Showing 372001 words to 375000 words out of 452169 words
Chapter 125 - Mayrah Complete By Khaleesat Haydar
karaf tace "Tana can kitchen tana hada ma mijinta abinci, tun bayan la'asar take gidan nan yau" Usman dai yayi murmushi, ya mike ya ba Mama Ladi Babyn dake hannunsa, ta amshesa ta kwantar da shi kan gadonsa, Abba yace "Nan kuma aka dawo da su?" Mama Ladi ta sauke wani bayanannen ajiyar zuciya tace "Da dalili babba Mamuda, ba haka kawai aka kwaso su aka fito da su ba, kai dai in ka sahirta ko Ammi ka aiko ta sanar min, amma kafin nan don Allah taso ka ga jikin yaran nan" Mikewa Abba yayi ya tafi inda suke kwance, Shi dai Usman kallon yaran kawai yake, Mama Ladi ta bude masu jikin yaran, Abba ya duka yana kallonsu da kyau, haka ma Usman, Mama Ladi tace "Me ku ka gani?" Usman yace "Meye wannan din?" Mama Ladi tace "Dubawa zaka yi da kyau" Kunna fitilar wayarsa yayi yana haska jikin babies din, Abba yace "Konewa suka yi ne?" Mama Ladi tayi kwafa tace "Alhamdulillah, to in gaya maka Mamuda daga mun je kasuwa da Ammi muka dawo muka tarar da jikin yaran nan a haka suna ta tsala ihu zar tausayi, kuma daga su sai uwar muka bari a gidan nan don yarinyar nan Bilkisu girki muka bar ta tayi a kitchen, har yanzu mun rasa gane da me tayi masu wannan izaya a jiki haka, mun tisata a gaba ni da Ammi taki fada" Abba ya juya ya kalli Maheer, Mama Ladi tace "Meye kake wani kallon Mashir ina maka maganar arziki, wannan solobiyon me kake ga zai iya yi? Ai ko bin ta kansa ban yi ba kai kawai nake jira kai me sa Usuman ya wanketa a kotu" Abba yayi shiru sai kallon jikin yaran yake haka ma Usman, Mama Ladi tace "Ka je dai ka huta gani nan zuwa" Abba ya sauke ajiyar zuciya yace "Toh Allah ya kyauta" Daga haka ya juya ya wuce sama, Usman yace "Kuma kun tabbatar ita din tayi masu haka a jiki?" Mama Ladi tace "Aa karya ni da uwarka Hajara muka mata" Usman ya juya ya bar parlon zuwa dakinsa, Maheer dake kallon Mama Ladi yace "Baki masa maganar Badiyyar ba kuma" Da sauri Mama Ladi ta kallesa tayi kasa da murya tace "Kai kuma baka san wasa ba" Shiru Abba yayi yana sauraron Mama Ladi dake zaune a Parlonsa attentively, har dai ta kai aya, sai kuma ta kara da cewa "Sabili da haka gobe da asuba sai mu je da Usuman tasha ayi shatar golf, tana baya ni ina gaba don bazan ma zauna waje daya da ita ba, muna isa garin Kaduna mu tsaya mu dau Mariya sannan mu karasa kano, in ma iyayen sun dubi Allah sun hakura oho, in ma basu hakura ba oho mu dai mun kai ta mun kuma nuna mu manyan mutane ne, idan sun so bayan tafiyar mu su sake korata ta shiga duniya ba ruwanmu" Abba ya sauke ajiyar zuciya yace "Shawara ce me kyau Mama, amma kuma abinda bai min ba a duk bayanin nan naki shine da kika ce za a bar yaran nan wajen Ammi, ta yaya za a raba jariran nan da uwarsu, jariran da ko sati daya basu yi ba, ni a ganina hakan bai kamata ba, tamkar an shiga haƙƙinta ne da ma na yaran" Mama Ladi ta katse sa da sauri tace "Wai halan baka ga fatar jikin yaran nan bane da na nuna maka dazu Mamuda? Uwar kirki ce zata ma yaranta haka? Ni fa daga karshe na zargi tawul ta dinga dorawa kan garwashi take nana masu a jiki idan ya dau zafi, A gaskiya Mamuda in kace Hasinu ta ci gaba da zama gidan nan duk ma me zai je ya dawo babu ruwana, babu abinda ya shalli Ladi wllhi, kuma yau da ace abun zai tsaya kan kai da 'ya yanka maza ne, bazai taɓa 'ya ta Ammi ba to da sai ince ku karata, bazan ma sa Mera ba don kakanta Alhaji Saminu ba yarda zai yi ba, wai ma tsaya Mamuda, ko dai ka manta gubar da ta sa ma Mera a abinci ta ci ne har muka fidda rai da Mera? Magana ta domin Allah fa Mamuda" Abba ya ɗan yi murmushi, speaking calmly yace "Mama ina ce har gida an kama mata, ba lallai sai nan gidan zata zauna ba, ga can gidan da aka kama mata sai a samar mata me aiki, ni tausaya ma yaran nake, it won't be fair a rabasu da uwarsu..." Mama Ladi tace "Shi kuma jaririn da uwarsa ta mutu ta barsa sai a tona rami gefen na uwar a saka shi tsabar tausayi ko?" Abba ya sauke ajiyar zuciya yace "Toh shikenan, goben sai a yankar maku ticket din jirgin sama zuwa kano in sha Allah" Mama Ladi ta washe haƙora tace "Jirgin sama kuma, toh Alhamdulillah, abinda nake ta son ka fahimta kenan Mamuda, jarirai nawa iyayensu ke mutuwa su barsu wajen haihuwa kuma su girma cikin aminci, ba da son ranmu za mu raba er banzar da jariranta ba sai don muguwa ce, gashi har yaran nata bata bari ba, gwara kakarsu ta rikesu ta kula da su har su yi wayo" Abba yace "Toh Allah ya rufa asiri" Mama Ladi tace "Ameen, kaga kafin jirgin namu ya tashi sai a sanar ma Mariya ta tafi tasha ta hau mota mu hadu a kanon gaba daya" Abba yace "Amma su iyayen nata ya za su ji in suka ga an hanata shayar da yaranta?" Mama Ladi ta mike tace "Mamuda ka daina mayar da hannun agogo baya, ni na ma gaji da magana wallahi, ina ruwanmu da iyayenta da su kansu sun sallama ma duniya ita, yanzun ma kawai sbda dattako da kuma nuna ma iyayen mu yan babban gida ne yasa za mu kai ta, banda haka Hasinu mugun abinda tayi mana ai bai kamata mu sake bi ta kan lamarinta ba, dama bakina bakin iyayen nata zan ce sai dai kuma ayi hakuri mun karbe yaranmu sbda Hasinu bata da halin kwarai da zata rike mana su, snn in labarta masu abinda tayi ma jariran da muka je kasuwa, kamata yayi ma su mikata dawanau don a binciki ƙwaƙwalwarta" Daga haka Mama Ladi ta fice ta bar ma Abba parlonsa. Wajen karfe tara Mayraah na kitchen zata zuba abinci Maheer ya shigo kitchen din, ta ci gaba da zuba abincinta ta ki kallonsa, kulle kofar yayi ya nufeta a hankali yace "Mimi ki zuba a food warmer mu tafi gida it's getting late" Tace "Ni yau a nan zan kwana" rasa abinda zai ce mata yayi yana kallonta, sai kuma yayi kasa da murya yace "Amma fa ba mu yi haka da ke zaki kwana a nan ba Mimi" A takaice tace "To make things easier for you yasa zan kwana a nan yau, kaga ba sai kana sneaking din zuwa nan da sassafe ba, ko kuma ka min karyan zaka je wani waje sai ka zo nan" Daga haka ta nufi kofa ya bi ta da kallo babu ko kiftawa, bayan ta bude kofar kitchen din ta juya ta kallesa ta wani turo masa baki sannan ta fita, ɗan murmushi yayi yana shafa kansa, after few seconds shi ma ya fita daga kitchen din. Zaunawa yayi parlor yana kallon Ammi dake rungume da one of the twin, Bilkisu ma na rike da dayan, zuwa sannan babies din sun ɗan fara shan madaran da Ammi ta siyo masu, Haseenah dai na can an bar ta ita kadai a daki gashi an kwashe yaran, ruwan nononta sai zuba yake, Ammi na kallon Maheer tace "Mimi tace kace mata nan za ku kwana?" Ya sauke idonsa a hankali yace "Eh" Ammi bata sake ce masa komai ba, ya mike ya wuce sama. Maheer na murda kofar dakin Mayraah yaji ta sa makulli, ya fi minti daya tsaye bakin kofar, can yayi knocking a hankali, sai da ya sake knocking yaji tace "Waye" Yayi shiru yaki cewa komai, ganin ba bude kofar zata yi ba don da alamar ta gane shi ne, kawai ya juya ya bar bakin kofar. Washegari flight din karfe goma na safe Usman yayi ma Mama Ladi da Haseenah booking, Tuni Mama Ladi ta cakare cikin tsadadden atamfarta da sabon mayafi ga jakarta na yan gayu shi ma sabo fil, hatta takalmin kafarta sabo ne me tsada, kai kace gidan biki zata, ta wani hakikance a parlon bayan an kai sabon akwatin ta booth din motar Usman tana jiran fitowar Haseenah, a fusace Mama Ladi tace "In fa muka biye wancan matar sai mu rasa jirgin nan, Bilkisu ki leka ki ga uban me take har yanzu a dakin da bata fito ba" Mayraah dai na zaune gefen Ammi tana rike da one of the baby tana basa madara a feeder, Ammi kuma na ba dayan madaran shi ma, Maheer dai na zaune dinning da cup din coffee a gabansa, Haseenah na biye da Bilkisu suka fito daga dakin kanta a kasa, sosai idanuwanta suka kumbura saboda kuka, Mama Ladi na kallon Bilkisu tace "Ina akwatin kayan nata?" Bilkisu tace "Ai na kai parking space tun dazu" Mama Ladi ta mike tana kallon Ammi tace "Toh ni dai daga kano kaduna zan koma, Allah ya baki ikon rainon yaran nan cikin aminci, tun da Bilkisu tana nan komai zai zo maki da sauki" Daga haka Mama Ladi ta nufi kofar fita parlon Mayraah na mata Allah ya kiyaye hanya, Ammi ma haka, mikewa Maheer yayi ya fita parlon, Haseenah ta durkusa da kyar hawaye na sauka idonta tayi ma Ammi sallama, Ammi ta kasa kallon cikin idonta, Mayraah ma dai bata iya ta kalli Haseenah ba, lkci daya zuciyarta ya karaya, babu uwar da zata so a rabata da yaranta daga haihuwarsu, a haka Haseenah ta mike ta bi bayan su Mama Ladi tana goge hawayen da yaki tsaya mata.....
Mayraah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
118
Ammi na kallon Maheer har ya karaso cikin ward din daga office din pediatrician da yayi admitting yan biyun, tace "Test din meye ya rubuta ayi masu Maheer?" Maheer na kallon twins din dake kwance suna bacci yace "Aa ba wani abu bane, kawai tsarkewan da suke after feeding yasa za a yi masu Xray to check if there is any Airway disease...." Ammi tace "Toh zafin jikin kuma me yace a kai? sannan da an basu abinci fa sai amai" Maheer yace "Amai kuma?" Ammi tace "Dazu ma a gaban likitan suka yi" Maheer yace "Za dai a ci gaba da basu magunguna ne kawai har zuwa sanda result din test da za a masu zai fito" Ammi bata sake cewa komai ba, Maheer ya daga kai ya kalli Mayraah dake zaune kusa da yaran... Bayan la'asar Maheer ya maido su gida daga hospital, Ammi dake rike da Ayman ta wuce sama Mayraah na biye da ita da other twin din, parlor Maheer ya zauna bayan ya amsa gaisuwar da Bilkisu ke masa, sai da Ammi ta fara yi ma jariran wanka sannan ta hada masu madara ta ba Mayraah na Ayman, ita kuma ta dau Aryan zata basa nasa, kadan yaran suka sha kamar sun hada baki, Ammi na kallon Mayraah tace "Duk yau fa basu yarda sun sha madaran ba, wanda suka sha a asibiti ma a gaban likitan suka amayar, tun sannan ko na basu basa sha...." Ko rufe baki Ammi bata yi ba Ayman ya fara amai, Mayraah ta dago sa da sauri ta dinga kallonsa da mamaki don ita bata taɓa ganin jariri na amai ba, Ammi ta kwantar da Aryan tace "Kawo shi" Mayraah ta mike ta kai mata shi, Ammi bata gama amsan Ayman a hannun Mayraah ba Aryaan dake kwance shi ma ya fara aman, sai kawai Ammi ta bar ma Mayraah Ayman din ta dau Aryaan da sauri, a bit confuse Mayraah tace "Ammi kamar lactose intolerance ne ke damunsu fa" Ammi ta kalleta tace "Meye shi?" Mayraah zata yi magana Maheer ya shigo parlon, Ammi ta kallesa bata ce komai ba, ya karasa shi ma yana kallonsu yace "Me ya faru?" Ammi tace "Aman dai suka yi, daga an basu madara, meye ma'anar hakan" Maheer ya duka yana kallon Aryaan dake hannun Ammi, daga rigarsa yayi yana kallon jikinsa, sai kuma ya kai hannu cikinsa as if examining something, ya fi second talatin yana kallon babyn kafin ya mike tsaye, Ammi dai sai kallonsa take, juyawa yayi ya tafi ya zauna kan kujera, Ammi tace "Nayi tambaya kuma kayi shiru" Maheer yace "I think their system is having trouble digesting the milk, they are intolerant to the formula, madaran bai amshesu ba, they are having milk intolerance, ga jikinsu nan ya fara kuraje, kuma cikinsu ya ɗan kumbura" Ammi tace "Nima dai na yi tunanin haka, kuma sai da likitan ya tambaye mu wani madaran ake basu na gaya masa, kilan sai gobe mun je duk ya mana bayanin nan, to yanzu ya kake ganin za ayi, me za a basu tunda madara kace bai amshe su ba?" Maheer yace "Sai dai a canza masu madaran" Ammi tace "To wanne za a canza yanzu?" Maheer yace "Aa wannan pediatrician din ne zai yi recommending maku, i can't say" Da damuwa Ammi tace "To yanzu haka za su kwana babu abinci har sai Allah ya kai mu gobe?" Maheer yace "Haka nan za ki basu madaran amma kar yayi ƙauri, gobe da safe in an koma hospital din definitely zai canza masu" A hankali Ammi tace "To Allah ya kai mu" After isha Mayraah na parlon Ammi tana rungume da Ayman da jikinsa yafi na Aryaan zafi, Maheer ya shigo parlon, ya kalli Aryaan dake bacci, ya zauna yana kallonta yace "Ammi na daki ne?" Mayraah ta girgiza masa kai tace "Ta je ta kai ma Abba abinci" Maheer yace "Ohk, ki shirya mu tafi gida it's late already, kin ga gobe zan je aiki da safe" Mayraah na kallonsa ta marairaice tace "Yaya ka bar ni in kwana a nan kai ka tafi pls, ka ga basu da lafiya kuma ba wanda zai taya Ammi kula da su" Maheer yace "Ni kuma wa zai kula da ni idan na tafi?" Mayraah bata san sanda tayi dariya ba tace "Sai kace wani jariri" Yayi kasa da murya yace "Pls ki tashi mu tafi gida Mimi, Bilkisu zata taya Ammi kula da su" Mayraah ta bata fuska taki ce masa komai, yayi shiru yana kallonta, a hankali yace "Toh amma on one condition zan bari ki kwana nan" Ta ɗan kallesa tace "What is the condition?" Ya mike ya koma gefenta ya zauna yace "You will kiss me first" Kauda kai tayi da sauri ta turo baki tace "Kamar ya" Yace "To kwantar da shi ki tashi mu tafi kawai" Ta marairaice masa tace "Baka jin tausayinsu ne yaya?" Yace "Ina ji mana sai dai bai kai yanda naga kike tausayinsu ba ke" Murmushi tayi kawai, yayi kasa da murya yace "Pls Mimi" a hankali tace "Idan Ammi ta shigo fa" Yace "Ai kwantar da shi za ki yi mu je Bedroom dinta kawai" Ta zaro ido ta kallesa, yace "To bari kawai in fita in ce ma Ammi ta maki magana za mu wuce gida, kin san dai zan iya" Mayraah ta dinga kallonsa kamar zata yi kuka tace "Bedroom din Ammi fa kace" Mikewa yayi yace "Ki sameni parking space" Da sauri ta rikosa tace "Toh ai bance bazan yi ba" Bedroom din Ammi ya nufa yace "Am waiting for you" ta bi sa da kallo har ya shiga dakin, a hankali ta kwantar da babyn hannunta kusa da ɗan uwansa, ta mike ta nufi dakin tana tafiya a hankali har ta shiga, tana shiga taga ya kulle kofar, ta marairaice masa ta ki yarda su hada ido tace "Ni dai kunya nake ji" Yace "Toh bari a rage hasken dakin, in kika bata lokaci kuma Ammi ta shigo ke zaki ji kunya ba ni ba" Bai jira cewarta ba ya sauya wutan dakin zuwa mara haske, haka kawai Mayraah taji gabanta na faduwa ta tafi ta zauna gefen gado, har cikin ranta da gaske kunyan take ji, ya dawo ya zauna gefenta yana kallonta da lumsassun idonsa, kasa kallonsa tayi duk da babu haske sosai a dakin, yayi kasa da murya yace "You are wasting your time Baby gal" Rungumesa tayi cike da jin kunya tace "Allah yaya kunyan nake ji da gaske" Ya dago kanta yana kallonta a hankali yace "Toh in rufe ido?" Gyada masa kai tayi, ya lumshe idonsa ta dinga kallon lips dinsa, lumshe idon ita ma tayi, a hankali ta kai bakinta kan nasa ta fara kissing dinsa passionately, Maheer bai taɓa tunanin Mayraah zata yi kissing dinsa ba, kawai ya sa a rai at the end idan ta gama bata masu lokaci shi ne dai zai yi kissing din nata, he was so surprise... she kissed him for more than 3 minutes kafin ta kwantar da kanta kan chest dinsa ta lumshe ido tana sauke numfashi a hankali, gaba daya ta gama rikitasa, he never expect she could kiss so perfectly kamar haka, she really turned him on, ya marairaice mata yana magana da kyar yace "Pls Baby gal, let go home, Ammi can take care of the boys" Mayraah ta daga kai ta kallesa a hankali tace "But that wasn't the agreement" Ya kara marairaice mata yace "I know but... Plss" Mayraah ta zaro ido jin an bude kofa a can parlor tace "Kaga Ammi ta dawo ko" Bata jira cewarsa ba ta mike da sauri ta nufi kofar dakin ta bude ta fita kamar munafuka, Bilkisu ta gani ta shigo da flask din ruwan zafi zata ajiye, Mayraah ta nufi kofa ta fita daga parlon ta tafi dakinta, kwanciya tayi gefen gadon ta lumshe ido, har sannan zuciyarta bai daina bugawa ba, after some minutes taji an bude kofar dakin, bude ido tayi da sauri, ta mike zaune ganin shi