya basa, hannun bibbiyu Inuwa yasa gami da russunawa can ƙasa ya amshi kudin yace "Allah ya saka da alheri", Nurain yayi murmushi yace "toh Allah ya tsare hanya" bai jira mai zaice ba ya wuce parking space yana kallon Hajar dake tsaye jikin mota tana jiransa, Inuwa dai ya saki baki yana kallon uban kuɗin, jiya fa ya basa Albashinsa yau ma gashi ya ƙara masa wasu, ga kuma kayan abincin da ya basa yace ya kai gida, shiyasa Garba yace aiki gangariya ya samo masa, a