Showing 390001 words to 393000 words out of 452169 words

Chapter 131 - Mayrah Complete By Khaleesat Haydar

din da bata san yana da shi ba ya fara, da kyar ya iya cewa "I... Will... Prefer, the Milk" Juyawa tayi tana taku dai dai ta nufi kofa, ai kawai ji yayi ya kasa controlling kansa, tun bata isa kofa ba ya risketa carrying her like a baby into the room, cike da shagwaba tace "To Milk din fa...." Cuddling her bare chest at the same time Whispering into her ears yace "I will get it here....."

Mayraah is 500 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence via 07087865788

124
Few months later....


Maheer ya karasa rufe akwatin gabansa ya juya yana kallon Mayraah da shigowarta dakin kenan, tana kallonsa tace "Honey hope baka manta min komai ba dai?" Yace "Yes, your royal highness" Er dariya tayi ta karasa kusa da shi tayi kissing lips dinsa tace "Thanks my Man" handbag dinta ta dauka da gyalenta shi dai bin ta da kallo kawai yake, tace "In zaka ci abinci kawai dauka zaka yi a deep freezer kayi microwaving, i cooked variety for you" A hankali yace "Thanks Pumpkin" Daukan box dinta yayi ya nufi kofa ta bi bayansa suka fita daga dakin, ita ta kulle gidan bayan ta kashe duk Electrical appliances din gidan, sannan ta nufi parking space inda yake jiranta, bude front seat tayi ta shiga ta ajiye masa makullin gidan tana kallonsa, kwantar da murya tayi tace "Haba My Man, why are you moody, kwana uku fa kawai zan yi, ran sunday ai zan dawo in sha Allah" A hankali yace "The 3 days will look like 3 years to me..." murmushi tayi ta ɗan matsa kusa da shi tace "Toh na rage kwana daya, just 2 days kawai zan yi, sai in dawo ranan Saturday, is that okay Honey?" Ya sauke ajiyar zuciya, sai da ya kalli ta madubi making sure mai gadin gidan baya kallon direction dinsu sannan ya jawota kusa da shi, French kiss yayi mata na few seconds sannan ya tada motar suka bar compound din, all through the journey zuwa gidan Abba Maheer na sauraronta tana basa labarin movie da ta kalla jiya da daddare bayan yayi Bacci, a haka har suka iso gida yayi parking a kofar gida tana kallonsa tace "Zaka shiga ciki ne?" Ya jinginar da kansa da kujeran motar yace "Kawai ki duba if she is ready sai ku fito, kar ku yi missing train din....." Mayraah tace "Ohk dear" Bude motar tayi ya bi ta da kallo har ta shiga compound din, sam bai son Mayraah na nisa da shi, tafiyan nan da zata yi kaduna ji yake kamar zai yi zazzaɓi, Mayraah is now part and parcel of his life, baya jin zai yi rayuwa in babu ita, he just can't understand or explain wani irin so ma yake mata, sai bayan kusan minti sha biyar Mayraah ta fito tare da Ammi, Bilkisu na biye da su tana rike da karamin akwatin Ammi ta sa booth bayan Maheer ya bude, back seat Mayraah ta bude ma Ammi, sai da ta shiga sannan ta bude front seat ta shiga ita ma, Maheer ya gaida Ammi ba tare da ya bari sun hada ido ba, Ammi ta amsa tace "Ya aiki?" Yace "Alhamdulillah" kunyan hada ido yake da ita don yau kusan sati kenan rabonsa da zuwa gidan sai dai ya kirata a waya ya gaisheta, tada motar yayi suka bar layin ya dau hanyar train station. Suna isa ya kalli Mayraah yace "Kafin Jirgin ya tashi sai ki kira barrister ki gaya masa za ku taso" Mayraah tace "Toh" Mayraah na ganin Ammi ta sauka daga motar, tayi masa wani romantic touch that made him go stiff, da sauri ta bude motar ta sauka tana murmushi, ya sake baki yana kallonta... Karfe shidda na yamma Mayraah suka iso garin Kaduna, Usman na train station din shi ma bai jima da zuwa ba jirgin ya iso, bayan ya gaida Ammi ya sa masu boxes dinsu a booth, suka shiga motar ya dau hanyar cikin gari, Usman na kallon Ammi yace "Gidan Aunty Mariyan zan kai ku Ammi?" Ammi tace "Eh, ita sai ka karasa da ita can Malali" Yace "Ohk" Gidan Aunty Mariya ya fara sauke Ammi, sai da suka shiga ciki suka gaida Aunty Mariya sannan shi da Mayraah suka fito zai karasa da ita Malali, Mayraah ta kalli wayarsa da ya sa a caji jin yana ringing, Eeman ta gani a gaban screen din, ta daga kai ta kallesa, daga call din yayi ya kai kunne yace "Are you just seeing the call? I will call u back, i am driving" Daga haka ya katse wayar ya ajiye, ita dai Mayraah bata ce komai ba. Suna isa Malali bayan yayi parking kofar gidan Grandparent dinta tana kallonsa tace "Eeman din tana kaduna ne Yaya?" Usman yace "Yea they came to write Jamb" Mayraah tace "Oh, ok Allah ya bada sa'a" Yace "Ameen, yaushe za ku gama bikin ku koma Abuja" Mayraah tace "Gobe Friday ne daurin Aure, i think that same friday za ayi dinner, mu dai ranan Saturday za mu koma Abuja" Usman ya gyada kai yace "Ohk" Bude motar tayi ta sauka, shima ya sauko ya ciro mata box dinta a booth, ta amsa tayi masa godiya sannan ta shiga cikin gidan. Tun da Mayraah ta shiga part din Grandma dinta bata yarda ta sake fitowa ba don gidan cike yake da jama'a yan biki, kasancewar Aunty Halima tun bayan da suka rabu da mai gidanta kusan shekara goma kenan yayi watsi da al'amarinta da na 'ya yanta, wanda gaba daya responsibility dinta da na yaranta uku ya koma kan Alhaji Saminu, amma duk da haka a kano gun mahaifin Farrah Alhaji Saminu yace za ayi daurin auren tunda can aka kai kudi ma, sai da bikin ya kusa ana ta shirye shirye dangin baban nata suka kara sati shidda haka kawai don nuna isa kuma aka bi su a hakan, taron biki ne kawai za ayi a gidan Alhaji Saminu, dalilin nan ne yasa gidan ke cike da yan uwa da abokan arziki tunda har da bikin cousin din Dad din Mayraah. Bayan magrib Hajiya Ramatu ta sa mai aiki ta kai ma Mayraah abinci a bangarenta, duk da baƙin dake cike gidan bata mance da jikar tata ba, Mayraah na kwance tana danna wayarta a parlor Hajiya Ramatu ta shigo tace "Har kin ci abincin Mayraah?" Mayraah ta mike zaune tana kallon warce suka shigo parlon tare da grandma din nata tace "Eh na ci" Hajiya Ramatu tace "To ga wata bakuwar mara son jama'a kamar ki, duk da ita ba lafiya ma gareta ba" Mayraah ta ɗan yi murmushi wanda iyakarsa lips, Hajiya Ramatu na kallon warce suka shigo tare tace "Sai kiyi zamanki a nan kin samu abokiyar hira" Ɗan murmushi Jiddah tayi ta zauna kan kujera bayan ta ajiye handbag dinta, tana kallon Mayraah tace "Sannu" Mayraah ta amsa mata, kana ganinta kasan tayi rashin lafiya wanda da alama bata ma gama recovering ba, cause she look so pale and lean, Hajiya Ramatu na kallonta tace "Kina iya cin abinci ko a kawo maki tea?" Jiddah ta girgiza mata kai tace "Zai kawo min abincin anjima" Hajiya Ramatu tace "Toh shikenan, ki yi kwanciyarki a nan" Daga haka Hajiya Ramatu ta fita daga parlon Mayraah dai danna wayarta kawai take, Jiddah na kallonta s hankali tace "Ya kwana biyu?" Mayraah ta ɗan mata murmushi tace "Alhamdulillah" Kwanciya Jiddah tayi kan kujera ta rufe ido, Mayraah dai ta ci gaba da danna wayarta, Bayan Isha aka bude kofar parlon ya shigo da sallama, Mayraah na jin muryarsa taki dago kanta daga chatting din da suke yi da Maheer ta WhatsApp, dama ba facing din kofar parlon take ba balle ya ganta farat daya, ya karaso cikin parlon direct ya nufi inda Jiddah ke kwance kan 3 seater, dukawa yayi gabanta yace "Princess are you comfortable ko kawai mu tafi gida?" Jiddah ta girgiza masa kai a hankali tace "I am fine" Yace "Sure?" Ta gyada masa kai, ledan hannunsa ya bude Jiddah na kallon Guava da Yalon dake cikin leda tace "Ka sa min a fridge yayi sanyi? Kar in je inyi amai" Yace "Ehh yayi sanyi, let me get a plate ki ci kafin ya huce" Mikewa yayi ya juya, sai a sannan ya ga Mayraah da har sannan bata dago kai ba tana danna waya, da mamaki yace "Mayraah" Ta ɗan kallesa tace "Good evening" Yace "How are you, ya mai gidanki?" Tace "Alhamdulillah" Dai dai nan wayarta ya fara ring ta daga ta mike ta shiga dakin kakarta... Washegari sai wajen karfe sha daya Ammi ta iso gidan ita da Aunty Mariya da Baaba yahanasu, Mama Ladi ce ta tarbesu ta kai su can wani bangare da ba jama'a sosai ta dinga jido masu duk abinda aka girka na biki, Ammi da Aunty Mariya mamaki yaki barinsu, Mama Ladi na fita Baaba yahanasu ta rike haɓa tace "Ikon Allah, kun ga wani kalan dangi irin na Ladi, wai ita ce me tarban baki, to duka duka yaushe ta zama er gidan bamu da labari" Ammi da Aunty Mariya dai basu ce komai ba, sai ga Hajiya Ramatu ta shigo tana masu sannu da zuwa da fara'a tace "Yanzu Hajiya Ladi ta sameni take ce mun kun zo" Ammi na murmushi tace "Ai kam dai, ya taro Hajiya?" Hajiya Ramatu tace "Alhamdulillah" Aunty Mariya da Baaba yahanasu suka mata Allah ya sanya alkhairi, ta amsa da fara'a tace "Bari in sa a kawo maku wainar shinkafa da miya, naga bata kawo maku ba" Tana fadin haka ta fita daga parlon, sai ga Mama Ladi da cooler cike da kaji ta ajiye masu tace "Wallahi duk wanda ma ya biya ma Mera kudin motar zuwa bikin nan ya cuci kansa yayi asaran kudin motarsa a banza a yanda kudi ke wahala yanzu, ni na taɓa jin kauyanci irin na Mera ma kuwa, sam bata da wayewa yanda ku ka san daga kauye ta zo bikin nan, ni ban ma san tana gidan nan ba sai dazu da safe ake gaya min, gidan nan fa cike yake da yan uwanta da sa'anninta mata har ma da wanda suka girmeta, ko wacce fa ta ci ado na kece raini ta caɓa kwaliyya a fuska tana sheki, amma Mera na can makale daki ko kayan kirki ina jin bata zo dashi ba gidan nan, wani ba sai yace dama lefen da Mashir din yayi mata na karya bane ayi zaton duk ya mayar kasuwa inda yayo renting su, to ni dai ba ruwana abun kunya da abun zagi kawai take ja mana a gidan nan ku ji in gaya maku, har sai da kakarta ta nuna min rashin jin dadin hakan, ni dai nafi tunanin don a kurnan asabe ta taso ne shi sa komai nata a kauyance ba gayu a lamarinta, kar fa ta sa Mashir ya fara hange hangen wasu matan a waje, bari dai inje in kira maki ita in ma daga nan tafiya za kuyi da ita to zai fi alkhairi gaskiya don nagaji da jin kunya, baku ji kunyan da ya lullubeni ba ganin shegen kayan jikinta yau" Daga haka ta fita daga parlon, ba a dau lokaci ba sai ga Mayraah ta shigo part din da su Ammi suke bayan Mama Ladi ta mata kwatance, Daga Ammi har Aunty Mariya kallon Mayraah suke, Yahanasu tayi kwafa tace "Sharri gun Ladi, wallahi shaidan ma jinjina ma Ladi yake akan iya sharri, kuma in ba ayi hankali ba sharri ne zai yi ajalinta, yanxu ina lefin kayan jikin Mera?" Ammi dai kallon tsadadddn lace din jikin Mayraah da mayafinta take wanda kudin lace din kadai yayi 160k, hatta dankunnen da ta saka na gold ne da tsarkansa kuma ba na lefenta ba don ko wata biyu ba ayi ba da Maheer ya siya mata, zoben hannunta ma gold din ne, shima kuma babu shi a lefe, Mayraah na murmushi ta karasa gun su Ammi ta zauna tana gaishesu, Aunty Mariya tace "Yaushe kika sa kayan nan Mimi?" Mayraah tace "Tun karfe bakwai na safe da nayi wanka" Yahanasu ta yi wani kwafan tace "Na fa ce maku tsabagen sharri ne irin na Ladi, mata ta zo gidan mutane tayi kalan dangi ko kunya bata ji, wannan ai mu zata dinga ja ma zagi wallahi" Ita dai Mayraah Murmushi kawai take don tun da garin Allah ya waye bata ga Mama Ladi ba tun ganin da ta mata da asuba, Ammi ta taɓe baki tace "Yi tafiyarki kinji Mimi, amma bana son wannan shegen zaman dakin da kike, ki tafi ki shiga cikin yan uwanki" Aunty Mariya tace "Haba Mimi sai kace ba wayayyiya ba, kema shiga cikinsu za ki yi ba wai ki makale a daki ba kamar kece amaryar" Mayraah dai tayi murmushi ta mike ta fita daga parlon, Yahanasu tace "Baiwar Allah, ni na zata ma zan ganta da juna biyu, to Allah dai ya kawo masu albarka" Aunty Mariya tace "Ameen" Bayan La'asar su Ammi suka bar gidan, karfe biyar da rabi kuma aka kawo amaryar Cousin din su Musharraf nan gidan don a ranan za ayi dinner, washegari a kai ta Abuja, ita kuma Farrah nan kaduna zasu zauna da mijinta.... Babu yanda Hajiya Ramatu bata yi da Mimi kan ta shirya aje dinner da ita ba amma sam taki wai kanta na ciwo, zuwa yanzu dai Hajiya Ramatu ta gama karantar Mayraah, ta gano kwata kwata bata son shiga jama'a ne, kyaleta kawai tayi ta fita zuwa gun wasu baƙi da tayi, bayan duk an tafi dinner gidan ya rage sai daidaiƙun mutane, Mayraah ta idar da sallan magrib ta dau plate din da ta ci abinci ta sauka downstairs da shi, masu aikin gidan su biyu ta gani a babban parlorn suna faman tsaftace ko ina na parlon, kallon yaran dake kwance kan 2 sitter suna wasa ta dinga yi, can ta karasa har inda suke tana kallonsu they are so cute and chubby, dariya suka fara mata, ta juya tana kallon daya daga mai aikin tace "Babies din waye wannan?" Mai aikin tace "Mamarsu tana kitchen zata dama masu abincin su, ina jin da ita aka kawo amarya daga kano" Dai dai nan Haseenah ta fito daga kitchen rike da bowl din Cereal da ta dama na yan biyunta, juyawa Mayraah tayi ta nufi sama bayan sun hada ido... Wajen karfe sha dayan dare suna waya da Maheer, a hankali tace "Toh train din babu na yamma ne?" Maheer yace "Sai Sunday Baby gal, don't worry in sha Allah zuwa 12 zan shigo Kd din sai in dauke ku" Shiru tayi, yayi kasa da murya yace "Amma wai me yasa baki son in zo in dauke ku wife?" Tace "Aa kawai dai bana son kayi stressing kanka ne, da ka bari zuwa Sunday din sai mu hau train kawai" Yace "No Baby gal, I've miss ur presence so much, ba wani stress before 12 in sha Allah zan shigo Kd din" A hankali tace "Allah ya kai mu" Washegari bayan azahar Ammi da Aunty Mariya da Maheer suka iso gidan Alhaji Saminu, tun karfe sha biyu Maheer ya iso Kaduna ya tafi gidan Aunty Mariya direct, Maheer bai yi niyyar shiga gidan Alhaji Saminu ba amma Ammi tace ya shiga yayi masu Allah ya sanya alkhairi, bai mata musu ba suka shiga gidan gaba daya, Mayraah dai na sama parlon kakarta duk da Maheer ya kirata ya sanar mata ya shigo kaduna, Har a sannan gidan Alhaji Saminu akwai baƙi sosai, ganin haka Aunty Halima tayi masu iso zuwa second parlor da babu kowa, Ammi ta zauna kan kujera tana kallon yan biyun da aka ma shimfida a kasan parlon su kadai suna kuka, ita ma Aunty Mariya kallon yaran take, haka ma Maheer da ya zauna kan kujera, Aunty Halima tace "Ko ina uwarsu ta shiga ta barsu a gantale a nan, ina jin daya daga wa enda suka kawo amaryar Bashir ne daga kano uwar tasu, bari in nemo ta" Aunty Mariya ta karasa ta dau daya daga yan biyu tana jijjiga sa. Ganin dayan ma na ta tsala ihu Maheer ya mike ya daukosa ya zauna kan 2 sitter, dai dai nan Haseenah ta shigo parlon rike da bowl din cerelac tare da wata budurwa dake biye da ita da ruwan gora, tana ganinsu Ammi ta sauke kanta kasa ta duka kan carpet ta gaishesu, amsawa Ammi da Aunty Mariya suka yi, Aunty Mariya tace "Bikin kika zo kema?" Haseenah ta girgiza kai tace "Aa, er kanwar mijin aunt dita muka kawo jiya, mijin nata ɗan gidan nan ne" Aunty Mariya tace "Ohk, bikin biyu ne dama, Allah ya sanya alkhairi" Mika mata Ayman Aunty Mariya tayi, Haseenah ta karbesa sannan ta kalli yarinyar dake bayanta tace "Firdausi amso Aryaan" Tana fadin haka ta mike tana kallon Maheer dake rike da Aryaan dake babbaka masa dariya kamar yasan ubansa ne ke rike da shi, shi ko sai kallon yaran yake, Firdausi ta amshesa daga hannun Maheer, Haseenah ta fita parlon Firdausi na biye da ita, Aunty Mariya tace "Ikon Allah yara sun girma sun yi wayo maa sha Allah" Ammi tace "Tun da na gansu na ganesu kawai dai nayi shiru ne" Shi kansa Maheer tun da ya kallesu sau daya yasan boys dinsa ne, Hajiya Ramatu ce ta shigo parlon, bayan sun gaisa, Maheer ya mata Allah ya sanya alkhairi, Ammi tace "To Hajiya mu za mu koma Abuja" Hajiya Ramatu tace "Au wai yau za ku koma, to mu je sama ku gaisa da yayata" Tare suka bar parlon zuwa upstairs, shi dai Maheer bai bar parlon ba yana zaune, su Ammi na fita da kusan minti goma sai ga Haseenah ta shigo parlon da yaran biyu, tana rike da daya, dayan kuma ta goyasa, zaunar da na hannunta tayi kusa da shi, na bayanta ma ta saukesa ta zaunar da shi kusa da ɗan uwansa, shi dai Maheer kallon kyawawan yaran kawai yake, ta zauna kan kujeran dake

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login