Showing 336001 words to 339000 words out of 452169 words

Chapter 113 - Mayrah Complete By Khaleesat Haydar

ba, ki bari in an kawo dinner yau sai in ce ma Omar ba sai ya kawo breakfast gobe ba" Mayraah tayi shiru tana kallonsa yace "C'mon Mimi" A hankali tace "Toh shikenan, Allah ya kai mu goben" Yace "Ameen" maida naman tayi tace "Amma yaya kai ne ka siyo drinks din cikin fridge?" Ya jingina da kofar kitchen din yace "Noo, bani bane" Tace "To bana son su" Yace "Ohk, bari ayi magrib sai mu je mu siyo wasu drinks din, sai a siya maki har da junk food dinki, cornflakes and golden morn" Tayi murmushi tace "Toh yaya" juyawa yayi ya fita daga kitchen din, ta wanke hannunta ta fito. karfe shidda Omar ya kawo abinci gidan, Maheer ya shigo dakin Mayraah yana kallonta yace "Ki fito ku gaisa da Omar, he is around" Shiru tayi tana kallonsa, can tayi kasa da murya tace "Ni dai yaya kamar bazan iya fita ba fa" Yace "To saboda me?" Kasa cewa komai tayi, yace "To ke da kika ce in kai ki gida wajen Ammi gobe" Mayraah ta kallesa a hankali tace "Kaga su sai su ga kamar we are Husband and wife, na fasa ma zuwa gidan" Dariyar da bai shirya yi ba yayi, yace "Kamar yaya kin fasa?" Sunkuyar da kanta tayi, yana murmushi yace "To amma ai ni da ke mun san we are not husband and wife, So why bother ur self?" Cikin sanyin murya tace "To ai mu kadai muka san haka, su kuma baza su taɓa sanin haka ba, ni fa yaya i see this more like an abomination and i don't know why others are seeing it to be normal, may be because they are not in our shoes" Maheer ya gyada kai, calmly yace "Abomination din ne ma" daga manyan idonta tayi tana kallonsa, ya mata murmushi yace "Ki fito ku gais" Kwanciya tayi gefen gadonta ta juya masa baya a hankali tace "Ni dai kawai kace masa ina bacci, i can't" Shiru yayi yana kallonta, jin shirun yayi yawa ta juya ta kallesa, sauke kansa yayi ya juya ya fita daga dakin, haka nan taki fita zuwa gun Omar don ita gani take za su dinga tunanin ai ita da Maheer yanzu mata da miji ne, that tot alone ba karamin daga mata hankali yake ba. Bayan magrib Mayraah ta shirya kamar yanda Maheer ya ce mata, ta fito parlor tana kallonsa, Hijab ne har kasa jikinta, ya kalleta yace "Can we" Ta gyada masa kai tana karasowa cikin parlon, kallon kafarta yake yace "Is it paining you Mimi, naga kamr you are limping?" Ta girgiza masa kai tace "Aa ba sosai ba, i am fine" Mikewa yayi ya dau makullin motarsa don dama ita yake ta jira, ya nufi kofa tana biye da shi, sai da ya fara bude mata kofa ta fita sannan shi ma ya fita ya kulle gidan, yace "Mimi dingishi fa kike" Ta langwabar da kai tace "Nace maka zae daina fa yayaaa" A haka suka bar gidan mai gadi yayi masu Allah ya tsare, wani babban shopping Mall Maheer ya kai su, bayan yayi parking sun sauka a motar duk da yanda kafarta ke ciwo haka ta dake tana tafiya a hankali zuwa cikin mall din don kar ya sake mata maganar kafar, cart ya dauka ta amsa a hannunsa tana turawa yana biye da ita ta fara daukan abubuwan da take so, shi dai bin ta kawai yake duk inda tayi idonsa na kanta, ta saki cart din ta tafi zata dau pack din wani chocolate ta juya don tambayarsa ko shima yana so ta daukar masa, kallonta taga yana yi baya ko kiftawa, gani yayi ta kara wani haske tayi kyau sosai, sai glowing take, nan kuma duk gyaran jikin da aka mata a kaduna ne, yana ganin ta juyo lkci daya yace "Oh ok, you want the chocolate?" Ta nufesa tace "In daukar maka Yaya?" Kai kawai ya gyada mata ta juya ta koma wajen, bin ta yayi da kallo sai kuma ya dauke idonsa tun kan ta sake juyowa, bayan ta debi chocolates din zata tura cart din suka ji ance "Maheer" Juyawa suka yi a tare, wata mace ce ta nufo su tana masa kallon mamaki, Maheer ya ɗan buda ido yace "Zeenat" Zeenat tace "OMG Maheer, I can't believe my eyes, is this really you" Yana murmushi yace "Ashe kina Nigeria dama Zeenat" Tace "Ai ni nafi shekara uku a Nigeria yanzu, ya kwana da yawa Maheer? ya bayan saduwa?" Yace "Alhamdulillah" Kallon Mayraah dake kallonta tayi sai kuma da sauri tace "Sorry matar ka kenan Maheer?" Maheer ya kalli Mayraah yana murmushi ya girgiza kai yace "Aa, kanwata ce wannan, her name is Mayraah" Mayraah ta daga kai tana kallonsa, Zeenat tace "Waow maa sha Allah, ai kam gashi naga kuna kama sosai, har dai nose dinku iri daya" Yace "Yeah, autan Ammin mu ce" Zeenat na murmushi tace "Hi Mayraah?" Mayraah ta kalleta kamar bazata ce komai ba sai kuma can ciki tace "Hello" Zeenat tace "My name is Zeenat Abubakar, mun yi karatun Degree tare da Maheer, kin ga yayan nan naki sam baya zumunci, duk yayi watsi da mu wllh, ko an masa magana ta Whatsapp no reply, layinsa kuma ina jin ya rufe ne..." Mayraah dai tayi murmushin da iyakarsa lips bata ce mata komai ba, can ta ci gaba da daukan abubuwan ta tana sakawa a cikin cart a hankali, Zeenat ta kalli Maheer tace "Maheer kar dai kace min har yanzu baka yi aure ba?" Yace "Ban yi ba, ko za ki samar min budurwa that is ready for marriage" Mayraah ta juya ta kallesa, Zeenat tayi dariya tace "Kai haba dai, nima kaga har yanzu ban yi auren ba" Yace "Allah sarki" Er dariya tayi tace "Wa ya sani ko juna muke jira all this while" Maheer couldn't help it but laugh, kamar yanda ita ma take dariya tana kallonsa, Mayraah dai tsayawa tayi tana kallonsu da chocolate a hannunta, Maheer yace "To ke ya kika ga" Zeenat ta ɗan buda ido, calmly tace "Kawai memories ke dawo min kamar ba mu yi rayuwa tare ba Maheer, wa zai ce ko ta Whatsapp za mu daina magana, abun da mamaki" Yace "Ba ni da number ki gaskiya yanzu" Tace "Ai ko ni ina da naka, kwanaki can da dadewa nayi pinging dinka via WhatsApp but no reply, bari ma ka ga" Jakarta ta bude ta ciro wayarta ta shiga contact ta fiddo number dinsa ta nuna masa, Mayraah ta dinga kallonta, Maheer yace "Yeah, that's my number Zeenat, ki kirani sai inyi saving number dinki yanzu...." Mayraah ta ajiye chocolate din hannunta da kyar tace "Yaya kafana ciwo yake min, na gaji i have shop enough....." Maheer ya kalleta yace "Ohk Mimi, za mu tafi yanzu in sha Allah" Zeenat tace "Ayya sannu Mimi...." Dialing number Maheer tayi, ya ciro wayarsa a aljihu yana kallon number nata bayan ya shigo wayarsa yace "I will save right away Zeenat" Nan take yayi saving number nata, a hankali tace "So a Abuja kake aiki kenan?" Yace "Yea nan nake aiki" Tace "As a medical Dr?" Tuni Mayraah ta bar wajen ta bar masa cart din gaba daya, Maheer ya bi ta da kallo sannan ya kalli Zeenat yace "We will talk on phone Zeenat, my sis is sick, za mu tafi gida" A hankali Zeenat tace "Allah sarki to ba damuwa Maheer, am so happy to meet u again after many years, you look more handsome and matured now...." Murmushi kawai yayi yace "Za mu yi waya" Daga haka ya bar ta wajen yana tura cart din da Mimi ta bar masa, Zeenat ta bi sa da kallo babu ko kiftawa, Maheer na isa counter ya biya kudi, ga mamakinsa bai ga Mayraah a cikin mall din ba gaba daya, workers din wajen suka dau siyayyan da ya biya suka kai masa har bakin motar sa, tsaye ya ganta jikin motar ta rungume hannu, yace "Ina ta dubaki ashe kina nan Mimi" Ko kallonsa bata yi ba balle ta basa amsa, bayan an saka masa siyayyan a booth din mota ya duba aljihunsa ya ciro kudi ya basu yana masu godiya, Mayraah ta bude back seat ta shiga ta zauna ta kulle, shi dai bai ce mata komai ba ya zaga ya shiga driver seat suka bar haraban mall din, a hanya yace "Sosai kafar ke ciwo Mimi?" Kyalesa tayi, hakan yasa bai sake ce mata komai ba har suka iso gida, sai a snn ya kunna wutan motar ya juya yana kallonta, hawaye ya gani idonta, da mamaki ya sauka daga motar ya dawo back seat yace "Mimi what happened?" Cikin kuka tace "Ni dai kafata ciwo take min, ka daina tambayata what happened" Yace "Subhanallah, bari mu je ciki sai in duba maki, za ki iya sakkowa kuwa?" Taki cewa komai ta sauka daga motar hawaye na sauka idonta, yayi kasa da murya yace "Ko in dauke ki??" Banza tayi masa ta fara tafiya da kyar, ya kalli bakin gate ganin mai gadin ya fita waje bayan ya rufe gate din, kawai ya dauketa kamar er yarinya, zaro ido tayi tace "Na shiga uku, ni fa zan iya yaya, ka ajiyeni plss" Yace "Toh shikenan" Zai sauketa ta wani turo baki tace "To mu je" Dariya sosai ta basa amma bai yi ba yana dauke da ita jikinsa suka shiga cikin gidan, dakinta ya kai ta ya ajiyeta kan gado sannan ya durkusa yana duba fararen kafanta, ya daga kai a hankali yace "Bari in dauko man zafi in shafa maki" Da kyar tana harhade rai tace "Sai nayi wanka ni dai...." Yace "Toh je kiyi, let me pray isha too" Ya bi ta da kallo har ta shiga bandakin sannan ya mike a hankali ya fita daga dakin. Mayraah na fitowa daga wanka har ta gama shirin bacci bata ga ya shigo dakin ba, har sannan abinda yace ma Zeenat na makale ranta ta rasa dalili, ta karasa saka hair net dinta tana kara jan sabon rigar baccin jikinta da ya kusa knee dinta kasa, ta nufi kofa a hankali ta bude ta fita yanda bazai yi making noise ba, dakinsa ta nufa ta jingina da kofar ta kasa kunnenta don jin abinda yake, dai dai nan ya bude kofar dakin, da sauri ta koma baya kamar munafuka lkci daya ta birkice, yana kallonta daga sama har kasa, a hankali yace "Mimi..." Ta marairaice masa tana langwabar da kai tace "Yaya ciwo fa kafar yake min sosai kuma naga baka zo ka shafa min ba, kilan ma waya kake yi a ciki" Ya sauke idonsa don ko kadan bai ma fahimci abinda take cewa ba, juyawa yayi kawai ya koma dakin ta bi bayansa.

105
Mayraah ta bi sa da kallo ganin ya shiga bandaki, juyawa tayi ta kalli wayarsa dake ajiye kan gado, ta karasa kusa da gadon ta dau wayar tana dubawa, mamaki ne ya cika ta ganin wayar da password, shi da baya sa ma waya password ko pin, ta dinga kallon wayar babu ko kiftawa, can ta zauna gefen gadon ta ajiye wayar tana jiran ya fito ta tambayesa yaushe ya fara sa password a waya bata sani ba, wanka taji yake yi a bandaki wanda hakan ya bata mamaki don ko da ya bude kofa taga alama he just took his bath, ita dai bata fita ba tana zaune tana ta jiran fitowarsa, bayan kusan minti goma sha biyar ya fito daga bandakin, jallabiyar jikinsa ya mayar ya kalleta sau daya ya dauke kai yana goge kansa da karamin towel, Mayraah dake kallonsa tace "Ba naga kamar kayi wanka ba Yaya?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Ban gama ba dama" Zata yi magana wayarsa dake kusa da ita ya fara vibrate, ta juya tana kallon wayar taga Dr Zeenat jikin Screen din, tuni ya karaso kusa da gadon ya dau wayar, Mayraah ta dinga kallonsa, yayi picking call din yace "Hi Zeenat, i will call you back" Daga haka ya katse kiran ya ajiye wayar yana kallon Mayraah, sai kuma yace "Ohh bari in dauko man zafin...." Ƙin cewa komai tayi, ya tafi inda first aid box dinsa yake ya bude ya duba yaga babu man zafi a ciki, dawowa yayi yana kallonta yace "I think i will have to go out and get it, babu a nan" Still taki ce masa komai, ya tafi ya dau makullin motarsa da wayarsa ya fita daga dakin, hawayen da bata san dalilinsa ba ya cika idonta, sai kawai ta fashe da matsanancin kuka ta fada kan gadon ta rufe fuskarta da pillow, tayi kukanta me isarta.... Har ta fara bacci Maheer ya dawo gidan, yana shigowa dakinsa yayi mamakin ganinta don bai yi tunanin zai dawo ya sameta a dakin ba, karasawa yayi ya zauna gefen gadon yana kallonta from head to toes, bayan minti daya ya mike a hankali ya koma kusa da kafarta still yana kallonta, yana kai hannu kan kafar ta bude ido, da sauri yace "Erm, zan shafa maki lotion din ne" Yana fadin haka ya nuna mata tube din hannunsa, ita dai ta wani hade rai bata ce komai ba, ya sauke idonsa yace "Wani kafar ne?" Nan ma taki ce masa komai, duba kafar ya fara yi da kansa, yana kai hannu inda ke mata ciwo ta janye kafar da sauri tana turo baki tace "Ni dai bana so" Kasa kallonta yayi yace "A hankali zan maki ai" Saboda yanda ya san ta da shegen raki kawai shafa mata lotion din yayi kamar yana shafa mata mai a kafar bayan ya tabbatar ba dislocation bane, duk da haka har da kukanta, ita dai tasan kukan me take don shi kam gently ya shafa mata lotion din balle tace zafi taji, yana kallonta ya mike ya koma kusa da ita ya zauna yace "Amma dai ba saboda man zafin da na shafa maki kike kuka ba?" Ta kara fashewa da kuka tace "Don baka san zafin da kafar yake min bane shi sa zaka ce haka, kuma sai da kaje ka gama wayarka zaka wani zo ka shafa min saboda ba kai ne ke jin ciwon ba" a fusace ta fara kokarin sauka daga kan gadon shi dai idonsa na kan lap dinta, tun kan ta sauka yayi saurin rikota da murya yace "C'mon Mimi, daga pharmacy fa nake wllhi, nasan ai yana maki ciwo shi sa har na fita da daddaren nan...." Ta kara rushewa da sabon kuka, ya jawota kusa da shi yayi kasa da murya yace "To yi hakuri Mimi" Ta daura kanta saman chest dinsa tana sheshekan kukan, lumshe ido yayi, sai kuma ya rungumeta a hankali yayi kasa da murya yace "It's okay" Bai yarda ta dade a jikinsa ba ya ɗan ja baya, bayan few seconds yayi karfin hali yace "Za ki je ki kwanta Mimi?" Ta daga kai ta kallesa, sauke idonsa yayi not wanting to have eye contact with her, yace "It's late yanzu, ki je ki kwanta" Tace "Saboda kana son zaka yi waya ko?" Ɗan murmushi yayi still shi dai bai kalleta ba yace "To idan ban yi waya ba me kike son inyi Mimi? Ni ba namiji bane? ko haka kike son inyi ta zama baki son yayanki yayi aure? Ko kina da budurwar da za ki min nima kamar yanda MD yace min kin masa" Mayraah dai bata ce komai ba ta sauke kanta, dai dai nan wayarsa ya fara vibrate, ita ta rigasa juyawa da sauri tana kallon wayar taga Dr Zeenat a saman screen din, yace "Ki je ki kwanta, let me pick a call, ko nan zaki kwanta?" Ita dai bata ce masa komai ba, kwantar da ita yayi saman gadon yace "Toh kiyi kwanciyarki a nan" Daga haka ya dau pillow daya ya ajiye kan carpet ya dau wayarsa sannan ya kashe wutan dakin ya kwanta kan carpet din, dialing number Zeenat yayi, yana fara ring ta daga, duk da ba a handsfree ya sa ba amma saboda silence din dakin Mayraah na jin maganarta radau, bayan sun gaisa Mayraah taji tace "So what are ur plans now Maheer?" Maheer that was speaking calmly yayi murmushi yace "Aure, and setting up a family" Zeenat tace "Really? Kamar zuwa yaushe kai kake son kayi auren kuma kana da budurwar da zaka aura ne yanzu?" Yace "Not at all, i am single, ni ko gobe na samu warce ta shirya i am ready nan da wata daya" Zeenat tace "Amma dai da mamaki kamar ka kace min baka da budurwa Maheer, naji zuciyata ta kasa yarda da hakan" Maheer ya ɗan yi shiru, sai kuma yace "Ba budurwa ba har aure na taɓa yi Zeenat, but auren bai yi 6 months ba muka rabu da matar" Zeenat tace "Subhanallah, garin yaya Maheer, in dai ba canzawa kayi ba kai din na san mutum ne me hakuri, kawaici da kauda kai, wacece wannan tayi ma kanta asaran miji kamar ka?" A hankali Maheer yace "Bata son family dina Zeenat, and she poisoned my Lil sis warce kika ganmu tare a mall, duk da ni tayi niyyar poisoning...." Zeenat tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, to yanzu tana ina?" Maheer ya ɗan sauke ajiyar zuciya yace "Ai nace maki na saketa babu aure tsakaninmu" Zeenat tace "I mean ba ayi mata wani hukunci ba akan abinda ta aikata ko ba kuyi involving hukuma bane?" Maheer yace "I did, ni ne ma na mikata gun yan sanda, Unfortunately she is pregnant for me as she said, so bayan abinda tayi which i have evidence, an yanke mata hukunci yanzu haka tana gidan yari, amma saboda cikin dake jikinta my dad had pity for her, yace babu aure tsakanina da ita amma ta ci albarkacin yaron cikinta duk da idan an haifesa dama za ayi DNA test ne, so my dad had to persuade my brother Barrister Usman, sannan ya biya wasu manyan lauyoyin don ayi appealing din case din

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login