Mayrah
Chapter 114 of 152
kafar da sauri tana turo baki tace "Ni dai bana so" Kasa kallonta yayi yace "A hankali zan maki ai" Saboda yanda ya san ta da shegen raki kawai shafa mata lotion din yayi kamar yana shafa mata mai a kafar bayan ya tabbatar ba dislocation bane, duk da haka har da kukanta, ita dai tasan kukan me take don shi kam gently ya shafa mata lotion din balle tace zafi taji, yana kallonta ya mike ya koma kusa da ita ya zauna yace "Amma dai ba saboda man zafin da na shafa maki kike kuka ba?" Ta kara fashewa da kuka tace "Don baka san zafin da kafar yake min bane shi sa zaka ce haka, kuma sai da kaje ka gama wayarka zaka wani zo ka shafa min saboda ba kai ne ke jin ciwon ba" a fusace ta fara kokarin sauka daga kan gadon shi dai idonsa na kan lap dinta, tun kan ta sauka yayi saurin rikota da murya yace "C'mon Mimi, daga pharmacy fa nake wllhi, nasan ai yana maki ciwo shi sa har na fita da daddaren nan...." Ta kara rushewa da sabon kuka, ya jawota kusa da shi yayi kasa da murya yace "To yi hakuri Mimi" Ta daura kanta saman chest dinsa tana sheshekan kukan, lumshe ido yayi, sai kuma ya rungumeta a hankali yayi kasa da murya yace "It's okay" Bai yarda ta dade a jikinsa ba ya ɗan ja baya, bayan few seconds yayi karfin hali yace "Za ki je ki kwanta Mimi?" Ta daga kai ta kallesa, sauke idonsa yayi not wanting to have eye contact with her, yace "It's late yanzu, ki je ki kwanta" Tace "Saboda kana son zaka yi waya ko?" Ɗan murmushi yayi still shi dai bai kalleta ba yace "To idan ban yi waya ba me kike son inyi Mimi? Ni ba namiji bane? ko haka kike son inyi ta zama baki son yayanki yayi aure? Ko kina da budurwar da za ki min nima kamar yanda MD yace min kin masa" Mayraah dai bata ce komai ba ta sauke kanta, dai dai nan wayarsa ya fara vibrate, ita ta rigasa juyawa da sauri tana kallon wayar taga Dr Zeenat a saman screen din, yace "Ki je ki kwanta, let me pick a call, ko nan zaki kwanta?" Ita dai bata ce masa komai ba, kwantar da ita yayi saman gadon yace "Toh kiyi kwanciyarki a nan" Daga haka ya dau pillow daya ya ajiye kan carpet ya dau wayarsa sannan ya kashe wutan dakin ya kwanta kan carpet din, dialing number Zeenat yayi, yana fara ring ta daga, duk da ba a handsfree ya sa ba amma saboda silence din dakin Mayraah na jin maganarta radau, bayan sun gaisa Mayraah taji tace "So what are ur plans now Maheer?" Maheer that was speaking calmly yayi murmushi yace "Aure, and setting up a family" Zeenat tace "Really? Kamar zuwa yaushe kai kake son kayi auren kuma kana da budurwar da zaka aura ne yanzu?" Yace "Not at all, i am single, ni ko gobe na samu warce ta shirya i am ready nan da wata daya" Zeenat tace "Amma dai da mamaki kamar ka kace min baka da budurwa Maheer, naji zuciyata ta kasa yarda da hakan" Maheer ya ɗan yi shiru, sai kuma yace "Ba budurwa ba har aure na taɓa yi Zeenat, but auren bai yi 6 months ba muka rabu da matar" Zeenat tace "Subhanallah, garin yaya Maheer, in dai ba canzawa kayi ba kai din na san mutum ne me hakuri, kawaici da kauda kai, wacece wannan tayi ma kanta asaran miji kamar ka?" A hankali Maheer yace "Bata son family dina Zeenat, and she poisoned my Lil sis warce kika ganmu tare a mall, duk da ni tayi niyyar poisoning...." Zeenat tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, to yanzu tana ina?" Maheer ya ɗan sauke ajiyar zuciya yace "Ai nace maki na saketa babu aure tsakaninmu" Zeenat tace "I mean ba ayi mata wani hukunci ba akan abinda ta aikata ko ba kuyi involving hukuma bane?" Maheer yace "I did, ni ne ma na mikata gun yan sanda, Unfortunately she is pregnant for me as she said, so bayan abinda tayi which i have evidence, an yanke mata hukunci yanzu haka tana gidan yari, amma saboda cikin dake jikinta my dad had pity for her, yace babu aure tsakanina da ita amma ta ci albarkacin yaron cikinta duk da idan an haifesa dama za ayi DNA test ne, so my dad had to persuade my brother Barrister Usman, sannan ya biya wasu manyan lauyoyin don ayi appealing din case din just for the sake of her pregnancy, we were all against that even our mother, but we had no choice, let it not be as if we are noncompliance to our dad, so ranan monday din nan za a fara zaman court.... And hopefully da irin lawyers da Abbanmu ya daukar mata sannan ga brother na, za a wanketa daga laifin da ta aikata, amma hakan ba yana nufin ni da family dina mun yafe mata bane" Zeenat tayi wani ajiyar zuciya tace "Abun dai bai yi dadi ba Maheer, sorry about that...." Yace "Thank you Zeenat" Tace "Toh yanzu da gasken aure kake son ka sake?" Yace "I am serious Zeenat, i am tired of staying single" Zeenat na murmushi tace "Gashi ka saba da mace" Duk wannan conversation din nasu Mayraah na jin su, A hankali Zeenat tace "Amma in tambayeka?" Yace "Ina jin ki" Tace "Tell me the truth za ka iya aurena Maheer" Sai da Mayraah ta daga kai ba tare da tasan tayi hakan ba, Maheer yayi murmushi yace "Me zai hana, in dai baki canza daga Zeenat din da na san ki ba" A hankali tace "Ina nan yanda ka san ni ban canza ba Maheer, kuma son ka ma bai canza ba a raina" Maheer yace "In dai haka ne me zai hana to, barin in zaki so wannan lil sis dina da kika gan ni tare da ita dazu don a duniya bayan Ammina babu wanda nake ji a raina sama da ita, sannan kuma zaki so family dina da relatives dina" Zeenat tace "Wallahi baka da matsala Maheer, nima fa ina da kannin nan, sannan ai zan so kyautata ma relatives dinka don kai ma ka kyautata ma nawa" Maheer yace "Then we are good to go Zeenat" Zeenat tace "Yanzu yaushe zaka zo mu yi magana?" Yace "Kina ina ne a nan Abuja?" Tace "Gidan aunt dina, ina aiki a wani Private hospital ne" Yace "Ohk gobe friday zan zo after magrib" Tace "Toh Allah ya kai mu, Allah dai ya sa da gaske kake Maheer" Er dariya yayi yace "Ba dai ni nace maki zan zo ba? Just text me the address" Mayraah bata san sanda ta fashe da kuka ba, kawai ita ma ganin kanta tayi tana kuka, Maheer ya mike zaune da sauri yace "I will call u back Zeenat, ina zuwa" Daga haka ya katse wayar ya mike ya hau saman gadon ya zauna kusa da ita da mamaki yace "Mimi what happened? Baki yi bacci ba ne?" Kuka kawai take taki ce masa komai, ya dafa shoulder dinta yace "Talk to me plss Mimi, me ya faru" Buge masa hannunsa tayi ta cire daga kafadarta tace "Ni ka kyaleni cikina ne ke min ciwo" Yace "Subhanallah, yanzu ya fara?" Taki ce masa komai ta fada kan gado ta dinga rusa kuka kamar an aikota, yace "Toh bari in maki allura" Daga haka ya sauka daga kan gadon da sauri, kunna wutan dakin yayi ya juya ya kalleta lkci daya yayi saurin dauke kai don duk rigar baccin ya tattare, har ya gama hada alluran bai sake juyawa ya kalleta ba, yana tafiya a hankali ya nufeta.... Ya zauna kusa da ita yace "Toh bari in maki alluran" Taki ce masa komai, ya dagota yayi mata alluran a lap, ita dai bata fasa kukan da take ba, bayan ya gama mata alluran ya dinga massaging mata wajen yana kallonta ya jawota jikinsa ya kai bakinsa kunnenta murya can kasa yace "Pls ki daina kukan haka, zai daina in sha Allah" he was so carried away da abinda yake yi da har shi kansa bai sani ba, lkci daya ta cire hannunsa daga cinyarta fuska daure tace "Ni ya daina" Da sauri ya saketa ya koma baya, yana kame kame yace "Dama ai nace maki zai daina, let me go and take coffee" Ita dai share idonta kawai take taki ce masa komai, kasa tashi yayi daga inda yake zaune, bai yarda ya kalleta ba yace "Ko zaki je dakinki ki kwanta" Bata tankasa ba ta ja pillow ta kwanta, a hankali yace "To tashi ki kashe wutan dakin sai ki kwanta" Tace "Na fi son sa a kunne" Yace "Ohk, ni bazan iya bacci da shi ba" Tace "Ba coffee zaka je kayi ba" Bai ce komai ba ya zamo kasa daga kan gadon ya kwanta kasan carpet yayi backing dinta, har kusan 12 Maheer bai yarda ya juyo ba, yayi pretending yayi bacci, wajen sha biyu da rabi ya juya a hankali ya daga kai yana kallonta, yaga tayi bacci, tashi yayi da kyar ya fita daga dakin. Can cikin dare Mayraah ta farka, da sauri ta mike zaune ganin baya dakin, idonta na sauka kan wayarsa da ya bari kan carpet kawai ta koma tayi kwanciyarta nan da nan ta ci gaba da baccin ta... Karfe hudu ta sake tashi taje tayi fitsari bayan ta fito ta dau wayar tasa, can dai ta ajiye karkashin pillow, kofa ta nufa ta bude a hankali ta fita har zuwa parlor, kunna wutan parlon tayi ta gansa kwance kasan carpet yayi rub da ciki, ta karasa tana kallon cup din dake kusa da shi, ta dau cup din ta ajiye gefe, sannan ta duka gabansa tace "Yaya" Da sauri ya dago kansa, tace "Yaya me yasa ka kwanta nan? Are you okay?" Ya maida kansa kan throw pillow yace "I am having stomach pain amma na sha magani da sauki" Ita dai kallonsa kawai take, sai kuma da sauri yace "Kin san ban cika son ginger drink ba, i think shi ne ya sa min ciwon ciki" a hankali tace "Allah ya sauwake yaya, to ka sha magani ne?" Ya kalli cup din gefensa yace "Yeah na sha, ai da sauki" Tace "Toh kaje daki ka kwanta" Yace "Aa ai asuba tayi, don't worry je kiyi kwanciyarki, switch off the light for me" Tace "Ohk" Mikewa tayi tace "Bari in kawo maka bargo naji parlon da sanyi" Bata jira me zai ce ba ta tafi ta dauko masa bargon, lulluba masa tayi yace "Thank you" Ta ɗan yi murmushi sannan ta mike ta kashe wutan parlon ta wuce dakinsa ta dau wayarsa sannan ta tafi nata dakin da wayar. Ana idar da sallan asuba Maheer yayi kwanciyarsa kan 3 seater ya fara baccin da bai samu ba sosai jiya, soye soyen da Mayraah take a kitchen ne ya tashesa bacci wajen karfe takwas na safe, da kyar ya mike zaune don kansa yayi masa nauyi ga kuma ciwon da yake masa, har a sannan cikin nasa bai daina ciwo ba, tashi yayi ya wuce dakinsa, yaga ta gyara masa gadon banda kamshi babu abinda dakin yake, bandaki ya shiga yayi wanka, bayan ya fito wanka ya lura wayarsa baya dakin kuma shi yasan bai kai parlor ba, shiryawa yayi yana son fita ya siyo magani tayi knocking kofar dakinsa sannan ta bude tana kallonsa tace "Yaya ina kwana?" Ya sauke idonsa yace "Lafiya lau Mimi, how was ur night?" Tace "Alhamdulillah, cikin ya dena maka ciwon?" Yace "I told u ginger drink ne da na sha, i am fine now" Tace "Toh na gama mana breakfast" Yace "Ohk i am coming" Juyawa tayi ta fita ya bi ta da kallo, yana tafiya a hankali ya fita zuwa parlorn ya tarar har ta hada masa tea ta debar masa abubuwan da ta soya, ya ja kujeran dinning din ya zauna yace "Weldone Mimi" Tana murmushi ta bude wani tsadadden warmer dinta tace "Nayi har da pepper soup" Yace "Thanks Mimi" Haka nan yake breakfast din amma shi kadai yasan abinda yake ji, ganin ya bar abincin tace "Yaya naga baka ci da yawa ba?" Yace "Yeah, i am having headache zan je in siyo magani in dawo yanzu" A hankali tace "Ba maganin ciwon kai a gidan?" Yace "Aa babu, i will be back immediately" Tace "To ko in raka ka?" Yace "Yanzu fa zan dawo" Tace "Toh" Makullin motarsa ya dauka da Atm card, shi dai har sannan bai tambayeta wayarsa ba... Bai wani dade ba ya dawo gidan bayan ya siyo drugs din, a nan cikin motar ya sha maganin da bottle water da ya siyo a hanya, sannan ya ajiye maganin da ya sha a cikin motar, ya dau ledan sauran drugs din ya shiga gidan, zaunawa yayi kan kujera yana kallonta, atamfa ne jikinta dinkin yayi mata kyau sosai, ta karaso ta dau ledan magungunan ta fiddo da su tana dubawa, ya ɗan yi murmushi bai dai ce mata komai ba, bayan ta gama ganin maganin ta tafi ta dauko masa ruwa, ya dau paracetamol din ya sha, tace "Yaya me zan dafa mana da rana?" Yace "Ki bari later mana, ko yunwa kike ji" Tace "Aa ni dai zan yi yanzu, don ina son ka kaini in ga Ammi yau" Ya ɗan buda ido yana kallonta yace "Jiya fa kika ce baza ki je ba, ko kin manta ne" Tace "Aa ni dai kawai in zaka tafi masallaci ka kai ni gidan, yanzu ina son zan je" Yayi shiru, sai kuma yace "Ki bari ranan lahadi...." Ko rufe baki bai yi ba ta marairaice tace "Plss yaya, i am missing Ammi so much, har mafarkinta fa sai da nayi" Yace "Toh ki bari anjima in na dawo masallaci" Ta hade rai tace "Meyasa baza mu fita tare ba sai ka ajiye ni gidan" Yace "Na dai ce ki bari in the evening, dauko min wayata" Ta wani kallesa bata ce komai ba ta bar parlon. Sai wajen karfe shidda saura Maheer ya kai Mayraah gida, har da kukanta da taga la'asar ya wuce bai kai ta ba, wnn ne ma yasa kawai ya kai ta gidan, Bilkisu da Ammi ne kadai a gidan, Omar yaje kai Aunty Mariya da Mama Ladi gidan surkar Dr Khalil za su mata godiya sannan su bata kayan garan da aka debar mata, Sosai Ammi tayi farin cikin ganin Mayraah, Mayraah dai taki barin su hada ido da Ammi sai kallon TV take, Shi kam Maheer danna wayarsa kawai yake tun bayan da ya gaisheta bai sake dagowa ba, as if shi ma dai bai son kallon Ammin tasa, sai suka zama kamar wasu baƙi a parlon, Ammi tayi breaking silence din parlon tace "Amma sai Monday din sama zaka koma aiki ko?" Maheer bai kalleta ba yace "Aa wannan Monday din ne, in sha Allah" Ammi tace "Da wuri haka, na zata sati biyu ka dauka ai" Ya girgiza mata kai yace "Aa, sati daya ne" Mikewa Ammi tayi ta tafi dakinta zata dauko ma Mayraah turaren da Hajiya Amina ta bada a kai mata 3 days ago, Mayraah na ganin Ammi ta shiga daki ta mike ta bi bayanta Maheer ya bi ta da kallo, Ammi ta dauko babban ledan turarrukan tana kallon Mayraah da ta shigo dakin tace "Mimi ga shi Auntynki tace a baki wannan, Mancewa nake ban ba Omar in zai kai maku abinci ya tafi maki da shi ba, in kun koma gida sai ki kirata ki mata godiya" Mayraah ta zauna gefen gadon Ammi tayi shiru, Ammi dai sai kallonta take ganin yanda mood dinta ya canza gaba daya lkci daya, Ammi ta dawo kusa da ita a hankali tace "Lafiya Mimi?" Kamar jira take ta fashe mata da kuka sosai, Ammi ta zauna kusa da ita amma sai ta kasa ci gaba da tambayarta menene don ita inda hankalinta ya tafi daban a lokacin, sosai taji nauyin ci gaba da tambayarta kukan me take don bata san abinda zata bude baki ta ce mata ba, Ammi ta dake, ta jawota jikinta a hankali not knowing what to say to her, dai dai nan Maheer ya shigo dakin da wayar Amminsa da ake kira, ya karasa ya ajiye ma Ammi wayar a kan gadon, Ammi dai bata kallesa ba tana kallon Mayraah tace "Kina waya da Abbanki kuwa?" Mayraah ta girgiza mata kai hawaye na zuba idonta tace "Bani da kati, dama Ammi yaya ne duk inda muka je sai ya dinga ce ma mutane ai ni kanwarsa ce shi bai yi aure ba, shine har da amsan number wata mata lukuta a shopping mall, kullum yayi ta waya da ita da daddare har da ce mata zai aure ta nan da wata daya" Da wani irin mamaki Ammi ta daga kai tana kallon Maheer da ya buda baki yana kallon Mayraah, da kyar Ammi tace "Maheer?? ashe dama kai mutumin banza ne ban sani ba?" Kasa cewa komai Maheer yayi yana kallon Ammin sa, he was so shock, Ammi ta kalli wayarta dake ring ganin Aunty Mariya ke ta kiranta yasa ta dau wayar tace "Ina zuwa yanzu Mimi" Daga haka Ammi ta fita fuskarta a daure, Maheer na kallon Mayraah da kyar yace "Mimi ashe haka kike dama?" Ta wani kauda kai taki kallonsa balle tace komai, ya wani hade rai ce "Ina ce kece kika ce we are still siblings??" Ta wani juyo a fusace tace "To shine nace kaje kana fada ma mutane a titi? Is it not just between us? Duk wanda ya tambayeka kayi aure ba sai kace masa eh ba kawai kayi wucewar ka, har da wani ce mata zaka je gidansu yau bayan magrib, to wllh gwara ka kirata yanzu kace mata ni matarka ce in ba haka ba har Abba sai