Showing 426001 words to 429000 words out of 452169 words
Chapter 143 - Mayrah Complete By Khaleesat Haydar
ko dai Mashir ba shi da hankali ne?" Ammi ta daga kai ta kalleta, Mama Ladi tace "To naga yau sati daya da dauko yarinyar nan daga gidansa rai kwakwai mutu kwakwai amma bai zo duba ta ba, yana nufin ya hadata da wahala kenan ya kama gabansa ko menene haka?" Ammi dai ta ci gaba da danna wayarta bata tanka Mama Ladi ba, Ihsaan ta shigo parlon da shayin da tayi ma Ammi exactly yanda Mayraah ke yi mata, ta duka gabanta tana kallonta bayan ta ajiye tace "Ammi gashi na gama" Sosai Ammi ke jin Ihsaan a ranta don kusan personality dinsu daya da Mayraah in so many ways, wani lkci in tayi wani abun sai Ammi taga kamar Mayraanta, shi sa take jin yarinyar sosai a ranta, Ammi ta mata murmushi tace "To sannu da aiki daughter, ina Eeman fa?" Ko rufe baki bata yi ba sai ga Eeman ta shigo parlon fuskarta ba walwala, duk suka bi ta da kallo har ta tafi ta nemi kujera ta zauna tana cika tana batsewa, Mama Ladi tace "Lafiya?" Ko rufe baki bata yi ba Usman ya bude kofar parlon, yana kallon Eeman fuska daure yace "Ke ina maki magana kika wuce??" Eeman dai bata ce komai ba ta sunkuyar da kai, Mama Ladi ta kyalkyale da dariya har da saukowa kan carpet tana kallonsu, nan da nan hawaye ya cika idon Eeman, Mama Ladi tace "Me kika masa hala?" Sai ta kara kwashewa da dariya kamar an aiko ta, Usman na kallon Eeman fuska murtuke yace "Zo ki fita" Mikewa tayi ta goge idonta ta nufi kofa ta bi ta gefensa ta fita daga parlon, Mama Ladi sai kyakyata dariya take kamar taga wawan zama, Usman ya kullo masu kofar parlon ya bi bayan Eemaan, Mayraah dake kwance parlon tayi murmushi kawai tana cin Garden egg din hannunta, Ihsaan ma dai murmushin tayi ta mike ta dau wayarta ta fita daga parlon, Mama Ladi ta hadiye dariyar da take da kyar tace "In kin bibiya wani azababben rawan kan tayi masa, dama na baro ta wai zata dafa masa shayi da kyar in ba gishiri ta lafta masa a madadin sugar ba ko kuma barar masa da shayin tayi a jiki don dai in ba idona ne ba kamar ba kayan nan na gani a jikinsa ba dazu" murmushin da Ammi bata yi niyya ba tayi tana ci gaba da danna wayarta, Mama Ladi ta rike haba tana zare ido tace "Tsorona Allah tsorona yarinyar nan Eeman, tun da ta kona min er sabuwar atamfata wajen guga kuma ta wani zo tana nuna min tana murmushi na sha jinin jikina da ita, ranan har hawaye sai da na zubda, in kun lura sam na dena sa ta aiki, na yarda mu zauna mu yi hira tana baɓɓaka dariya amma ba ruwana da sa ta aiki" Ita dai Ammi bata ce komai ba, Mama Ladi tace "Dama Usuman din ne dai dai ita, shi zai seta mata zama, shegen rawan kanta ya fi karfinta ga dariya kamar er mahaukata, ni dai ina nan har yau ina kokarin shawo kansa a makala masa ita su je can ya gyara mata zama, duk tsiyar da zata tafka masa dama ko yaki Allah sae dai yayi hakuri, in kuma har yanzu yana kan bakansa to gaskiya sai ta kai kamar Mera za a aurar da ita kar taje ta maida mijin mahaukaci, dama mazan yanzu ba hakuri garesu ba, ba kowa ne zai jure shashancin nan nata ba, haka ranan da Uwar Zainab ta zo da jikokinta yan biyu muna kasa a zaune daga nace Eeman ta dauko min jakata in basu dari biyar su siyi biscuit sai ga yarinya da akwati, kuma jakar fa akan akwatin yake, sai ta sauke jakar ta kinkimo min akwatin, to ina lafiya a nan" Ita dai Ammi bata ce komai ba, Mama Ladi ta mike tace bari dai inje inga halin da suke ciki, Mama Ladi na fita parlon sai da ta tafi dakin yan biyun ta bude kofar a hankali tana leka ciki, kwance taga Eeman tana shesshekan kuka, ta karasa cikin dakin tace "To wai me kika masa ne? Shi fa Usuman din nan dama ya saba cin zalin 'ya yan mutane, ji zamanin Badiyyah haka yayi ta narkarta kamar ya samu er banza, kema dai maganin ki kenan kullum baki da aiki sai makale masa kuna turanci, ai ga irin ta nan" Eeman ta mike zaune tana kuka a hankali, Mama Ladi tace "Gaya min me kika masa?" Zata yi magana aka bude kofar dakin, Eeman ta goge idonta da sauri ganin shi ne, yana tsaye daga bakin kofar yace "Wa kika bar ma sauran?" A hankali tace "Aunty Bilkisu tace in bar shi zata dauke" Ya daure fuska yace "Fito kije ki dauke" Sauka tayi daga kan gadon tana cika tana batsewa ta bi gefensa ta fita, Mama Ladi ta nufo Usman bayan Eeman ta fita tace "Gwara dai ka dinga yi kana seta mana ita kana mata jan ido, sam bata da kai, wani shegen za mu dauketa a haka mu kai masa salon wataran ya koro mana ita, kanta rawa yake kamar kararrawa"
Bayan fitan Mama Ladi parlon Ammi da kusan minti sha biyar aka bude kofar parlon a hankali, Ammi ta daga kai tana kallonsa, karasowa ciki yayi kansa a kasa, ya zauna kan carpet yace "Ammi ina yini" Ammi tace "Lafiya lau, ya aiki?" Yace "Alhamdulillah" Tun da Mayraah taji muryansa ta rufe ido kamar tana bacci, Ammi tace "Dazu Mama Ladi ta gama cigiyarka ashe kana hanya" Maheer ya ɗan yi murmushi bai ce komai ba, after a while Ammi ta mike ta fita daga parlon da cup din shayin da ta sha, tana kulle kofar Maheer ya mike ya tafi inda Mayraah ke kwance ya duka gabanta yana kallonta, sai kuma ya zauna murya can kasa yace "Mimi" Ƙin bude ido tayi still Pretending she is asleep, a hankali ya dagota, amma tana jin kamshin turarensa ta kasa resisting ta bude ido da kyar tana kallonsa, ya ɗan mata murmushi yace "Ya jikin? I am sorry i didn't come all this while, bana son maganan Mama Ladi ne billah, i just have to gather much courage in zo yau in ga jikin ki, Hope kina ɗan cin abincin?" Nan ma ta gyada masa, ya kalli Garden egg ɗake kusa da ita, yace "Shi kike ci?" Still ta gyada masa kai kawai, yace "Are you comfortable here?" kallonsa kawai take babu ko kiftawa, bude kofar parlon aka yi ya juya da sauri sai ga Mama Ladi ta shigo, dauke kai yayi, Mayraah ta zame jikinta ta koma ta kwanta, Mama Ladi tace "Bawan Allah, dazun nan na gama cigiyarka nace ko aikin ne yayi maka yawa kwana biyu shiru" Mayraah ta dinga kallonta tsabar mamaki, Maheer ya ɗan yi murmushi ya gaisheta tace "Lafiya lau Mashir, to da aiki zaka ji ko da zuwa dubiya kullum, ai mu da muke nan duk mun wadatar muna bata kulawa yanda ya kamata, ɗan uwanka kuwa har ya saka adashin Yalo da fiya duk dare, sai dai Allah ya saka masa" Shi dai Maheer bai ce komai ba ya mike ya koma kan kujera ya zauna, Mama Ladi tace "Sai kaji an kara sati biyu bikin Mendi da yarinyar nan Ihsaani ko?" Maheer yace "Eh haka yace min" Mama Ladi tace "To wai me yasa yace a kara sati biyun ne?" Maheer yace "Yana da wani taro da za su yi a ne a kasar waje, a satin bikin" Mama Ladi tace "Ba shakka, to Allah ya sa a cikin sati biyun ita ma er uwar ta samu mijin, ba dadi daya tayi aure ta bar daya" Maheer yayi murmushi yace "To ba ga abokin aikin MD dake sonta ba ku ka ce Aa" Mama Ladi tace "Kaji ka da wata magana, mata fa aka ce garesa da yara biyu, ina Eeman ina me mata? Ai ni ce ma nace ta ce masa an mata miji, Ammi ma ta goyi bayan hakan, gwara ta samu mijinta ita kadae, ranan ma ina zaune a dakin ta gaya masa an mata miji a gida, kaga da yake yana da hankali shikenan ya rabu da ita" Maheer yace "Allah ya zaba abinda yafi zama alkhairi" Mama Ladi tace "Ameen, na fi hango mata Usuman a abinda ya fi zama alkhairin" Shi dai Maheer bai ce mata komai ba, Mama Ladi ta rike haɓa tace "Ni ko zan so in ga irin zaman da Mendi zai yi da yarinyar nan Ihisani in sun yi aure" Sai kuma ta daga hannu sama tace "Allah Ubangiji yasa da ni za aje kai ta Canada din idan an yi bikin" Maheer na kallonta yace "Kamar ya wani irin zama za su yi?" Ta kyalkyale da dariya ta gyara zama zata fara koro masa bayanin abinda idonta ke gane mata duk in MD ya zo gidan wajen Ihsaan, don in dai ta lura ya zo to tayi ta zarya a parlor kenan kamar me nakuda ta shiga kitchen ta fito, taje dakin Bilkisu ta fito, ta tafi dinning ta fito, nan kuwa duk hankalinta na kan MD da Ihsaan, zata fara koro bayani kenan sai ga Ihsaan ta shigo parlon da sallama, ba shiri Mama Ladi ta canza maganarta ta marairaice tace "Yanzu yaya kake yi da abinci in ka dawo daga gun aiki ba mata a gida?" Murmushi Maheer yayi ya mike ya fita daga parlon bayan ya amsa gaisuwan Ihsaan. Tun daga ranan duk bayan kwana biyu sai Maheer ya zo gida duba Mayraah, duk in zai zo kuma abinda yaga take iya ci yake siyo mata, a gefe guda kuma ana ta shirye shiryen bikin Ihsaan da MD, Eemaan kuwa ta tsiri avoiding Usman a gidan, dama tana jin shigowar motarsa zata shige dakin Ammi wani lkcn ma nan take bacci, da safe kuwa sai ta tabbatar ya fita take fitowa, duk Mama Ladi na kula da ita.... Mayraah na zaune parlon Ammi ita kadai tana cin shinkafa da mai da yaji bayan magrib don haka tace take son sa, zuwa yanzu kam jikinta da sauki ba laifi, har Ammi nata mamakin ita laulayin na wata biyu kacal tayi, komai yanzu tana iya ci, Maheer ne ya shigo parlon da sallama, ya karaso kusa da ita yana kallonta yace "Me kike ci haka?" Kallonsa tayi ta ci gaba da cin abincinta, ya ajiye ledan yoghurt din hannunsa da tace ya siyo mata, ya zauna yana kallon abincin ganin yajin da ta lafta yace "Baya maki yaji ne Dear?" ajiye cokalin tayi don dama ta gaji da cin abincin, yace "Ina su Ammi fa?" Tace "Sun je dubiya da Mama Ladi da Eeman" Yace "Dubiya kuma? Waye ba lafiya?" Tace "Ummi, anyi admitting dinta a hospital daxu" Yace "Allah ya sauwake, driver ne ya kai su?" Mayraah ta gyada masa kai, A hankali ta matsar da abincin daga kusa da ita, yace "You need anything?" Ta kallesa cikin sanyin murya tace "Kamar ice cream nake son sha ba yoghurt din ba" Yayi kasa da murya yace "Ko muje in siya maki ice cream din mu dawo kafin su Ammi su dawo daga hospital din" Shiru tayi tana kallonsa, ya mike ya dagota yace "Come on Baby, ai ba dadewa za mu yi ba" Daki ya tafi ya dauko mata Hijab dinta don dama dogon riga ne jikinta tayi wanka kenan ta fara cin abincin da Bilkisu ta kawo mata, dakansa ya sa mata Hijab din, ta marairaice tace "In su Ammi suka dawo fa?" Yace "I assure you za ma mu riga su dawowa, nearest ice cream spot za mu je in siya maki" Daga haka ya kama hannunta suka fita daga parlon.
Mayraah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
137
A hankali Mayraah ta bude ido ta dalilin yunwan da ya dameta cikin bacci, da mamaki take tattaba gadon da take kwance duk da duhun dakin, how did she manage to get here, tunda ta dawo gidan Ammi bata kwanta saman gado ba, dakin ma gaba daya bata so a parlor take kwanciya kan shimfida, garin yaya kuma take jin ta kamar a kan gado, da sauri ta mike zaune tana zaro ido trying to figure out where she is, Maheer dake zaune saman darduma ya idar da sallah ya juya yana kallonta duk da ba wani haske ne da dakin ba, can ya mike ya kunna wutan dakin, he can see how shocked she was tana kallonsa kamar idanunta za su fito, ya karasa kusa da ita ya zauna gefenta yace "Baby kin tashi" kamar zata yi kuka cikin tashin hankali tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku yaya, idan su Ammi suka dawo fa?" Ya kamo hannunta yayi kasa da murya yace "Nayi ta tashin ki in maida ke gida kika ki tashi Baby, at the end kika ce in kyaleki" Mayraah ta fashe da kuka tana kokarin sauka daga saman gadon, sai kuma ta rufe jikinta da sauri da duvet ta wani kallesa, kuka ta fara rera masa kamar er yarinya, muryarta na rawa tace "Don girman Allah ka rufa min asiri kai maida ni gidan kafin su dawo" Maheer ya ɗan yi murmushi ya dauke kai bai dai ce mata komai ba, ta lallaba ta sauka daga kan gadon ta jawo clothe dinta cikin few seconds sai ga ta ta shirya ta saka har hijab dinta tana kallonsa tace "Ni ka tashi ka maida ni gida plss" Ya juya ya kalleta, calmly yace "Kin san karfe nawa kuwa?" Ta wani zaro ido ta nufo sa ta duka gabansa cikin tashin hankali tace "Karfe nawa?" Ya dau wayarsa dake kan bedside drawer ya kunna ya nuna mata agogo, bata san sanda tayi wani kara ba ganin karfe biyu da rabin dare, Maheer yace "Ke, baki san dare bane Mimi?" Tayi zaman dirshan kan carpet tace "Na shiga uku na lalace" Sai kuma ta hade kai da gwiwa tana rusa kuka, shi dariya ma take basa, ganin da gaske take kukan ya dawo kasa ya zauna kusa da ita yayi kasa da murya yace "Wallahi na tasheki kika ki tashi Mimi, har masifa kika min in kyale ki" Ita dai kuka kawai take kamar an aikota, babu warce ta tsaya mata a rai lokacin kamar Mama Ladi, da ta tuno Mama Ladi sai ta kara sautin kukanta, shikenan ta shiga uku ta lalace kuma wajen Mama Ladi, Maheer ya dukar da kansa dai dai fuskarta cikin kwantar da murya yana murmushi yace "Kawai ba sai mu ce baki da lafiya bane na kai ki hospital aka sa maki drip karami, zan iya sa maki Cannula ma a hannu da sassafe sai mu tafi can gidan mun ce daga hospital muke, dama ga sauran magungunanki a nan da ban kai maki ba sai mu tafi da shi like wanda aka baki a hospital" Sai a sannan Mayraah ta daga kai tana kallonsa hawaye na sauka idonta cikin rawan murya tace "Baza su gane ba?" Ya gyara zama yace "Ba wanda zai gane mana, ga dai cannula zan sa maki a hannu, infact sai mu tafi da karamin drip ince ai ance karfe tara na safe a kara sa maki wani drip din, kawai around 9am sai in koma in sa maki drip, no body will suspect anything" Mayraah ta fara shara hawayen idonta a hankali alamar she is convinced with his plan, sai kuma ta wani kallesa kamar zata fashe da wani kukan tace "Da naki tashi ba sai ka daukeni ka kai ni motar haka ba, ai in dai na ji ni a mota dole zan tashi" Yayi kasa da murya trying hard not to laugh yace "Billah dubaran hakan bai zo min ba wife" Tace "To yanzu karfe nawa za mu tafi can gidan?" Yace "As early as 7am in sha Allah" Ta cire hijab dinta ta ajiye gefe tace "Toh ni yanzu yunwa nake ji" Yace "Ohk za ki ci Indomie?" Shiru tayi tana tunanin ko zata iya cin Indomie, tun da ta fara laulayi bata ci Indomie ba don sam ji tayi bata son ko kamshinsa, yanzu kuma da yace Indomie sai taji tana sha'awarsa, ta daga kai ta kallesa taga kallonta yake babu ko kiftawa, ya sakar mata murmushi yace "In dafa maki Indomie din?" Ta gyada masa kai a hankali tace "Amma ina son yayi yaji" Yace "To ai ba Fresh pepper a gidan wife" Tace "Akwai dakakke a kitchen din mana ka duba sai ka sa min a Indomie din" Yace "Ohk dear, how about egg? Should i fry or cook it for you" Tace "Just cook 2" Yace "Alright baby, but kafin in gama kije kiyi wanka pls" Bai jira cewarta ba ya dagota ya fara undressing dinta ya kai ta har cikin bathroom din sannan ya baro ta ya fito ya tafi kitchen don dafa mata Indomie din. Mayraah na kwance ta dukunkune da bargo bayan ta fito daga wanka, har bacci ya dauketa Maheer ya shigo dakin da plate din Indomie da ya dafa mata a kan tray da bottle water da fork, ya karaso ciki ya ajiye tray din kan carpet sannan ya nufeta ya zauna kusa da ita ya yaye duvet din yana kallon lallausan jikinta, a hankali ya kai forehead dinsa saman nata yana shafa chest dinta yayi kasa da murya yace "Ur food is ready Mimi" Baccinta kawai take, ya ɗan yi murmushi ya dagota yace "Tashi ki ci abincin Baby" Bata bude ido ba tana kokarin komawa ta kwanta yaki barin ta ta kwanta yace "Baby ga abincin fa na gama" Kamar dazu da ya dinga tashinta ya maidata gida yanzun ma ƙin tashi tayi, baccin take as if her life depends on it, da ya takurata ta tashi ta sakar masa kuka tana tura sa, hakan yasa kawai ya kyaleta yana murmushi ya rufa mata duvet din ya tafi kitchen ya dauko plate ya rufe Indomie din sannan ya kashe wutan dakin ya kwanta