Mayrah

Chapter 140 of 152

rasu, yanzu gani za ayi don naga bata da rai yasa na amince" Abba dake ta sauraronta ya sauke ajiyar zuciya yace "Allah ya sa mu dace, in mun je katsinan zan ma yayan Mahaifin nasu magana mu ji ya za su ce, don da kaina nake son in mika masu yaran, Usman zai mana booking flight zuwa kano, daga can kanon yayi driving dinmu zuwa katsina" A hankali Ammi tace "Allah ya kai mu" Washegari throughout haka Ammi ta yini babu walwala bayan Abba da Usman sun tafi kai su Eeman katsina, ta rasa dalilin da yasa take jinta cikin damuwa haka, sai taji da ma Mama Ladi na gidan ko ba komai zaka yi dariya ko baka yi niyya ba, wajen karfe hudu na yamma ta kira Maheer bayan sun gaisa tace "Kana gida ne Maheer?" Maheer yace "Aa ina wajen aiki" a hankali tace "Toh shikenan, na zata kana gida ne ince ka taho min da Mayraah" Maheer yace "Is everything alright Ammi?" Ammi tace "Lafiya lau, girki da nake son tayi min ne" Maheer yace "Toh bari in kirata tayi ordering bolt ya kawo ta" Ammi tace "Aa kar ka damu, zan sa Bilkisu tayi, sai anjima" Daga haka ta katse wayar... Bayan magrib Ammi na zaune kan darduma sai ga Mayraah ta shigo tare da Maheer dake biye da ita a baya, Ammi ta dinga kallonsu, Mayraah ta karasa ta ajiye food warmer din hannunta, Maheer ya ajiye warmer din miya dake hannunsa, Mayraah ta karasa gun Ammi ta zauna da murmushi tace "Ina yini Ammi" Ammi ta sauke ajiyar zuciya sosai taji ta samu relieve na damuwar da ya cunkushe mata a zuciya tace "Lafiya lau Mimi, yanzu sai da yasa kika yi girkin" Mayraah na murmushi tace "I cooked ur favorite" Zaunawa Maheer yayi ya gaida Ammi, Ammi ta amsa tace "Ya aiki?" Yace "Alhamdulillah" Mikewa Mayraah tayi ta sauka downstairs don dauko plate da spoon, Maheer na kallon Ammi a hankali yace "Ammi kamar kina da damuwa" Ammi ta sauke idonta jin hawaye ya kawo idonta, cike da karfin hali tace "Maheer baza ka gane yanda mutuwar baiwar Allahn nan ya tsaya min a rai ba, i am feeling guilt da bansan dalilinsa ba, bani da rest of mind kwata kwata" Maheer ya dawo kusa da ita ya zauna cikin kwantar da murya yace "Ammi addu'a kawai take bukata a garemu sai kuma kyautata ma marayun da ta bari, mu ma nan duk lokaci muke jira, sai dai Allah ya sa mu cika da imani" Hawaye na sauka idon Ammi tace "Ameen, but i am really disturbed, i never gave her a chance while she was alive, i am feeling guilty" Maheer ya sauke idonsa, Ammi na share idonta tace "Ina jin zan je wajen Hajja ko sati daya inyi, i need to rest" Maheer ya daga kai yana kallonta, can ya kwantar da murya yace "But Ammi ba yanzu ya kamata ki je ba, just yesterday ku ka dawo daga Saudiya, ki bari in an kwana biyu" Shiru Ammi tayi bata ce komai ba, Maheer yace "Ko Mimi ta dawo nan tayi 2 days so that she can keep u company" Ammi ta girgiza kai tace "Aa, ba komai ai Bilkisu tana nan Maheer" Maheer dai ya dinga kallonta, Ammi ta goge idonta tace "Dama Mama Ladi zata zo ne, ba komai yasa na kara jin kaina cikin damuwa ba sai tafiya da yan biyun nan, tausayinsu nake sosai i am just hoping dangin uban nasu baza su bari su yi kukan marairaici ba, they are too young for that" Mayraah ta shigo parlon da sallama ta tafi ta fara debar ma Ammi abincin da ta girka mata, Kawo abincin tayi ta ajiye ma Ammi a gabanta, Ammi tayi murmushi tace "Thanks daughter" Mayraah ta zauna gefen Maheer tana kallon Ammi, bude kofar parlon aka yi Usman ya shigo da sallama, Ammi ta daga kai da sauri tana kallonsa tace "Kun dawo Usman?" Ya karaso ya zauna a hankali ya gaisheta, Ammi ta amsa tace "Ya ku ka baro su Ihsaan din?" Usman ya sauke idonsa don har sannan he is still heartbroken at the way the twins were crying da za su baro su gidan yayan babansu, without looking at Ammi yace "Lafiya lau" Ammi tace "Abbanku ya shigo ne?" Usman yace "Ehh ya shigo" Mikewa Ammi tayi tana kallon Mayraah tace "Mimi rufe abincin barin inje in dawo" Daga haka ta fita daga parlonta, Mayraah ta juya ta gaida Usman ya amsa, tace "In zubo maka abincin yaya?" Yace "Sallah zan yi Mimi" Daga haka ya mike ya fita daga parlon, Ammi na isa parlon Abba bayan tayi masa sannu da dawowa Abba ya sanar mata yanda suka yi da dangin uban yan biyun Hajiya Amina, Ammi was speechless, can tace "Toh sai yaushe suke ganin za su isa auren?" Abba ya ɗan yi murmushi yace "Baza su bada auren bane ba fa, from the look of things so suke in cire hannu a lamarin yaran gaba daya, they were emphasizing on abinda ya hada ya raba, ko makarantar da yake cewa zai nema masu ba haka bane, from my observation gadon da uwarsu ta bari suke hari, they were even asking me of her Atm cards" Ammi ta kasa rufe baki don mamaki tana kallon Abba, can tace "To yan uwanta fa?" Abba yace "Ita kadai ce ai, duk siblings dinta died of sickle cell, her parent are late, sai distance relatives" Ammi ta kasa cewa komai, after few seconds Abba yace "Yara dai nasu ne, we have no say akan su, kawai iyaka namu mu bi su da addu'a" Abba na kaiwa nan ya mike ya shiga bedroom dinsa. Ammi na zaune parlonta tare da Bilkisu dake ta mata hira Usman ya shigo parlon da sallama, mikewa Bilkisu tayi ta fita daga parlon, Usman ya zauna yana kallon Ammi, sai kuma yayi kasa da kai yace "Ammi dama za a zo gaishe ki ne gobe" Ammi dake kallonsa tace "Wa zai zo gaisheni kuma?" Usman ya daga kai yace "Sunan ta Maryam" Ammi ta kasa daina kallonsa, a hankali tace "Toh Allah ya kai mu" Yace "Ameen" Mikewa yayi, Ammi tace "Amma..." Usman ya tsaya yana kallonta, a hankali tace "Eeman din kuma fa Usman?" Usman ya ɗan yi murmushi yace "Aa, ai ba wannan zancen kuma Ammi, tunda kika nuna a'a tun a lkcn na bar maganar" Ammi ta girgiza kai tace "Aa Usman, baza ka bar maganar ba yanzu...." Zaunawa Usman yayi yace "Kiyi hakuri Ammi, na bar maganar nan tuntuni, Eeman da Ihsaan a matsayin wa nake garesu yanzu" Ammi was speechless, after a while Usman ya mike yace "Zan je in ci abinci" Da ido Ammi ta bi sa har ya fita daga parlon, Yana dakinsa Ammi ta bi sa, tana daga tsaye bakin kofa tace "Amma zan fita gobe Usman, sai dai wani lkcn ka kawota" Usman dake kallonta yace "To Allah ya kai mu"
Wajen karfe biyun dare Maheer ya farka bai ga Mayraah kusa da shi ba, mikewa zaune yayi after a while don at first yayi tunanin tana bandaki ne, ya sauka daga kan gadon ya fita, dakinta ya nufa yana bude kofar ya ganta zaune kan darduma ta hade kanta da gwiwa tana jin an bude kofa ta daga kai da sauri tana goge idonta, ya karasa kusa da ita yana mata kallon mamaki ya duka gabanta yace "Mimi" Bata yarda sun hada ido ba tace "Sallah nake ne" Cike da damuwa yace "Why are you crying Mimi? Did i offend you in anyway?" Daga kai tayi ta kallesa nan da nan hawaye ya cika idonta, sosai hankalinsa ya tashi ya dagota ya zaunar da ita gefen gado ya zauna gefenta cike da damuwa yace "Don Allah ki gaya min me ya faru wife?" Ta rufe fuskarta a shoulder dinsa tana shesshekan kuka, sosai ta rikita sa ya dinga lallashinta, da kyar ya samu ta daina kukan yana rungume da ita, bayan wani lkci yayi kasa da murya yace "Tell me what the problem is Mimi?" Ta lumshe idonta tana jin wani sabon kukan na taho mata, a hankali yace "Wife" Muryarta na rawa tace "I will write it down tomorrow" Shiru Maheer yayi, yana patting bayanta a hankali yace "Why not now wife?" Ta girgiza masa kai tace "I will tomorrow" Ɗagata yayi suka fita daga dakin nata ya koma nasa da ita, tana rungume jikinsa bacci ya ɗauketa, ya dinga shafa bayanta yana shakan daddadan kamshin da gashinta ke yi ya lumshe ido, a haka shima bacci ya daukesa.... Da asuba Maheer na dawowa masallaci yaga Mayraah bata dakinsa, ya dinga kallon takardan da ta ajiye masa kan gado, ya karasa ya dau takardan ya warware yana karanta content din, zaunawa yayi gefen gado bayan ya gama karanta abinda takardan ya kunsa, after few minutes ya sauke ajiyar zuciya ya mike ya linke takardan ya ajiye, yana tafiya slowly ya fita daga dakin nasa ya tafi nata, yana bude kofar ya ganta zaune kan darduma, ita dai bata daga kai ba har ya karasa inda take ya duka gabanta yana kallonta.

Mayraah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence via 07087865788

133
Mayraah ta bude mota ta sauka bayan Maheer yayi parking, ta juya tana kallonsa tace "Ko dai kawai ka bar shi Dear" Yace "No, let me get it in dawo yanzu, Flight din ai na karfe shidda ne so there is still time" Mayraah tace "Just an hour and a half fa" Yace "Don't worry, am not taking long wife" a hankali tace "Ohk dear, Allah ya tsare" Yace "Ameen my love" Gate ta nufa ta shiga gidan shi kuma yayi reverse, tun da ta bude kofar parlor ta shiga take kallon sa, yana daga kai tayi masa murmushi ta karasa cikin parlon ta zauna tace "Ina yini yaya?" Yace "Lafiya lau, how are you doing?" Tace "Alhamdulillah, ya su Mami?" Yace "They are fine, ina Maheer din?" Tace "Yaje ya dawo yanzu, yaushe ku ka zo yaya?" Yace "Not too long, ke mu ke jira ai" Mama Ladi ce ta sauko parlon daga sama, ta karaso tsakiyar parlon tana washe baki hannunta rike da ledan gyada me gishiri tace "Sannu da zuwa Mendi, yanzu Hajiya Ramatu ke ce min ai tare ku ka zo" ɗaga kai MD yayi yana kallonta, Mayraah dai ta sunkuyar da kanta tana murmushi, Mama Ladi ta zauna kujeran dake kallon wanda yake zaune tace "Ashe wai kai zaka raka su kasar wajen" MD yace "Ina wuni Mama" Mama Ladi tace "Lafiya lau Mendi, ya aiki?" Ya ɗan yi murmushi yace "Alhamdulillah" Mama Ladi tace "To madallah" Mayraah ta gaida Mama Ladi, Mama Ladi tace "Lafiya lau, ina mijin naki?" Mama Ladi bata jira cewar Mayraah ba tana kallon sama ta kwalo ma Ihsaan kira, ba a dau lokaci ba sai ga Eemaan ta sauko downstairs ta karaso kusa da Mama Ladi tace "Gani Mama" Mayraah dai kallon Eeman kawai take ganin yanda ainahin haskenta ya dawo, skin dinta sai glowing yake, kwanansu goma kenan da barin katsina amma har sun dawo hayyacin su, Mama Ladi ta daga kai tana kallon Eemaan tace "Kece Ihsaan ko neman magana..." Eeman na murmushi tace "Aa Mama tana can parlon Ammi ne shi sa na zo" Mama Ladi ta dauke kai tana cin gyadar hannunta tace "To ba ke na kira ba, ki tafi kice mata Mama Ladi na kiranta" Eemaan da har sannan fara'a ke kwance fuskarta ta kalli MD dake kallonta ta dan risina tace "Ina yini?" Ya gyada mata kai yace "Lafiya lau" Kallon Mayraah tayi ita ma ta gaishe ta, Mayraah ta amsa mata da murmushi fuskarta, Eemaan ta juya ta koma sama, Mama Ladi na kallon MD tace "Bari yanzu za a zo a kawo maka ruwa Mendi" MD ya daga kai yana kallonta yace "Mama sunana fa Aliyu" Mayraah ta kyalkyale da dariyar da bata yi niyya ba, Mama Ladi tace "Ai nasan sunan ka Aliyu, ba su Hajiya Ramatu naji suna kiran ka Mendi ba, sun ma fi kiran ka Mendin ai akan Aliyu" MD ya jinginar da kansa da kujera after letting out a sigh, bai sake ce mata komai ba, Mama Ladi na mika masa ledar gyadar hannunta tace "Ko zaka ci gyada me gishiri, Halima ce ta bani nima" MD ya girgiza mata kai yace "Alhmdlh" Mayraah dai ta kasa daina dariya, tana son tafiya sama ta gaida Ammi da kakarta da Aunty Halima da ke can bangaren Ammi amma saboda tana son ta ga yanda za a kwashe idan Ihsaan ta sakko ya sa taki tashi daga parlon, Ba a wani dau lokaci ba sai ga Ihsaan ta sauko downstairs ta karaso kusa da Mama Ladi, Kallon Mayraah dake kallonta tayi tace "Ina yini Aunty" Mayraah ta amsa mata tana murmushi, Ihsaan ta juya ta kalli MD that was looking at her a bit confused, a takaice tace masa "Ina yini" Mama Ladi dai sai washe baki take tana kallon MD kasa kasa tace "Naga kamar ka rude ko Mendi, to yan biyu ne ai" MD yayi murmushi yace "Ai nayi tunanin haka..." Mama Ladi ta kalli Ihsaan tana washe baki ba tace "Tafi ki dauko masa lemo da ruwa a kitchen Ihsani, kanin uban Mera ne" Juyawa Ihsaan tayi ta nufi kitchen, MD da ya bi ta da ido sai kuma ya maido da dubansa kan Mama Ladi yace "Aa Mama, na sha ruwa kafin in shigo, dama Mayraah mu ke jira yanzu za mu tafi airport" Ihsaan ta tsaya jin abinda yace amma bata juyo ba, Mayraah dai sai murmushi take tana kallon ikon Allah, Mama Ladi tace "Banda abun ka ko kadan ne ka sha mana Mendi, maza tafi ki dauko ruwan Ihsani" MD ya kalli Ihsaan sai kuma ya kalli Mama Ladi yace "Ai da ta farkon ma kika ce ta kawo min ruwan, naga tafi fara'a" Ihsaan ta juya ta kalli MD dake kallonta, Mama Ladi ta kyalkyale da dariya har da kyakyatawa tace "Toh banda abun ka kai din ma ai ba fara'ar bace da kai Mendi, shi sa nace a kira min ita ta baka ruwan..." MD ya ɗan buda ido jin abinda Mama Ladi tace, Ihsaan dai tuni ta tafi ta dauko ruwan da drink, sai gata ta dawo parlon ta durkusa gabansa ta ajiye, shi dai kallonta kawai yake ganin ko alamar fara'a babu a fuskarta har a lkcn, Mama Ladi dake kallonsu kasa kasa ta gefen ido sai wani murmushi take tana cin gyadar hannunta, ita kuwa Mayraah Mama Ladi ce ke bata dariya ganin yanda take wani kallonsu kasa kasa tana murmushi tana taunar gyada kamar wata boss, Tsabar dariya sai da Mayraah ta sauko daga kan kujera ta zauna a carpet, Mama Ladi ta kalleta ta wani hade rai tace "Ji mahaukaciyar banza" Mikewa Ihsaan tayi zata bar wajen shi dai MD bin ta kawai yake da ido, da sauri Mama Ladi tace "Ke dawo ki zuba masa a kopi, haka ake yi a Katsinan naku zaki wani dungurar masa da lemo a gabansa ki tafi" Mikewa Mayraah tayi tana dariya har sannan tayi hanyar stairs da sauri ta bar masu parlon ganin wani shegen kallo da Mama Ladi ta bi ta da shi, Ihsaan ta koma ta duka gabansa ta zuba masa drink a glass cup sannan ta daga kai ta kallesa taga kallonta yake, mikewa tayi ta bar parlon tayi hanyar stairs, Mama Ladi kuwa kamar bakinta zai yage tsabar murmushi, sai da taga Ihsaan ta haura sama ta maido da dubanta kan MD tace "Sam bata shiga sabgar da ba tata ba, ba kuma ruwanta da hayagaga kamar er uwarta da kaga tana ta fara'a ba kwantral, sannan ka ga girman gidan nan wallahi kafin mu tashi bacci duk ta gyara ko ina, azababben tsafta gareta har ya wuce misali wllh, yanzu mai aikin gidan nan ma bata da wani amfani don duk wani aikin gidan Ihsani ce ke yi, er uwarta da kaga tana ta fara'a kamar wawiya ba abinda ta iya sai bacci da son jiki, sai ta kai karfe goma sha daya na safe bata tashi ba Al-qur'an, don ma Ammi na taka mata birki, kaga yanda ta wanke kofin nan kafin ta kawo maka to da Imani ce haka zata dauko kopin tana fara'a ta kawo maka" MD dake ta sauraronta murmushi kawai yake bai ce komai ba, har sai da tayi shiru sannan ya daga kai yace "Hutu suka zo kenan" Shiru Mama Ladi tayi, sai kuma ta fara matsar kwalla a hankali tace "Wani hutu Mendi? 'ya yan Marigayiyar matar Mamuda ne fa, marayu ne ba uwa ba uba a duniya sai tsinannun dangin ubansu yan katsina da suka handame duk gadon su, a takaice dai yanzu gatansu a duniya Ammi da Mamuda sai ni Ladi, don uwarsu mutuniyar kirki ce wllhi, duk in zamu hadu da ita sai ta ban dubu ashirin, ko a ranan da zata rasu dubu ashirin ta bani muna zaune da ita a parlor kafin a kirata ace yaran ba lafiya ta kama hanya ashe ajali ke kiranta..." Shiru Mama Ladi tayi tana matsar kwalla, kasa cewa komai MD yayi da farko don sosai jikinsa yayi sanyi, bayan few seconds a hankali yace "Allah Ubangiji ya gafarta ma iyayen su" Cikin rawan murya Mama Ladi tace "Ameen ya Allah, kuma a haka tsinannun dangin uban suka maka Mamuda a kotu wai sai ya fita sabgar yaran, duk hankalinsu ya tashi sun zata Mamuda zai kai su kotu a kan gadon yaran da suka handame shine suka riga makasa kotu, ai ko na ba Mamuda shawara bayan Usman yayi hayan tijararrun lauyoyi a tozarta yan iskan a idon duniya sannan su fito da gadon marayun duk inda ma suka kai" MD dake ta sauraron Mama Ladi yace "Ikon Allah" Mama Ladi tace "Wallahi kuwa, shekaranjiya aka kawo ma Mamuda sammaci, ni dai na kara tsorata da lamarin katsinawa wllh, ni ban ma taɓa

Download complete TXT · Novel page