Showing 354001 words to 357000 words out of 452169 words

Chapter 119 - Mayrah Complete By Khaleesat Haydar

boyayyen ajiyar zuciya yana kallonta. Karfe biyar saura Maheer ya gama shirin zuwa asibiti after making sure ta kulle kofa bayan ya fita, tana makale jikin window tana kallonsa babu ko kiftawa, bai ko sani ba, har ya ajiye takeaway din pepper soup da tayi masa, sannan ya zaga ya shiga motarsa, mai gadi ya bude masa gate ya bar gidan, lumshe ido tayi ta bude, sannan ta juya ta bar wajen ta koma dakinta. karfe takwas Mayraah na gaban madubinta tana gyara turrukan dake wajen wayarta ya fara vibrate, Mikewa tayi da sauri ta tafi inda wayar yake ta dauka, ganin Maheer ke kiranta ta zauna gefen gado sannan ta daga ta kai kunne tayi shiru, Calmly yace "How are you Mimi" Ta sauke idonta kamar yana wajen a hankali tace "Fine" Yace "Kin ci abincin?" Tace "Na ci" Yace "Aint you lonely?" Shiru tayi, Yace "Yesternight was... Superb, i can't stop thinking of that lovely moment, you are rare Mimi...." Duk da ba a gabanta yake maganar ba sai da ta rufe fuskarta da pillow, yace "Hello" Shiru tayi, yace "Mimi, nasan kina ji na" Ta rasa me yasa yanzu muryarsa ke sending mata quivers all over her body, ya kwantar da murya yace "say something pls Mimi" Ta dago a hankali tace "Ai ina jin ka" Yace "Tell me how u felt Yesternight" Ji tayi kamar kasa ya bude ta shige, kamar yasan halin da ta shiga, as if whispering in her ears yace "So now you know we are husband and wife not siblings ko?" Jin taki basa amsa yace "Toh shikenan kilan bacci kike ji, je ki kwanta, sai da safe" Bata san sanda tace "Aa" Yace "So now tell me, was it painful?" Turo baki tayi tace "Ni dai na manta" yana murmushi yace "Toh zaki tuna da safe in na dawo.... Za mu shiga theatre yanzu, idan baki yi bacci ba anjima zan kira ki" A hankali tace "Toh" Daga haka yayi mata sallama ta katse wayar ta ajiye. Washegari Mayraah na tashi da safe sanin karfe takwas zuwa tara yake dawowa daga asibiti, nan da nan ta fara hada breakfast, sannan ta gyara gidan gaba daya ta saka air freshener....
Mayraah na duke dakin Maheer wajen karfe goma na safe tana hada masa shayi bayan ya sa ta kawo masa breakfast dinsa dakin after taking his bath, duk movement din da tayi idonsa na kanta, har dai ta gama dibar masa breakfast din sannan ta daga kai tana kallonsa, calmly yace "Ke kin ci?" Kai ta gyada masa, dai dai nan wayarsa ya fara ring daga ita har shi suka juya suna kallon wayar, daukar wayar yayi ganin Ammi ce, yayi picking ya kai kunne, yayi sallama sannan ya gaisheta, shiru yayi yana sauraronta, Mayraah dai kallonsa kawai take ganin yanda mood dinsa ya canza, after almost a minute yace "To a ni ban san me zance bane kuma Ammi, i don't have anything to say here...." Daga nan kuma yayi shiru yana ta sauraron Ammi, after some seconds yace "Zan shigo da yamma in sha Allah" Katse wayar yayi ya ajiye gefe, Mayraah dai kallonsa kawai take ganin sosai mood dinsa ya canza ya dinga juya shayin gabansa da teaspoon absent-mindedly, can dai tayi gathering courage a hankali tace "Yaya menene?" Daga kai yayi da sauri ya kalleta, tayi maza ta sauke idonta don ita har sannan bata iya hada ido da shi, kunya bazai bar ta ba, yayi feigning smile yace "Nothing Mimi" Daukan shayin yayi ya fara sha, bata sake cewa komai ba amma haka kawai taji hankalinta yaki kwanciya she wants to know what it is, a hankali ta mike yace "Ina za ki?" Without looking at him tace "Zan je in kwanta, i woke up very early" Daga haka ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita ta kulle masa kofar, kasa yin breakfast din yayi, bayan wani lokaci ya mike ya bi bayanta zuwa dakinta, kwance ya sameta kan gadonta ya hau saman gadon duk da ta rufe idonta kamar me bacci amma yasan ba bacci take ba, dagota yayi ta marairaice masa tace "Bacci fa nake yi Yaya, kaje kayi breakfast dinka mans" Kamar me rada yace "Ba yunwar abinci nake ba.... Mimi" Da farko gardama ta so tayi masa da ta lura da inda ya dosa, amma cikin mintuna kadan yasa ta sakankance ba tare da ta ankara ba.... Sai kusan azahar Maheer ya farka, ya juya yana kallon Mayraah dake bacci, murmushi yayi ya mata kiss a lips dinta ya rufa mata duvet a jikinta sannan ya sauka daga saman gadon ya fita daga dakin.... Da yamma Maheer ya shirya zai je can gida kamar yanda yace ma Ammi, da mamaki yake kallon Mayraah da ta saka hijab ta dauko handbag sannan ga Nikab a hannunta wai ita ma zata je, yayi murmushi yace "No Mimi ki bari next weekend in sha Allah" Girgiza masa kai tayi tace "Aa ni yau nake son in je" Shiru yayi yana kallonta......

112
Mayraah ta gama daura nikab din dake hannunta ta nufi kofa zata fita, Maheer da ya bi ta da kallo yace "Mimi" Juyowa tayi amma bata kallesa ba, yace "Ina za ki je da Nikab?" Ta ɗan yi shiru sai kuma a hankali tace "Dama ai ina sa wa" Yace "Naga dai tun da kika yi sauka baki kara sa Nikab, so why putting it on today?" Ta marairaice tace "Kawai ina son in sa ne yau" Bai sake ce mata komai ya kashe Ac din parlon da TV dake kunne sannan ya nufi kofar shi ma, har ta kusa parking space ya fito daga parlorn bayan ya kulle kofar ya tsaya kallonta har ta isa parking space ta jingina da motarsa tana jiransa, Walking slowly ya isa parking space din shi ma, bayan yayi unlocking motar ta bude ta shiga ta kulle, shi dai ya kasa daina kallonta kamar ranan ya fara ganinta, he is just realizing how everything about Mayraah is just so perfect, kilan bond din marriage dake tsakaninsu yanzu ne yasa fara ganin wasu abubuwa a tare da ita masu daukan hankalin ko wani ɗa namiji, wanda a baya taɓa lura da duk abubuwan nan ba sai a yan kwanakin nan, it's now he is realizing how beautiful and Gorgeous she is, with all this thought ya shiga driver seat mai gadi ya bude masu gate suka bar gidan. Sai da suka yi nisa Maheer ya ɗan kalleta, idonta na kan side window tana exploring the beauty of Abuja, gently ya kamo hannunta, ta juya da sauri amma bata kallesa ba, kokarin janye hand dinta take daga nasa amma yaki sake mata, idonsa na kan titi yana murza mata hannun a hankali, ta maida dubanta kan side window, after some minute taji yace "Kar fa mu je gida kice za ki kwana a can" ita dai bata ce masa komai ba, yace "Ohk you have that in mind kenan ko?" A takaice tace "Eh" Yayi murmushi bai sake ce mata komai ba, daga karshe ta samu ta zame hannunta daga nasa. The remaining journey was absolutely silent, suna isa gida Maheer yayi parking a waje ya juya yana kallonta, ita ta fara sauka ta nufi gate, bayan ya kulle motarsa ya bi bayanta, ta gaida securities din bakin gate sannan ta shiga compound din, tana isa entrance din shiga gidan sai ta kasa bude kofar parlon, ta koma gefe ta tsaya har ya iso entrance din, yana kallonta yace "Take off that Nikab Mimi" Duk da baya ganin fuskarta ta wani hade rai ta girgiza masa kai kan tace komai ya fizge nikab din daga fuskarta, bata fuska tayi kamar zata yi kuka taki yarda ta kalli idonsa ta fara kokarin kamo hannunsa da sauri tace "Don Allah yaya ka bani bazan iya shiga haka ba wallahi" Ya matsa dab da ita yana rike da nikab din yayi kasa da murya yace "You are giving them hint that you are not longer a virgin...." Mayraah ji tayi da ma kasa ya bude ya hadiyeta kawai ta huta da wannan kunyan da ya lullubeta, juya masa baya tayi da sauri she never expect to hear that from him, yayi murmushi yana kallonta yace "On one condition zan baki nikab din" Shiru tayi bata ce masa komai ba, tana jin ya bude kofar parlon ta juya da sauri ta marairaice masa tace "Don Allah fa nace" Yace "I said on one condition" Kamar za tayi kuka tana bubbuga kafa tace "To ka fada in ji mana" shagala yayi da kallonta baya ko kiftawa, zata kwace nikab din a hannunsa yayi saurin mayar da shi bayansa, yana magana can kasa yace "You are not ready" Kofar parlor ya bude yana shiga ta bi bayansa da sauri, turus tayi a parlon tana kallon Haseenah dake zaune kasan carpet da tsohon cikin ta a gaba wanda kai sai kayi tunanin yan uku zata haifa, Maheer tun da ya kalleta sau daya shi ma by mistake yayi saurin dauke kansa, tayi wani irin baƙi kamar na zunubi, kai baka ce ta taɓa haske ba a rayuwarta ga uban ramar da tayi, ga ciki ya tsufa sosai, tana kallonsa cikin sanyin murya tace "Ina wuni" Fuskarsa a murtuke yayi hanyar stairs without looking at her for the second time balle ya amsa gaisuwan, Mayraah dai ta sauke idonta kawai ta bi bayansa ita ma bata sake kallon Haseenah da ta sunkuyar da kanta ba, ko da Mayraah ta haura sama taga Maheer bangaren Ammi ya nufa, tana tafiya a hankali ta nufi dakinta ta bude ta shiga, lkci daya mood dinta ya canza ta zauna bakin gado tana kallon windan dakin. Maheer na shiga Parlon Ammi ya sameta zaune ita da Usman, Maheer ya karasa ciki ya zauna sannan ya gaisheta, ya kalli Usman shi ma suka gaisa, duk wannan abun bai kalli idon Ammi ba, infact rabonsa da gidan ma tun last friday bayan ya tafi da Mayraah, sai dai suna waya kullum, A hankali Ammi tace "How is Mimi?" Yace "She is downstairs" Ammi bata sake cewa komai ba, amma tana kula da how moody he is kuma tasan hakan bazai rasa nasaba da kiran da tayi masa dazu ba, bayan wani ɗan lokaci Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace "Ni dai ina ga Abban ku kilan don ba shi ya ci poison din bane shi yasa har ya nemi a wanke yarinyar nan, tunda gashi har anyi granting mata bail jiya, duk wannan bai ishe sa ba sai gashi ya sake ce mata ta zo min nan, wai ta je kano mahaifiyarta ta koreta sannan ta hanata zuwa gun yan uwanta gaba daya, to uwar me ni zan mata da ya sa ta taho min nan?" A fusace Ammi ta kare maganar, Maheer dake ta kallon Ammi a hankali yace "Ni dai nasan babu aure tsakanina da ita balle a kawo min wani batu can, imagine relatives dinta wa enda su ne dolenta sun yi disowning dinta sun koreta balle mu, i don't think she is suppose to be here, Barrister ya kamata tun farko yayi ma Abba maganar rashin dacewar haka, don nasan Abba bazai ce ta zo gidan nan ba without his knowledge" Ammi tace "Ni fa don takaici wllhi har yanzu ban sauka parlon ba balle in ganta, tun da Bilkisu ta shigo nan tace min ai ga wance ta zo na kira Abbanku nan take, sai yake ce min wai shi yace tazo nan kafin a san yanda za ayi idan ya dawo, Idan haka ne me yasa bazai kai ta wajen matarsa a kano ba? Ina ce can ma gidansa ne ko? To ai sai ya kai ta can ta zauna, don Wllhi in har gidan nan yarinyar nan zata kwana to barin gidan zanyi bazan kwana a ciki ba, duk wanda zai iya saka ma mutum poison don ya ci ya mutu to babu mugun abun da bazai iya aikatawa ba a rayuwa, tsaf zata iya yin komai, zuciyarta ta riga ta kekashe komai zata iya aikatawa, don haka in dai bata bar gidan nan yau ba to ni zan bar gidan" Usman dake ta sauraron Ammi ya daga kai yana kallonta, calmly yace "Abba fa ba wai yace nan zata zauna bane, mu ma ai baza mu yarda ta zauna mana a nan ba, Abba is just being considerate because of her pregnancy, and she just have 6 weeks remaining to put to bed...." Ammi tace "Sai aka ce lallai lallai sai a wajenmu zata haihu? In uwarta ta koreta to ta tafi dangin ubanta mana, wlh daga kai har Abban naka kuna bani mamaki, ku a ganin ku wannan shawaran da ku ka yanke a tsakaninku dai dai ne ko? Mu kuma bamu da right da za aji namu opinion din tunda kun gama shawara ko" Murmushi kawai Usman yayi, Ammi ta mike tace "Ina nan ina jiran Abban naku ya dawo in ji abinda yake nufi" Daga haka ta fita daga parlon rai bace. Bayan Magrib Mayraah na zaune parlon Ammi da plate din abinci a gabanta tana ci a hankali, har sannan taki sakin jikinta kai kace bakuwa ce ita a gidan, sai da ma Ammi ta bi ta har dakinta dazu kafin ta iya fitowa bayan tayi pretending kamar sallah ta shiga dakin tayi, ko da taje gaida Abba a bangarensa bata dade ba on like before ta dawo bangaren Ammi ta zauna, duk Ammi na lura da ita abun ma dariya yake bata, tana gama cin abincin ta mike zata fita da plate din Ammi tace "Ya isheki?" Gyada mata kai tayi, sai ga Bilkisu ta shigo da sallama, plate din ta amsa hannun Mayraah sannan ta dau warmers din abincin ta fita. Karfe takwas da yan mintuna Abba na zaune parlon parlon Ammi, sai Haseenah dake kan carpet ta sunkuyar da kanta, daga kusa da Ammi Mayraah ce zaune sai Maheer da Usman da su ma duk suna parlon, Ammi dai fuskarta babu yabo babu fallasa a parlon don ko kallon Haseenah taki yi, da Haseenar ma ta gaisheta a takaice ta amsa mata babu yabo babu fallasa without looking at her, da ta tuna irin wahalan da Mayraah ta sha sai taji they have nothing to do with Haseenah, cikin jikinta ma kawai fata take kar ya kasance na Maheer, don sam bata son su hada zuri'a da irin Haseenah, duk kawaicinta da hakurinta tunda har ta kasa yi ma Haseenah wnn kawaicin to ba karamin kullatar ta tayi ba a ranta, Abba yayi gyaran murya cikin nutsuwa ya fara magana yace "Da farko dai nasa an daukaka karan wannan yarinya ne ba don komai ba sai don albarkacin juna biyun da take dauke da shi, sannan Allah ma muna masa laifi mu nemi gafararsa ya yafe mana, ko ma ba don haka ba iyayenta mutanen kirki ne, duk da suna da damar daukan lauya da zai kareta tun farkon shari'a amma basu yi hakan ba, they neva supported her deed, sai ta dawo kamar mara galihu a lokacin, anyway all that aside, ban sa a daukaka karar nan don yarinyar ta dawo cikin rayuwarmu ba, Aa ina son mu yi considering condition dinta, sannan Maheer is suppose to take her responsibilities har zuwa sanda Allah zai sauketa lafiya, in ta yarda zata shayar da yaron it's left for her, idan kuma bazata shayar ba shi ma it's okay" Ammi dake ta kallon Abba zuciyarta na tafarfasa tace "So yanzu me kake nufin zai faru?" Abba ya kalleta, shi dai Maheer kansa na sunkuye bai taba jin zai bijire ma umarnin parent dinsa ba amma wnn umarnin kam baya jin zai iya because he have nothing to do with Haseenah, ko ganinta ma bai son yi har cikin ransa yaji yana mugun tsanarta, Abba ya katse masa tunaninsa ta hanyar cewa "Abinda zai faru, kawai wajen da zata zauna har zuwa sanda zata haihu Maheer zai samar mata a cikin garin nan, ko da self contain ne, sannan zai dau duk wani responsibilities nata tun daga ciyarwa har zuwa magani da abubuwan bukatan yau da kullum" Ita dai Haseenah kanta na duke hawaye na ta sauka idonta, A takaice Ammi tace "Na ga dai duk wannan responsibilities din da kake fadi za a iya mata a ko ina ba lallai sai an samar mata waje a Abuja ba, don't she have relatives? Ta tafi wajensu mana, sai lallai tana nan ne za ayi taking responsibilities dinta" Abba dai kallonta kawai yake, Haseenah ta fashe da kuka muryarta na rawa tace "Don girman Allah Ammi kiyi hakuri ku yafe min, wallahi ban san inda zan je ba kuma daga nan, Mum dita ta koreni kuma ta hanani zuwa gun yan uwanta gaba dayan su, dangin babana duk yan Nijar ne, bayana ciwo yake min bazan iya zaman motar zuwa can ba wllh, don Allah ku rufa min asiri ku tausaya min..." Tana kai wa nan ta fashe da matsanancin kuka, Abba na kallon Maheer yace "Get her a self contain apartment, zan tura maka kudin" Abba na kai wa nan ya mike, Ammi ta bi sa da wani irin kallo, har ya kusa kofa ya sake juyowa yace "Kafin a samu gidan, ka biya mata hotel ko na 3 days ne ta zauna a can, so in za ku tafi gida sai ku tafi tare da ita ka samar mata hotel a hanya ka ajiyeta" Bude kofar parlon Abba yayi ya fita, Ammi da ranta yayi mugun baci ta mike ta wuce dakinta, Sai a sannan Mayraah da gaba daya mood dinta ya canza ta dago kanta a hankali sannan ta mike ta nufi kofa ta fice daga parlon Maheer ya bi ta da kallo, Usman ya mike shi ma ya fita daga parlon, Haseenah na kuka ta hade hannunta biyu tana kallon Maheer cikin rawan murya tace "Don girman Allah ka yafe min Maheer, wallahi nayi nadamar duk abinda na aikata, son zuciya ne

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login