Showing 27001 words to 30000 words out of 60875 words

Chapter 10 - Auren Huce Haushi Book 3 Complete

21 May 2025

27801

haka abun Nan yake Kika kyaleni Ina ta bulayi da faman Shan magani? k'afata k'afarki duk inda Zan shiga a duniyar Nan Wallahi bazan iya twenty four hours ban jiki a jikina ba sai a samu matsala, fada min Dan Allah Wai menene sirrin yau though out ni sai a hankali fa gashi doctor tayi Mana tsakani Wai sai anyi two days bamu had'u ba".
Ya Kai hannunsa Yana shafa abinda yafi tsone Masa idonu a Hankali. Hannunsa ta rike tana kara narkewa a jikinsa tare da Dan kukan kissa sabanin na rabuwa da Aunty Hasaanar.
" Plsss.... meu Amor ka.....Bari da ciwo fa har yanzu zafi suke".
"Ya salam! Bari na duba har can din na gani, sorry SHADI I am very sorry nayi laifi ko? Ni kaina lokacin bana gane komai Allah yayi Miki Albarka ya bamu zuri'a masu Albarka, kin Gama min komai a rayuwa kin bani abinda ban tab'a samunsa ba, kin bani farin cikin da mafarkina da hasashena Basu taba hasaso min akwai irinsa a cikin duniyar nan ba, Dan Allah fada min duk abunda kike bukata a cikin duniyar nan matukar akwai sa zan Nemo Miki In Sha Allah".
Ya Gama fada Yana kokarin zuge zip din gaban rigar data saka Mai Dan balance wadda bazata ringa takuta Mata ba saboda ba karya taking jiki a kaijin Nan nata.
Tana a'a Saida ya duba ya gani Nan da Nan hankalinsa ya tashi.
"Previoussss! Haka gurin Nan ya kumbura gara muje muga consultant na bangaren".
"Ni fa yanzu babu ciwon sosai Kuma ai kumburin ma babu a Kan dazu, Kuna ai an bani magunguna ma Kuma Ammah ma ta turowa Aunty Hassana wasu Kuma an sawo su d'azu suma na Sha kawai ka Bari basai munje ko'ina ba".
Rigar ya gyara Mata duk jikinsa a sanyaye, Yana zargin kansa da nuna Mata karfin da yayi, Amma Kuma Shima abin ne ya wuce tunaninsa ya kasa controlling din kansa.
Kiran insha'i da Kiran wayar Hajiya Inna lokaci Daya ya shigo kunnensu zip din rigar ya gyara Mata sannan ya daga Kiran Hajiyar.
"Wai Ina zahara'un ne daga Rakiya Kuma sai naji shiru? To tazo maza yanzu nasa anyi mata irin abincin daya kamata taci Kuma taje dakina ta kwana kafin ta samu lafiya Dan Naga ba iya kawar da Kai kukeyi ba 'ya'yan zamani".
Wata munafukar dariya ce ta kubce Masa Yana jinjina karfin halin Hajiyar, tab dole ya tattara su Kama gabansu so take tasa' yayi kwanan tsaye kenan ai shifa yaga guri Yana jin ko tafiya zatayi baze iya barinta tayi kwanaki ba Dan saiya zauce gaskiya.
"Wai bakaji abinda na fada bane kayi kunnen uwar shegu dani".
"Naji Mana ai bama gidan ne, mun wuce tun dazu mun koma sai dai idan daukoki zansa ayi ku kwana tare a Nan din".
Ya fada Yana Dan Jan cheeks dinta yana kashe Mata ido daya tare da dage Mata gira Daya.
"A'a Allah ya tsari gatari da Saran shuka ai shikenan Daman gata ne Zanyi muku tunda kun gano ba haka ba ki cinye junan ku ai jiki magayi ba'a kwacewa yaro garma ga gurin Nan Bari ba shegiya bace da ubanta, gashi Nan za'a kawo Mata abinda nasa akayi Mata idan kaga dama ka Bari tayi amfani dashi taci kuma abincin idan kuma ka Hana duk Daya Wai makafi sunyi dare,duk Wanda Rai ze yiwa dad'i ai ba Kamar me Shiba".kit ta kashe Kiran.
"Subhanallahi! Allah ya kawo mu kiji min tsohuwa da Hana ruwa gudu, Bari naje masallaci na dawo mu wuce bazan iya da rigimarta ba gara mu Kara gaba kafin ta Kira Abbie yace nayi wani abun".


******* Cikin galabaita Salma ta dubi wadda ke tare da ita a asibiti.
"Dan Allah kirowo min nurse din Nan tazo ta dubuta min maganin ciwon baya da mara wallahi ciwo suoe Kamar zasu fita".
Tsaki tayi matar Mai suna Saude, tana gadin "ba dole kiji jiki ba Ina cewa da hankalinki da komai Kika biyewa wannan gantaellen yaron Nan kuka dunga badala shi namiji ai ba abin kunya gare shi ba tunda bashi da tabo mace kuwa? Ina Jin baya garin ma ya wuce warri inda yake aikin kamfani ya barki da wahal ga kin rasa martabarta ta har abada,'.
Tunda matar tafara mata magana Salma ke kuka tayi Dana sani yafi cikin kwando. Ga mahaifinta da wane Ido zata kalleshi Ranar da yaji wannan.abun data aikata, ga Mama ciwo Yana can Yana ta nukurkusarta a garin mutane,sai kawai ta fashe da kuka Mai Jinyar tata Dan haushi kasa bata hakuri tayi ta wuce Abinta ta nufi Kiran nurse din tana fadin "ba dai bin maza Kika zaba ba bakiga komai ba wallahi yarinya babu abunda Kika nema Kika rasa Amma kin biyewa wani sakarai Wanda Bai San inda yake Masa ciwo ba.
*_ AUREN HUCE HAUSHI_*

AISHAT ISAH MUSAH
Maman Fateemah.

09061432330
08055362975


DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINQAI SALATI DA DAUKAKA DA AMINCI SU QARA TABBATA GA SHUGABAN MU FIYAYYAN HALITTA ANNABIN RAHAMA MUHAMMAD S.W.W.W DA ALAYANSA DASAHABBANSA WANDA SUKA BISHI DA SALIHAN BAYI HAR ZUWA RANAR TASHIN ALQIYAMA AMIN.

Muna rokon ubangiji s.w.a ya Dora mu Kan dai dai abinda mukayi na kuskure ubangiji ka yafe Mana Dan isar Manzon Allah s.a.w.w Domi shine Mai gafara Mai jinqai.

Page. 88

________Cikin shigar Atamfa super Riga half bubu da straight siket sai gyale blue black Dan madaidaici kalar touching din ganyen jikin Atamfar ta zuba turarenta Mai sanyin kamshi, a hankali cikin nutsuwa ta ratsa parlours din ta nufi kofar ficewa daga bangaren, haka Nan taji bazata iya biye Masa ba su yiwa Hajiya Inna irin wannan rashin kirkin ba, gara taje Kamar yanda ta umarceta idan ta biyewa drama dinsu sai taji kunya a banza ba abin mamaki bane su tarar ta rigasu zuwa can din to gara ta yiwa tubkar hanci kawai.
Katin data gani a jikin wani da dan abu a jikin bangon kofar ta dauka ta zura a kofar ta bude ta fice, har lokacin gidan shiru duk da ba wani dare ne yayi ba,yanzu ba dadewa aka idar da sallar insha'i.
Ta cikin barandar Nan da tayi linking da part din Innar tayi amfani da kofar wadda har lokacin ba'a rufe da key ba ta shiga, kafin ta karasa taji Hajiyar na fadin "magajiya hada Mata da wand'ancan kafafun shanun na cikin freezer saita ringa dafa Masa a can nasan tunda yace ya tafi tafiyar zeyi baya magana biyu, Daman ai kinibibi ne yasa ya kinkimo yarinya ya kawo min ita tunda shi baya jaffarar rantsuwa, Kuma ki ...
Sallamar Zahra cikin siririyar murya ita ta katse Mata hanzarin abinda zata fad'a.
"Wa'alaiki Salam warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu, yau Naga shegantaka ni Hadiza Ashe Kuna Nan ya tadani tsaye da tsohon dare yace min kun wuce gida?".
Dan murmusawa Zahra tayi kafin tace "muna Nan fa kawai ya fada ne Dan ya zolayeki, ya fita sallah ne lokacin da Kika Kira Yana cikin gidan Nan".
"To qaraso ki zauna muyi magana Daman bana son Yana kusa kinsan ba hakuri gare shi ba akan abinda yasan Yana da gaskiya".
Har kusa da ita ta qarasa ta zauna a Kan carpet tana gaishe da Innar.
"Tashi ki zauna Nan kusa Dani dan mi Zaki zauna a Qasa akul na gara ganin haka, Nan gidan jama'a ne kada ki Kara yin haka mijinki yaro ne Amma ba karamin mutum bane,Dan Tani babu komai kishiya ce ki dai ringa yiwa iyayensa haka Amma Banda ni kada kiji nauyina ki sake Dani Kamar yanda yake sakewa dani baya boye min komai sai rigimar suce kawai nasan yaqi fada min asalin abin Shima Kuma gajen hakuri nayi na yanke Masa hanzari badan nayi haka ba da Ina tunani babu Inda ze tafi harna tsawon lokaci Nan to mutum Bai isa ya goge qaddararsa ba, haka rubutaccen al'amarin yake Sai hakuri gashi kuma ya wuce har abada in Sha Allah, kina jina ki yiwa mijinki biyayya zakiga Nan gaba yaja Miki layi da wasu mutanen a cikin danginsa to ki bishi da yanda yake so saboda nasan kome za'ayi baze Kara Hulda da wasu ba sai da gaisuwar musulunci da zumunci Amma babu mu'amala irin ta da Kuma bazan Hana ba Dan an Bata Masa kwarai da gaske, kuma Banda yarda da kowa a cikin dangi ki Zama Mai kamewa a gurin ci da Sha kinji ki nutsu ki gane Ina kowa ya dosa kafin ki yarda da kowa, akwai Yara irin ki da wadanda suka d'ara ki babu adadi a cikin dangin kowa kuma zeyo chaaa a kanki to kiyi taka tsan-tsan da kowa, duk Wanda yazo ki karbe shi da girma Amma kada ki yarda da raini a gurin ko way kuwa,ai kinji abinda na fada Miki ko?".
"Eh naji Hajiya na gode in Sha Allah Zan kula".
"Yauwa haka nake so Bari kici abincin da ze gyaraki da wuri tunda su mazan naku ba masu kauda Kai bane duk nasara sun Bata su".
Mukus Zahra tayi Dan da alama Inna irin hands free din Nan ne ba ruwanta komai ma saita fada ita.
Magajiya ta saka ta ciro Kayan abincin daga cikin basket din tasa ta shimfida table mat a Nan kusa dasu aka kawo abincin.
Sauka ki zuba Mana zahara'u Nima tayaki cin zanyi, ba musu ta tashi ta sauka ba bude babbar warmer tuwon dawa ne kaura Mai kyau sosai irin 'yar katsina din Nan sai miyar kuka wadda taji kayan kamshi da Naman rago sai yajin daddawa da pure man shanu, Zahra na ganin abincin ya tuna Mata da mubi kusan haka abincin Inna mainuna yake.
"Matso da wancen kwanon ki Zubar ki Fara cinsa so nake yabi Miki jiki ko kin warware da wuri,Ni Miko min ruwan can da silver na wanke hannu na".
Saida Hajiya Inna ta matsawa Zahra ta ci dahuwar kusan rabinsa sannan ta kyaleta tace taci tuwon Shima,Dan kad'an ta zuba Hajiyar Ba tayi Mata korafi ba tasan cikinta ze iya cika Amma ta matsa ta zuba yajin da man shanun sosai a cikin miyar tana cikin cin tuwon ya shigo da sallama da alama ita yake nema dan har wani ajiyar zuciya yayi.
A hankali yake takowa har inda suke zauna idonsa Yana Kan Zahra, ita Kuma Hajiya Inna nata idon na kansa tana kallon ikon Allah Dan tamkar ya cinyeta danya yake kallonta.
"Kai Kuma lafiya irin wannan kallon qurillah ai har ka gano muninta haba".
"Me Kika Bata Naga tana jibi a goshinta duk A/Cn dake aiki?"
Wani kallon baka da wayo tayi Masa "abinda nanu iyayen suka bamu a rin wannan lokacin na Bata ba dai ka kawo min ita ba ai kayi Mai wahalar".
Zama yayi musa da Zahra Yana Kai hannunsa a goshinta ya Dan shafo gumin.
"Kinga fa Hajiya".
Ya nuna Mata tafin hannunsa, na gani hakan ai shi nake son gani Daman,gashi Nan Idan zakaci ta zuba maka Idan bashi kake so ba kaje ga naka can a Kan tebirin nasara kaci".
"A'a ai kowa yabi tunda taci ai nima dole naci".
Hannunsa ya wanke ya saka cikin abinci Zahrar, Loma Daya yayi da kyar ya hadiyeta saboda yaji.
"Haba Hajiya kinji kuwa abincin nan? Previous maza cire hannunki ai sai ciwo ya kamata kisani a uku".
"Ungo nan, ita ai wannan babu abinda ze Mata sai gyara".
"A'a abar shi gaskiya da matsala" ya fada Yana wanke hannunsa.
Kallonsa Zahra take duk ya gigice ita fa bataji wani yaji ba tana tunanin abinda taci ne yasa gumin ke tsatsatowa Dan ta Fara Jin can kasanta daga cikin Kamar ana hada wani Abu sai wani Abu takeji.
"Ikon Allah na kwance ya fad'i to Kai Daman Ina ruwan biri da gada kaje kaci nake ita ta fada maka bazata iya ci ba Ina ganin idan Allah ya kawo haihuwa Dole ka kawo min ita Nan in dai Allah ya ara Mana numfashin".
Gaba yayi baice komai ba ya nufi dining ya zauna,lokacin Zahrar ta ida cinye Dan sauran Daya rage tana wanke hannunsa.
"Tashi kije ki bashi abinci, ni Zan shiga daga ciki da safe magajiya zata kawo Miki kayayyakin dana aka hada Miki ki kula da kanki sosai su maza da Kika gansu ba hakuri ke garesu ba bare wannan miskilin Daya shafawa idonds kwallin rashin ta Ido baya Jin komai Dan Ina guri cewa fa yayi ko daukoni za'ayi naje gidan ku mu kwana, to kuwa ba karamin aikinsa bane yayi abinda zesa na fita da gudu, nasan tunda ya ambata tafiyar zakuyi".
"Kai Hajiya Dan Allah na kwana a Nan din Mana".
"Keni rabi da kinibibi ku Kama gabanku, nagode hakan ma duk da raddi ne ya mayar min".
"Dan tagwaye mu kwana lfy na shiga ciki a rufe min kofata ta baya tunda Kaine me abin budewanda rufewar".
Tayi gaba abinda.
"Allah ya tashemu lafiya".
Ya fada tana daddanna wayar hannunsa da alama Abu Mai mashimmanci yake turawa.
Kujerar daura dashi ta janyo zata zauna ya janyota ya zaunar a cinyarsa Yana fadin.
"Me yasa kikayi min haka keda a gabanki nace Mata bama gidan shine Kika since min zani a kasuwa ko?".
Yana kwanto da kansa saitin wuyanta wannan kamshi Mai sakashi a cikin wani yanayi yaji Yana shigar masa hanci.
"Ina tambayarki kinyi shiru".
Wayar ya aje Kan table din da Alama ya Gama tura sakon, duka hannunsa ya saka ya zayayo ta saman cikinta ya Kara kwantar da kansa sosai a gefen wayan nata Yana Dan hura Mata iska kadan a gefen fuskarta.
"Ba komai kawai dai gani nayi nace Mata Zan dawo ne kaga bazataji dad'i ba idan ban dawo ba".
Dan lakuce cheeks dinta yayi "Mai wayo kawai,bani abinci naci mu tafi barci nakeji'.
Shima tuwon semovita ne da miyar agushi.
"Barshi bazanci ba".
Dago da kanta tayi ta kalleshi, Kai ya gyada Mata yana mik'ewa da ita tsaye.
"Muje ki bani coffee kawai, ji nayi Shima Kamar yajin zanji".
Ya riko hannunta suka gangaro parlour. Ta bayan suka fice ya rufe kofar suka wuce. Mai makon taga sun nufi part din da sukayi masauki Wanda ya zamar Mata wani gurin tarihi a cikin babin rayuwarta, sai taga ya nufi wata motar da akayi parking dai dai karshen barandar.
"Ina kuma zamu?".
"Inda mukafi wayo ai Nan Kuma aikinsa ya Kare sai dai Idan munyi tafiya mun dawo to Nan ne farkon sauka haka tsarin yake Nan ne kashen sallama Kuma farkon sauka".
"To muje na dauko kayana Naga Kai baka barin a dauki komai Idan ka tashi kawai gaba kakeyi baka daukar komai Ni kuma da magunguna a ciki".
"Cool down shadi, harda turarikan dake hanani sakat na dauko ai ba'a Wasa da garin gona, Fad'a min wai waye ya baki wadannan turarikan ne?".
"Ance kada na fad'a maka fa".
"Kai! harda sirrin da Zaki boye min yanzu precious? Ni fa na Gama ganin karshen sirrin?.
Ya Dan shafi wani guri.
"Wash!!! ka Bari Dan Allah, wallahi da ciwooo har yanzu. Kuma turarikan Aunty Aishat ce ta kawo min su fa tace mummy Badi'a ce ta taho min dasu".
Baki ya bude ya kasa magana, babbar magana wato su Mata basa girma wallahi, Bai Kara ce Mata komai ba suka nufi motar.
Shiya bude Mata ta zauna sannan ya zagayo gurin driver ya zauna.
Suna fita taga ya dauki wata hanyar Dan kallonsa yayi.
"Ina zamu kuma Naga ka biyo ta wata hanyar?".
"Very good, gaskiya kina da sharp brain in some days kin Fara gane Kan garin nan, to Nan bypass ce zamu bi".
Sunyi nisa Zahrar ke nuna Masa wata mota a bayansu wadda take binsu sauda kafa Kuma taki wucewa.
Hannunta dake cikin nasa ya Dan qara matsewa.
"Kina tsoron kada ayi kidnapping dinki sunga kalar da za'a karbi dollars ko?"
a tsora ce da dube shi "Da gaske kenan ana yin abin Nan ga garin nan?".
"Of course ana yinsa sai dai in Sha Allah kina da kariyar da babu Wanda ze iya cimmiki ta zahiri data badini, wannan motar su zayyan ne a cikinta da Shirin Kota kwana shine Babban guard dina Yana tare da yaransa ne na zahiri kenan, kinsan wasu sun wuce mu suna gabanmu kosu zayyan din Basu San da zamansu ba, wasu Kuma suna bayan su zayyan din ai kin gane, ko ke kadai ce Kika fito to ki qaddara team kusan uku suna biye dake duk inda Zaki shiga kuwa ba mazan ba ba matan ba".
"Mata Kuma?'.
Kai ya gyada Mata alamar haka ne "kina mamakin hakan ne?".
"Eh gani nayi aikin maza ne wannan'.
Saida ya shiga wata kwana sannan yace Mata.
"Ai kuwa Mata suna bada gudunmawa sossi a cikin aikin DSS sunyi abinda mazan basuyi ba gurin Kama criminals sai da aikin akwai risky a cikinsa sosai gaskiya" .har suka shiga unguwar tasu ta mawadata Yana yi Mata bayanin irin gudunmawar da Mata ke badawa.
Lokacin da suka shiga ciki shiru gidan ba motsin kowa Amma ko Ina neat sai kamshi ke tashi da sanyi mai nutsuwa.
Hade jikinsu yayi Yana Kara shinshinarta.
"Previous da sauki ko? Tunda Naga tafiyar ta Dan gyaru muje kiji dani wallahi a matse nake dake?".
Bai jira amsar ta ba yayi sama da ita ya nufi stairs.
Kuka take Masa ba k'ak'k'autawa shi kansa ya rasa dalilinsa na koma Mata duk da itama ta bada goyon baya kafin yayo famin Daya ruda Mata lissafi, Tasha sambatu kamar ze zauce yau dai da Bata Suma ma taji abinda ya girmi kunnuwanta Albarka kuwa har Amminta yau Tasha ta saboda jiya baze iya karar da komai ba Amma na yau yayi abin cikin hankali da nutsuwa yaji wani bakon lamari tunda itama ta taka rawar gani kafin labarin yasha banban Amma dai taji jiki saida yayi ta faman ban Baki da lallashi saboda Kuka wiwi ta rirrik'e shi tana yinsa ga Daman ya lafiyar kura.




******** Karfe goma Mai kyau Abba ya sauka a sokota shida Hamza da Abdul Hakeem,. Sameer ne yaje airport ya dauko su direct asibitin suka nufa, lokacin da sukaje dakin likitan bayan Nan yaje round duba patient dinsa basufi minti biyar ba doctorn ya dawo office hannu sukayi dasu Alhaji Jafar tunda ya gansu da Sameer yasan mijin matar can ne patient din DANGE.
Tare suka shiga ciki Saida suka zauna sannan doctor din ya cire glass din dake idonsa ya dubi Sameer Yana fadin .
"Alhaji ne mijin patient din tamu?'.
"Eh shine doctor kuma sirikinku shine mahaifin ita wife dinsa".
"Ah haba dai?".
"In Sha Allah haka yake".
Wata gaisuwar ya Kara yiwa Alhajin Yana fadin .
"Ai Dange abokina ne tare mukayi karatu a UK dashi sannu da hanya, to Alhaji Yaya akayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login