Showing 306001 words to 309000 words out of 452169 words

Chapter 103 - Mayrah Complete By Khaleesat Haydar

MD, a hankali Ceo tace "Why not try ur luck Aliyu" MD ya daga kai da sauri yana kallonta without blinking, Ceo ta gyada masa kai tace "Zan shige maka gaba" Da mamaki still yake kallonta, can yayi karfin halin cewa "Budurwar kanina ce fa Ma" Ceo tace "So? You just told me yace ya hakura, sannan har za a kai kudin aurensa so i see nothing wrong, ai duk cikakken namiji baya saurin sarewa yanda ya sare, so may be ba rabonsa bace, and what if taka rabon ce" Shi dai kallonta yake ya ma rasa me zai ce, mikewa tayi tace "Bari ta kawo maka abinci, u need not to worry ba masu aiki bane suka yi, she made it herself, in ka gama zaka iya tafiya gobe za mu yi magana i have a call to receive" Daga haka ta bar parlon MD ya bi ta da kallo, dariya ma kawai ta basa don yasan last thing da zai iya on earth kenan dating his brothers once girlfriend balle har aje ga ya aureta, don ko dazu da safe a kaduna babu yanda bai yi da Musharraf kan ya janye maganar cewar ya hakura da Mayraah amma ya ki, Mami kuma na supporting dinsa don bata son a sake breaking heart din ɗan ta for the second time, with the way Ceo reacted a parlon ranan da kuma yanda Ammi tayi saurin backing dinta hakan kawai ya nuna tana da wata manufar daban akan Mayraah shi yasa duk familyn suka ma cire ran za a ba Musharraf Mayraah, wani tunani ne ya fado ma MD, yayi shiru yana nazari, Ceo na tafiya babban dakin da ta sa masu aiki suka kai box Mayraah taga bata cikin dakin, hakan yasa ta fito ta nufi bangaren kanwarta, tana bude kofar dakin ta ganta kwance gefen uwarta dake bacci, karasawa tayi bakin gadon tana kallonta Mayraah dai ta kasa daga kai ta kalleta, Ceo ta mata alamar ta taso don bata son tashin er uwarta, Mayraah ta sauka daga saman gadon a hankali, Ceo ta kama hannunta suka fita daga dakin, bayan ta kullo kofar tana kallon Mayraah soothingly tace "Kukan me kike Daughter? I thought tun wancan lokacin ke da shi kun yi give up akan auren junan ku, har kun hakura ku ka ci gaba da harkokin rayuwarku, so me yasa hakan zai dameki yanzu don yace dama shi ya hakura?" Mayraah ta sunkuyar da kanta trying hard not to cry, Ceo ta jawota jikinta cikin kwantar da murya tace "Cheer up dear, everything happens for a reason, and the excuse he gave wasn't enough yace ya hakura" Ita dai Mayraah ta kasa cewa komai, Ceo ta dago kanta tace "Now go downstairs and serve Aliyu the food u cooked" Ta gyada mata kai, da ido Ceo ta bi ta da kallo har ta fara sauka downstairs, Mayraah na shigowa parlor bata kalli direction din da MD yake ba ta wuce kitchen, cikin minti kadan ta kai masa abincin dining area ta ajiye masa sannan ta tsaya tana kallonsa, Mikewa yayi ya nufi dining area din yana kallon warmer din abincin da plate with cutleries da ta ajiye masa, sae kuma taga ya dau hanyar kitchen ta bi sa da kallo, ba a dau lokaci ba sai gashi ya dawo da wani plate din da cutleries with another cup duk ya wanke, yana zaunawa ya bude warmer din abincin, a takaice tace "To ai har Food warmer din ba a dauraye ba aka zuba abincin, tukunyar da aka yi girkin ma haka" Ya daga kai ya kalleta, ta juya ta bar dining area din... Daren ranan Mayraah kasa bacci tayi abubuwa biyu suka tsaya mata a rai, wanda da ta tuna sai hawaye, na farko maganganun Usman akan wai ta auri Maheer, Maheer fa??? sai kuma na MD da yake gaya ma Ceo wai Musharraf ya hakura da aurenta, daga karshe ta sauka daga gefen Mahaifiyarta ta tafi bandaki ta dauro alwala... Washegari Mayraah na idar da sallan asuba ta sauka downstairs zata girka ma uwarta breakfast, su kansu masu aikin gidan basu fito ba cause it was still early, kallon dining area tayi sai kuma ta karasa can, ta bude warmers din, ga mamakinta taga MD bai ci abincin ba yayi tafiyarsa, ta kalli plate din da ya dauko jiya da cutleries, haka nan sai jikinta yayi sanyi, tana ta tsaye a wajen, bayan wani lokaci ta kwashesu ta kai kitchen. Wajen karfe tara na safe Mayraah ta shigo dakin da akwatinta yake, kulle kofar dakin tayi ta karasa ta zauna gefen gado, bata san ta saka damuwar jiya haka a ranta ba sai da taga ta kasa yin breakfast, gaba daya bata da wani sukuni, ta goge hawayen da ya taru idonta a hankali, lokaci daya tana tunanin when zata gama kuka a rayuwarta, daga wannan issue din sai wannan issue din, yaushe rayuwarta zai koma kamar da, mikewa tayi tana tafiya a hankali ta karasa gaban madubi ta dau wayarta wanda rabonta da shi tun jiya da daddare, tun da abubuwa suka yi ta faruwa a rayuwarta ta rage rike waya, wani lokacin ma mancewa take tana da waya unlike before da take manne da wayarta a ko da yaushe, ta koma ta zauna tana kallon wayar taga miss calls din Ammi kusan biyar, dialing numberta tayi yana fara ring Ammi ta daga, a hankali Mayraah ta gaisheta, Ammi tace "Are you sleeping?" Mayraah ta girgiza kai cikin sanyin murya tace "Aa wayar na daki ne, ya gida Ammi?" Ammi tace "Lafiya lau, ya mutanen gidan?" Mayraah tace "They are all fine" Ammi tace "To maa sha Allah, hope dai kin saki jiki?" Mayraah ta ɗan yi murmushi tace "Eh Ammi" Har zata tambayi Ya Maheer sai kuma ta kasa, ta sunkuyar da kanta, Ammi tace "Ashe baku yi sallama da Maheer ba kika tafi" Mayraah ta dago kai a hankali tace "Ai baya nan Ammi" Ammi tace "Amma ai ko bai nan ki kan kirasa ki gaya masa ko fita za ki yi Mimi" Mayraah dai tayi shiru bata ce komai ba, sai kuma a hankali tace "Toh zan kirasa Ammi" Ammi tace "Ko fada ku ka yi ne da yayan naki?" Mayraah ta ɗan yi murmushin karfin hali tace "Aa Ammi" Ammi tace "Atoh nasan ai bakwa fada" Mayraah dai kawai tayi murmushi, Basu jima suna magana ba Ammi tayi mata sallama, Mayraah ta dinga kallon wayar bayan Ammi ta katse, can tayi dialing number Maheer, bayan few seconds kawai taji ta fasa kiran ta maza ta katse not knowing ya riga ya shiga, bayan ɗan lokaci sai gashi ya kirata, ta ɗan hade rai, sai da ya kusa katsewa ta daga ta kai kunne tayi shiru, Calmly yace "How are you?" Tace "Fine" Yace "Ya gidan?" Tace "Lafiya" Yace "To maa sha Allah" Ta ɗan yi shiru, jin bai ce komai ba tace "Sai anjima" Yace "Ohk, my regards to everyone" Bata ce komai ba ta katse wayar, bayan kusan minti biyar a hankali tayi dialing number Musharraf, wayar bai shiga ba alamar ya sa a Do not disturb ko kuma ya saka ta a busy, lkci daya jikinta yayi sanyi tana ta kallon wayar, a hankali ajiye wayar ta dalilin knocking din kofa da taji ana yi, ta mike ta isa bakin kofar ta bude, daya daga workers din Ceo ce, da ladabi ta sanar mata Ceo na kiranta a kasa, Mayraah ta fita daga dakin ta sauka downstairs, zaune ta ganta a parlon da MD with Dr Khalil, Mayraah na kallon Dr Khalil cike da mamakin ganinsa ta buda ido tace "Dr ina kwana..." Yana kallonta yana murmushi yace "Lafiya lau Mayraah, congratulations Mayraah...." nan da nan hawaye ya cika idonta tana kallonsa ta ma rasa abinda zata ce masa, can ta zauna kan kujera tana goge idonta cikin sanyin murya tace "Thank you Dr, ina yan biyu?" Yace "Suna nan lafiya lau" Ceo ta mike tana kallonta tace "Ki kai masu Breakfast dinning" Dr Khalil wanda wnn shine karonsa na farko da ya zo gidan Ceo ya kalli Ceo da sauri don shi yayi breakfast, amma dai bai iya yace mata komai ba, shi dai MD bai dago kansa ba, Ceo ta bar parlon ta wuce sama, Mayraah na kallon Dr Khalil a hankali tace "Ya Aunty Zainab fa?" Dr Khalil yace "She is fine Alhamdulillah, congratulations once more Mayraah, i am really happy for you with how things turn out" Mayraah ta sauke idonta cikin sanyin murya tace "I will forever be indebted to you Dr, i will always appreciate you in my life, bazan taɓa mance kulawarka gareni ba da kariyar da ka bani" Tana kai wa nan ta mike ta nufi hanyar da zai kai ta kitchen tana tafiya a hankali nan ko tunanin effort din Dr Khalil a kanta ta dinga yi tun farkon zuwanta Abuja har karshen zamanta ita kadai a Abuja, Dr Khalil ya kalli MD that is pressing his phone, kawai dai yayi murmushi bai ce komai ba, bayan wasu yan mintuna MD ya mike ya nufi hanyar kitchen din Dr Khalil ya ɗan buda ido ya bi sa da kallo.... Juyawa Mayraah tayi jin an bude kofar kitchen din tana ganinsa ta ci gaba da abinda take, ba tare da ya kalleta ba yace "Kar ma ki wahalar da kanki kiyi da nawa, i am not interested...." Ta bi sa da wani kallo ganin ya dau cup yaje yana wankewa zai yi making coffee da kansa, bata san sanda tace "To kai kafi kowa tsafta kake tunani ne?" Juyawa yayi ya kalleta calmly yace "Eh" Ta kyabe baki ta ci gaba da abinda take, ya gama dauraye daurayensa yayi making coffee ya nufi kofa, ta bi sa da wani kallo har ya fita, ta ci gaba da abinda take yi, bayan some minutes ta fita, ta kai ma Dr Khalil Breakfast dinning table, yana zaune area din tare da MD, Ta ajiye masa tana kallonsa tana murmushi tace "Dr ga breakfast, hope dai kai lafiyarka qlau?" Ya ɗan buda ido don bai gane abinda take nufi ba, MD ya ajiye coffee din da yake sha yana kallonta, ko kallonsa bata yi ba zata bar wajen taga wayarsa da ya ajiye yana vibrate, kallon screen din ta dinga yi ganin Dr Musharraf, daukar wayar tayi Dr Khalil ya buda ido yana kallonta da mamaki, bata tsaya wajen ba ta sauka parlor, sannan tayi picking call din kafin ya katse, ta bar parlon gaba daya, MD ya bi ta da kallo, muryar Musharraf taji yace "Good morning" Da kyar tayi gathering courage a hankali tace "Why did u decide to break your promise Musharraf?" Shiru Musharraf yayi bayan yaji muryarta, bata taɓa kiran sunansa ba sai ranan, ta shiga daki ta kulle ta fashe da kuka a hankali tace "I never expect this from you, shi yasa kaki barin mu hadu in maka magana ranan?" Calmly Musharraf yace "Mayraah, we should stop deceiving our self haka" Cikin rawan murya tace "How please?" Yace "Mu yi hakuri, ur parents have better plans for you and you know that wannan ne ma yasa ranan kika yi shiru a parlon baki ce komai ba" Mayraah that was confuse tace "Ban gane nayi shiru ba, me kake so ince a wajen? Kai ma ai ban ji kace komai ba" Yace "No problem, dama ba komai mutum ke nacin so yake samu ba a rayuwa, kuma Allah shi yasan dai dai....." Trying hard to control her self tace "So what are you insinuating now?" Yace "Look Mayraah, am not taking a second risk i promise, probability din samunki bai wuce 5% ba, sai zuciyata ta buga ko kin ga na fadi na mutu za ki san ina sonki da gaske? Wait kina tunanin da bana sonki zan ta ɓata lokacina ina ci gaba da bibiyarki after all that happened?" Mayraah ta dake tace "Amma ai kudin aurenka za a kai Adamawa yanzu haka, ni kuma wa kaga ya kawo kudin aurena? Tell me plsss" Musharraf yayi shiru bayan yaji abinda tace, bayan few seconds a hankali yace "Jiddah is my cousin sister, a rashin ki yasa na amince zan auri Jiddah ba don mun yi courtship ba, i need rest of mind Mayraah, bana son ciwon zuciya ya kamani at my young age..." Mayraah dake ta sauraronsa ta ɗan yi murmushi hawaye na sauka idonta tace "Is that so?" Yace "Yeah, where did u get my brothers phone, kuna tare ne?" Cike da karfin hali Mayraah tace "It is not necessary you ask me that" Musharraf ya ɗan yi murmushi, bayan few seconds yace "Let me be blunt to you Mayraah, ur foster parents plan is for you to marry one of their sons, baza su taɓa barin someone outside of their children su aureki ba, ni kuma ban ki idan Allah ya ƙaddara min ban aureki ba Yayana ya aureki ki dawo cikin mu, ur foster parent are being selfish, kansu kawai suka sani.... Why trying to manipulate you lallai sai kin auri daya daga yaransu? Suna tunanin ta haka ne kawai zaki biyasu rikon da suka maki? By all means suna nufin za su sake nisanta ki da mu dangin mahaifinki bayan kaddara ce ta hanaki rayuwa da iyayenki, me yasa suke da son kansu haka? Yau monday, gobe Tuesday, next Wednesday then Thursday za mu ga abinda zai faru a wannan rana, kuma a ranan zaki tabbatar da abinda na gaya maki yau" Kasa cewa komai Mayraah tayi tana jin duk abinda yake cewa zuciyarta na bugawa don bata yi expecting maganganun nan nasa ba, a haka taji ya katse wayar ta dinga kallon screen din wayar ko kwakkwaran motsi bata yi, hoton Mami ne jikin screen din wayar, Mayraah ta daga kai da sauri jin ana knocking kofar dakin, goge hawayen idonta tayi cike da karfin hali ta karasa bakin kofar, ji tayi gaba daya bata son wannan ranan alhamis din da Musharraf yace mata ya karaso don bata san me zai zo mata da shi ba a rayuwarta, har cikin ranta taji da ma a bar ta da wani batun aure a kyaleta kawai.

Mayraah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788

96
Mayraah na bude kofar dakin taga mai aikin Ceo a tsaye, da ladabi matar tace "Hajiya dama MD ne yace za a amso wayarsa a wajen ki" Mayraah ta sauke idonta ta juya ta koma dakin ta dauko wayar ta dawo ta ba matar sannan ta kulle kofar ta koma tana tafiya a hankali ta kwanta gefen gado maganganun Musharraf na ci gaba da yi mata zarya a kai, ɗan murmushin takaici tayi tana goge hawayen da ya gangaro mata fuska. MD na zaune compound din gidan Ceo bayan ya raka Dr Khalil ya tafi, Number Musharraf yayi dialing a wayarsa don tun da worker din Ceo ta kawo masa wayar bai samu kiransa ba sai yanzu da ya dawo daga rakiyar Khalil, yana fara ringing Musharraf ya daga, Calmly MD yace "How r you doing?" Musharraf yace "Alhmdlh, good afternoon" MD yace "You know what i want to tell you...." Musharraf ya ɗan yi shiru, sai kuma yace "Ina ji" MD yace "Ina son a yanzu ka ajiye wani batun ka hakura da kake cewa, let wait and see what they are up to on Thursday" Musharraf yace "Me yasa ku ke son in ci gaba da deceiving kaina ne ina kara sa ma kaina damuwa pls?" MD yace "Matsalata da kai kenan baka jin magana, when is this Thursday? Why not be patient till then, or is it too far?" Musharraf ya dakatar da shi yace "Look Bro, my heart is tired, with reckless abandon my emotions have been tampered with, and i pray this is just the best for me, on that very Thursday kamar yanda nace maku bazan je ba because it's not going to favor me" MD yace "Kamar son nata a bakin ka kawai ya tsaya fa, in ko ba haka ba bai kamata kayi give up just like that ba, come to think of it, shekaru nawa ka ɓata a kanta? kai a soyayyan ma matsoraci ne" Musharraf yace "I pray u won't get carried away in love just like it happened to me, i pray u don't fall victim, it's not funny" Tun daga nisa MD ke kallon Ceo that is coming toward him, hakan yasa ya katse wayar kawai ya ajiye saman table din gabansa, ta karaso ta ja kujera ta zauna tana kallonsa speaking calmly tace "Aliyu i am not accepting you resignation letter! Kana ganin ko don abinda kawunka ya min baka yi deserving aiki a karkashina ba ne kuma? Paternal Relatives dinka ne suka yi min ai ba kai ba" Kallonta ya dinga yi, can ya girgiza kai yace "Not at all Ma'am, ba haka bane wallahi, kawai dai ina son..." Ceo ta dakatar da shi ta hanyar daga masa hannu tace "You will work with me har zuwa sanda zaka mallaki naka hospital din Aliyu, it's something da ni da kaina zan maka planning dinsa, ba wai zaka yi ta zama ka dawwama a karkashina bane, Sannan have you pondered over what i told u about Mary Ann yesterday?" MD ya daga kai yana kallonta, can ya ɗan yi murmushi yace "Ma, i am sorry but bazan iya cewa zan auri Ex din brotherna ba ko da da gasken har cikin ransa ya hakura da ita, it's something that will never be possible, instead kamata yayi i should go to any extent na ganin ya mallaki heart desire dinsa, tun jiyan ina ta nazari da tunanin how I will arrive at that, at the end na fahimci abu daya kawai zan yi amma kuma ban san outcome din da hakan zai haifar ba, shi yasa still nake contemplating, but i will love to see my brother marry his love" Ceo tayi shiru while looking at him alamar ba haka ta so ba, a hankali tace

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login