Showing 174001 words to 177000 words out of 252835 words
na wajen grandma dinsu ko...?", Sakeena tace "Eh", Mami tace "Alright please a ware 100 pieces daban", Sakeena tace "Sure", da haka Mami ta juya ta fita, Sakeena ta kalli Hajar tace "je kici Abinci kiyi sallah sai mu ƙarasa", Hajar tace "Toh" da haka ta tashi ta fita. the same time daya kira jiya ta wayar Noor yau ma haka ya kira saidai ta wayar da ya bata, shi asuba ce a can nan kuma ƙarfe tara na dare, Hajar ta ciro wayar da ta ajiye cikin handbag dinta tin safe jin tana ringing, ta ringa kallon exact number da ta kirata jiya, turo baki tayi bayan tayi wani tunani, gashi da Sim 1 ake kiran snn kuma numbern ba ta Nigeria bace, lokaci guda ta makawa wayar harara ta dannata a silent ta mayar cikin jaka, bathroom ta shige tana turo baki gami da juya lulu eyes dinta, tana fitowa daga wanka ta tarar da Noor na jiran fitowarta, da sauri Noor ta miƙa mata wayar hannunta tace "take it Yaya ne zai kira ynxu" tana gama fadin haka ta fita da sauri don kallon stuff na Kdrama data saba take yi ya kira, gashi yace lallai lallai ta bar abinda take ta kaiwa Hajar waya, tana zuwa ta tarar da Hajar na wanka gashi sai azalzalanta yke sai kace zai fito daga wayar, Noor na fita kiransa ya shigo, Hajar ta ringa kallon wayar har kiran ya katse wani ya sake shigowa, kan mirror ta ajiye wayar ta barta sai ringing take, ta dauki kayan baccinta ta saka tayi kwanciyarta tana ji wayar nata ringing, bayan wani lokaci taji kiran ya dena shigowa, kasa bacci Hajar tayi duk da baccin da take ji, idonta ne kawai a rufe amma ba baccin take ba, jin an buɗe door ta ɗan buɗe idonta, azatonta Khausar ce sai taga Noor ai kam tayi sauri ta rufe ido, Noor ta duba sides din Hajar tana neman wayarta tinda jiya ma anan ta ganta, ganin bata ganta ba saita fara dube duben ɗakin har ta hangota a kan mirror, zaro ido tayi ganin 10+ missed call, wani kiran nashi ne ya kuma shigowa, Noor tayi picking ta kara a kunne tace "Hello", from the other side Nurain ya haɗe thick eyebrows dinsa da muryansa da bata daidaita ba yace "Hey Noor kin kai mata wayar..", Noor tace "wllh na kai mata hand to hand..", ya sauke numfashi yace "where is she..?", Noor ta dubi Hajar da take baccin ƙarya tace "she's already at sleep", yace "wake her up", Noor tace "Ohk" da haka ta durƙusa gaban Hajar ta fara tapping dinta, tamkar sumammiya haka Hajar ta naɗe samm taƙi ta motsa ma, Noor tace "Yaya she's deeply at sleep taƙi tashi fa", yayi ajiyar zuciya tace "ki san yacca za kiyi ki tasheta nan da 5mins" ƙit ya katse kiran, Noor tayi tagumi tana kallon Hajar tace "na shiga uku", ganin lokaci na tafiya Noor ta kai hannu tayi tapping dinta tace "Please Hajar wake up ki rufamin asiri", sau ɗaya ta sake tapping dinta sai ta fara mutstsuka ido kamar gaske ta miƙe zaune, Noor tayi ajiyar zuciya don wani relief taji tace "Sorry Yaya ne yace na tashe ki", Hajar dai sai mutstsuka ido take ta gyaɗa kai, 5mins na cika dot ya kira, Noor tayi picking tace "gata nan na tasheta ynxu zan bata wayar", yace "Better", tini Noor ta miƙa mata wayar, Hajar ta amsa ta kai kunne ba tare da tace komai ba, fita daga ɗakin Noor tayi tana jin daɗi Allah ya rabata dashi, almost 1mins wayar na kare kunnenta taƙi tace masa komai, ya rage murya yace "Hajar are you there...?", shiru ta masa taƙi mgana sam, slight breathing dinta da yake jiyowa ta wayar ne ya basa assurance cewar tana ji mgana ne dai baza ta masa ba, yayi ajiyar zuciya yace "Hajar are you hearing me", ta haɗe gira ba tace uffan ba, babu yacca Nurain baiyi ba akan ta masa mgana amma taƙi, daga ƙarshe yace "i must open that small mouth of yours until you beg for mercy", da haka ya katse kiran, Hajar ta turo baki ta koma ta kwanta zuciyarta wasai. Haka nan two days Hajar taƙi sauraron Nurain, idan ya kira ta wayarta daman bata picking, ta wayar Noor kam zata dauka amma ba za tayi mgana ba, sosai Nurain ya damu da hkan da take masa, lafiyar Allah fa ya baro Silly girl dinsa toh me ya faru ne, wayar da sukay na farko ma harda sassanyan gaisuwar da kwana biyu take masa tayi fa, wai what is exactly happening ne, tini ya fara shirin dawowa 9ja duk da bai gama abinda zaiyi a can ba ya bar Mr Lee zai ƙarasa masa shikam ya kamo hanyar gida Nigeria. Zuwa wnn lokaci gida ya fara cika da ƴan uwa na nesa wnda suka zo biki, gobe ne za'a fara gudunar da ƙananun shagulgulan na bikin wnda Amarya da ƙawayenta ne zasu warwasa. Khausar ta dubi Noor dake zauna kan hannun kujera tace "Please Noor kixo mu tafi wajen Salon din nan don mu dawo da wuri", Noor tace "Hajar nake jira ynxu zata fito", Khausar ta haɗe gira tace "wace Hajar kuma ita amarya ce da sai kunje wajen Salon tare", Noor tace "Yaya Sakeena ce tace muje tare", Khausar tace "Ohk alright amma ai komai na bride is different from others", Noor tayi dariya tace "wankin kai ne fa kawai ba make up ko Outfits ba", Khausar ta taɓe baki ba tace komai ba, Hajar ta fito sanye da hijab da handbag dinta a hannu, da haka suka wuce wajen Salon din bayan sun sanar da Mami. ƙarfe 11 na safe Nurain ya iso gida, direct part din Mami ya wuce wacca ya tarar da ita tayi shirin fita, don haka suna gaisawa Mami ta fita don already driver dinta ma ya gama warming mota, Nurain na fitowa part din Mami ya buɗe room din Noor after knocking for almost 1mins, haɗe gira yayi ya juya ya koma bangaren Mami kuma saida ya duba ko wane room na part din snn ya fito, at last ya shiga kitchen ya duba shima dai baiga abinda yake nema ba, infact ma ya lura da babu kowa a main house din don ko baƙin da suka fara zuwa suna can Cabins din gidan, a ransa ya ayyana may be suna tare da Noor tinda bai ga kowa a gidan ba. Sai wajen huɗu su Hajar suka dawo daga wajen Salon, Noor cewa tayi ba zata shiga ciki ba sai taci abinci, Khausar sai wani cin mur take tin bayan da aka gama musu gyaran gashin, gani tayi na Hajar yafi na kowa kyau duk da cewa assistance din me Salon din ce ta mata, shiyasa tace kar aje da ita ai ga irinta nan nata yafi na amaryar ma kyau, ita dai ce taga hakan don kowa da zubin gashinsa amma na Noor yafi tsada da cin lokaci ai, a palour suka zauna cin abincin, Hajar da Noor eating from the same plate Khausar na cin nata daban, a kusan tare suka ɗago jin an fito daga great room din Abba, wani irin bugu zuciyar Hajar tayi after their eye contact, Khausar ta waro ido tace "Laa Ya Nurain", Hajar kawai yake kallo wacca ta sunkuyar da kanta tana juya spoon din hannunta, Khausar tace "Yaya yaushe ka dawo..?", speaking with a repartee yace "Since 11..", tace "Okay welcome", Noor ta masa snnu da zuwa tare da gaishesa, kaf saida ya amsa gaisuwar tasu banda ta Hajar, da haka ya nufi door hands dinsa zube a pocket don daman mosque zai fita sallar la'asar, tini Hajar taji ta tsani abincin, ta ajiye spoon din ta zuba ruwa ta sha, Noor tace "kin ƙoshi ne?", Hajar ta gyaɗa kai sai kuma ta ɗauki handbag dinta ta shiga ciki. bata sake fita ba sai after magrib da ta ɗakko shoes dinta a motar Sakeena, tinda ta koma ɗaki tayi zamanta sai kace prisoner, yau ko ɗan kallon ma bata fita palour tayi ba, wajen ƙarfe goma ta tashi ta shiga wanka, bayan ta fito ne ta tsaya gaban mirror tana kallon gyaran gashin da akay mata, zaro ido tayi ganin babu ear ring a kunnenta na hagu, sharp sharp ta ƙarasa shiryawa ta saka nities dinta, hijab ta zumbula saman nities din snn ta nufi ƙofa ta buɗe ta fita don ta duba ear ring dinta, main palour kitchen duk saida ta duba ba taga ɗan kunnen ba, tunawa tayi ai ɗaxu ta fita ko wajen ɗakko shoes dinta ta yar a compound, tana buɗe door abinda ta fara ji shine pure scent dinsa, sai kuma ta hango Khausar zaune kan kujera a balcony din, bata fita ba ta ɗan leƙa balconyn ai kam ta hangosa, shima yana zaune kan kujera suna facing juna da Khausar wacca take ta zuba masa zance, ya bata rabin attention dinsa while the other half yana kan wayarsa, and worst part of it the smile on his face, ba shiri Hajar ta juya ta koma ciki, ƙafarta har harɗewa take tayi sauri ta zauna kan tiles, saida abinda take ji ya ɗan ragu snn ta miƙe still ƙafarta na harɗewa ta shiga room din Noor, sulalewa tayi kan carpet tana jin wani iri a zuciyarta, duk yacca taso ta daure amma kasa jurewa tayi, ba tasan lokacin da ta fashe da kuka ba, samm bata iya danne kuka indai ya taho mata toh sai tayi, door aka buɗe Noor ta shigo, da sauri Noor ta ajiye bowl din farfesun kazar da ta shigo dashi ta duƙa gaban Hajar da ta kasa danne kukan da ya ci ƙarfinta, with care Noor tace "Ya salam what happened Hajar...?", Hajar ta girgiza kai tana ƙoƙarin tsayar da hawayen dake zuba cheeks dinta, Noor tace "please tell me Hajar me ya faru..?", da ƙyar Hajar tace "kai na ne yake ciwo", Noor tace "Ayya Sorry bari na kawo miki drug", Noor ta tashi ta fita bbu jimawa ta dawo da glass of water da satchet din Panadol, Hajar na yamutsa fuska haka tasha maganin, zata kwanta kan carpet Noor ta mata dole ta hau gado ta kwanta, sosai zuciyarta take mata wani iri wnda bata san a yadda zata fasaltasa ba. sai wajen ƙarfe sha ɗaya Khausar ta shigo, ta ringa nunawa Noor abinda Nurain ya taho mata dashi daga China, Hajar da idonta ke lumshe duk tana ji tayi sauri ta juya musu baya tana turo baki. Washe gari da safe Khausar ta fito daga kitchen da mug a hannunta, stairs ta dosa zata hau, dakatawa tayi ganin Sakeena na sakkowa daga stairs din, Sakeena ta kalleta a takaice tace "Khausar ina zuwa haka..?", Khausar tace "Ya Nurain ne yace na kai masa Coffee", Sakeena ta ƙarasa sakkowa tace "kawo Coffee din", Khausar tayi jim sai kuma ta miƙa mata mug din, Sakeena ta amshi mug din snn ta miƙa mata paper bag din data sakko da ita tace "take it to Mami", Khausar tace "sure" da haka ta bar wajen, ita dai Sakeena tasan Nurain ba zai sa Khausar ta kai masa Coffee room dinsa ba saidai cewa yayi ta haɗa ta ajiye masa zai zo ya amsa, kamar kwa ta san hkan sukay dashi, har Sakeena ta juya zata koma saman ta hango Hajar ta fito palour, Hajar na ganin Sakeena tayi bowing tace "ina kwana", Sakeena tace "morning how are you doing...?", Hajar tace "Alhmdllh", Sakeena tace "masha Allah, Noor tace jiya kanki na ciwo how are you feeling now...?", Hajar tace "ya dena alhmdllh", Sakeena tace "Ohk toh Allah ya ƙara sauƙi", mug din Coffee ta miƙa mata tace "ki kaiwa Nurain", daram zuciyar Hajar ta buga ta amshi mug din, Sakeena ta ringa kallonta ganin bata motsa ba tace "yana room dinsa..", Hajar ta gyaɗa kai tace "ai bansan room din nasa ba", saida Sakeena taji hakan odd kafin ta kwatanta mata room din nasa, a hankali Hajar ta haura stairs din zuciyarta na ɗif ɗif, tana isa ƙofar room din nasa ta kai hannu tayi knocking a hankali, tafi minti biyu a tsaye amma no respond, tunani tayi may be ma baya ciki don haka bari ta shiga ta ajiye masa idan yaxo ya gani, da wnn tunanin ta murɗa handle ta shiga, ɗakin sanyi ƙau sai kace freezer, kaɗan ta shiga tana ɗaga kanta sukay ido huɗu dashi ta cikin mirror, a tsaye yake bakin mirror yana taje sumar kansa da towel ɗaure a waist dinsa alamar daga wanka ya fito, Hajar ta fasa ƙara ta rufe idonta da other hand dinta, a miliyan ta juya ta nufi door saida tayi karo da bango sbd idonta dake a rufe snn ta wawaki ƙofar ta fita, rabin coffee din kam duk ya zube mata a legs kuma taji zafi sosai, Nurain yayi wani murmushi irin zaki shigo hannu ne, yayi kwafa ya cigaba da combing hair dinsa, zai kamata ne wllh sai ta nemi mercy kamar yadda ya faɗa mata, duk ta gama guje gujenta da zille zillenta ai zasu koma gida ne sai yaga ƙarshen gudu. A gigice Hajar ta sauka stairs kawai taji tayi karo da mutum, Khausar ta hangame baki tana kallon jikinta da Hajar ta wanke mata shi da ragowar Coffeen, Hajar tace "please kiyi haƙuri ban...", katseta Khausar tayi da ɗan tsawa bayan ta ƙarewa palourn kallon tace "Shut up.. I don't need your apology..", Hajar ta maka mata wata shegiyar harara tace "Au haba toh kar Allah yasa ki haƙura sai kije can kisha wankin madara" tana gama faɗin haka ta kewayeta ta wuce gami da jan dogon tsaki, Khausar ta saki baki galala tabi ta da kallon mamaki.......✍️
💛 HAJAR 💛
{74..}
A fusace Hajar ta juyo ta fixge veil dinta tace "Am not single..", murmushi yayi yace "ai ko idan duk jikina kunne ne i will not believe you An mata", bata sake ce masa ƙala ba ta juya ta nufi ƙofar hall din, bai haƙura ba ya sake bin bayanta, Nurain da zuciyarsa take tafasa hundred degree Celsius sai a lokacin ya iya buɗe motar ya fito, ya riga da yayi mistake din farko da ya riƙe mata veil, wnn time din kam hannunta yaso kamowa da nufin tsayar da ita, saidai me bai kai ga riƙe hannun nata ba yaji saukar wani mugun punch a fuskarsa, tini Abokin ango ya riƙe gefen fuskarsa yana jin taste din blood a bakinsa, a gigice Hajar ta juyo tana ganin Nurain jikinta ya hau shivering, da sauri tasa hannu ta rufe bakinta gami da yin ƴar ƙara ganin bakin abokin Ango na zubar da jini, with husky voice Nurain da idonsa ya rine yace "daga yau bazaka sake mistake din riƙema wata veil ba.." da haka ya fixgi hannun Hajar zuwa inda ya yasar da motar, saura ƙiris taci da ka sbd yadda ya finciketa, fashewa tayi da kuka jin kamar zai ɓalla mata hannu tace "ni ka sakeni wayyo Ummana zai karya min hannu", front seat ya buɗe ya cillata ciki ya rufe ƙofar saura ƙiris ya haɗa da hannunta, ya zaga driver seat ya shiga da haka ya fita da motar daga event center din da reverse, wani irin cin taya yayi a kan kwalta snn ya fixgi motar with high speed ya bar area din, Hajar ta fasa ƙara ta haɗe kanta da guiwa don harta saddaƙar yau sai ya kifar dasu, gaba ɗaya Nurain daina ganin gabansa yayi sbd yadda zuciyarsa take tafasa, kawai hango yacca wnn banzan ya riƙe veil din Silly girl dinsa yake, how dare him da zaiyi ƙoƙarin riƙe mata hannu, a lokaci guda ya gangara bakin road ya tsayar da motar gami da kifa kansa ga steering, ya lumshe idonsa trying very hard to control himself, Hajar ta ɗago kanta jin ya tsaya da tuƙin, ta ɗan kallesa har lokacin kansa na haɗe da steering, after a while ya ɗago sukay ido huɗu tayi saurin janye nata, zuciyarta ta hau lugude ganin yanayinsa, Nurain exhale heavily his eye fixed on her, ya dubi dressing dinta da kyau, ji yayi kamar ya wanka mata mari amma bazai yi hakan ba, not in this situation gsky, ko a Abuja da ya mareta yasan bata ji da daɗi ba, toh this time around ma yace zai mangareta wllh sai tayi jinya, dunƙule hannunsa yayi ya sauke ajiyar zuciya, after few seconds ya furzar da iska ya cigaba da driving din, koda wasa Hajar bata sake ɗago kanta ba har suka je gida, a daidai main door ya tsayar da motar ba tare da ya dubeta ba yace "get out", jikinta har rawa yake tayi sauri ta zura takalmanta ta bude ƙofa ta fita, ɓangaren Hajiya ta shige walking gently, Hajiya da har lokacin take tare da Farooq ta kalleta tace "Ah ah ƴar nan har kun dawo daga wajen chasun da wuri haka...?", Hajar ta gyaɗa kai tace "Eh Hajiya", Hajiya ta taɓe baki tace "yo wnn ai ba chasun akai ba du du mintinku nawa da tafiya", Hajar ta ɗanyi bowing ta gaida Farooq, ya amsa da sakakkiyar fuska yace "how are you doing..?", tace "fine alhmdllh", yace "Good anata shan biki..", door aka buɗe aka shigo, Hajar na ganin wnda ya shigo tayi sauri ta shige bedroom din Hajiya, Nurain yayi kwafa ya bita da kallo sai kuma ya ƙaraso ciki ya zauna gefen Farooq ya ajiye masa key din mota, Farooq ya ringa kallonsa ganin ydda ya wani haɗe rai sai kace bai taɓa murmushi ba a rayuwa, rage murya Farooq yayi yace "ka kyauta da ka hana yarinya morewa Dinner", Nurain ya tamke fuska yace "what are you talking about...?", Sosai Farooq yayi dariya yace "Oh yeah ni dae kasan bazaka min wasa da hankali ba..", Nurain yace "Whatever", sai a lokacin Nurain ya kalli Hajiya da tin shigowarsa take kallonsa ta ƙasan glasses dinta, ya waro ido yace "Iron lady barka..", Hajiya ta katsesa da faɗin "kkkk