Showing 333001 words to 336000 words out of 452169 words

Chapter 112 - Mayrah Complete By Khaleesat Haydar

ta karasa dinning taga an kawo breakfast, duk wnn abincin da ake kawowa dai dai yanda Ammi tasan suke cin abinci take zuba masu sai ta kara kadan sbda mai gadin gidan, Mayraah taga babu plate a dinning din ta fara kalle kalle tana neman hanyar kitchen, inda take tunanin kitchen ne ta nufa ta bude kofar a hankali tana leka ciki, hada ido suka yi da shi ta koma baya da sauri kamar munafuka ta bar bakin kofar, ya gama hada coffee dinsa ya fito daga kitchen din, tana tsaye gefe daya ta sunkuyar da kai da kyar tace "Ina kwana" Ita kanta bata san sanda hakan ya fito bakinta ba, gani tayi yayi wucewarsa bai ko kalleta ba, ta bi sa da kallo har ta daina hangosa alamar dakinsa zai tafi, turo baki tayi ta jingina da bango ta rungume hannunta, nan da nan hawaye ya cika idonta, ƙin shiga kitchen din ta dau plate tayi ta wuce dakinta da sauri ta fada kan gado ta rufe fuskarta da pillow ta fara shesshekar kuka.... Mayraah na kwance tayi lamo kan pillow taji an bude kofar dakin, da sauri ta mike zaune tana kallon kofar, bai shigo dakin ba yana kallonta yace "What did i tell u yesterday?" Sauke idonta tayi kasa, yace "Ba magana nake maki ba?" Da kyar tace "Yanzu zan je in deba" Yace "Ke, kar fa ki bari in sake tuna maki, in ma baza ki ci ba ki fito ki diba ki ajiye a dakin, daga baya zaki iya zuwa ki zubar, i don't want to remind you this again" Da ido ta bi sa har ya bar bakin kofar, hawaye ya cika idonta ta sauko daga kan gadon ta fita daga dakin tana tafiya a hankali, bayan ta zuba abincin har zata wuce sai kuma ta tsaya tana kallonsa a hankali tace "Yaya in zuba maka?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Nace maki zan ci?" Sunkuyar da kanta tayi ta wuce daki. Haka nan Maheer ya ci gaba da bi da Mayraah a gidan, kwata kwata bai bata chance da fuskar fara sabon rashin kunyan da ya ga ta tsiro masa ba, a kwana ukun da suka yi tare a gidan sae dae ta fito ta debi either breakfast, lunch or dinner, a dar dar ma take fitowa daukan abincin, ko haduwa sai ya daina yarda su yi da ita, da yaji ta bude kofar dakinta zai bar parlor in dai yana parlon, deep down him he wish he isn't doing this to her, amma wannan kadai ne samun lafiyarsa don yafi kowa sanin wacece ita, avoiding dinta kawai yake by all means. Yau har kusan karfe tara na dare bai ga ta fito ta debi dinner ba, for the pass 3 days ana magrib take fitowa ta zuba abincin, ganin har 11 bata fito ba ya mike ya nufi dakin nata, bude kofar yayi ya ganta kwance ta rufa da bargo, da sauri ya karasa kan gadon ya cire bargon yana kallonta yace "Mimi are you okay?" ta bude idonta da yayi ja ta fashe masa da kuka ta rike hannunsa tace "Yaya cikina" Dagota yayi zaune, shi ma ya zauna yana facing dinta a hankali yace "Ba gobe bane Mimi?" Muryarta na rawa tace "Bai zo ba...." Goge mata hawayen fuskarta yayi yace "Bari in je in kawo maki magani" Mikewa yayi ya fita daga dakin, ba a dau lokaci ba ya dawo da plate din abinci da ya debo mata da ruwa, ya ajiye abincin ya dagota yace "Ki ci kadan sai ki sha maganin" Cikin rawan murya tace "Bazan iya ci ba" Ya dau abincin ya fara bata yace "Za ki iya Mimi, kadan fa za ki ci...." Da kyar ta bude bakin ta amshi abincin da yake bata a baki, spoon biyu kawai ta yarda tayi tana langwabe masa, ya bude maganin da ya dauko ya bata da ruwa, ta amsa ta sha ta koma ta kwanta ta dukunkune waje daya, rufe mata duvet din yayi a jiki, yana zaune dakin har sai da bacci ya dauketa sannan ya mike ya fitar da sauran abincin da ruwa, kafin karfe biyu da rabi na dare ya shiga dakin nata ya fi a kirga yana dubata, ita kuwa baccinta kawai take, hakan yasa daga karshe ya tafi dakinsa ya kwanta don all through yana zaune parlor ne, har yayi bacci wajen karfe hudu yaji an bude dakinsa, kunna wuta yayi ya mike zaune yace "Mimi" ta nufosa da sauri ta durkusa kusa da gadon, tuni ya sauko kasa, ya duka kusa da ita yana kallonta yace "Ya zo ne?" Da kyar take gyada masa kai, ya dagota ya zaunar gefen gadon yace "Let me get you hot water" Ta rikosa cikin kuka tace "Wayyoo kawai ka min allura bazan iya ba wllh" Yace "Ai ba alluran, sai gobe zan siyo maki...." Ta rushe masa da kuka ta fada jikinsa tace "Na shiga uku, me yasa baka siyo ba" Lallashinta ya fara yi a jikinsa, yace "Bari ki kara shan maganin gobe sai a siyo a alluran da safe" a haka ya samu ta sakesa ya tafi ya dauko maganin da ta sha da daddare kafin tayi bacci, sai ana kiran asuba ya samu Mayraah tayi bacci, gently ya kwantar da ita saman gadon yana kallonta, tana sanye ne da rigar bacci da ya wuce cinyarta, ya sauke idonsa, bayan few seconds ya dau hular ta da ya fadi kasa ya ɗan dago kanta ya sa mata sannan ya rufa mata blanket a jiki, mikewa yayi ya fita daga dakin. Wajen karfe takwas na safe Maheer ya shigo dakinsa bayan ya fita da sassafe yaje asibiti saboda alluran nata, karasawa yayi kusa da gadon yana kallonta ya cire duvet din a hankali yace "Mimi" Ta bude idanuwanta da suka kumbura tana kallonsa, yayi kasa da murya yace "Da sauki?" Girgiza masa kai tayi, ya dagota yace "Toh bari ayi alluran" Da kyar tace "I want to ease my self" Yace "Ohk, come down" Saukowa tayi daga saman gadon, ya kalleta sannan ya kalli bedsheet din, a hankali yace "You are stained Mimi" Kallon gadon tayi, sai kuma tayi kasa da murya tace "Na manta ban sa pad ba" Yace "Shiga bandaki let me get you" Da kyar take tafiya ta shiga bathroom din sannan ya fita yaje dakinta, wani seperate demarcation ne a babban dakin nata inda aka ajiye mata 18 boxes dinta, kallon boxes din kawai yake yana tunanin ta ina zai fara duba pad, dawowa dakin yayi zai fita yaje ya tambayeta, har ya kai kofa yaga pad a gaban madubi ta ajiye, ya koma ya dauka sannan ya tafi press dinta ya bude ya dau underwear ya fita ya koma dakinsa, cire bedsheet din gadon yayi, ya saka wani, ya zauna gefen gadon yana jiranta. Wanka Mayraah ta daure tayi duk da azaban da take ji, kafin ta fito ya sake fita ya tafi kitchen ya hado mata shayi yana shigowa dakin yaji tace "Yaya pad din pls..." Ya ajiye shayin hannunsa ya dau pad din da under wear ya nufi bandakin ya ɗan bude kadan yana mika mata, amsa tayi tace "My hijab" a hankali yace "Ohk" Dakinta ya koma ya dauko mata Hijab din ya mika mata, bayan ta saka ta fito, kwanciya tayi gefen gado ta lumshe ido, ya duka kusa da ita yana kallonta yace "Sannu" Ita dai bata iya ta ce komai ba, yace "Ki sha shayi sai in maki alluran" Bai jira cewarta ba ya dauko shayin, ya ajiye sannan ya dagota, haka ya dinga lallabata ta sha shayin, har ta sha kadan ya ajiye sauran ya dauko ledan injection din ya hada ya dawo kusa da ita yana kallonta, buda ido tayi ganin alluran hannunsa ta daga hijab dinta, towel dinsa ne a jikinta, on a norms dama yawanci a cinya yake mata duk allura in tana cramps, bai cika mata a baya ba, calmly yace "A cinya za a maki ko baya?" Baya ta nuna masa sannan ta ɗan kwanta, ya sauke idonsa, bayan few seconds sai kuma yace "Bari dai ayi a cinya, kar ya dameki later on" Daga haka ya ɗan kara daga towel din yayi mata alluran a lap dinta, yana mata alluran ba dadewa ta fara bacci, ya gyara mata kwanciyarta ya cire hijab din jikinta ya lullbeta ya shiga bandaki don wanke zanin gadon. Wajen sha biyu saura Maheer ya shigo dakin, zaune ya sameta ta tashi bacci a lokacin, ya karasa har gaban gadon yana kallonta yace "How are you feeling?" Ta ɗan turo baki taki cewa komai, sai kuma ta kauda kai tana kallon different direction, shiru yayi yana kallonta, wato ta samu sauki bari ta ci gaba daga inda ta tsaya, dama ciwon cikin nata bai wuce na kwana biyu, kuma ana mata allura shikenan sai kuma wani watan, Ya dake yana nuna mata kofa yace "To tashi ki fita" Kallonsa tayi da sauri, sai kuma ta fashe da kuka tace "Ni ka sa min kati a wayata in kira Ammi da Abba ko ya Usman a zo a tafi da ni gida kawai, kullum sai kayi ta min fada da masifa a gidan nan, idan na gaisheka bazaka kulani ba, ranan har cewa kayi zaka mareni" Hawaye ke zuba idonta take maganar, da kamar bazai ce komai ba sai kuma yace "To na mare kin?" Taki cewa komai tana share hawayen dake zuba idonta, yace "Kuma saboda me zan kula ki ni da kike ma fitsara yanzu" Ta kallesa da sauri tace "Ni yaushe na maka fitsara?" Kallonta kawai yake, ta turo baki ta rungume hannunta tace "Ni kawai dai..." Sai kuma tayi shiru, Yace "Kawai dai me?" Ta daga manyan idonta ta kallesa muryarta na rawa tace "Ni dai kawai kai yayana ne" Yace "To wa ya canza ni daga yayanki dama?" Ta sauke idonta kasa, yayi kasa da murya yace "Ai forever ni Yayanki ne" Ta ɗan kallesa tace "Da gaske" Yace "Da gaske me?" Sunkuyar da kanta tayi tace "Abinda kace mana, kaga ai...." Kasa ci gaba tayi, ya zauna gefen gadon yace "Ae ke ce kika yi complicating issues Mimi, dama ta yaya zan canza ki from my lil sis? It's not possible ai" a hankali tace "To don Allah kayi min alkawari" Yace "Alkawarin me?" Ta sauke idonta tace "Ka min alkawarin we are still siblings" Sauke nasa idon yayi shi ma, can yace "Tun da mu ke dake na taɓa maki karya?" Ta girgiza masa kai, yace "Toh i am telling you the fact Mimi, we will still remain siblings in sha Allah, nothing can ever change that" Mayraah taji sanyi har cikin ranta da abinda yace mata, can ta daga kai a hankali tace "To yaya kayi hakuri da abinda nayi" Ya ɗan yi murmushi yace "To nima kiyi hakuri" Turo baki tayi tace "Bayan har kace zaka mareni" Yace "Ke ma kinsan wasa nake" Marairaicewa tayi tace "You were serious wllhi" Yace "So kike Ammi tayi disowning dina" Tace "Bayan ina ta jiran Ammi ta kirani taki kirana, kuma katina ya kare" Yace "Ta bari ne ki gama koke koken ki, amma yanzu bari in kira maki ita" Daukar wayarsa yayi ya kira Ammi, har ya gama ringing bata daga ba, ya kalleta yace "May be tana downstairs" Tace "Yaya don Allah zaka kai ni in ganta yau?" Maheer ya ɗan yi shiru, sai kuma yace "To ai baki da lafiya Yau, ki bari gobe friday" Tace "Toh" Sauka tayi daga kan gadon sai kuma ta duka kasa da sauri ta ɗan kallesa bayan tayi realizing towel ne jikinta, sau daya ya kalleta ya sunkuyar da kai yana danna wayar hannunsa, hijab dinta ta jawo a hankali ta saka tace "Yaya pls ka dauko min Pad da kayana a daki" Yace "Ohk" Mikewa yayi ya fita daga dakin.....

104
Maheer ya daga kai yana kallon Mayraah da ta shigo parlon tana tafiya a hankali, sai kuma ya ci gaba da wayar da yake yi da abokinsa, ta karaso cikin parlon ta zauna kasan carpet shi kuma yana kan kujera, bayan sun yi sallama da abokin nasa ya kalli agogo dake nuna after 4 yace "Cikin yayi sauki?" Ta gyada kai tana kallonsa, yace "Ga abinci ki je ki zuba, you've been sleeping since" ta kalli hanyar dining din sannan tace "Yaya wa ke kawo abincin?" Yana danna wayarsa yace "Omar" Tace "Yaya shine bai tambayeka ni ba?" Yace "Yanzu dai ki je ki zuba abinci ba wani abu da kika ci tun safe" Tace "Yaya kasan me, kawai Ammi kar ta sake bada abinci a kawo mana ni zan yi girkin Dinner yau" Ya kalleta yace "Ke da baki da lafiya" Tace "Aa ni dai na samu lafiya ina son inyi girkin dinner da kaina" Yace "Ohk then" Mikewa tayi ta nufi dinning din ya bi ta da kallo sai kuma ya maida idonsa kan wayarsa dake hannunsa, bayan ta zubo abincin ta dawo tana kallonsa tace "Yaya kai ka ci?" Without looking at her yace "Na ci" a hankali tace "Yaya naga kamar fushi kake da ni har yanzu, pls baka hakura bane?" Ya daga kai ya kalleta sai kuma yayi murmushi yace "Dama can ai ni ba fushi nake da ke ba Mimi kawai i gave u space ne, me za ki girka anjiman?" Ta dan buda ido tace "Ur favorite" Yace "Good, i miss your food Mimi" Murmushi tayi tace "Bari in gama ci sai in maka" lkci lkci yake kallonta tana cin abincin gabanta, har ta gama tace "Yaya har yanzu ban san yanda gidan nan yake ba, kawai bedroom dina da kitchen na sani sai kuma dakin ka" Yace "To mu je sai ki gani yanzu" Mikewa tayi, shi ma ya tashi yana gaba tana biye da shi a baya, bedrooms din gidan kaf ya fara nuna mata, duk dakunan uku where well furnished sannan suna da girma sosai ko wanne kuma da bathroom a ciki, ta buda ido sosai tana kallonsa tace "Sun yi kyau sosai yaya" Ya dan murmushi kawai ya fita daga last dakin da ya shigar da ita, ta bi bayansa, wani hanya taga sun dauka zuwa wani bangare daban, suna isowa ya bude kofar shiga wajen suka shiga wani babban parlor, ta wara ido tace "Waow yayi kyau sosai yaya" Shi dai bai ce mata komai ba ya karasa da ita har cikin babban dakin dake part din, ta wara ido tana kallonsa don sosai dakin ya hadu komai fari a ciki, ya juya ya kalleta yace "I think this the master part" Tace "To wancan dama ba dakina bane?" Yayi murmushi yace " Duk naki ne, har wannan din, in kina son kwana nan ma zaki iya dinga zuwa ki kwana" Bai jira me zata ce ba ya fita ta bi sa a baya, suka dawo main parlor din gidan, kitchen suka shiga ya bude babban store din ciki, nan taga uban garan da aka mata daga kaduna na cin cin da sauransu, daga gefe kuma ga kayan abinci kamar za a bude shago, ta juya ta kalli Maheer dake kallonta, dan murmushi tayi tace "To yaya ni bana son cin cin da dublan kai ma haka, yanzu ya za mu yi da su?" Yace "Kyautar wa mana" Bai jira cewarta ba ya fita ta bi sa a baya, kofar fita daga parlon taga ya nufa ita dai tana biye da shi, har ya fita sai kuma ya juya ya kalleta kafin ta fito yace "Ur hijab" Ta juya ta koma ciki sai ga ta ta dawo da hijab dinta, Mai gadi ne kawai a zaune kusa da dakinsa, Maheer ya zaga da ita bayan babban compound din gidan, wani hadadden garden da shukoki masu kyau ta gani, the back yard has enough space, ya karasa wani kofa ya bude ya shiga ta bi bayansa, zaro ido tayi ta rufe baki da hannunta ganin wani portable swimming pool, sai kuma ta kallesa da sauri tace "Yaya swimming pool??" Yana kallon pool din yace "Ai Abba yasan kina so ne shi yasa aka yi" Mayraah was so happy ta karasa kusa da pool din da sauri ta durkusa ta saka hannuwanta biyu cikin ruwan tace "I love it soo much Yaya" Shi dai kallonta kawai yake, ji tayi har ta kagu ta gama period ta zo tayi wanka a pool din, kallonsa tayi ya dauka kai, tace "Yaya to ai bani da swimming trunk" yace "An sa maki a kayanki" Ta wara ido, sai kuma ta debi ruwan da hannu biyu ta watsa masa, ya hade girar sama da ta kasa yana kallonta, Kara debo ruwan tayi tun kan ta watso masa ya nufeta ta mike da sauri tana kokarin gudu yayi hanzarin riketa kamar zai sakata cikin ruwan, tace "Wayyo yaya fa wasa nake maka, kai baka san wasa ba...." Saketa yayi nan da nan ta nufi kofar fita daga wajen da sauri tana dariya ya bi ta da kallo, sai kuma ya juya yana kallon swimming pool din, after a minute ya fara tafiya a hankali ya fita daga wajen, dai dai stairs din shiga parlor ya ganta zaune ta marairaice tana kallonsa tace "Yaya ka sa na buge kafana" Ya karaso da sauri yace "Ni kuma? How?" Mikewa tayi tace "Eh mana, na zata ka biyo ni ashe baka biyoni ba" Yace "Where did u hit the leg?" Bai jira cewarta ba ya duka yana kallon kafarta tace "I am fine yaya, dama ba sosai na buge ba" Ya mike yace "Ohk" Ita ta fara shiga parlon sannan ya bi bayanta, kitchen ta tafi don fara girkin da tace zata yi, babu abinda babu a gidan na girki, har nama akwai a deep freezer, ta ciro nama kenan zata fara wankewa ya shigo kitchen din, yana kallonta yayi kasa da murya yace "Are you sure you are not stressing ur self Mimi, kin ga nasan su Ammi sun yi girki da mu, bamu gaya masu tun wuri

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login