Showing 399001 words to 402000 words out of 452169 words
Chapter 134 - Mayrah Complete By Khaleesat Haydar
gate ta shigo min gidana" Yana fadin haka ya zaga ya bude driver seat ya shiga motar, Haseenah that was speechless har sannan ta sake baki tana kallon Maheer sai kuma ta kalli direction din entrance din shiga gidan don tabbatar da Mayraah bata wajen tana kallon abinda ke faruwa, da sauri ta juya kamar munafuka ta nufi gate ganin Mayraah bata bakin kofar, fita tayi daga gidan ta tsaya a kofar gida tana jiran fitowar motar Maheer, yana fitowa ta marairaice tace "Ban gane kar in shiga motar ka ba Maheer, yara na ne fa cikin motar and they need me the most a halin nan da suke ciki, kamata yayi ka bani listening ears kaji dalilina na zuwa nan kafin...." Tuni Maheer yayi zoom off ya bar ta tsaye wajen ta bi motarsa da kallo baki bude, she was soo shock bata taɓa tunanin zai yi haka ba, to ina za shi kuma da yaranta? Da sauri ta bi bayan motar da har yayi corner. Ammi ta mike da sauri tana kallon Maheer da ya shigo parlonta da yara tace "Maheer daga ina haka da yara cikin ruwan nan? Where did u get them from" Bata jira amsar sa ba ta nufesa da sauri ta amshi Aymaan daga hannunsa, Mama Ladi da ta saki baki tace "An shiga uku, meye haka kuma yara a jike jagab, a ina ka samo su ni Ladi?" Tuni Ammi ta tafi dakinta da Aymaan don parlon ma akwai sanyi, Mama Ladi ta amshi Aryaan tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, garin yaya ruwa ya ma yaran duka haka" Dakin Ammi ta shiga da shi shima, Maheer ya zauna kan kujera ya tallabi chin dinsa with different thought running his mind, babu bata lokaci Ammi da Mama Ladi suka cire ma yaran jikakkun kayan jikinsu, Dama da sabbin kayansu a gidan wanda surkar Dr Khalil ta kawo ma Ammi bayan an kai yaran Kano, Ammi ta shafesu da Rub sannan aka sa masu kayan, Tana rike da daya Mama Ladi na rike da daya, sosai jikin yaran yayi zafi hancinsu har ya toshe, sai bin su Ammi suke da ido ba kuzari tattare da su, Mama Ladi ta fashe da kuka tace "To ko dai hauka Mashir din ya fara ne da zai taho da su cikin ruwa? Babba ma ya ya kare da dukan ruwan sama balle yan yaran nan da basu da haƙƙin kowa a kansu, a gidan uban wa ma ya samo su ma dai tukun, ba suna gun uwarsu ba a kano?" Kwantar da Aymaan dake tari Ammi tayi ta lullubesa sannan ta mike ta fita daga dakin ta dawo parlor tana kallon Maheer tace "Me yake faruwa ne Maheer? A ina ka samo yaran nan haka?" Sai ga Mama Ladi ta fito ita ma bayan ta kwantar da Aryaan, Maheer ya daga kai ya kalli Ammi, sai kuma ya dauke idonsa, a takaice ya gaya masu abinda ya faru tun daga jiya da Haseenah ta shigo Abuja da su, amma yayi excluding part din abinda Mayraah tayi masa bai gaya masu ba, Mama Ladi ta saki salati tace "Allah ya tsine ma Hasinu albarka, wallahi so kawai take ta kashe yaran ta bar mu da bakin ciki don taga sun shiga ranmu, banda haka tun da garin Allah ya waye ake tsuga ruwa a Abuja balle tace ta fito da su ne ruwan ya tsuge da su a hanya, da gangan ta shiga da su cikin ruwan don ta musguna mana, kuma ma ya aka yi tasan gidanka tukun?" Maheer ya sauke ajiyar zuciya yace "Ban sani ba wallahi" Mama Ladi tace "Toh amma kai da ta kai su can din ba sai ka amshe yaranka ka shiga da su ciki ba Mera ta basu agajin gaggawa tunda ita ma Nas ce amma saboda rashin lissafi irin naka ka sake shigowa cikin ruwa da su ka kawo mana su nan? Ni kaina da ruwa ya dokeni dazu zazzabi nake yanzu haka balle en jariran nan, jikinsu na can yayi zafi ƙau sai tari suke, anya Hasinu zata gama da duniya lafiya kuwa? To kuwa ita da su har abadan abidina, cikin sauki ta dawo mana da su sai kuma ta kama gabanta, Allah ya isa tsakanin mu da ita kawai" Ammi dai gaba daya ta rasa abun cewa tayi shiru tana tsaye bakin kofar dakinta, Mama Ladi tace "Baka ga ta zama ba, sai ka sake fita cikin ruwan ka nemo masu maganin mura da na zazzaɓi, don wllhi ba ruwan wasa ne ya jibgesu ba hatta pampas dinsu a jike yake, Ammi dai ta mulke masu jiki da man zafi" Dai dai nan aka bude kofar parlon Haseenah ta shigo a jike, rabewa tayi jikin kofa ta tsaya kamar munafuka ruwa na diga a jikinta, Mama Ladi ta gwalo ido tace "Kun ga matsiyaciya, to uwarki kika biyosa nan kiyi? Maza fita kar in saka masu gadi su daga min ke sama su yi waje dake er iska, ko ba ke kika haifi yaran na ba baza ki shiga ruwa da su ba balle ke kika haifesu, ban taɓa ganin azzalumar uwa ba sai a kanki tunda uwata ta haifeni" Haseenah ta marairaice tace "Mama wallahi da gangan dai bazan shiga ruwa da yarana ba, ina ta kiransa baya dagawa kuma duk yaran basu da lafiya shine dalilin da yasa na taho da su inda yake..." Maheer da temper dinsa ke rising ya dinga kallonta trying to control himself, Juyawa Ammi tayi ta shiga bedroom dinta, Mama Ladi ta nufi kofa cikin daga murya tana cewa "Fita er iska, uban wa zaki ma bayani kamar an tambayeki, in sha Allahu ke da yaran nan har duniya ta nade makira kawai, fita kar in kira masu gadi su yi waje da ke, " Haseenah sai matsar kwalla take tana kallon Mama Ladi, Mikewa Maheer yayi da sauri jin Ammi na kwalo masa kira ya nufi dakin, Mama Ladi ta gwalo ido ita ma ta juya da gudu ta bi bayansa, sosai gaban Haseenah ya fadi don daga jin yanda Ammi ta kwalo ma Maheer kira ba lafiya ba, bata san sanda ta nufi dakin da gudu ba ita ma, zaro ido tayi ta dafe kirjinta ganin Aymaan in a convulsive state Maheer na rike da shi trying to give him first aid, wani ihu ta kwala ta shige dakin da gudu a gigice ta daura hannu a ka ta durkusa gabansu tace "Nashiga uku na lalace, don girman Allah Maheer ka rufa min asiri nothing should go wrong with my son" Babu wanda ya lura da ita a wajen don duk hankalin Ammi da Mama Ladi yayi mugun tashi, Mama Ladi sai zaga dakin take tana rafka uban salati, bayan some minutes yaron ya dawo dai dai amma sai tari yake kamar yanda Aryaan dake hannun Ammi ke tarin shi ma, sai a sannan hankalin Mama Ladi ya dawo kan Haseenah dake durkushe kusa da Maheer duk jikinta na rawa, buda baki tayi tace "Uban wa ya shigo mana da ita kuma, yaushe ta shigo mana nan...." Da sauri Mama Ladi ta fizgo zanin Ammi dake kan gado ta dinga shauda ma Haseenah iya karfinta tana cewa "Shegiya tashi ki fita, uban wa ya shigo da ke, fita er iska kawai" Haseenah ta mike tana matsar kwalla ta nufi kofa ta fita daga dakin tana waigen Aymaan, Ammi da har sannan hankalinta a tashe yake tace "Maheer ko dai mu tafi asibiti ne?" A hankali Maheer yace "Zan fita in siyo masu magani yanzu, ko mun je maganin dai za a basu" Mikewa yayi don ana kiran magrib ya nufi kofa ya fita daga dakin, Haseenah dake tsaye parlon sai hawaye take ta nufesa da sauri ta durkusa gabansa tace "Pls Maheer kar komai ya samu yarana plss" Ko kallonta Maheer bai yi ba ya fice daga parlon yana kokarin controlling temper dinsa... Babu bata lokaci Maheer ya dawo gidan bayan ya je pharmacy ya siyo masu magunguna, har a sannan Haseenah na durkushe parlon Ammi idonta har ya kumbura saboda kuka, tana ganinsa muryarta na rawa tace "Don Allah Maheer ku bar ni in kasance kusa da yarana basu da lafiya, let them feel my warmth plss" Maheer bai ko kalleta ba ya karasa cikin dakin, Ammi na sallah, haka ma Mama Ladi, ya ajiye ledan maganin hannunsa da Cerelac da madara da ya siyo masu ya nufi yaran yana kallonsu... Ammi na idar da sallah ta juya tana kallon Maheer, durkushe ta gansa bakin gadon kan kneels dinsa ya rungume Aymaan jikinsa ya runtse ido, mikewa Ammi tayi dai dai lokacin da Mama Ladi ta idar da sallahn ita ma, Ammi ta nufi Maheer da ya bude idonsa da ya kada sosai, kasa karasawa Ammi tayi kusa da shi, a hankali ya zauna kan carpet har sannan yana rungume da yaran yana kallon Ammi, da kyar Ammi ta iya cewa "Ka basa maganin ne?" Ya girgiza mata kai cikin karfin hali yace "Ya rasu" karaf a kunnen Mama Ladi da ta jefar da darduman hannunta ta kwala wani ihu tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, ya rasu fa kace Mashir?" A gigice Haseenah ta shigo dakin jin Mama Ladi na furta rasuwa, daura hannu tayi a ka ta kwala wani uban ihu jikinta na rawa ta nufi Maheer da gudu ta durkusa gabansa tana kokarin amsan Aymaan dake hannunsa, turata yayi daga kusa da shi yana kallonta da idanuwansa da suka yi ja, A hankali Ammi ta zauna gefen gado hawaye na sauka idonta tana kallon Aymaan dake jikin Maheer ya rungumesa har sannan. Duk da kukan da Mama Ladi ke rusawa hakan bai hanata yi ma Haseenah koran kare daga dakin Ammi ba don Charger wayar Ammi ta dauka ta dinga tsula mata tana cewa "Fita ki bamu waje kin kashe daya hankalinki ya kwanta" Haseenah dawowa tayi kamar warce aka kwance ma nut daya a kai ko jin dukan da Mama Ladi ke mata bata yi, Bilkisu ta shigo dakin a gigice jin ihun Haseenah da muryar Mama Ladi dake rusa kuka, Mama Ladi na ganin Bilkisu tace "Ja ta ki yi mana waje da ita Balkisu ta kashe mana yaro daya saura daya, ja ta ku fita ta bamu waje mu yi kukan mu cikin nutsuwa...." A haka Bilkisu ta kama Haseenah da ta dawo kamar mahaukaciya ta fitar da ita daga dakin, Ammi na kallon Maheer da kansa ke a kasa, hawaye na zuba idonta a hankali tace "Kayi hakuri, Allah ya sa me ceto ne, Allah ya raya mana ɗan uwansa" Shi dai Maheer bai dago kansa ba har sannan gawar Aymaan na rungume jikinsa, Ammi ta dauko Aryaan ta rungumesa tana bude ledan magungunan da Maheer ya shigo da shi zata basa, Usman ne ya shigo dakin da sauri ya nufi gun Maheer, Mama Ladi ta kara rushewa da kuka tace "Mun rasa daya daga yan biyun Usuman, ta kashe mana daya sauranmu daya, ba don ba don ba sai ince kai da Mamuda ne ku ka ja mana" Usman ya duka gaban Maheer yana kallon yaron hannunsa, shi dai Maheer bai dago kansa ba....
Wajen karfe goma Ammi na parlonta ta goya Aryaan, Abba bai dade da barin parlon ba ya koma bangaren sa, Mama Ladi dai na zaune kan carpet ta rafka uban tagumi sai gyangyadi take zubawa, hankalinta bai kwanta ba sai da ta tabbatar Usman ya kori Haseenah daga gidan, da kanta kuma ta jaddada ma masu gadi kar su bari ta shigo gidan, hakan yasa Haseenah ta makale a gate din gidan tana kuka kamar ranta zai fita, Maheer na zaune kan kujera ya jinginar da kansa da kujeran, Usman dake ta tsaye parlon ya juya kawai ya fita, Ammi ta juya ta kalli Maheer a hankali tace "Maheer ka tashi ka tafi gida dare yayi ga Mayraah ita kadai a gidan" Mama Ladi ta daga kai ta kalli Ammi da sauri tace "Ya tafi wani gidan? ba gwara ya tsaya ya sa ma dayan da ya rage mana ido ba, kina gani shi ma sai da yayi tafiyar ruwan nan a hannun Mamuda dazu" Ammi na kallon Mama Ladi tace "Naga jikin nasa ba zafi yanzu, kuma ai har abinci ya sha, gashi kuma yana bacci" Mama Ladi tace "Duk da haka ni dai ba ruwana, kamata yayi yaje gidan ya dauko Meran su dawo nan tare mu yi zaman makokin mu cikin kwanciyar hankali" Mama Ladi ta kalli Maheer tace "Ka gaya mata rasuwan ma kuwa?" Maheer ya girgiza mata kai, Mama Ladi tace "Gwara haka, kar ka gaya mata ka daga mata hankali ita daya a gida, ke kuma Ammi da kike cewa an bar ta ita kadai a gida in yana da aikin dare a asibiti ba ita kadai take kwana gidan ba dama" Ammi bata sake cewa komai ba, Mikewa Maheer yayi ya nufi kofa ya fita daga parlon Ammi ta bi sa da kallo cike da tausayinsa, Maheer na shiga dakinsa ya dau wayarsa yayi dialing number Mayraah, har ya katse bata daga ba, ya ajiye wayar a hankali gefensa ya jingina da pillow, yana ta zaune a haka wajen karfe sha daya Ammi ta shigo dakin, har sannan Aryaan na goye a bayanta, tana kallonsa tace "Maheer baka samu ka ci abinci ba fa, bari in kawo maka shayi" Tana fadin haka ta fita daga dakin ta tafi kitchen ta hado masa shayi ta kawo masa, ya amsa yana kallonta yace "Nagode" Ammi ta zauna edge din gadon, shayin ya fara sha, Ammi na kallonsa tayi kasa da murya tace "Duk hakuri za mu yi Maheer, haka Allah ya kaddara mana sai dai muce Alhamdulillah ala kulli haal, haka Allah ya tsara shi ba me tsawon kwana bane, Allah ya sa me ceto ne" Maheer ya daga kai ya kalleta yace "Haka ne, Ameen ya Allah..." Ammi tace "Amma kar ka gaya ma Mayraah, ka bari sai da safe" Ya gyada ma Ammi kai yace "In sha Allah" Ammi na ta zaune dakin bayan kusan minti ashirin ta mike ta nufi kofa ta fita, throughout half of the night Maheer yaje sama parlon Ammi to check on Aryaan yafi sau biyar haka ma Abba da Usman, duk in Maheer ya shiga parlon zai tadda Ammi idonta biyu tana goye da yaron a bayanta, Mama Ladi kuma tayi shimfida a kasa da carbi a hannunta tana ta bacci, da taji an bude kofa sai ta bude ido da sauri tana jan carbin hannunta, wajen karfe uku da rabi Maheer ya shigo dakin yaga Ammi na kokarin goya Aryaan bayan ta bashi madara sannan ta basa paracetamol don jikinsa yayi zafi sosai, Ya karasa kusa da Ammi yace "Ammi ko zaki kawo sa kema ki kwanta ki huta, you need to rest too" Mama Ladi da ta mike zaune bayan Maheer ya shigo parlon tana jan carbin hannunta tace "Tun tuni nake son in amshesa ta huta amma sai ya fara kuka, yafi gane ma bayan ne..." Ammi ta gama goya Aryaan tace "Ka bari kawai, Ya fi son goyon ne" Maheer dai bai ce komai ba yana kallon Ammi, Mama Ladi tace "Kai ma ka samu kaje ka kwanta Mashir" Juyawa Maheer yayi ya fita daga parlon.... Wajen karfe hudu da rabi Maheer ya dawo parlon Ammi, Ammi na zaune da yaron a bayanta tana bacci a haka, Mama Ladi kuwa har da guntun minsharinta ga carbinta ya fadi daga hannunta, Maheer ya karasa kusa da Ammi ya kirata a hankali, Bude ido tayi da sauri, ya kwantar da murya yace "Ammi ki bani shi plss ki huta haka" Ammi tace "Alwala ma nake son inyi...." Kwance yaron tayi daga bayanta ta dawo da shi kafarta, Maheer ya dinga kallon yaron kamar yanda Ammi ma ke kallonsa, sai kuma ta daga kai da sauri ta kalli Maheer, daukan yaron yayi daga kafarta ya sauka kasan carpet yana kallonsa, da kyar Ammi tace "Ko za a kara basa maganin muran don dazu paracetamol kawai na basa" Maheer bai dago kansa ba bai kuma ce ma Ammi komai ba, Ammi ta sauka kasan carpet din ita ma ta zauna tana kallonsa, sai a sannan ya daga kai yana kallonta da idanuwansa da suka sauya launi, da kyar ya iya bude baki yace "He is gone too" Ammi ta mike tsaye da sauri tana girgiza kai hawaye na sauka idonta tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Da sauri Mama Ladi ta bude ido ta mike zaune tace "Lafiya??" Hawaye na zuba idon Ammi ta kalli Mama Ladi tace "Shi ma ya rasu" Mama Ladi tayi wani ihu ta dau carbinta ta tashi da sauri ta fita daga parlon tana rusa kuka.....
Mayraah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
128
Yanda Haseenah taga rana haka ta ga dare a cikin flowers din kofar gidan Abba da ta rakube, tayi kuka har ta gode Allah, ga insect dake ta cizon ta a jiki, har a sannan ta kasa yarda wai yaronta daya ya mutu, ta yaya ma zai mutu yaran da ta taho Abuja da su hale and hearty, so full of life, bazai taɓa yiwuwa ba ace daya ya mutu, gani take kamar mafarki take kuma zata farka daga mugun mafarkin, a haka aka fara yayyafi wajen karfe hudun asuba, kawai abubuwan da suka faru a gidan Maheer ne ya dinga dawo mata daya bayan daya, har da yanda Mayraah ta hanasa shiga da su cikin gidan, ta fashe da matsanancin kuka zuciyarta na tafarfasa tace "Wallahi ita ta kashe min yarona, ita ce sanadi, ita ce silar mutuwarsa, don da mun shiga gidan duk haka bazai faru ba, dole in dau revenge din kashe min yaro da kika yi" Har aka kira sallan asuba tunaninta na kan abinda zata ma Mayraah as revenge, ta zo Abuja da mission iri iri amma ko daya bata yi achieving ba sai ma mutuwa da ɗan ta daya yayi, ji tayi gaba daya zuciyarta ya kekashe, har ranta taji zata iya yin