Showing 330001 words to 333000 words out of 452169 words
Chapter 111 - Mayrah Complete By Khaleesat Haydar
ma Adamawa muka je na Musharraf" Damsel ta gwalo ido bayan ta hango Sadiya Ummu Hanan, Aunty Amzaj, Aunty Zahrah, Ummu Sultan, Mera Garba da Mom Asas, Ant Maryam, Autan palace, Me lamurje, har da coursemate zaune cikin compound sun cakare cikin tsadadden ankonsu sai murmushi suke ga teburinsu cike da abinci iri iri da drinks, nan da nan hawaye ya cika idon Damsel ganin pamilynta a ciki ita kuma ga ta a bakin gate, tsautsayi yasa ta biyo Meenah parrot ashe bata da wani connection da Maheer din ma, Mama Ladi da ta sha gwaggwaro da jan baki ganin yanda aka cika bakin gate ta karasa can da gudu tana makale jakarta a hammata tana cewa "Yau na ga jaraba, ku kuma daga wani kauyen ku ka zo haka? abun nan fa 'yar gayyata ne, babu gayyar sodi sam a taron nan wllhi, in ba a gayyace ka ba ta yaya zaka ce kai lallai sai ka shigo gidan mutane fisabilillahi, doo Allah masu gadi ku korasu ku garkame mana get, mu je ma ayi ta lafta mana sata mu shiga uku..." Nan da nan securites din suka kulle gate din, Ma'ani ta fashe da kuka tana kallon Parrot da idonta yayi jajir. Sai kusan karfe hudu Maheer ya shigo gidan tare da few of his frnds shi ma saboda hotuna da za ayi da shi da aka ishesa da kira amma da bazai ma shigo gidan ba, Farrah da cousin sisters dinta couldn't take their eyes off him, shi kam ko hada ido baya iyawa da iyayen nasa mata da ma duk matan dake cikin gidan, Ita dai Mayraah na zaune kamar marainiya kusa da Hajiya Amina that was by her side all through the occasion, a haka har Aunty Mariya ta taho da Maheer yayi hoto da Hajiya Amina, ya ɗan kalli Mayraah da ta sunkuyar da kanta taki yarda ta kallesa, Hajiya Amina tace "Toh ni ban ga kunyi hoto da amaryan ba ma ae" Aunty Mariya tace "Ai kuwa dai basu yi ba" Ita dai Mayraah kanta na kasa gabanta sai faduwa yake, Aunty Amina ta nuna masa gefen Mayraah tace "Ka zauna a maku hoto" Shi ma kansa a kasa ya zauna inda ta nuna masa, a hankali Mayraah ta ɗan matsa daga kusa da shi saboda kamshin turarensa da ya cika mata hanci, a haka aka yi ta masu hoto, duk kowa kallonsu yake a compound din don ba karamin matching suka yi da juna ba, hancinsu ma iri daya sak, Aunty Mariya ta hade rai tana kallon Mayraah tace "To kiyi murmushi mana Hajiyata" Da kyar tayi murmushin da kiris ya rage ya zame mata kuka, mai hoton yayi ma Maheer alamar ya matsa kusa da ita don da distance tsakaninsu, sanin all eyes where on them ah compound din yasa Maheer ya matsa a hankali har yana goga jikinta, Mayraah ji tayi tsikar jikinta na tashi duk ta takure a wajen tana Allah Allah a gama hoton, Aunty Mariya ta tafi kiran Ammi dake can cikin mutane ta taho su yi hoto da yaran nata, farin cikin Ammi ya kasa boyuwa a fuskarta a wannan rana sai fara'a kawai take, Kamar ance Mayraah ta daga kai suka yi ido hudu da Umar, bata ma san sanda ya zo ba, murmushi ya sakar mata daga inda yake a compound din ya daga mata hannu, nan da nan hawaye ya cika idonta da sauri ta sunkuyar da kai tana kokarin ganin hawayen bai zubo mata ba... Karfe biyar aka fara shirin za a tafi da amarya don su Mami juyawa za su yi a ranan, nan fa hankalin Mayraah yayi mugun tashi banda kuka babu abinda take duk ta rikice kamar ance za a kai ta wuta, a haka aka sa ta shirya sannan aka daura mata tsadadden lapayan da aka turara mata, bayan duk su Mama Ladi da manyan gidan sun mata nasihar da za su mata aka kai ta bangaren Ammi, har bedroom din Ammi aka shiga da ita don tana ciki da 2 of her friends sai Mother in law din Dr Khalil, Mayraah ta rungume Ammi tana rusa kuka cikin tashin hankali, Ammi dai ta kasa cewa komai, can ta dago kanta da kyar tana kallonta, Mayraah tayi kasa da murya cikin kuka tana kara kankame Ammi tace "Ammi bani da lafiya fa, wallahi bani da lafiya har yanzu" Kwantar da ita Ammi tayi saman gadonta, ai ko kamar jira take ta dukunkune waje daya zuciyarta na bugawa, Hajiya Safiya ta saki baki tana kallon Ammi ganin ta kwantar da Mayraah, Ammi ta mike ta karasa gun su a hankali tace "Ina jin kawai sai dai yan Kaduna su yi hakuri su tafi, kun ga tun jiya haka ta yini ba lafiya yau ma karfin hali kawai take, daga baya ko su Mariya sai su rakata...." Aunty Mariya dake tsaye dakin ta buda baki tana kallon Ammi da mamaki, Ummi tace "Aa, Hajiya ni ban taɓa jin inda aka yi haka ba, don Allah ki bari su kai ta dakinta zata warware a can, tun jiya fa ya kamata a kai yarinyar nan muka basu uzirin mu kuma yau ma sai a basu wani story din, gaskiya a ganina hakan bai yi ba" A hankali Ammi tace "Zan yi ma ita Mamin magana, nasan she will understand, ai ita tasan bata da lafiya tun daga kadunan" Daga haka ta fita duk frnds dinta suka bi ta da kallo baki bude, ai ko Ammi ta samu Mami ta sanar mata abinda ta gaya ma su Hajiya Safiyyah, Mami ma rasa abinda zata ce mata tayi da farko, can tayi murmushi tace "Amma da kin bari an kai ta zata warware a can Hajiya, all this is normal ai" Ammi tayi kasa da murya tace "Nafi son ta kara hutawa ne ko zuwa nan da sati daya ko biyu, stress din yayi mata yawa" Mami dai tayi murmushi tace "Toh shikenan Hajiya if you insist, bari in sanar masu bata jin dadi, sai mu tafi kawai....." A haka dangin Alhaji Saminu suka bar gidan basu kai Mayraah ba wanda su kansu hakan bai masu dadi ba tunda dalilin da yasa suka kara kwana kenan, Mama Ladi sai abinda ta manta ne kawai bata gaya ma Ammi ba don bacin rai, tana kallon Yahanasu tana huci tace "Rashin lafiyar karya kawai da na hofi, duk mu ma ai mun yi haka amma ba a fasa kai mu daki ba, barin ita Meran da kowa yasan yanda take shige ma Mashir take makale masa, to wani sabon ne kuma bata yi da shi ba da har baza a kai ta dakinsa ba, ni nake ganin kinibibi da salon munafurci, yanzu me bayin Allahn nan za su dauke mu banda kananun mutane, tun jiya suka so su mikata dakinta aka hanasu aka ce sai anyi casu, yau kuma a zo masu da wannan tsinannen walakanci don anga suna da kawaici, ni ai ban san wainar da ake toyawa ba wallahi da bazan yarda da hakan ba ko ni sai in fixgo Meran daga cikin dakin in turata a mota su je su mika ta" Yahanasu ta girgiza kai tace "Gaskiya Ammi wani lokacin ban san inda take kai tunaninta ba, a ina aka taɓa haka fisabilillahi?" A fusace Mama Ladi tace "Sai a pamilyn mu, dama nan abun kunya ya kare ai" Yahanasu tace "Yanzu kawai ta saka an tafi da mu a baki, ga yan kaduna da kacalcala magana Malam" Mama Ladi ta fice daga dakin a fusace, ita dai Aunty Mariya ta ma rasa abun cewa don ko kadan ita ma abinda Ammi tayi bai mata dadi ba, don son Mayraah ya rufe mata ido sai ta biyeta aki yin abinda ya dacd, ita ma dai bata taɓa jin inda aka yi haka ba sai yau, kuma tasan don Maheer ne mijin yasa Ammi tayi haka, da wani bare ne can ita ma bazata fara ba ai. Bayan Isha Mayraah na kwance dakin Ammi zuwa sannan ta cire Lafayanta ta canza kaya, sosai hankalinta ya kwanta don sai da ta ɗan ci abincin ma da aka kawo mata, Aunty Mariya ta shigo dakin tana kallonta tace "Kinyi Sallah?" Gyada mata kai tayi, Aunty Mariya tace "Toh tashi ki maida lapayan mu je ki gaida Abba yana parlonsa ya dawo" A hankali Mayraah ta mike zaune tana kallonta sannan ta sauko daga kan gadon, Aunty Mariya ta taimaka mata ta maida lapayan nata dake ta baza kamshi, sannan ta kama hannunta suka fita zuwa parlon Abba, har a sannan da mutane a gidan, ita dai Mayraah kanta na sunkuye duk da ta rufe fuskarta da lapayan jikinta suka iso har parlon Abba, Ido hudu suka yi da Maheer dake zaune kasan carpet, ta sunkuyar da kanta da sauri ta zauna kasa kusa da Aunty Mariya, da kyar ta iya kallon Abbanta cikin sanyin murya tace "Abba ina yini" Yana murmushi yace "Lafiya lau my daughter, ya gajiya?" Mayraah ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, Ammi ma na zaune parlon, Nasiha sosai Abba yayi mata tare da Maheer, daga ita har shi babu wanda ya dago kai a parlon, ita dai sai hawaye take don zuwa yanzu ta riga ta yi give up kuma da tunanin ko zata farka taga mafarki ne, Abba yayi kusan minti talatin yana masu nasiha most especially yafi karkata kan Maheer, daga karshe Abba ya mike yana kallon Aunty Mariya yace "Ba wani abu da zata tafi da shi yanzu?" Mayraah ta daga kai da sauri ta kalli Abba, Ammi ma kallonsa take, Aunty Mariya tace "Jakarta kawai zan dauko mata sai wayarta" Abba yace "Toh dauko mata" Mikewa Aunty Mariya tayi ta fita, Abba yana kallon Maheer yace "Ku tashi zan yi dropping din ku da kaina a gidan" Kuka Mayraah ta fara yi sosai tana kallon Ammi hankali a tashe, Ammi dake kallon Abba tayi kasa da murya tace "Yallabai bata da lafiya ne fa, ina ce dazu na gama maka bayani" Abba yace "Zai kula da ita a can gidan nasu" Bai sake sauraron Ammi ba ya fita daga parlon yace "Mariya ta taho min da ita parking space immediately" Mayraah ta kara rushewa da matsanancin kuka, Hukuncin Abba yayi mugun yi ma Aunty Mariya dadi don iya shegen Mayraah ya fara isanta kuma haka, haka Mayraah na ji na gani aka kai ta har motar Abba tana kuka, Aunty Mariya da su Mama Ladi da Yahanasu da frnds din Ammi ne suka rakata parking space din Mama Ladi na cewa "Hakan shine dai dai dama Uba ya kai er sa dakin mijinta da kansa, Allah maka albarka Mamuda, ita kuma Ammi Allah ya shiryeta" Sai da Aunty Mariya tayi ma Mayraah jan ido sannan ta shiga bayan motar, Abba bai yarda Maheer yayi driving din ba yace shi zai yi da kansa, Maheer ya koma front seat ya zauna Abba ya tada motar suka bar gidan, Sai kusan karfe goma da rabi na dare Abba ya isa gidan da ya mallaka masu su biyu, Babban gida ne hadadde a unguwar masu hannu da shuni cikin garin Abuja, Abba da kansa ya bude back seat Mayraah dake kuka ta sauko daga cikin motar, ya kama hannunta yayi leading dinsu har zuwa cikin parlon gidan, daga nan kuma ya kai ta har dakinta da dangin ubanta suka mata furnishing, ya juya yana kallon Maheer dake biye da su kawai a baya, Maheer ya sauke kansa kasa, Calmly Abba yace "Ga amanar daughter na Maheer, take care of her for me, Allah ya baku zaman lafiya...." Mayraah na ganin Abba zai fita ta mike ta rungumesa tana rusa kuka tace "Na shiga uku, don Allah Abba kar ka tafi ka bar ni, Wayyo Ammi" Shi dai Maheer bai yarda ya dago kansa ba.
103
It took Abba another 10 mintues to console Mayraah dake kuka a jikinsa, after calming her down daga karshe dai ya bar gidan, duk da haka bata daina kukan da take ba kamar ranta zai fita tana kiran Ammi, Maheer ya fi minti ashirin zaune parlor bayan Abba ya tafi, can ya daga kai ya kalli agogo dake nuni da karfe sha daya da yan mintuna, mikewa yayi yana tafiya slowly ya karasa kofar parlon ya kulle da makulli sannan ya tafi ya zuwa wani seperate daki bayan ya shiga ya kulle kofar, after taking his bath ya saka jallabiya yayi kwanciyarsa a dakin wanda shi ma aka yi furnishing, har bacci ya fara daukarsa ya mike zaune da sauri, sauka yayi daga kan gadon ya nufi kofa ya fita daga dakin, after walking toward her room ya bude kofar dakin a hankali yana leka cikin dakin, kwance ya ganta a kasan dakin bacci ya dauketa har sannan kuma bata cire lapayar jikinta ba, ya karasa ciki yana tafiya a hankali leaving the door open, remote din Ac ya dauka ya rage, har zai fita dakin sai yaji bazai iya barinta ta kwana kasa ba, ya kusa minti daya a tsaye kafin ya karasa inda take ya durkusa yana kallonta, he was just looking at her for some seconds, kawai sai kuma ya fasa tashinta ya mike ya dau duvet dake saman gado gently ya rufa mata a jiki sannan ya bar mata wuta mara haske sosai a dakin ya nufi kofa ya fita ya kullo mata kofar a hankali. Sai asuba Mayraah ta farka a dakin, ta dinga kallon duvet din jikinta da mamaki, sai kuma ta mike zaune da sauri tana bin dakin da kallo, kiran sallahn da ta ji ya sa ta gane Asuba yayi, ta buda ido sosai don har ta mance yaushe rabon da tayi bacci me nauyi haka daga dare har asuba, a hankali ta cire duvet din ta mayar gefe ta tashi tsaye, Lapayan jikinta ta kunce ta ajiye gefen gado, tana tafiya kamar me tsoron taka ƙasa ta isa press din dakin ta bude, kayanta ta gani well organized a ciki, sai kuma ta rufe ta juya ta shiga bandaki, sai da ta wanke baki tayi wanka sannan ta dauro alwala ta fito.... Tana zaune saman darduma bayan ta idar da sallah tayi nisa tunanin da take taji an bude kofar wani dakin ba wanda take ciki ba, sosai gabanta ya fadi ta takure waje daya ta dinga kallon kofar dakinta, bayan kusan minti daya bata ga an bude ba, a hankali ta mike ta kwanta gefen gado ta lumshe ido zuciyarta na bugawa. Har karfe sha daya na safe Mayraah na kwance dakinta tayi lamo gefen gado, ta dai hakura da tufka da warwaran da take ta yi a zuciyarta tun da gari ya waye, zuwa sannan dai ta fara jin yunwa sosai, ji tayi an bude kofar dakin, bata san sanda ta mike zaune da sauri ba tsabar yanda ta tsorata tana kallon kofar, yana tsaye bakin kofa ba tare da ya bari sun hada ido ba kamar yanda ita ma taki kallonsa, babu yabo babu fallasa yace "Fito ki dau breakfast" Ta wani daure fuska ta jingina da gadon ta dau pillow ta daura saman cinyarta, still kuma taki kallonsa, hade rai yayi yace "Ke.. ba da ke nake bane??" Ta wani kauda kai tana kara daure fuska taki ce masa komai, shigowa dakin da yayi yasa ta juya ta kallesa a fusace tace "To ni nace maka yunwa nake ji ne wai" Calmly yace "I will give you a dirty slap you if you tell me nonsense" Kallonsa Mayraah ta dinga yi bata ko kiftawa, fuska daure ya nuna mata kofa yace "Fita ki debi abinci, what is my business with kina jin yunwa ko bakya ji" Sauke idonta tayi don tunda take da shi bai taɓa ce mata zai mareta ba, Sounding very serious yace "Ba magana nake maki ba?" a hankali ta sauka daga kan gadon dama har sannan Hijab din da tayi sallah na jikinta, bata yarda ta bi ta inda yake ba ta zaga daya side din tana satan kallonsa ta nufi kofa ta fita, sai a sannan ta waigosa taga ya biyo ta a baya, da sauri take tafiya har ta shigo Babban parlon kafin ya iso har ta tafi dinning din ta debi abincin, shi dae bai ko kalleta ba ya zauna parlon, bayan ta zuba abincin tana tafiya a hankali ta koma dakinta, ajiye plate din abincin tayi ta koma kan gado ta zauna har sannan abinda yace mata ke yawo a kanta, lokaci daya hawaye ya cika idonta, sai kuma ta fada kan gadon ta fashe da kuka, daga karshe yunwa ne yasa ta dau breakfast din da ya sandare a dakin ta fara ci bayan tayi sallahn azahar, tana cikin ci ya bude kofar dakin, da sauri ta mayar da plate din bayanta tana kallon kofar dakin, a takaice yace "Breakfast, Lunch, Dinner, duk ba sai kin jira an maki announcement ba, lokacinsu nayi ki fito ki nemar ma kanki alternative, i don't want to repeat this again, bana son in sake tuna maki...." Mayraah dai kallonsa kawai take har ya juya ya fita, tana ta zaune kamar bazata fita ba, amma can kasar zuciyarta shakkar kar ya dawo ya sameta take, hakan yasa ta mike ta nufi kofa tana tafiya a hankali ta fita, bata gansa a parlon ba ta karasa dinning area taga an kawo lunch daga gida, dan kadan ta diba a plate, ta bar dinning din ta koma dakinta. Da daddare kamar yanda yace bata jira yayi reminding dinta ba ta fita parlor, zaune ta gansa da laptop gabansa, satan kallonsa tayi taga ko daga kai bai yi ba, tana tafiya kamar munafuka ta tafi dinning, kadan ta diba tuwon, har ta wucesa kuma bai daga kai ya kalleta ba, tana shiga corridor sai da ta sake juyawa ta kallesa still taga idonsa na kan laptop, turo baki tayi ta nufi dakinta. Washegari karfe tara da rabi Mayraah ta fito ba don tana jin yunwa ba sai don kar ya sake tuna mata kamar yanda yace, babu kowa parlon