Showing 18001 words to 21000 words out of 120027 words
ta juya kawai tayi tafiyarta ta bar wajen, cikin bacin rai ta nufi inda driver ke parking yana jiranta. Khaleesat na isa gun motar ta bude back seat zata shiga, still tayi tana kallonsa, yana zaune driver seat ya saka Black glasses irin no respect din nan yana kallon gabansa kamar bai san ta bude motar ba, ta ɗan taɓe baki ta rufe back seat din ta bude front seat ta shiga motar, Without looking at him kamar ana tilasta ta tace "Good evening" Bata ji ya amsa ba ya ja motar suka bar wajen, ba hanyar gida taga ga nufa da ita ba, ita dai tana ta kallon hanya wondering where he is taking her to, sai da suka yi tafiyar kusan awa daya sannan yayi parking a wani babban Mall, ya kashe motar ya sauka, ganin bata sauko ba yace "Don't waste my time" Bude motar tayi fuskarta babu walwala ta sauka, yana gaba tana biye da shi suka shiga wajen, Abayoyi masu tsadan gaske da dogayen riguna ta dinga gani, ita dai tana biye da shi a baya, without looking at her yace "Pick the ones u need" Ta daga kai ta kallesa, yana duba agogon wrist dinsa yace "Do not waste my time" Ita dai tayi shiru bata ce komai ba, can ta daga wani Abaya da take ta kallo tun da suka shigo wajen, tana ganin price dinsa bata san sanda ta mayar da sauri ba, taga ya dau Abayan yana dubawa, ita dai kallonsa kawai take, ya duba size din, daga haka bai sake bin ta kanta ba ya ci gaba da duba Abaya da tsadaddun dogayen riguna yana daukan wanda yaga yayi kyau, sai da ya dau riguna biyar duk masu shegun tsada a wajen, don mamaki ma abun ya bata, yayi payment suka fita wajen ya shiga wajen takalma da jakunkuna designers, ta buda ido sosai tana kallonsa, nan ma duk shi ya zabar mata kala uku uku har tayi mamakin ta yaya yasan size din takalminta ga riga ma da ya siya yasan size dinta, sosai jikinta yayi sanyi ganin prices din items din da yake dauka ba na wasa bane, bayan yayi payment suka fita daga wajen takalman kuma duk shi ke rike da kwalayen da aka zuba masu kayan, ta wani zaro ido ganin wajen designers jewelries zai shiga, ita dai a hankali take tafiya tana bin sa a baya, nan ma set din jewelries lafiyayyu uku ya daukar mata ita dai tana ta kallon ikon Allah, taga ya kara mata da zobuna biyu duk designers, sai wristwatch, zoben ne ma ya bata ta gwada without looking at her, daga nan ya biya kudaden suka fita daga wajen, inda ake siyar da hair accessories irin na turawa ya gani ya shiga wajen tana dai biye da shi cikin sanyin jiki, hadaddun ribbons din gashi ya siya mata iri iri bayan ya biya suka bar wajen sannan suka fita babban Mall din gaba daya, she don't even want to start calculating the amount he spent in just this shopping cause the money was huge especially when converted to Naira, millions masu dama kenan fa in anyi lissafi, bayan mota ya bude ya ajiye kwalayen kayan hannunsa sannan ya bude driver seat ya shiga, ita ma ta shiga gaban motar ta kulle, sae da suka kusa gida after almost an hour and 15 mins ride sannan ya tsaya wani eatry ya siya abinci takeaway biyu, daga nan kuma suka wuce gida wajen karfe bakwai na dare.... A nan parlor Ajay ya bar mata kayan a takaice yace "Get ready za mu yi tafiya gobe karfe biyar na asuba, iya wa ennan kayan zaki tafi da" Yana kai wa nan ya wuce sama ta bi sa da kallo, a hankali ta dau package din kayan gaba daya ta wuce sama ta kai daki, kara fitowa da kayan daya bayan daya ta dinga yi tana duba su, ya subhanallah... they were soo beautiful and unique, the designer bags and shoes where more than gorgeous, har cikin ranta suka yi mata kyau sosai, gashi ya iya zabe ya ma fi wata macen iya zaban kaya, ta gwada takalman taga kamar don kafanta aka halitto su, ta zaune gefen gado ta fito da jewelries din su ma tana duba su, they were screaming nothing but luxury, ta gwada 2 rings din dake ta kyalli ta ɗan yi murmushi sai kuma murmushin yayi fading daga fuskarta ta cire su a hankali ta ajiye bayan ta tuna zoben da Housemate dinta ya siya maya, lokaci daya duk mood dinta ya canza, ɗan farin cikin kayayyakin da take yi yayi disappearing at once daga ran ta, tafi minti sha biyar zaune kafin daga karshe ta mike a hankali ta goge hawayen dake makale idonta ta nufi banɗaki zata yi alwala, sae da tayi sallan magrib sannan ta fita daga dakin, ta jima tsaye corridor as if contemplating on what she is about to do, at the end kawai ta karasa ɓangarensa tana tafiya a hankali ta bude kofar ta shiga kamar munafuka, yana zaune parlor ta samesa yana duba wayarsa, taki barin su hada ido ta tsaya jikin kujera a hankali tace "Thank you so much for the wears, Allah ya kara budi" Bai daga kai ya kalleta ba, bayan few seconds taji yace "Thank God instead" Still not looking at him tace "Okay" Daga haka ta juya ta fita daga parlon ta kullo masa kofa, sai bayan da ta koma daki ta fara tunanin kaddai fa convocation din Hadiyah za su je gobe, sosai gabanta ya fadi bayan wannan tunanin ya zo mata rai, lokaci daya jikinta yayi mugun sanyi taji ƙafafuwanta sun mata nauyi sun ma kasa ci gaba da daukan ta, anya zata amince ta bi sa kuwa? da kyar ta karasa edge din gadon dakin ta zauna kamar warce ruwa ya cinye tunani iri iri na yawo a ranta, after some minutes ta jawo wayarta cikin sanyin jiki zata kira Safiyyah ta gaya mata.
*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah, ur evidence via 07087865788*
HALYSAAH PAGE 112
Karfe hudu dai dai na asuba Ajay ya bude kofar dakin da Khaleesat take ya kunna wutan dakin yana kallonta, bacci take ta rufe har kanta da Duvet, ya karasa kusa da gadon ya sauke duvet din yace "Kee" firgit ta bude ido ta mike zaune da sauri tana komawa baya, sai kuma ta fara duba hulanta a kan gadon zata rufe gashinta, juyawa yayi ya fita daga dakin, ta jawo wayarta tana duba agogo taga karfe hudu da minti biyu, ajiye wayar tayi ta sauka daga kan gadon ta shiga bandaki.... Kafin karfe hudu da minti hamsin Khaleesat har ta gama shiryawa dama tun daren jiya ta hada duk sabbin kayan da ya siya mata a box dinta ta shirya, tana tsaye gaban madubi tayi oiling dogon gashinta tana combing dinsa zata daure da daya daga ribbons din da ya siya mata jiya, sai kallon baƙin gashin nata take ganin kamar ya kara yawa ma, banda sheki babu abinda gashin yake, bude kofar dakin aka yi ta juya da sauri ta kalli kofar tana daure tulin gashin nata waje daya cikin hanzari, kallo daya yayi ma gashin yace "Ke Malama you are wasting my time, ko bakya duba agogo ne" Ta ɗan turo baki ta dauke kanta tace "Ni sai nayi sallah tukunna" Tana fadin haka ta ci gaba da abinda take, can ta juya ta kalli direction din kofar taga ya bar wajen, biyar da kusan minti goma ta fito daga dakin da box dinta da handbag ta sauka downstairs, high waisted palazzo ta saka with matching top sai karamin veil dinta da handbag tayi kyau sosai ba kadan ba duk da babu abinda ta shafa a fuskarta sai eye pencil da ta sa a idonta, yana zaune parlor alamar ita yake jira, jin footstep dinta ya juya ya kalleta sai kuma ya dauke kai, kara kallonta yayi kamar zai yi magana sai kuma dai ya fasa ya mike ya nufi kofar parlon ta bi bayansa tana jan trolley dinta, driver na tsaye jikin mota yana jiransu, yana hangota ya tafi ya amshi box din hannunta sannan ya bude mata back seat ta shiga bayan sun gaisa da shi, kallon Ajay dake zaune gaban motar tayi, murya can kasa tace "Good morning" Bai ce komai ba, hakan yasa tayi tunanin bai ji ba ta sake gaishesa a takaice yace "Same" Wani kallo tayi masa ta dauke kai, driver ya shigo motar ya tada suka bar gidan.... Karfe biyu saura suka sauka Ingila Ajay yayi masu order din Indrive da zai kai su har gida, sai bin sa da wani kallo take don he is not even helping with her box, iyaka hand luggage dinsa kawai ya dauka, driver din motar ya dau akwatin ya sa a booth ta bude motar ta shiga don tuni Ajay ya shiga kamar ba tare suke ba, Suna isa gida Khaleesat dai ta tsaya bakin apartment din da taga Ajay ya sa driver ya ajiye akwatin ta, ya gama wayar da yake sannan ya danna bell din apartment din, not long after aka bude kofar apartment din, step sis dinsa Baby ce ta bude kofar tana ganinsa ta rungumesa tace "Oyoyo Yaya...." Yace "How are you?" Tace "Am fine, welcome" Juyawa tayi ta kalli Khaleesat, ya dau box dinta ya mika mata yace "Can't you greet?" Baby tace "Ina wuni" Daga haka ta amshi akwatin Khaleesat ta shiga ciki, ya juya ya kalli Khaleesat dake rakube gefe daya bayan ta amsa gaisuwar Baby, ya hade rai yace "Baza ki shiga ba Malama" Shiga parlon tayi sannan ya bi bayanta ta cire takalmanta nan bakin kofa, Aunty ce zaune parlor sai Ummi uwar Hadiyah da Gimbiya Firdausi, Mami ma na zaune parlon da Hajiya Nafisa, Khaleesat sai da gabanta ya fadi sosai ganinsu gaba daya, duk suka daga kai suna kallon ita da Ajay, kasan carpet ta duka a hankali ta gaishesu tana kallonsu gaba daya, Ajay ya zauna kan kujera ba tare da ya yarda ya hada ido da su ba ya gaishesu shi ma, just Hajiya Nafisa da Ummi sai Gimbiya Firdausi ne suka amsa gaisuwansa babu yabo babu fallasa, Mami dai ko kallon inda suke bata yi ba, ita kuwa Khaleesat dama babu wanda ya bi ta kanta suka ci gaba da labarin da suke a parlon, ko ya hanya babu wanda ya tambaye su, jikin Khaleesat yayi sanyi sosai ta daga kai ta kalli Ajay dake danna wayarsa kawai, bude kofar parlon aka yi sai ga Jay ya shigo yana gyara face cap dinsa, Khaleesat dake durkushe kan carpet bata san sanda ta karasa zaunawa a kan Carpet din ba bayan sun hada ido da shi, within few seconds ya dauke idonsa daga nata, ita kuwa bata fasa bin sa da kallo ba ko kiftawar kirki bata yi, Ajay dai bai yarda ya dago kansa ba tunda ya lura Jay ne ya shigo parlon wayarsa kawai yake ta dannawa, a hankali Khaleesat ta gaida Jay har sannan tana kallonsa, Jay ya zauna without looking at her yace "Lafiya lau, sannu da zuwa" Mami na kallonsa tace "Baka zo kayi breakfast ba yau Jawwad and ur phone isn't reachable" Yace "A restaurant nayi" Mami tace "To Lunch fa?" Yace "Sai anjima" Baby ce ta shigo parlon rike da wayar Aunty ta nufeta tace "Momy u have a call" Aunty ta amshi wayar, Jay na kallon Baby ya nuna mata Khaleesat yace "Take her upstairs Baby" Baby ta kalli Khaleesat tace "Ok let go" Khaleesat ta sauke idonta ta mike ta bi bayan Baby da ta kai ta sama zuwa dakin da su Hadiyah suke, Hadiyah na kwance kan gado sai Maryam da Khadijah sisters din Walid, da Shahuda yarinyar Gimbiya firdausi ta biyu, sai Iklima yarinyar Hajiyah A'isha, ga kuma Bilkisu yarinya Hajiya Sumayya gaba dayansu cousins ne a dakin, kuma duk Shahuda ce babba sai Maryam Kanwar Walid, duk suka juya suna kallon Khaleesat kamar sun ga Alien ta shigo, ita kuwa ji tayi kamar an saka mata chain a kafa tsabar yanda ƙafafuwanta suka yi mata nauyi ganin zuka zukan matan dake dakin gashi duk sun zubo mata ido suna kallonta daga sama har kasa, tayi karfin halin karasawa cikin dakin ta zauna kasan carpet ta gaishesu gaba daya, Hadiyah dai sai kallonta take a walakance kamar taga bola, Shahuda na yatsine fuska ta kalli Baby tace "Wacece wannan kuma Baby kika shigo mana da ita?" Baby ta taɓe baki ta karyar da kai tace "I think Ya Ajay's wife, yanxu suka zo" Shahuda ta mike zaune a hankali daga kwancen da take tana kare ma Khaleesat kallo daga sama har kasa, can tace "Dama wannan ce matar tasa? Ikon Allah, ashe zabiya ce" Tsaki Hadiyah ta ja tace "Don Allah mu ci gaba da maganar da muke, what were we even saying before we were interrupted?" Maryam na kallon Baby fuska daure tace "To ke uwar wa yace ki kawo mana ita nan? Duk dakunan dake sama ki rasa inda zaki shigo da ita sai wannan? Ko baki da kai ne? Dama akwatin ta ne wancan kika shigo mana da shi daki?" Baby ta bude ido ta langwabe kai tace "Ya Jawwad ne fa ya ce in kawo ta Aunty" Hadiyah ta mike zaune jin abinda Baby tace, fuska a murtuke tana kallonta tace "Yace ki kawo ta ina? Ina kika gansa yace ki kawo ta nan, yaushe ya zo? Dalla dau akwatin can ki fitar mana da shi daga nan, kinga nan yayi kama da inda za a kawo bare" Ita dai Khaleesat kallon direction daban take babu ko kiftawan kirki tana jin duk abinda suke cewa, Iklima ta juya tana mata wani matsiyacin kallo tace "Keee duk nan da kike gani jinin sarauta ne babu wani bare, babu ordinary blood don haka can you kindly get out of here? They are other rooms ba wannan kadai bane daki a gidan nan, ko kuma ki tafi Garage dama babu komai a ciki...." Khadijah tace "Can you imagine don rainin wayo ma wani wajen daban take kallo ana mata magana ko er uban wacece ita oho, bari ki ji duk nan babu sa'an ki wallahi, mu ba class din ki bane ta ko ina, don haka get out of this room" Baby na kallon Khaleesat tace "Sun ce ki tafi wani dakin you are not welcome in their midst" Mikewa Khaleesat tayi a hankali bata dai ce komai ba, Baby ta kalli yayyin nata tace "Ko in kai ta dakin Granny kawai?" Shahuda ta jefa mata wani harara tace "Are you stupid? What is Granny's relationship with her da zaki kai ta dakinta? Ordinary person kamar ta zaki kai ta dakin Granny ko baki da kai ne, pls take her out before i loose my temper" Baby tace "Oh ohk, bari in kai ta dakin da ku ka ajiye boxes din ku to" Daga haka ta dau akwatin ta nufi kofa Khaleesat na biye da ita, Hadiyah ta bi ta da wani matsiyacin kallo kamar yanda Shahuda ma ta bi ta da kallon tsana don mutuwa ne kawai bata yi akan son Junaid ba amma daga karshe wai Khaleesat ta samesa a sama kusan a banza ba wani wahala tana er matsiyata da ita shine zata zama matar ɗan sarki me jiran Gado, Iklima ta rike haɓa tace "Dama ita ce Ya Jawwad ya so ya aura ya hadata da ke Hadiyah?" Hadiyah ta hade rai sosai tace "Plss bana son wannan maganar Iklima, keep quiet if you have nothing good to say" Shahuda ta koma ta kwanta tana jin wani irin bakin ciki a cikin ranta mara misaltuwa, gani daya da tayi ma Khaleesat taji duk duniya babu wanda ta tsana kamarta, Khadijah tayi dariya tace "Ko yaushe ma aka aurota da zata fara cuso kanta cikin abun da ya shafi gidan sarauta, who is she to intrude in our affairs? Who even invite her to this Convocation? Wallahi sai tayi da ta sanin zuwa taron nan, next time duk abinda ake a familyn gidan sarauta bazata yi marmarin sake zuwa ba balle ta shigo cikinmu, dama ace ba ordinary person bace da sauki, amma ke ba er kowa ba ki wani ce zaki shigo cikinmu ana mamaki magana ma kina kallon wani waje daban, to mun sa kafar wando daya da ita kuwa" Iklima tace "Wallahi she will regret coming to England" Hadiyah dai kokarin kiran Jay kawai take da wayarta fuskarta daure amma baya shiga. Dakin da Baby ta kai Khaleesat babu kowa ciki sai akwatunan wasu daga yan matan, a hankali Khaleesat ta zauna kasan carpet bayan Baby ta fita, lokaci daya hawaye ya fara sauka idonta kamar an bude pampo, daya bayan daya maganganunsu suka dinga dawo mata kai, Baby na sauka downstairs Jay dake zaune parlor har sannan ya kirata sannan ya mike ya fita waje ta bi bayansa, tuni dama Ajay ya bar gidan bayan da Baby ta raka Khaleesat sama, Baby na kallon Jay bayan ta bi sa waje tace "Gani yaya" Yace "Hope you gave her a separate room?" ta gyada masa kai yace "Ohk akwai abinci a gidan ai?" Ta ɗan karyar da kai tace "Akwai, fried rice Ummi suka dafa mana da chicken and Salad, very delicious" Yace "Ok now ki je ki xuba abincin ki kai mata da ruwa" Buga kafa tayi ta rungume hannu kamar zata yi kuka tace "Yaya na gaji da hawa stairs fa, sai ni ce kawai za ayi ta aika a gidan nan" Yace "C'mon Baby, be a good gal and do what I ask you" Ta langwabe kai a hankali tace "Ohk" Daga haka ta juya ta koma cikin gidan, shi kuma daga nan yayi tafiyarsa gidan da ya sauka which isn't far from this House kuma duk gidajensu ne, Gimbiya Firdausi da Hajiya Sumayya ma can suke kwana da yayar mahaifin Hadiyah, Baby tayi yanda Jay yace mata ta kai ma Khaleesat abinci da ruwa