Showing 12001 words to 15000 words out of 120027 words

Chapter 5 - Halysaah Book 3 By Khaleesat Haydar

because he makes sure everywhere is clean, ko nace zan yi gyara gyara da asuba sai in ga ko ina neat, kinga yana gyarawa kenan" Safiyyah ta rike haɓa tana kallonta da mamaki, can tace "Tabb, to ku kuma haka naku salon auren yake kamar yanda ake yi a film? Ba ruwansa ma ko kina lafiya ko otherwise a matsayinsa na mijin ki? Ko kun mance mata da miji ne ke da shi?" Khaleesat tayi ma Safiyyah wani kallo sai kuma ta kauda kai, Safiyyah tayi shiru tana ta kallonta kamar dai tana son yin tambaya amma bata san ta yanda zata fara tambayar ba, bayan few seconds kawai tace "So you mean ba ku ma taɓa kwana daki daya ba kenan har yanxu da shi?" Khaleesat ta juya ta kalleta tace "Daki daya kamar ya? Saboda me za mu kwana daki daya?" Safiyyah ta zuba mata ido tana kallonta, Khaleesat ta kauda kai fuska daure tace "For what reason za mu kwana daki daya?" Safiyyah tayi mata kallon gefen ido kamar dai tayi shiru sai kuma dai tace "Kin fi ni sanin reason din ai" Khaleesat taki kallonta tace "Ban san wannan reason din ba" Safiyyah tayi er dariya, bayan kusan minti daya tace "No matter yanda aka yi auren dai mijin ki ne shi ki ji in gaya maki, in ma ke kika ki yarda ku kwana daki daya nasan kin san repercussion din hakan, ba ruwan Allah da yanda aka yi auren ko kuma abubuwan da suka janyo aka yi auren, aure dai aure ne koma yaya yake, yanxun nan sai ya kai ki wuta idan baki yi hankali ba" Khaleesat ta fara harhada kayan karatun ta without looking at Safiyyah cause she finds the conversation nasty in her ears, a takaice tace "Zan tafi gida since we are done with today's lecture....." Safiyyah dai kallonta kawai take, can ta ɗan yi murmushi bata sake cewa komai ba, har sai da Khaleesat ta mike zata bar wajen sannan Safiyyah tace "Yau kuma da wuri zaki koma gidan kenan? ke da kike jin kamar ki dawo kwana cikin makaranta tsabar rashin son zaman gidan?" A takaice Khaleesat tace "Ehh, na gaji ne yau, bacci zan je gida in yi... Sai gobe" Daga haka tayi wucewarta tana dialing number driver dinta don yana nan area din, Safiyyah dai ta bi ta da kallo tana murmushi a ranta ta fara tunanin banda dai abubuwan da suka faru wacce mace ce zata samu irin Ajay tayi ta claiming bata son sa? Ai sai dai shi yace baya so cause he gat everything, ilimin ne, kyan ne, asalin ne, wayewar ne, ko kuma dukiya? uwa uba ga sarauta, ai sai dai macen ta yaudari kanta tace bata so, although tasan ita dai Khaleesat da gaske take har cikin ranta ba lallai duk wannan qualities din su yi freaking dinta ba tunda ita ga wanda zuciyarta ke so.... Khaleesat ta dade bata ji haushin Safiyyah ba kamar irin wannan rana, she was really angry at her cause bata yi expecting irin wannan maganar daga gareta ba, ta yaya zata gaya mata haka ita da bata taɓa kallon Ajay a matsayin wanda za su yi wani abu wai shi aure tare ba, status dinta da shi will remain the way it is, ba wani aure a tsakaninsu, shima kuma a wajensa tasan irin kalan tunaninta yake yi, bazai taɓa kallonta a warce za su yi rayuwan aure ba, basu hango wani abu wai tarayyan aure between dem ba, har ta isa gida her mood was really spoilt, ta bude motar ta sauka tayi wucewarta cikin gidan, Allah ya so gobe Saturday ba ma ta da lectures balle taje school ta hadu da Sophie taji sabon takaici, ita da kullum ke cewa an ci amanar Housemate menene zai kai tunaninta zuwa irin wannan tunanin da tayi yau, what came over her to think that way? wato so take a ci amanar Housemate din da gaske kenan, tsaki Khaleesat tayi ta shiga cikin parlor, as usual babu kowa parlon tayi wucewarta sama zuwa daki, wanka tayi ta canza kaya tayi sallah tayi kwanciyarta, sai wajen biyar da rabi ta fita daga dakin zata tafi kitchen ta dora girki yanxu dai kwata kwata ta dena ganin Legend, tun da ta sauko downstairs take kallon wanda ta gani zaune cikin parlon har ta karaso inside of the parlor sannan ta gaishesa, ya juya ya kalleta greeting her also, Ajay dai na zaune parlon yana danna wayarsa fuskarsa babu yabo babu fallasa, sauke kanta tayi ta nufi kitchen, tana shiga kitchen din da few minutes sai ga Ajay ya shigo ta juya tana kallonsa ya hade rai yace "Ke baki da hankali ne da kika ga mutum a parlon baza ki koma sama to cover ur self up properly ba?" Ita dai bata ce komai ba tana dibar vegetables da zata yi amfani da shi wajen girki, ya juya ya fice daga kitchen din, kusan awa daya tayi a kitchen din tana girki don ba iya ita da Driver ta dora ma girkin ba har da Walid da ta gani a parlor, bayan ta gama ta fito har sannan Walid na parlon, Ajay ma na zaune and none of them is saying anything kamar kurame, shi Ajay wayarsa kawai yake dannawa at the same time yana operating din laptop dinsa dake gefe, shi kuma Walid kallon TV yake ya ƙishingiɗa kan 2 sitter, Khaleesat ta wuce sama Ajay ya bi ta da kallon gefen ido. Sai a sannan Ajay ya juya ya kalli Walid yace "Oxford din nan garin suka maido convocation din nasu na wannan shekaran kenan?" Kamar Walid bazai ce masa komai ba, sai kuma dai yace "How will that be possible?" Ajay yace "Da na ganka a nan ne nayi tunanin a nan kasar za su yi convocation din" Walid ya kallesa yace "However, su Aunty ma idan suka ga dama nan gidan za su sauka not England, cause babu inda aka ce an siya gidan nan da sunan just one or two persons...." Daga haka ya mike yaki jiran yaji me Ajay zai ce yayi wucewarsa sama ya tafi dakin da yake sauka idan ya zo gidan, wanda rabonsa da Maryland yayi 3 years yanxu, after a while Ajay ya mike ya tafi sama shi ma ya nufi bangarensa. Khaleesat ta idar da sallan magrib ta fito sanye da hijab dinta har kasa ta sauka downstairs zuwa kitchen zata debi abinci, tana shiga kitchen din taga an ci abincin an bar plate da mug din da aka sha Coffee a sink, tunda take gidan bata taɓa ganin an bar used utensils unwashed a kitchen ba, sai da ta fara wanke plate din ta goge inda aka yi littering da abinci sannan ta dau plate ta fara dibar wanda zata ci kenan aka bude kofar kitchen din ta juya, Walid ne ya shigo ya kulle kofar, ta sauke idonta ta kauda kai ta ci gaba da abinda take, yace "Akwai abincin ne?" Kai ta gyada masa without looking at him tace "Akwai...." Ya dau plate ya karasa har inda take tsaye ya tsaya yana kallonta yace "Can i have some of it?" Bata yi tunanin zai karaso har wajenta ba hakan ya ɗan sa ta daburce ta gyada masa kai da sauri tace "Ga abincin nan...." wanda ta fara zubawa a plate ya dau spoon ya diba ya kai baki yana gyada kai yana kallonta kamar me kirga kalamansa yace "Waow, you are a great cook, the meal taste delicious, did you learn catering? Are you a chef?" Ita dai sai kokarin matsawa take daga kusa da shi don dab da ita ya tsaya, bata yarda ta dago kai ba ta fara zuba wani abincin a plate with confusion, hannu ya kai ya rike plate din har hannun nasa na taɓa nata yace "John Hopkins kema kike na gan ki big gal" Ƙin cewa komai Khaleesat tayi tsabar shock, kawai bata ankara ba taga ya kai hannu chin dinta ya dago kanta yana kallon fuskarta yace "Hey I am asking you a question" Daburcewa tayi ta fara gyada masa kai alamar eh, sai kuma ta sakar masa plate din ta juya zata bar kitchen din yayi saurin rikota yace "Kee, are you alright? Ina maki tambaya zaki fita" Warce hannunta tayi da sauri ta fice daga kitchen din zuciyarta na bugawa, sama ta tafi tana waigen ko ya biyota don duk ya tsorata ta, tana shiga Bedroom dinta ta kulle kofar ta tafi gefen gado ta zauna with shock tana processing abinda ya faru.

*Halysaah is 500 via 3276052019 Hauwa Bello Jiddah, ur evidence via 07087865788*
HALYSAAH PAGE 109

Wajen karfe goma Khaleesat na kwance daki duk da yunwan da take ji taki fita ta zuba abinci saboda fargaban haduwa da Walid, har sannan mamaki da shock da tsoro sun ki barin ta, she couldn't believe her self, bude kofar dakin taji anyi ta mike zaune da sauri tana kallon kofar gabanta na faduwa, ganin Ajay ne sai da ta sauke boyayyen ajiyar zuciya, ta koma a hankali ta kwanta, ya tsaya daga bakin kofar yana kallonta yace "Have you dish the food for you self ko katti kawai kika yi ma girkin dama?" He asked that question because sau hudu yana ganin Walid na cin abinci daga sanda ta gama girkin zuwa yanxu, ta sauke idonta murya can kasa tace "My waist is aching me, bazan iya zuwa downstairs ba kuma" Yace "To wa zai je maki downstairs din? Ke tsohuwa ce da waist din ki zai maki ciwo" Ita dai tayi shiru bata ce komai ba, jin bai sake cewa komai ba ta daga kai ta kallesa taga kallonta yake, ta sauke idonta, juyawa yayi ya fita daga dakin ya kullo kofar, after almost 10 mins sai gashi ya dawo dakin da plate din abinci da bottle water, ko kallonta bai yi ba ya ajiye abincin a gaban mirror ya fita daga dakin, ajiyar zuciya ta sauke ta mike ta tafi ta dau abincin cause she was very hungry, a nan dakin ta bar plate din bayan ta gama cin abincin gudun ta fita da plate zuwa kitchen ta sake haduwa da Walid, ta tafi bandaki ta wanke bakinta don tayi wanka tun sanda tayi isha'i sannan ta dawo, kofar dakin ta nufa tana kallon kofar wishing me makulli ne amma keyless door ne, and she don't know the Code, kawai ta kashe wutan dakin tayi addu'a ta kwanta tunani iri iri na yawo a ranta, a haka bacci ya dauketa. Ajay na zaune parlor yana danne dannen laptop har kusan karfe sha dayan dare, Walid ma na parlon yana kallon TV ba me cewa kowa komai cikinsu, daga karshe Walid ya kwanta kan 3 sitter ya dora handkerchief dinsa a fuska, har karfe sha biyu da rabi Ajay na parlon, daga karshe ya juya ya kalli Walid don for an hour now same position yake alamar yayi bacci tun daxu, mikewa Ajay yayi ya kashe TV din da wutan parlor ya dau laptop dinsa ya wuce sama, kofar dakin da Khaleesat take ciki ya bude ya shiga ya kunna wutan dakin yana kallon saman gadon, tana kwance ta rufe har kanta da duvet tana bacci, duk da ba frequently suke haduwa a gidan ba amma kusan duk dare idan ya gama abinda yake yi yakan zo dakin ya tsaya daga nan bakin kofa ya dubata, wani lkcn karfe dayan dare wani lokacin biyu, duk ya bude kofar kuma zai ganta kwance ta rufe har kanta tana bacci, kashe wutan dakin yayi ya fita ya jawo kofar ya rufe sannan ya nufi bangarensa. Cikin bacci Khaleesat taji ana kokarin sauke duvet din jikinta, ta bude ido da sauri ta rike duvet din gam ta yunkura ta mike zaune duk da bata ganin koma waye saboda duhun dakin cikin firgici tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un" Muryar Walid taji yace "C'mon, why do u have to close ur face while sleeping, do you want to suffocate ur self?" Sosai hankalinta ya tashi ta fara komawa baya tana rike da duvet dinta taki barin ya sauke daga jikinta tace "Don girman Allah ka fitar min a daki, me yasa zaka shigo min daki? Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un" Yace "Hum, just to compliment you Halysaah, you've got a beautiful glowing skin and a fine body structure....." in hankalin Khaleesat yayi dubu ya tashi a wannan moment din, muryarta na rawa tace "Don Allah kayi hakuri ka fita plss" Yace "C'mon, meye big deal don na shigo dakin ki? why are you acting like a bush girl warce bata waye ba, sai kace ba a abroad kika yi karatu ba?" Kunna wutan dake kusa da gadon yayi yanda zai dinga kallonta da kyau, da sauri ta fara kokarin komawa daya bangaren gadon tana gyara hularta da ya kusa cirewa daga kanta, ya fixgota ya hau kan gadon yana rike da ita speaking in a low tone yace "Hey listen to me Halysaah, stop acting like you don't know where i am headed, this is just between i and you, beside i will even be more active then him ur so called husband, if you don't co-operate now i promise even without ur co-operation i will get what i want wallahi, balle gwara kiyi co-operating yanxu kawai a wuce wajen, just once, after this I won't bother you again...." Khaleesat bata san sanda ta kwala kara ba tsabar yanda ta gigice da kalamansa ta gatsa masa cizo da karfi a hannu don har sannan yana rike da ita yana kokarin cire duvet din da taki sakewa, tsabar tashin hankali har wani zufa da zafi take ji duk da Ac dake kunne dakin, lokaci daya ya saketa bayan ta kurma ihun ya mike da sauri ya ciro wata karamar wuka a aljihunsa yana nunata da shi cikin kakkausar murya yace "I will deal with you, kuma na rantse da girman Allah kika ce zaki gaya masa sai na hallaka ki kuma babu abinda zai faru wallahi, kin dai ji na rantse, kuma i will definitely get what I want" Yana fadin haka ya kashe wutan jikin gadon da ya kunna ya nufi kofa da sauri ya fice daga dakin ya kullo kofar in a haste ya sauka downstairs kamar yasan reaction din da zata yi kenan shi yasa sai da yayi wanka ya canza kaya don kar ma dakin ya dau kamshin turarensa sanin how sensitive his step brother can be, Khaleesat kuwa bata fasa ihun da take ba cikin firgici da tashin hankali, bude kofar dakin aka yi lokaci daya aka kunna wutan dakin, ya nufeta da sauri yana kallonta yace "Me ya faru?" Sosai ta fashe da kuka tana sauke numfashi, har lkcin kuma tana rike da duvet din jikinta gam gashi duk ta hada zufa, bai san sanda ya zauna kusa da ita ba yace "Bakya ji na ne? What happened?" Cikin rawan murya tace "I had a dream" Da wani expression yace "Dream? What dream?" Taki cewa komai tana kuka tana sauke ajiyar zuciya, bin dakin ya fara yi da kallo, sai kuma ya kalleta yace "Didn't you pray before sleeping??" Cikin shesshekan kuka tace "Nayi" Jawo pillow dinta yayi kusa da ita yana kallonta yace "Kwanta...." Ta fashe masa da sabon kuka ta matso kusa da shi kamar zata shige jikinsa muryarta na rawa tace "Ni wallahi bazan iya kwanciya a dakin nan ba" ya dinga kallonta, sai kuma ya cire duvet din jikinta ya mike yace "Come down" Da sauri ta sauka daga kan gadon tana goge hawayen dake sauka idonta, rigar bacci purple ne jikinta ya ɗan wuce gwiwanta, Ajay dai ya kauda kansa daga kallonta yayi shirun kusan minti daya, ita dai tana tsaye kusa da shi tana zare ido, can ya juya ya kalleta yace "Mafarkin me kika yi?" She look so afraid and confused tace "Kamar na manta" Wani kallo ya watsa mata, ta fara wani sabon kukan, yace "Mu je" Da sauri ta nufi kofa yace "Ke, ina hijab din ki?" Ta dawo ta tafi ta dau hijab din sallanta ta saka, kofa ya nufa ta bi bayansa da sauri, ya jira ta fito sannan ya kashe wutan dakin, ko jiransa bata yi ba ta nufi bangarensa shi dai ya bi ta da kallo kafin ya bi bayanta, zaune ya ganta kan kujera a parlor ta hade kanta da gwiwa tana shesshekan kuka, ya karasa har inda take zaune ya zauna, a tsorace ta dago tana komawa baya jin mutum kusa da ita, sai kuma ta fashe da kuka a hankali, yace "Ke, gaya min mafarkin me kika yi?" Cikin rawan murya tana kallonsa tace "Tsoro nake ji" Mikewa yayi yace "Ta shi" ta sauka daga kan kujeran yayi leading dinta har zuwa Bedroom dinsa, tana shiga dakin bata jira yace mata komai ba ta cire hijab dinta ta ajiye kan kujera ta tafi saman gadonsa, dai dai inda yake kwance kafin yaji ihunta ta tafi ta kwanta ta jawo duvet dinsa ta rufa jikinta har kanta da shi, ya ɗan hade rai ya kauda kai, bayan few seconds kawai ya juya ya fita daga dakin ya kullo kofar, Ya tafi kan 3 seater dake parlonsa ya kwanta har sannan fuskarsa a daure, duk da kamshin turarensa da ya cika Khaleesat ta ko ina both kan gadon, pillonsa da bargonsa haka bacci me nauyi ya dauketa.

*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah, ur evidence via 07087865788*
HALYSAAH PAGE 110

Da asuba Ajay ya shiga Bedroom dinsa zai dau darduma ya kunna wutan dakin mara haske sosai ya juya yana kallonta, ya kusa seconds talatin tsaye yana kallonta, can dai ya karasa har kusa da ita ya duka to be sure of what he is seeing, ya kara kunna wutan bedside lamp still looking at her, da mamaki ya kai hannu yayi raising gashinta yana feeling texture din, can ya cire hulan kanta da kadan ya rage ya fita daga kan nata yana kallon gashin gaba dayansa, lokaci daya Khaleesat ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login