Mayrah

Chapter 141 of 152

bin hanyar garin ba ko da wasa" After few seconds MD yace "Ina da aboki lauya, a kasar waje yake aiki amma yana Nigeria yanzu haka, zan masa magana akan case din in sha Allah" Mama Ladi ta saki kabbara tace "Allah yayi maka albarka Mendi, kuma ana gana Shari'a kyau dama a aurar da marayun kawai su je su karasa karatu a gidan mazajensu" MD dake kallonta yace "Ohk, dama da maganar auren nasu kenan a kasa?" Mama Ladi tayi kasa da murya tace "Aa ba haka zaka ce ba, ni ce dai nake ga hakan kadai ne rufin asirinsu tunda mata ne, sannan aure ne kadai zai kubutar da su daga tuggun dangin uban nasu, kaga ita wannan me washe baki kullum cikin fara'a dama Usuman ya kyasa ta tun da dadewa, yanzu ma bini bini zaka gan su tare a parlo tana zuba masa turanci, ita kuwa wannan kamilar da ake kira Ihsani so nake ace ita ma ta samu me tsafta da kamun kai irinta, to kaga ba ko ina suke zuwa ba tunda ance makarantar har an gama daukan dalibai sai wani shekara kuma, amma dai akwai wani ɗan aminiyar Ammi naga in dai ya zo sai yayi ta kallonta kuma shi ma yana da hankali da nutsuwa gaskiya..." Duk da karya kawai Mama Ladi ta lafta haka tayi keeping serious face kamar gaske, MD yayi shiru bai ce komai ba, Mama Ladi dai sai kallonsa take ta gefen ido.
Washegari karfe tara na safe jirgin su Mayraah yayi landing a Us after almost 14 hours of leaving Nigeria, Dad dinta har ya iso airport yana jiran saukan jirginsu, bayan ya ba MD hannu sun gaisa yayi ma Umman sa Side Hug yana murmushi yana kallonta a hankali yace "I miss you so much Mom" Hajiya Ramatu ta hade rai tace "Meye haka kai?" Aunty Halima dake dariya tace "Za ka fara ma Umma shagwaba ga dai Daughter dinka tana kallon ka" Sai a sannan Abdallah ya juya ya kalli Mayraah, ɗan murmushi Mayraah tayi ta gaishesa, ya sake Umman sa ya dawo gun Mayraah, giving her a side hug too yana kallonta da murmushi fuskarsa yace "How are you daughter?" A hankali tace "I am fine" A haka duk suka shiga motar sa yayi driving dinsu zuwa gidansa dake Los Angeles yana hira da MD dake front seat a zaune, Mayraah ta dinga kallon Mansion din Dad din nata, yayi leading din su har ciki, Mayraah was soo happy to see her Mom, ko lura da Ceo dake dakin bata yi ba ta tafi da sauri ta rungume Mom dinta dake zaune, Aaria was so surprise and at the same time very happy to see her daughter, don ba ace mata har da ita za a zo Us ba, Mayraah ta ɗan buda ido ganin Ceo dake zaune a dakin tana kallonta, a hankali ta zamo kasa ta gaisheta tana murmushi, Ceo tace "Sannu Mary Ann..." Mayraah taji kunya sosai don har ta mance rabon ta gaisheta ko ta WhatsApp ko ta phone call, sunkuyar da kanta tayi, Aaria dai sai kallonta take tana murmushi, ta dauko one of the twin dake kwance kan gado ta mika mata, Mayraah ta amshesa tana kallon babyn da yau suka cika wata daya a duniya, sosai taga yaran ke kama da ita, dai dai nan Aunty Halima ta shigo dakin cike da murna tana congratulating din Aaria, Aaria ta mike ta rungumeta da fara'a tana welcoming dinta at the same time tana tambayarta ina Umma, Aunty Halima tace "Umma sallah zata yi tukunna tana downstairs..." Aunty Halima ta gaida Ceo da fara'a sannan ta karasa ta dau other twin din dake kwance. Kwana biyu kacal Hajiya Ramatu tayi a gidan only son din nata a Us, babu yanda Aaria bata yi da ita ta kara ko da wani kwana biyun ne ba amma taki, haka nan ita da MD suka koma Nigeria leaving Aunty Halima and Mayraah behind, 24/7 zaka tarar da Mayraah makale da yan kannen nata guda biyu tana renon su, sosai take jin yaran har cikin ranta, gashi sam basu da rigima, Daya anyi naming dinsa After Abba (Mahmud) Dayan kuma (Alhaji Kabir Saminu) ana kiransu da Shuraim da Sudais, akwati biyu Abba yayi ma babies din na kaya, Ammi ma tayi masu siyayya sosai, bayan tafiyar Hajiya Ramatu da MD da kwana biyu Ceo ta shirya ita ma zata tafi Canada, Gaba daya Aaria ta dawo bata da walwala ganin yayarta zata tafi duk da watan ta daya har da kwana biyar kenan a Us, Mayraah ta bude kofar dakin da Ceo take ciki a hankali ta shiga, Ceo tayi hanging call da take yi ta ajiye wayar tana kallon Mayraah tace "Come in Mary Ann" Mayraah ta karasa cikin dakin ta zauna kan kujera, Ceo na kallonta tace "Ya mai gidan naki?" Mayraah na wasa da fingers dinta tace "Yana nan lafiya" After few seconds silence Ceo tace "Hope you are taking no contraceptive Mary ann" Mayraah tayi jim don she wasn't expecting the question, can ta girgiza mata kai ba tare da ta kalleta ba a hankali tace "Aa bana shan komai" Ceo tace "Ohk good, nan gaba za ku kara sati daya a Usa kafin ku koma Nigeria ko?" Mayraah ta gyada mata kai tace "Eh" Ceo tace "Alright then, i will get you some pills and their prescriptions yanzu kafin in tafi, sai ki fara sha tun daga yau kafin ku koma Nigeria..."
A kwana a tashi Mayraah da Aunty Halima suka fara shirin komawa Nigeria bayan sun yi kwana sha biyar a America, Aaria dai na zaune gefen gado tana ta kallonsu a sanyaye suna ta hada kaya, a haka Abdallah ya kai akwatunansu booth din motarsa zai kai su airport, Mayraah felt so bad leaving her mother and siblings, rungume Mom dinta tayi tana murmushin karfin hali, a hankali Aaria tace "Take care of ur self dear, ki gaida min Amminki da Abbanki da kyau, mijinki ma kice ina gaishe sa...." Mayraah tace "Za su ji in sha Allah" Dukawa tayi tana kallon cute siblings dinta dake kwance kan gadonsu tayi kissing dinsu gaba daya sannan ta mike ta fita daga dakin Aaria na biye da ita zata masu rakiya waje.... Sai washegari Mayraah suka sauka Airport din Abuja.

Mayraah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788

134
Ammi ta shigo dakin da Mama Ladi ke ciki da sallama, Mama Ladi ta amsa tace "Ai na zata kin tafi bangaren mijinki ne kika bar ni parlon ki kamar mayya shine na dawo nan" Ammi ta karasa ta zauna tace "Kin gama cin abincin ne Mama?" Mama Ladi tace "Tsohon zance" Ammi tace "Yanzu Alhaji ke gaya min wata magana, shine nace bara in zo in sameki" Mama Ladi ta buda ido sosai tace "Wace magana?" Ammi tace "Wai Alhaji Saminu ne ya kira sa dazu bayan magariba...." Mama Ladi tayi saurin gyara zama tace "Wai me?" Ammi na murmushi tace "Za su zo nema ma wan Musharraf auren Ihsaan" Mama Ladi ta zaro ido ta dafe kirji tace "Ke don Allah fa" Ammi tace "Wallahi, kuma dama ta gaya min suna waya da shi" Nan da nan fara'ar dake fuskar Mama Ladi ya bace tace "Kaji makira, wato ni da nayi silan hadata da shi ni ta mayar er banza kenan da bata gaya min ba?? Ina ce ni na dinga cusata gun sa ba wani yayi min wahalan haka ba ko" Dariya Ammi tayi tace "Ai in kin lura ba wai tana da magana bane kamar er uwarta Mama, ita Eeman ko baka ja ta jiki ba nan da nan take shige maka ta saba da kai, ita kuwa Ihsaan tana da miskilanci ba lallai kasan zuciyarta ba, shi sa in zaki lura nafi jan ta a jiki kan Eeman, ranan tana min gyaran daki ta gaya min" Mama Ladi tace "Can ta matse mata, sam bana son hulda da munafuki a rayuwata, ni dai ba Allah ya gani saboda Marigayiya Amina nayi ba, banda haka ai Mendi ya fi karfinta, mutumin dake rayuwarsa a canada" Ammi tayi dariya sosai tace "Ho Mama, a ina kika ji Canada har kika iya fadansa kai tsaye babu kuskure" Mama Ladi tayi kwafa tana murmushi tace "In fa kina gidan Alhaji Saminu dole ne ma ki iya fadan sunan kasashen turai, baki ga Uban Mera a Amurka yake rayuwarsa ba, ai kullum yan gidan cikin yawon zuwa kasashen waje suke, to duk ba wannan ba, yanzu me shi Mamudan ya gaya ma Saminun da ya kirasa?" Ammi tace "Sanar masa yayi dangin ubansu na nan katsina" Mama Ladi ta hade girar sama da ta kasa tana kallon Ammi, can tace "Amma dai Mamuda wani lkcn yana abu kamar wanda bai yi boko ba, ina ruwanmu da dangin ubansu na katsina da har zai ce ma Saminu suna da dangin uba?" Ammi ta girgiza kai tace "Aa Mama, ko anki ko an so dangin ubansu ne baza a canza ma tuwo suna ba, yanda Alhaji ya gaya ma Alhaji Saminun haka ya kamata dama gaskiya, sun fi mu iko da yaran nan" Mama Ladi ta kyabe baki tace "Toh ai shikenan, kilan in suka ga Alhaji Saminun ma jiki na rawa za su amince su bada auren yarinyar, tun ban gansu ba na riga nasan mayun kudi ne hadamammu, ma'aikacin gwamnati ma nan ya gansu ya kyalesu, kawai yanzu abinda ya kamata shine Alhaji Saminun ya nema ma har Usman auren ita Eeman din, ina gaya maki da gudu za su bayar da auren yaran wllh" Ammi ta ɗan yi shiru, sai kuma tace "Usman da za a kai kudin aurensa nan da sati uku" Mama Ladi ta kalleta da sauri tace "Ban gane ba, dama ba son Eeman din yake ba duk wannan kusancin da naga suke da shi?" Ammi ta girgiza kai tace "Nayi masa maganar ta, uban ma yayi masa, Maheer yayi masa amma duk ya ki, yace shi kawai a matsayin kanwa take a gunsa ta yanda zata kawo masa kukanta akan duk abinda ya dameta a ko wani lkci" Mama Ladi dake kallon Ammi baki bude tace "Ji jaraba, amma da ai yayi niyyar aurenta sanda uwarta ke da rai, ko dai wiwi yake sha ne Usuman?" Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace "To yanzu kam ya ki, uban kuma yace a kyalesa" Mama Ladi tace "Amma ban ji dadin wannan lamari ba wallahi, har ina murna yanda naga sun shaku tana masa turanci, yanzu shikenan Ihsaan sai tayi aure ta bar er uwarta a gida? A ina aka taɓa haka? Yan biyu ai rana daya ake aurar da su kamar yanda suka fito duniya rana daya" Ammi na murmushi tace "Aa Mama, ana yi, kilan kece baki taɓa gani ba, ita ma Eeman din Allah zai fiddo mata da miji in sha Allah...." Mama Ladi tace "Amma dai Usman gantalalle ne, sam ba a gane gabansa balle bayansa" Tagumi tayi ta e "Yanzu ta ina zan fara samo ma Eemani miji ni Ladiyo, abun ba dadi er uwarta tayi aure ta bar ta a gida wllh, ba don ba don ba ai da sai ace Mendi ya dakata har Allah ya fiddo ma er uwarta miji ita ma sai a hadasu" Ammi tace "Aa ba zancen dakatawa Mama" Mama Ladi tace "Ko da yake kada garin dakatawa lamarin auren ya bi ruwa in shiga uku, gwara kawai dayan ta tafi mu san daya ce ta rage mana, ita ma zan shiga in fita in samo mata nata mijin, to yanzu yaushe Saminun yace za su je katsinan?" Ammi tace "Gaskiya ban tambayi Alhaji ba" Mama Ladi tace "Ai ko don albarkacin zuciya me kyau irin na uwarsu to baza su taɓa tabewa ba a duniya, mijin marainiya duk Allah zai basu...." Murmushi kawai Ammi tayi bata ce komai ba, Mama Ladi ta gyara pillow ta kishingida tace "Ohh, yau sati nawa rabon Mashir da gidan nan, yaro duk ya talike gun Mera, wannan wannan da ba don er ki bace sai ince ta shanye maki ɗa ko ince ta asiricesa ta rabaki da shi kawai, huhuhu.... ko da yake ga kakarta can ita ma tana buga duniyancinta ita kadai ranta a kantamemen gidan Saminu, duk tayi bake bake ta hana kowa shigowa tun kuruciya, yana son kara auren ba wai bai so ba amma matar nan ta shiga ta fita ta hana, ni abun na daure min kai, da tsufanta ma ba lallai ta bar wata ta shigo gidan ba a yanda na lura da ita, ita kanta uwar Meran kinga ai Abdallan yaki wani auren har sai da ya jirata bayan kusan shekara ashirin da biyu sannan suka ci gaba da aure, kaf dangin nan ban ji ance ga me kishiya ba, ita ma uwar Mendi kin dai ga yara biyu ta haifa ma kanin Saminun, to har mijin ya mutu bata bar sa ya kara aure ba, suna da mugun tabon nan a pamilyn, to ga dai Mashir a hannun Mera sai yanda muka gani kuma" Ita dai Ammi bata tanka Mama Ladi ba.
Kamar yanda Mama Ladi ta fada kan dangin uban su Eeman hakan kuwa ya faru, don suna ganin Alhaji Saminu da tawagarsa ba shiri suka amshi kudin auren Ihsaan ba tare da wani bincike ba, a nan take kuma aka saka bikin wata biyu, tsabar mamaki Abba ya kasa cewa komai da Alhaji Saminu ya kirasa daga bisani yana sanar masa an kai kudin Ihsaan, ita kam Ammi bata yi mamaki ba don dama Mama Ladi ta fada. Mayraah na bacci a dakinta da rana wajen karfe uku taji ana kwankwasa kofa, ta mike xaune wondering who it could be, sauka tayi daga kan gadon ta dau Hijab dinta ta saka sannan ta fita zuwa parlor, sai da ta fara leka window ta ga Mama Ladi tsaye da su Eeman, ta karasa ta bude kofar parlon tana murmushi ta basu hanya tace "Sannu da zuwa Mama" Mama Ladi ta rike haɓa tace "Ba shakka, yau dai nace bari mu zo da yan biyu mu gaisheku tunda kwana biyu hanya bai biyo da ku ta gidan Mamuda ba" Murmushi kawai Mayraah take har suka shigo parlon tana amsa gaisuwar da su Eeman ke mata, Mama Ladi ta nemi kujera ta zauna tana bin ko ina da kallo tace "To ina Mashir din?" Mayraah tace "Bai dawo aiki ba" Mama Ladi tace "Bawan Allah, to xuwa nayi in sanar maku an saka bikin Ihsaan da Mendi wata biyu kacal..." Mayraah na murmushi tace "Ammi ta gaya ma Yaya jiya da ya kirata ai, dama cewa yayi in ya dawo aiki sai mu je can gidan anjima" Mama Ladi tace "Ni na zata ma bakwa garin ne ai..." Mayraah dai sai murmushi take ta tafi kitchen zata kawo masu ruwa, gashi yau kwana biyu rabon da tayi girki, kawai taji girkin ya fice a kanta gaba daya ta rasa me ke damunta a ranta, she is so tensed ga dai shi babu inda ke mata ciwo, wannan yasa da ya dawo aiki jiya ya duba Bp dinta yaga yayi kasa sosai, a daren ya fita ya siyo mata fruits iri iri ta zuba a fridge, haka nan Mayraah ta kawo masu ruwa da lemo, sai fruits sannan ta koma kitchen tana tunanin abinda zata dafa masu, tun bata fara girkin ba taji baza ta iya ba, kawai ta tuna akwai cup cake da tayi order jiya, ta dauka ta kai masu kawai. Har karfe biyar da wani abu su Mama Ladi na gidan, Maheer na dawowa aiki da takeaway din abinci da Mayraah tace ya yi masu a hanya Mama Ladi ta fara tattara cake dinta da bata ci ba da kwalin katon lemo duk ta saka cikin jakarta tace "Dama kai nake jira maza maida ni inda na fi wayo, cikina sai kugi yake, ta hadamu da kayan marmari kamar wasu marasa lafiya" Mayraah ta buda baki tana kallon Mama Ladi, Maheer yayi dariya yace "Ai ga abincin na taho maku da shi gas din girkin ya kare ne" Mama Ladi ta amshi ledan hannunsa ta cire takeaway daya ta saka a jakarta tace "Mu je ka ajiye ni gida" A hankali Mayraah tace "Don Allah ku kwana mana Mama sai mu je can gidan gobe gaba daya" Mama Ladi tace "Haram, in kwana inyi me a gidan yara, gashi wai ba gas, o'o ban saba kwana gidan mutane ba gaskiya, gwara kawai ya tafi ya ajiyeni gidan 'ya ta, in su Eemani za su kwana to su kwana tunda gidan yayyinsu ne dama" Haka nan Maheer ya tafi kai Mama Ladi gidan Ammi leaving the twins behind... Washegari da yamma wajen karfe biyar Mayraah ta fito parlor ta sa su Ihsaan su shirya don Maheer zai yi dropping dinsu gidan matar Dr Khalil ta haihu, sosai taji dadin kwanan da yan biyun suka yi a gidan don throughout bacci ta yini take yi, duk su suka yi komai a gidan har girki, iyaka da ta farka ta ɗan ci apple ta koma bacci, in lkcn sllh yayi ta tashi tayi, bayan Magrib Maheer ya kai su gidan, Mayraah ta juya tana kallonsa bayan yayi parking a waje, a hankali tace "Zaka shiga ne Dear?" Yace "Aa kawai ku shiga in kun gama ki kirani" Tace "Ina zaka?" Yace "Fueling station" Mayraah tace "Ohk Dear" Sauka tayi daga motar su Eeman ma suka sauka rike da ledan atamfa biyu da kayan baby da Mayraah ta siya ma babyn da Zainab ta haifa, A cikin jakarta dubu ashirin ne da Maheer ya bata ta ba Zainab din... Mayraah ta shiga compound din tare da su Ihsaan dake biye da ita, a bude suka tar da kofar parlon Mayraah ta shiga da sallama suna biye da ita, Zaune taga MD a parlon da Dr Hamid, sai shi kansa Dr Khalil din, tun da suka shigo parlon idon MD ke kan Ihsaan da taki yarda ta hada ido

Download complete TXT · Novel page