Mayrah
Chapter 110 of 152
tunanin nata bata dai ce ma kowa komai ba a gidan amma abun ya tsaya mata a rai sosai. Wajen karfe biyu da rabi Mayraah ta bude ido a hankali jin hannu a forehead dinta, MD dake kallonta ya cire hannunsa yace "Ya jikin?" Juyawa tayi taga Kakarta tsaye kanta, daga gefenta kuma Musharraf ne tsaye yana sanye da fararen kaya kal just like MD, kana ganinsu kasan daga daurin aure suke, suna hada ido shi ya fara sauke idonsa kasa, ta gyara Duvet din jikinta a hankali ita ma ta sunkuyar da kai, MD na kallon Hajiya Ramatu yace "Wani magungunan likitan ya bata?" Hajiya Ramatu ta dauko masa magungunan ta mika masa cike da damuwa tace "Har yanzu babu abinda ta ci fa Daddy, shayin ma da kyar ta sha ɗan kadan dazu, jiya ma haka ta wuni ba cin abinci, ga zafin da jikinta yake" MD yace "Ai jikin ba zafi yanzu" Musharraf na kallon Mayraah cikin sanyin murya yace "Allah ya sauke Mayraah" Ita dai bata daga kai ba tana kallon lafiyayyen lallen da aka zanzara mata a hannunta tace "Ameen" juyawa yayi ya fita daga dakin, MD yace "A kawo mata abincin zata ci yanzu" Hajiya Ramatu tace "To Allah ya sa, mu je sai ka taho mata da shi" Tare suka fita daga dakin nata, bayan ta kulle kofar suna tafiya tayi kasa da murya cike da damuwa tace "Anya Aliyu yarinyar nan na son auren nan kuwa? Sai kace warce aka yi ma auren dole? Tun fa da ta zo garin nan a haka take cikin damuwa da ƙunci, ko fa bacci bata yi da daddare, anya lamarin nan ba abun dubawa bane Daddy??" Da mamaki MD yace "Me zai hana ta so auren Umma? Yayanta ne fa, gida daya suka tashi da shi, kuma baki ga shakuwar da suka yi ba wllh, kawai dai kinsan kowa da yanda fargaban aure ke zuwa masa, barin ita da nake ganin kamar a sangarce take she look so pampered, don Allah kar ma ki kara wannan magana wani yaji Umma, beside ta yaya ma za su mata abinda zai cutar da ita, for 22 years basu cuceta ba sai yanzu? Don Allah kar ki bari wani yaji maganar nan" Hajiya Ramatu tace "To in sha Allah, hankalina ne kawai ya tashi wllh, amma ni dama wa zan je in gaya ma, da kai kawai nayi magana" MD yace "Yaushe ne za a kai ta Abujan?" Hajiya Ramatu tace "Gobe da yamma in sha Allah aka tsara" MD yace "Toh Allah ya kai mu, zata warware in sha Allah kar ki ji komai, sangarci ne yayi mata yawa" Hajiya Ramatu bata sake cewa komai ba, shi ya amshi abincin da ta dauko ya tafi yaje kai ma Mayraah, ya ajiye mata saman carpet yana kallonta yace "Sauko ki ci abinci" Ta mike zaune da kyar ta girgiza masa tace "Ni bazan iya ci ba, amai zan yi" Zaunawa yayi saman kujera yana kallonta yace "Mimi kike ko wa? me yasa kike da taurin kai ne, Why are you acting like u are not civilize kamar wata er kauye, Duk maganar da na maki last week ya tashi a banza kenan i just wasted my effort, kin zata ina bada shawara ne nan da kika gan ni? Now tell me what exactly is ur problem da kike sa ma kan ki damuwa haka?" Mayraah dai tayi shiru tana kallonsa babu ko kiftawa, whereas tunanin da take daban a ranta wato imagining Maheer a matsayin mijinta, ya ɗan mata tsawa yace "Malama ba shiru zaki yi ba kina kallona haka, answer my question now" Hawaye cike idonta muryarta na rawa tace "Yaya Maheer fa" Yace "So? Haramun ne aure tsakaninku? Tun watanni nawa baya kika san ba jininki bane shi din? Is it going to take u forever to assimilate that?" Ta fashe da kuka har da daura hannu a kai tace "Na shiga uku, wllhi bazan iya ba, baza ka gane ba" Yace "Ba a kai ki gidan nasa bane.... sanda zaki iya mu muna ina? Kilan ni ina Canada" Ta kara rushe masa da kuka tace "Yayana ne fa, wllh yayana ne, he is my brother...." Dariya ta ba MD ganin she is so serious tsakaninta da Allah take maganar, Yana zare mata ido yace "To yanzu get this stuck to ur head ba brother dinki bane shi, he is ur Husband, Maheer mijinki ne yanzu, ke duk wannan kinibibin da kike kar fa nan da wata hudu mu ganki da cikin Maheer a jikinki" Ai bata san sanda ta sauka daga kan gadon ba ta dawo kasa a rikice tace "Na shiga uku na lalace don Allah ka dena wannan magana, don girman Allah ka rufa min asiri ka daina" Gaba daya ta rikice sai gwale ido take irin ya fadi wani mugun abu din nan, dariya kawai yake yace "Za ki sani, don wallahi sai na tuna maki wannan ranan in dai na ganki da cikin Maheer" Ta hade kanta da gado da sauri tana kara rusa kukan wnn abu da yake gaya mata a kunnenta, MD ya kwantar da murya yace "Mayraah" Ta dago da sauri tana kallonsa hawaye na zuba idonta duk tayi mugun tsurewa da batun da yake mata, nan ya hau kwantar mata da hankali kamar yanda yayi wancan ranan a gidan Mami, for almost an hour he was trying to talk sense into her head, ita dai tana jingine da gado tana kallonsa kai kace she is paying attention, sai dai duk wannan abun da yake bai san her mind is absent ba, ta lula duniyar wani tunanin daban, a haka Babanta da wasu cousins dinsa da suka dawo daga Adamawa daurin aure suka shigo dubata a dakin su ma. Taro sosai aka yi a gidan Alhaji Saminu, don gidan ya dawo ba masaka tsinke saboda jama'a, kudi kam ba na wasa aka kashe ba a wannan biki, matan prominent people daga garurruwa daban daban suka halarci bikin da aka hada har da na Musharraf, komai baja baja, kaji har sai mutum ya ture, duk da babu amarya balle ango amma duk wani events da suka shirya sai da suka yi since Musharraf is also involved, ita Amarya Mayraah anyi considering bata da lafiya... Bayan magrib MD ya shigo babban parlon Alhaji Saminu tare da Maheer dake biye da shi a baya, duk yawan mazan parlon daga kannen Alhaji Saminu sai cousins da kuma abokansa ne, nan MD yayi introducing Maheer da ya zauna saman carpet bayan duk ya gaishesu da ladabi, yawanci duk basu san angon ba sai a lokacin, nan suka masa fatan alkhairi da zuri'a dayyaba, wasu suka masa nasiha akan zamantakewar aure aka dinga basa shawarwari, daga karshe Maheer suka bar parlon da MD, can gun relatives dinsu mata MD ya tafi da shi don ya gaida su, tunda Maheer ya zauna yan matan dake parlon ke kallonsa attentively, wanda yawancinsu sa'annin Mayraah ne, sai wa enda suka girmeta, Maheer dai ya gaida elders din parlon with respect, nan MD yayi introducing dinsa as Mayraah's Husband, duk sai da yan matan parlon suka kalli juna, shi dai Maheer kansa na kasa yana sauraron duk nasihar da tsofaffin parlon ke masa da fatan zaman lafiya, after like 15 mins suka bar Parlon, haka nan MD ya dinga kai sa gun dangi dake gidan yana gaishesu, daga karshe ya kai sa parlon Hajiya Ramatu da yan uwanta, second parlor dinta ta samesu don can suka zauna, da fara'a take welcoming din Maheer ta sa aka kawo masa ruwa har da abinci, Hajiya Ramatu na kallonsa tace "Yaushe ka shigo ne?" Maheer ya daga kai a hankali yace "Daxu da yamma" Hajiya Ramatu tace "Allah sarki, to ya su Amminku suka ji da taro" Yace "Alhamdulillah" Tace "Toh maa sha Allah, Allah Ubangiji ya baku zaman lafiya, ya kauda duk wata fitina tsakanin ku" Sunkuyar da kansa yayi, Hajiya Ramatu ta bar masu parlon, MD na kallonsa yace "Ka ci abincin mana" Maheer ya ɗan yi murmushi yace "I am okay, mun ci abinci da frnds dina" MD yace "Oh ok, suna ina frnds din?" Maheer yace "Hotel mu ka yi lodging" MD ya mike yace "Ka shiga ciki ka duba amaryar taka, ba ma ta jin dadi" Da sauri Maheer ya girgiza kai yace "No, ai ina ga ba sai na shiga ba, since, erm i know an dubata ai, ba sai na shiga ba" MD yace "Aa mu shiga ka dubata, kasan tun yaushe ne bata da lafiyan?" Zai yi magana sai ga Hajiya Ramatu da wani warmer cike da kaji, MD na kallonta yace "Umma wai bazai iya shiga dakin ki ya dubata ba" Hajiya Ramatu ta buda baki tace "Ni fa kakarku ce, ka manta kuma ni ce Uwargidan taka" Maheer dai yayi murmushi kawai kansa a kasa, MD yace "To kai ka ji, sai mu je dakin uwargida a duba amarya" Maheer ya ɗan kalli Hajiya Ramatu dake kallonsa tana murmushi don kawai nutsuwarsa ne ya burgeta, kana ganinsa kaga bafillatanin yaro, mikewa yayi ba don ya so har cikin ransa ba ya bi bayan MD zuwa Bedroom din Hajiya Ramatu, Mayraah har ta fara bacci kan darduma daga yin sallan magariba, MD ya tsaya yana kallon Maheer da ya kasa karasawa cikin dakin, Maheer ya kallesa calmly yace "Kaga bacci take MD, pls ba sai mun tasheta ba..." Bai jira me MD zai ce ba ya fita daga dakin, dariya abun ya ba MD yaga kamar shi ma bai son haduwa da ita ne, Maheer's reaction was so funny to him, ya ɗan yi murmushi ya juya ya fita daga dakin shi ma, Maheer bai kara minti ashirin a gidan ba ya koma hotel din da suka sauka da abokansa bayan Hajiya Ramatu tayi masa takeaway din kaji da drinks. Washegari da safe aka ci gaba da shagulgula a gidan Alhaji Saminu, ba laifi yau Mayraah ta fito cikin mutane duk da ba wani dadewa tayi ba kakar ta mayar da ita daki, tsadaddun kayan da aka mata na fitar biki kusan kala 15 uku kawai ta saka a ciki.... Bayan azahar aka fara shirye shiryen tafiya da amarya Abuja nan hankalin Mayraah ya kara mugun tashi ta dinga kuka gabanta na faduwa, tsadadden alkyabba fari da Gold Mayraah ta saka kan kayan jikinta, tayi kyau har ta gaji, kana ganinta ka ga amarya, haka aka bi da ita duk gun tsofaffin dake gidan wa enda duk yawancinsu kakanni suke a gareta suka dinga mata nasiha da yi mata fatan zaman lafiya da mijinta, daga nan aka kai ta gun kakanta shi ma yayi masa nata tare da kannesa dake parlon, shi dai Babanta na zaune a Parlon sai kallonta yake, daga haka aka maido hankali kansa shi ma yayi mata nasa nasihan, bai iya yace komai ba, kawai ya sa mata albarka aka fita da ita, dakin da Aaria take a gidan aka kai Mayraah, Aaria ma dai ta kasa cewa komai sai hawaye. Karfe hudu da rabi yan kai amarya suka sauka a cikin garin Abuja, ciki har da Mama Ladi da sae ka rantse er pamilyn Alhaji Saminu ce, Mayraah dai na jikin Mamin Musharraf ta kasa daina kuka, sai yanzu ta yarda all this while ashe ba mafarki take ba, biyar da yan mintuna convey din yan kai amarya suka iso gidan Abba, duk yawan motocin da suka kawota sai da compound din gidan ya dauke su tas, niyyar su Mami dama bayan an kai Mayraah gidan Ammi in ta mata nata nasihan Abba ma yayi mata sai su kai ta dakinta daga can su kuma su tafi masaukinsu washegari su koma Kaduna, amma sai Hajiya Safiyya da Surkan Dr Khalil ke sanar masu ai za ayi Mothers eve gobe, su yi hakuri goben sai su kai amarya in an gama, haka nan aka bar ma su Mami wani bangare na cikin gidan. Mayraah na kwance dakin da aka sauketa wajen karfe tara na dare, Badiyyah ce zaune kasan carpet din dakin duk ta dawo so calm kamar ba Badiyyah ba, ko maganar kirki yanzu bata cika yi ba sai dai ta bi ka da ido, daga daya side din kuma Farrah ce er wajen Aunty Halima sai cousins dinta uku, Farida da Maimoon sai Rabi'a wanda tare da su aka taho kawo Mayraah kusan sun zama kamar su ne kawayen amarya hiransu suke kasa kasa a dakin, duk yawan mutanen dake gidan sannan ga kuma family din Alhaji Saminu da suka kawo Mayraah kusan su Talatin hakan bai sa Ammi ta ki dinga shigowa gun Mayraah ba, don bi ni bini zata shigo dakin to check on her barin da taji jikinta da zafi tun da aka kawota gashi taki cin abinci, Mayraah dai bacci take restlessly a dakin, Ammi ta shigo rike da cup din shayi da ta hado mata ganin bata ci abinci ba, ajiye shayin tayi saman beside drawer ta cire duvet din jikinta a hankali tace "Mimi" Mayraah ta bude idonta da yayi ja tana kallonta, kasa cewa komai Ammi tayi jin jikinta yayi zafi sosai gashi sai rawan sanyi take, dama kuma Mami tace mata bata da lafiya, Ammi ta mayar mata da duvet din ta fita daga dakin ta tafi bangarenta ta dauko wayar ta, number Maheer tayi dialing, bayan ya daga da damuwa tace "Maheer baza ka shigo ka duba Mimi ba kuwa, zazzabi ne sosai fa jikinta, ga shi sai rawan sanyi take, dama sun ce tun a Kaduna bata da lafiya" Maheer dake sauraronta yayi kasa da murya yace "Amma.... ammi ko dai in kira abokina, yana nan area din yanxun nan zan...." Ammi ta katse sa tace "Har sai yaushe muka san zai karaso Maheer? pls kar ka bata min rai ka zo ka duba min yarinyata in magani zaka siyo kaje ka siyo mata sai kuma ka tsaya kana min maganar banza, in baza ka iya ba yanzu in yi ma Abbanku magana ya kai mu asibiti tunda ba kai kadai bane likita...." Kasa ce mata komai Maheer yayi, ta katse wayarta...... Ɗaga kai su Farrah suka yi suna kallon sa bayan ya shigo dakin da sallama murya can kasa, a tare suka gaishesa still looking at him, amsawa yayi sannan ya nufi inda Mayraah ke kwance, duk su Farrah suka zuba masa na mujiya, mikewa Badiyyah tayi tana kallonsu cikin sanyin murya tace "Ko za mu ɗan je wancan dakin tunda dubata zai yi" Duk suka wani juya suka kalleta, da daddaya da daddaya suka mike suka fita daga dakin sannan ita ma ta fita ta kullo kofar, shi dai Maheer na tsaye gaban gadon yana kallon Mayraah dake baccin wahala tana sauke numfashi da kyar, ya duka gaban gadon ya cire duvet din jikinta a hankali yana feeling temperature dinta, buda idanuwanta tayi lokaci daya suka hada ido da shi, hannunsa ta riko ta marairaice masa kamar zata fashe da kuka ta kai hannun nasa wuyanta tace "Yaya kaina ciwo yake min sosai, my temperature is so high, ko zaka min allura" Shi dai kallonta kawai yake, kamar dai yanda take langwabe masa a baya in bata da lafiya, a hankali ta cire hannunsa daga wuyanta ta fara komawa baya slowly kamar warce ta tuna wani abu, lkci daya zuciyarta ya tsananta bugawa, zata koma daya side din gadon da sauri kamar warce aka tsikara yayi saurin fizgota ya dawo da ita, gigicewa tayi tana zare ido, ya hade rai cikin muryar da bata san sa da shi ba yace "Ni dodonki??" Jikinta na rawa taki yarda ta kallesa tace "Wayyoo Ammi, ni dai ka kyaleni kar in gaya ka da Ammi" ƙin saketa yayi ta dinga mutsu mutsun kwace kanta da duk karfinta amma ta kasa, shi dai kallonta kawai yake, da ta ga ba sarki sai Allah ta gatsa masa cizo da karfi, hakan yasa ya cikata ta samu ta sauka daga kan gadon da gudu ta shige bandaki ta kulle kofar da makulli tana zare ido, tunda take da shi bata taɓa jin tsoronsa a zuciyarta ba sai yau.... Barin dakin Maheer yayi ya tafi pharmacy ya siyo mata magunguna, bayan ya dawo ko shiga gidan bai yi ba ya kira Badiyyah ya bata maganin ta kai mata sannan yayi wucewarsa.....
102
Washegari duk da garau Mayraah ta tashi amma sai kara dukunkunewa take cikin duvet tana sauke numfashi a hankali, nan kuma mothers eve din da za ayi ne bata son fita shine take kara narkewa cikin bargo kamar bata da lafiya, haka Ammi tayi ta lallabata bini bini ta shigo dakin dubata hatta shayi da kanta ta bata, wajen karfe goma aka bude kofar dakin, rufe ido tayi duk tunaninta Ammi ce ta kara shigowa dakin, muryar Usman taji yana amsa gaisuwan su Farrah, sai a sannan ta bude ido, ya karasa kusa da gadon ya xaga ta inda take yana kallonta yace "Ya jikin Mimi?" A hankali tace "Alhamdulillah" muryar Hajiya Amina ta ji ita ma tana amsa gaisuwan su Farrah da Badiyyah, Mayraah ta juya, Hajiya Amina ta karasa kusa da ita tana mata murmushi tace "Mimi Amarya, sannu, ya jikin?" Mayraah ta sauke idonta ta mike zaune da kyar, cikin sanyin murya tace "Ina kwana Aunty" Hajiya Amina na murmushi tace "Lafiya lau Mimi, jiya ina barin gidan ku ka iso...." Zaunawa tayi gefen gadon ta dafa goshinta tace "Allah Ubangiji ya sanya alkhairi my dear, Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a dayyaba, Allah ya kauda duk wata fitina tsakanin ku" Mayraah ta dinga kallonta ta kasa cewa komai nan kuwa wani iri take ji a ranta idan ana cewa Allah ya basu zuri'a, Ammi ce ta shigo dakin da lafiyayyen farfesun da ta sa Aunty Mariya tayi ma Mayraah, tana ganin Hajiya Amina ta juya ta fita daga dakin tun kan Hajiya Aminan ta juyo, Hajiya Amina dai ta ci gaba da kallon Mayraah tace "Tare muke da masu maki kwalliya yanzu..." Sosai gaban Mayraah ya fadi, ta marairaice tace "Aunty jikina babu kwari,
102
Washegari duk da garau Mayraah ta tashi amma sai kara dukunkunewa take cikin duvet tana sauke numfashi a hankali, nan kuma mothers eve din da za ayi ne bata son fita shine take kara narkewa cikin bargo kamar bata da lafiya, haka Ammi tayi ta lallabata bini bini ta shigo dakin dubata hatta shayi da kanta ta bata, wajen karfe goma aka bude kofar dakin, rufe ido tayi duk tunaninta Ammi ce ta kara shigowa dakin, muryar Usman taji yana amsa gaisuwan su Farrah, sai a sannan ta bude ido, ya karasa kusa da gadon ya xaga ta inda take yana kallonta yace "Ya jikin Mimi?" A hankali tace "Alhamdulillah" muryar Hajiya Amina ta ji ita ma tana amsa gaisuwan su Farrah da Badiyyah, Mayraah ta juya, Hajiya Amina ta karasa kusa da ita tana mata murmushi tace "Mimi Amarya, sannu, ya jikin?" Mayraah ta sauke idonta ta mike zaune da kyar, cikin sanyin murya tace "Ina kwana Aunty" Hajiya Amina na murmushi tace "Lafiya lau Mimi, jiya ina barin gidan ku ka iso...." Zaunawa tayi gefen gadon ta dafa goshinta tace "Allah Ubangiji ya sanya alkhairi my dear, Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a dayyaba, Allah ya kauda duk wata fitina tsakanin ku" Mayraah ta dinga kallonta ta kasa cewa komai nan kuwa wani iri take ji a ranta idan ana cewa Allah ya basu zuri'a, Ammi ce ta shigo dakin da lafiyayyen farfesun da ta sa Aunty Mariya tayi ma Mayraah, tana ganin Hajiya Amina ta juya ta fita daga dakin tun kan Hajiya Aminan ta juyo, Hajiya Amina dai ta ci gaba da kallon Mayraah tace "Tare muke da masu maki kwalliya yanzu..." Sosai gaban Mayraah ya fadi, ta marairaice tace "Aunty jikina babu kwari,