Showing 414001 words to 417000 words out of 452169 words
Chapter 139 - Mayrah Complete By Khaleesat Haydar
kauda kai da maida komai ba komai ba, Ammi tayi kuka har taji ba dadi don har sai da jininta ya hau sosai, sallamar da Hajiya Amina ta shigo har parlonta tayi mata na karshe har tana bata hakurin bazata samu zama ayi sadakan ukun yaran Maheer da ita ba ya kasa fita a ran Ammi, kuka wajen Mama Ladi ba a cewa komai kana ganinta kasan mutuwar ta girgizata don ko magana bata yi sai jan carbi da bin kowa da ido, Mayraah na kusa da Aunty Mariya ita ma ta kasa daina kuka, Aunty Mariya da hawaye ke sauka idonta sai addu'a take ma Hajiya Amina da yi mata fatan Allah ya sa ta yafi a sa'a, halinta na gari ya bi ta, Ba a gaya ma twins din Hajiya Amina rasuwar mahaifiyarsu ba sai kawo su Abuja kawai dangin babansu suka yi kamar yanda Abba yace.... Ranan da aka yi sadakan ukun Hajiya Amina ranan dangin mahaifinsu Eeman suka bar gidan Abba suka koma katsina leaving the twins behind, still a ranan Yahanasu da Hajja ma duk suka koma Kaduna tare da Grandma din Mayraah da Aunty Halima da suka zo Abujan a ranan don yin ta'aziyya, da yammacin ranan Ammi na zaune parlon ta daga gefenta Ihsaan ce kwance Maheer na kokarin mayar mata cannula dayan hannunta bayan ya cire daga hannun da ya fara sa mata saboda kumbura da hannun yayi, tun bayan da aka kawosu Abuja suka ji rasuwan mahaifiyarsu duk suke kwance critically ill, sosai yan biyun suka zama abun tausayi sun kasa absorbing uwarsu ta tafi ta bar su, gwara ma Ihsaan tana da dauriya sai dai ka kamata cikin dare tana kuka, amma Eeman abun ba a cewa komai, don haka Ammi ta ba Abba shawaran ya biya masu Umrah su je kilan Allah ya sa masu dangana da rest of mind, haka kuwa aka yi Abba ya fara processing na biya ma yan biyun da Ammi da Mayraah zuwa Saudi, Ammi na kallon Maheer a hankali tace "Ko zaka bari ta huta zuwa anjima ka sa mata" Maheer ya koma ya zauna, kwanciya Ihsaan tayi a gefen Ammi, sosai Maheer yake jin tausayin yan biyun har cikin ransa, daukar wayarsa yayi jin yana ring yana dubawa yaga MD ne ke kiransa ya mike ya fita daga parlon, Mayraah dai kallon Ihsaan kawai take, by mere looking at the teenagers sai zuciyarka ya karaya har ka zubar masu da hawaye, they are too young for the trauma, especially Eeman da ta fi shiga wani hali na rashin uwarta, it might take forever basu yi healing daga trauma din rashin uwarsu ba, Ammi na kallon Mayraah tace "Eeman tana gun Mama Ladin ne?" Mayraah tace "Eh, suna can parlorn kasa" Mikewa Ammi tayi ta fita daga parlon nata ta sauka kasa, Usman ne zaune parlon trying to comfort Eemaan that is crying silently a jikinsa, tsabar kuka ba dare ba rana duk idanuwanta sun kumbura, ya dora kanta saman shoulder dinsa yana mata magana a hankali yana patting bayanta, ita dai kai kawai take gyada masa hawaye na sauka idonta, duk bai lura da Ammi da ta sauko kasa ba, ya debi abincin dake gefensa wanda Mama Ladi ta zubo mata taki ci, ya kai mata spoon din baki, a hankali ta bude bakin ta amshi abincin, sai ga Mama Ladi ta fito daga kitchen da Custard din da ta dama mata a cup tace "In ma bazata ci shinkafar ba ga kwasta nan na dama mata shi ruwa ruwa, sai da na saka mata a firiji ya dan huce yanda zata ji dadin hadiyewa ba zafi" Daga kai Usman yayi yana kallon Mama Ladi, Mama Ladi ta karasa ta mika masa Custard din ya amsa....
132
Few week later....
Usman na tsaye jikin motarsa ya hango su sun fito daga cikin airport din da wani porter dake dauke da luggages dinsu a kan trolley, suna karasowa Usman ya bude booth dinsa for the porter to assemble the boxes, sannan ya zagayo yayi ma Ammi sannu da hanya yana murmushi, Ammi ta amsa tace "Mun same ku lafiya" Yace "Alhamdulillah" Eeman da Ihsaan suka gaishesa a tare ya amsa yace "How was the flight?" Suka ce "Alhamdulillah" Kallon Mayraah yayi, a hankali tace "Ina yini yaya" Yace "Welcome back Mimi, naji sai kamshin Saudi Arabia ku ke gaba daya" Murmushi Mayraah tayi bata ce komai ba don tun da suka fito haraban airport din mood dinta ya ɗan canza, she was expecting to see Maheer too amma sai bata gansa ba, Usman ya bude ma Ammi back seat ta shiga sannan su Ihsaan suka shiga bayan motar su ma, Mayraah ta bude front seat ta shiga, the journey back home was so silent sai karatun qur'ani dake tashi on a low volume a motar, lkci lkci Usman ke kallon Eeman da ta daura kanta a shoulder din Ammi idonta a kasa, ita dai Ihsaan ta jinginar da kanta jikin motar, a haka suka isa gida, bayan Usman yayi parking a space din parking ya bude motar ya sauka sannan su ma duk suka sauka, Usman ya sauko da duk boxes dinsu mai gadi ya karaso da sauri don karasa masu da box din entrance din shiga gidan, Mayraah zata dau box daya Usman yace "Don't worry Mimi, ku shiga ciki za a taho da su" Tuni Ammi ta nufi entrance din shiga gidan tare da su Ihsaan, Bilkisu har tayi girki tana jiran isowarsu, da fara'a ta tarbe su ta dinga kai masu akwatunan da masu gadi ke ajiyewa a bakin kofa zuwa sama parlon Ammi.... Ihsaan na tsaye parlon Ammi rike da handbag din da Eeman ta dawo da shi daga Saudi tana ciro mata duk abubuwanta dake ciki tana ajiyewa kan kujera, Mayraah dai kallonta kawai take, can tayi murmushi tana girgiza kai, Eeman ta ɗan ja tsaki ta duka gaban akwatinta ta bude, few abubuwan Ihsaan dake ciki ta dinga fiddowa tana ajiyesu kasan carpet, Mayraah dai bata ce masu komai ba don zuwa yanzu ta gaji da settling dispute, Ammi ce ta shigo parlon daga bangaren Abba don yana gidan, tana kallonsu tace "Ku je ku gaida Abbanku yana parlon sa" Mikewa Mayraah tayi twins din suka tashi su ma suka bi bayanta, Ammi ta bi su da kallo har suka fita, sosai take jin tausayin yaran nan har ranta, and she is trying all her possible best na ganin they don't lack motherly love. Bayan Isha Mayraah na parlon Ammi tana cin abinci, su Ihsaan na zaune kusa da Ammi dake seperating tsarabar kowa daga akwatin dake gabanta, a yan satittukan da suka yi a Saudiyya Mayraah ta lura jansu jiki da Ammi ke yi ya sa sun ɗan fara sakin jiki damuwarsu kuma ya ragu a kan yanda suka baro Nigeria duk da haka wani lkcn zaka gansu suna kuka barin Eeman, Bude kofar parlon aka yi Maheer ya shigo da sallama, Ammi ta amsa tana ci gaba da abinda take, tun da Mayraah ta kallesa sau daya ta dauke kai, har ya karaso cikin parlon idonsa na kanta, ya zauna kasan carpet ya gaida Ammi ta amsa, Su Ihsaan ma duk suka gaishesa ya amsa da murmushi yace "How was the trip?" Duk suka ce "Alhamdulillah" Kallon Mayraah yayi, without looking at him tace "Ina yini" Yace "Lafiya lau, ya gajiya" tace "Alhamdulillah" After a while Ammi ta kalli Mayraah tace "In za ku tafi gida ga tsarabanki nan Mimi" a hankali Mayraah tace "Ammi sai gobe" ɗaga kai Maheer yayi ya kalleta, Ammi dai bata kalleta ba tana ci gaba da abinda take, bayan few seconds tace "Haka yace maki" Shi dai Maheer kallon Mayraah yake, Mayraah tace "Ehh sai gobe" Ammi bata sake cewa komai ba, Usman ya shigo parlon da sallama Ammi na kallonsa tace "Ka ci abincin?" Usman ya zauna kan kujera yana kallonsu Ihsaan yace "Na ci" Mikewa Mayraah tayi ta fita daga parlon da plate din da ta ci abinci, tana fita ko 3 minutes ba ayi ba Maheer ya mike kansa a kasa ya fita daga parlon, downstairs ya sauka ya nufi kitchen yana shiga ciki ya ganta tana dafa ruwan shayi, karasawa yayi, yayi hugging dinta ta baya yace "Did you know how much i miss you wife" Kashe gas din tayi da sauri tace "Yaya idan wani ya shigo fa, don Allah ka sakeni" juyo da ita yayi yana kallon kwayar idonta a hankali yace "Billah i miss u so much wife, baki ga har ramewa nayi ba" Ɗan murmushi tayi ta kwantar da kanta kirjinsa ta lumshe ido murya can kasa tace "I miss you more yayana" Ya dago kanta yace "Really?" Hade rai tayi tace "Amma shine baka zo daukan mu a airport ba?" Yayi murmushi yace "Ina hospital then, baby gal, amma kiyi hakuri" Ta juya masa ido tace "Toh na hakura" Yace "Mu tafi gida?" Tace "Ai na riga nace ma Ammi sai gobe" yace "Toh meye a ciki in kin canza mind dinki?" Bai jira cewarta ba ya kama hannunta tana zaro ido ya fita da ita daga kitchen din suka haura sama, kwace hannunta tayi ganin ya nufi bangaren Ammi da ita, ya juya yana kallonta yace "Oh baza ki mata sallama ba" Ta marairaice tace "Ni dai plss ka bari gobe yaya, na riga fa nace mata sai gobe" Bai tsaya ya ci gaba da sauraronta ba ya tafi parlon Ammi yayi masu sallama sannan ya fito, duk magiyan da Mayraah ke masa ya bari gobe bai saurareta ba, haka nan ta sa Hijab dinta ya kama hannunta suka fita daga dakin, tun ma basu bar gidan ba ta fara jin kunya, a haka suka fita kofar gida ya bude mata front seat ta hade rai ta shiga ya kulle sannan ya zaga ya bude driver seat ya shiga. Wajen karfe goma Ammi na zaune parlon Abba tana kallonsa a hankali tace "Yanzu goben za su tafi katsinan kenan?" Abba da idonsa ke kan Tv yace "In sha Allahu" Shiru Ammi tayi, bayan few seconds tayi kasa da murya tace "Kana ganin baza su bari mu rike su ba yallabai?" Abba ya girgiza kai calmly yace "Gaskiya da kamar wuya, a sanda ku ke Saudiyya Yayan baban nasu ya kirani yafi sau uku, so nace masa kuna sauka yau washegari za a kai masu su" Ammi bata san sanda hawaye ya cika idonta ba, har cikin ranta take tausayin marayun taji kuma tana son a bar mata rikonsu da hakan zai yiwu but basu da wani say akansu sai yanda dangin mahaifinsu da mahaifiyarsu suka yi, ta so ta rikesu ta yanda ko da za su yi kukan marairaici bai wuce in sun tuno mahaifiyarsu ba amma ba don sunyi lacking motherly love and care ba, shi dai Abba bai sake cewa komai ba har a sannan idonsa na kan TV, Ammi ta share hawayen da yaki tsayuwa a idonta cike da karfin hali tace "Toh karatunsu fa, they told me they just wrote jamb not long ago" A hankali Abba yace "Na masa maganar yace min kar in damu they will take care of that, kawai dai a kawo masu su katsinan" Ammi ta dinga kallon Abba, can tace "Kamar nisanta su da mu suke son su yi" Abba ya ɗan yi murmushi ya girgiza kai yace "Eh kusan haka, don gani suke za mu ce za mu rikesu" Ammi ta kasa cewa komai har sannan hawaye na zuba idonta, after a while tace "Bana son su yi kukan marairaici ne, ka dai san halina kasan abinda zan iya aikatawa da wanda bazan aikata ba, amma da zan rike yaran nan iyakan rikon da Marigayiya xata masu zan masu" Abba na kallon Ammi yayi murmushi yace "Ae ba sai kin fada ba Hajara i trust you, tunda kika reni Mayraah to ko wa ma za ki rike da amana" Ammi ta goge idonta tace "Kasan wani abu yallabai?" Abba ya kalleta yace "Sai kin fada" Tayi kasa da murya tace "Wallahil azeem tun a ranar da mahaifiyarsu ta zo gaisuwan yaran Maheer naji na janye kalaman da nayi na kan cewar Usman bazai auri er ta ba, why because mun yi magana ta fahimta da kai a ranan da ka kira Mama Ladi ta taho daga kaduna, nauyin baki kawai nayi ban sanar maka ko shi Usman din ba, na sha gaya ma Mariya ni bani da matsala da Hajiya Amina kuma ba abinda ya taba hadamu da ita hasali ma bata taɓa min komai ba, da kai ne nake da issue don ina ganin kamar bani da sauran wani value a wajenka tunda sai ka yanke decision dinka kake sanar min ko yayi min dadi ko kar ya min, wallahil azeem dalilin da yasa nayi reacting haka kenan a parlonka ranan gani nake kamar iyakata kake nuna min ka mayar da ni bora a gidanka, sai gashi daga baya mun yi magana ta fahimta da kai ana ranan da yan biyun Maheer za su rasu, nayi nauyin baki ban sanar da abinda ke raina ba har Hajiya Amina ta rasu, yanzu gani za ayi don naga bata da rai yasa na amince" Abba dake ta sauraronta ya sauke ajiyar zuciya yace "Allah ya sa mu dace, in mun je katsinan zan ma yayan Mahaifin nasu magana mu ji ya za su ce, don da kaina nake son in mika masu yaran, Usman zai mana booking flight zuwa kano, daga can kanon yayi driving dinmu zuwa katsina" A hankali Ammi tace "Allah ya kai mu" Washegari throughout haka Ammi ta yini babu walwala bayan Abba da Usman sun tafi kai su Eeman katsina, ta rasa dalilin da yasa take jinta cikin damuwa haka, sai taji da ma Mama Ladi na gidan ko ba komai zaka yi dariya ko baka yi niyya ba, wajen karfe hudu na yamma ta kira Maheer bayan sun gaisa tace "Kana gida ne Maheer?" Maheer yace "Aa ina wajen aiki" a hankali tace "Toh shikenan, na zata kana gida ne ince ka taho min da Mayraah" Maheer yace "Is everything alright Ammi?" Ammi tace "Lafiya lau, girki da nake son tayi min ne" Maheer yace "Toh bari in kirata tayi ordering bolt ya kawo ta" Ammi tace "Aa kar ka damu, zan sa Bilkisu tayi, sai anjima" Daga haka ta katse wayar... Bayan magrib Ammi na zaune kan darduma sai ga Mayraah ta shigo tare da Maheer dake biye da ita a baya, Ammi ta dinga kallonsu, Mayraah ta karasa ta ajiye food warmer din hannunta, Maheer ya ajiye warmer din miya dake hannunsa, Mayraah ta karasa gun Ammi ta zauna da murmushi tace "Ina yini Ammi" Ammi ta sauke ajiyar zuciya sosai taji ta samu relieve na damuwar da ya cunkushe mata a zuciya tace "Lafiya lau Mimi, yanzu sai da yasa kika yi girkin" Mayraah na murmushi tace "I cooked ur favorite" Zaunawa Maheer yayi ya gaida Ammi, Ammi ta amsa tace "Ya aiki?" Yace "Alhamdulillah" Mikewa Mayraah tayi ta sauka downstairs don dauko plate da spoon, Maheer na kallon Ammi a hankali yace "Ammi kamar kina da damuwa" Ammi ta sauke idonta jin hawaye ya kawo idonta, cike da karfin hali tace "Maheer baza ka gane yanda mutuwar baiwar Allahn nan ya tsaya min a rai ba, i am feeling guilt da bansan dalilinsa ba, bani da rest of mind kwata kwata" Maheer ya dawo kusa da ita ya zauna cikin kwantar da murya yace "Ammi addu'a kawai take bukata a garemu sai kuma kyautata ma marayun da ta bari, mu ma nan duk lokaci muke jira, sai dai Allah ya sa mu cika da imani" Hawaye na sauka idon Ammi tace "Ameen, but i am really disturbed, i never gave her a chance while she was alive, i am feeling guilty" Maheer ya sauke idonsa, Ammi na share idonta tace "Ina jin zan je wajen Hajja ko sati daya inyi, i need to rest" Maheer ya daga kai yana kallonta, can ya kwantar da murya yace "But Ammi ba yanzu ya kamata ki je ba, just yesterday ku ka dawo daga Saudiya, ki bari in an kwana biyu" Shiru Ammi tayi bata ce komai ba, Maheer yace "Ko Mimi ta dawo nan tayi 2 days so that she can keep u company" Ammi ta girgiza kai tace "Aa, ba komai ai Bilkisu tana nan Maheer" Maheer dai ya dinga kallonta, Ammi ta goge idonta tace "Dama Mama Ladi zata zo ne, ba komai yasa na kara jin kaina cikin damuwa ba sai tafiya da yan biyun nan, tausayinsu nake sosai i am just hoping dangin uban nasu baza su bari su yi kukan marairaici ba, they are too young for that" Mayraah ta shigo parlon da sallama ta tafi ta fara debar ma Ammi abincin da ta girka mata, Kawo abincin tayi ta ajiye ma Ammi a gabanta, Ammi tayi murmushi tace "Thanks daughter" Mayraah ta zauna gefen Maheer tana kallon Ammi, bude kofar parlon aka yi Usman ya shigo da sallama, Ammi ta daga kai da sauri tana kallonsa tace "Kun dawo Usman?" Ya karaso ya zauna a hankali ya gaisheta, Ammi ta amsa tace "Ya ku ka baro su Ihsaan din?" Usman ya sauke idonsa don har sannan he is still heartbroken at the way the twins were crying da za su baro su gidan yayan babansu, without looking at Ammi yace "Lafiya lau" Ammi tace "Abbanku ya shigo ne?" Usman yace "Ehh ya shigo" Mikewa Ammi tayi tana kallon Mayraah tace "Mimi rufe abincin barin inje in dawo" Daga haka ta fita daga parlonta, Mayraah ta juya ta gaida Usman ya amsa, tace "In zubo maka abincin yaya?" Yace "Sallah zan yi Mimi" Daga haka ya mike ya fita daga parlon, Ammi na isa parlon Abba bayan tayi masa sannu da dawowa Abba ya sanar mata yanda suka yi da dangin uban yan biyun Hajiya Amina, Ammi was speechless, can tace "Toh sai yaushe suke ganin za su isa auren?" Abba ya ɗan yi murmushi yace "Baza su bada