Showing 429001 words to 432000 words out of 452169 words

Chapter 144 - Mayrah Complete By Khaleesat Haydar

gefenta. Bude kofar dakin da aka yi ne ya farkar da Maheer ya bude ido yana bin ta da kallo har ta fita daga dakin, ya mike zaune yana kallon tray din abincin da ya ajiye mata, tas ta cinye Indomie da kwan, ruwan goran ma ta shanye, ya dau wayarsa yana duba agogo yaga karfe hudu da rabi, ba a dau lokaci ba sai ga ta ta dawo dakin rike da bread da ta gani kan dinning, ta karaso ciki, yana kallonta yace "Baki koshi bane?" Ta ɗan yatsine fuska tace "Kawai ina son in ci bread din ne" Yace "Ohk, should i get u jam or butter?" Ta girgiza masa kai ta zauna kan carpet ta fara cin bread din, basu sake komawa bacci ba har aka yi sallan asuba. Mama Ladi na zaune wajen karfe bakwai da rabi na safe a parlon Ammi, Ammi dai laziminta kawai take tana kallon Mama Ladi da tun da gari ya waye ta shigo mata take zance daya, bude kofar parlon aka yi Bilkisu ta shigo da tray dauke da shayi da bread sukutum, sai soyayyen kwai a kan plate, tunda Mama Ladi ta xo gidan dama Bread dinta babba daya ne babu me yaga a ciki, kuma tas take cinye kayanta in ma ta rage zuwa take ta ajiye sauran saman akwatin ta, Ammi ta sauke boyayyen ajiyar zuciya kilan yanzu da taga kumallo zata hakura da zancen da take tun daren jiya, Bilkisu ta ajiye tray din gaban Mama Ladi sannan ta zauna ta gaisheta, Mama Ladi bata amsa ba ta dau spoon ta debo ruwan shayin ta kai baki don tabbatar da kaurinsa, ta gyada kai jin komai yayi dai dai tace "Lafiya lau Balki, to ke a jiyan sanda za su fita a kitchen kika hangosu ko daga cikin dakinki kika hangosu?" Bilkisu tayi murmushi tace "Aa fa Mama, na fito kitchen kenan" Mama Ladi tace "Ikon Allah, kuma baki tambayesu inda za su ba?" Bilkisu har snn murmushi take bata ce ma Mama Ladi komai ba, Mama Ladi tace "Je ki kawai, dama ke me aiki ina ke ina tambayarsu inda za su" Bilkisu ta fita ta kullo masu kofa, Mama Ladi ta kalli Ammi tace "Mu dai ai saboda Allah mu ka yi ba don wani shege ba, kuma Allah shi zai bamu lada, amma don ta munafurce mu ta kira mijinta bayan fitarmu tace ya zo ya dauketa ai kanta tayi ma ba mu ba, sanda take ganiyar laulayi ai har lambarsa mantawa tayi, matar dake kwance kamar ba rai a jikinta sai in kai ka ji tausayinta ka muskutata, wato sakayyar da zata mana kenan, mutumin da ina jin sai da ɗan uwansa ya zaga ya kirasa yayi masa fada tunda ba lissafi ke garesa ba snn ya fara zuwa dubata a gidan nan, don ranan da nayi ma Usman kwamfulan da safe ke kuma na maki da yamma sai gashi sumui sumui kamar agwan da aka yi ma satar shanu ya shigo mana parlor kai a kasa, bazan boye maki ba in nace raina bai baci akan abinda yaran nan suka mana ba nayi ma Allah karya, ko baccin kirki ban yi daren jiya ba, duk fadi tashin da muka dinga yi akan munafukar yarinyar nan kamar mu muka mata cikin bata gani ba, ni ce dama kunun masara ba dare ba rana a gidan nn har sai da fuskata ta fara canza launi sbda zafin wutan gas, na dawo kamar wata me blitting amma da abinda Mera zata saka min kenan, ke ko kullum cikin wanke amai a bandaki da kin wanke da ta kirba, wallahi don dai naka naka ne amma da Allah ya isa kawai zan ja masu bakina alekum...." Bude kofar parlorn da aka yi yasa Mama Ladi tayi shiru ta juya, sosai gaban Mayraah ya fadi bayan sun yi ido hudu da Mama Ladi, ji tayi kamar ta juya, can dai ta dake ta sunkuyar da kai tana tafiya a hankali ta karasa cikin parlon, juyawa tayi ta kalli kofa tana jiran Maheer ya fara koro bayani taga wayam ashe bai shigo ba, bata san sanda ta gwalo ido ba cikin tashin hankali, muryar Mama Ladi taji tana cewa "Shimfidan naki kika dawo dauka, yana can dakin ki an linke an kai an ajiye maki, ga sauran yalonki ma can an kulle a leda an cikin firij sai ki hada da shi" Mayraah ta fara matsar kwalla cikin sanyin murya tace "Daga asibiti fa muke" Ammi dake kallonta tace "Asibiti?" Mayraah ta gyada mata kai da sauri tace "Dama ai jiya da safe nace maki ina jin jiri, shine da ya zo sai muka je asibiti, ko gama kara min ruwan ba ayi ba yace zai sa min kawai a gida" Ammi tace "Amma me yasa bai kira yace kuna asibiti ba?" Mikewa Mama Ladi tayi ta dau tray din kumallonta ta nufi kofa ta yanda rainin hankalin bazai shafeta ba ta fice ta bar masu parlon, Ammi na kallon Mayraah tace "Ina Maheer din?" Ta juya ta kalli kofa kamar zata yi kuka tace "Dama ashe bai shigo ba" Ammi tace "To kin ci abinci?" Mayraah ta girgiza mata kai, Mikewa Ammi tayi ta fita daga parlon, Mayraah ta sauke wani ajiyar zuciya ta tafi ta zauna kan kujera, wato dama wayo yayi mata ba shigowa zai yi ba, ta wani hade rai kamar yana wajen yana ganinta, Ammi bata dade da fita daga parlon ba Mayraah taji an bude kofa ta juya da sauri, Eeman ce ta shigo parlon ta nufi dakin Ammi da sauri tana gaida Mayraah da ta bi ta da kallo har ta shige dakin, ko minti biyu ba ayi ba sai ga Usman ya shigo parlon, Mayraah ta gaishesa ya amsa yace "Eeman ta shigo nan?" Mayraah ta kalli kofar dakin Ammi, bai jira cewarta ba ya karasa cikin dakin yaga bata ciki alamar ta shige bandaki, ya juya kawai ya fita, Mayraah ta bi sa da kallo har ya fice daga parlon.

Mayraah ta bude kofar kitchen tun kan ta fito ta hango Mama Ladi zaune a parlor har ma sun hada ido da ita, da sauri ta juya ta koma kitchen din tana wondering yaushe ta sakko downstairs, Mama Ladi ta kalli Eeman dake kusa da ita tace "Maza je ki gano ko abinci ta zuba" Eeman ta mike ta nufi kitchen din da sauri, Mayraah ta fara cin abincin hannunta tana kallon Ihsaan dake girkin don bai ma dahu ba ta sa ta zuba mata, tace "Idan na fita don Allah ki kawo min abincin sama, in ma Mama Ladi ta tambayeki na wanene kice ke za ki ci" Ihsaan na murmushi tace "Toh Aunty" Sai ga Eeman ta shigo kitchen din, ta gefen ido ta kalli Mayraah sai kuma ta nufi fridge ta bude ta dau ruwan gora ta dauko cup ta ɗan debi ruwan kadan ta sha ta mayar da sauran cikin fridge, ko da wasa bata bari ta hada ido da Mayraah ba balle Ihsaan, ta juya ta fice daga kitchen din ta kullo kofa, Mama Ladi sai jiran fitowarta take, Eeman ta karaso ta zauna kusa da ita tayi kasa da murya tace "Shi ta zuba" Mama Ladi ta saki salati tace "Shi ta zuba? Duk ita ta cinye abincin dazu da bai ishi jama'an gida ba fa, tun bai sauka ba ake ta zuba mata take ci, duk yau babu wanda ya koshi a gidan nan tsabar yanda tayi ta narkan abinci kan a raba ma kowa hakkinsa, a gaskiya Mashir ya zo ya tafi da matarsa kuma haka tunda ta samu lafiya, mata tana ta ci da haƙƙin jama'a a gidan nan, in kuma bazai dauketa ba to ya kamata yayo cefane na kayan abinci ya kawo gidan nan, idan ya so sai a dinga kara rabin kwana a kan yanda ake girkin, shi yanzu ba don auren gida bane ya isa ya kai ta gidan iyayenta a halin da take ciki bazai yi masu guzurin kayan abinci ba, shi ko tausaya ma ubansa bai yi, a rana sai Mera ta sha shayi sau biyar a gidan nan duk muna zaune daga na safe sai na safe, ai ko ni dai zan kirasa in basa shawaran ya siyo kayan abinci kar uban yaga rashin hankalinsa ya kawo yarinya ya ajiye masa ba ko kwayar hatsi" Fitowar Mayraah ne ya sa Mama Ladi tayi shiru, Mayraah dai bata kalli direction dinta ba ta wuce sama da goran ruwa a hannunta, Mama Ladi ta bi ta da kallo murya can kasa tace "Ikon Allah" Eeman dai sai murmushi take kamar wata sabon kamu, Mama Ladi ta rike haɓa tace "Naga ma har wani mazaunai tayi, to yaki halal yaki haram, ta ci nata ta ci na wani" Da sauri Eeman ta kwanta kan kafar Mama Ladi ta rufe ido jin sallaman Usman, Mama Ladi ta amsa tace "Sannu da zuwa Usuman" Ya karaso ya zauna parlon ya gaisheta ta amsa tace "Ya aikin? Ko ba aiki kaje ba" Bai ce mata komai ba yana duba wayarsa da kira ya shigo, Ihsaan ce ta fito kitchen rike da plate din abincin Mayraah da ta rufe da wani plate din, Ihsaan ta gaida Usman sannan ta wuce sama, Mama Ladi tace "Yau dai Allah ya sa abincin nan ya isa kowa a gidan nan" Usman na kallonta yace "Wani abinci?" Mama Ladi ta wani taɓe baki tace "Abincin maraice mana, da rana ma duk ba a koshi ba wallahi Usuman" Usman bai kara tanka ta ba, Mama Ladi ta kalli Eeman da ta rufe ido kamar me bacci tace "Ita kuma wannan haka ta yini yau duk jikinta zafi, ga shegen son jiki tun dazu take makale da ni, in na koreta ta dawo, kyau ace ko er gasasshen kaza ne ta samu wai bakinta ba dadi, ko abinci bata iya ci" Usman ya dinga kallon Eeman da idonta ke lumshe, can yace "Me ke damun ta?" Mama Ladi tace "Canjin yanayi mana Usman, kaga yanzu an kare damuna lafiya, ga sanyi kuma ya taho" Tashi yayi after few seconds ya wuce sama, A hankali Eeman ta ɗan bude ido ganin ya haura sama ta mike zaune, Mama Ladi tayi kasa da murya tace "Wai har yau baku shirya bane da abokin turancin naki?" Eeman ta wani hade rai ta kauda kai tace "Ni bazan taɓa shiryawa da shi ba har abada" Mama Ladi tace "Atoh dai, dama kece baki ji kiyi ta shige masa kamar talaka ya ga Me kudi, haka wata jikata na nan muna ce mata Badiyyah, yarinyar nan taci azaba a hannunsa, wallahi jikinta duk shatin dukansa ne daga sama har kasa, ya ci zalinta ba kadan ba, baiwar Allah tana can tayi aure a wani gari kafin Bichi, baki ga babu me shiga sabgarsa a gidan nan ba sai ke me makale masa kamar kudin cizo, kinga Mera kafin ta auri yayansa ko ga maciji bata yi da shi wllh, saboda ta san halinsa, shi yasa har tayi aure bai taɓa kai mata hannu ba to ina yaga fuska" Shiru Mama Ladi tayi ganin Usman na saukowa daga sama, Eeman ta sauke idonta don da basu hada ido da shi ba dama komawa zata yi ta kwanta kafar Mama Ladi da sauri ta rufe ido, Mama Ladi na kallonsa tace "Yo ai na mance ban gaya maka ba Ammin bata nan ta tafi kaduna, mu kadai ne a gidan yau Usuman, facalolin Mariya ke aurar da 'ya yansu mata uku lkci daya kasan duk sun zo bikin Mera da Mashir, shine ta shirya ta tafi bikin, ni dai nace bazan je ba, ana zaune lafiya a gidan ma ya mutum ya kare balle ana biki, Ammi dai ana tafi biki Kaduna" Usman yace "Na sani ai" Eeman ta ɗan kallesa suka hada ido, murya can ciki kamar warce aka yi ma dole tace "Ina wuni" Fitarsa yayi daga parlon, yana kulle kofa Mama Ladi tace "Maganin ki kenan, wa ya aikeki ki gaishesa?" Eeman kamar zata tayi kuka tace "To ba kallona naga yayi ba shi yasa"

Mayraah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788

138
Mama Ladi tace "Ai ba kallonki ba, ko ta kusa da gabanki ya wuce jan bakinki ya kamata kiyi kiyi shiru, ba a fa abun arziki da Usuman, kece ma naga yana ɗan buda ma hakora kwanaki can" Eeman tace "Ai bazan sake gaishesa ba" Mama Ladi tace "Berry gud, dubo mana ko abincin ya tsotse" Mikewa Eeman tayi ta tafi kitchen. Mayraah na kwance parlon Ammi tana waya da Maheer, tace "Komai sai ta sa ma mutum ido, ni dai kawai gwara in koma gida" Maheer dake ta sauraronta yana murmushi yace "To ai kinga Ammi ta tafi kaduna wife, daga kaduna kuma zata tafi kano wajen Hajja, so kiyi hakuri ki bari ta dawo sai in gaya mata kince zaki dawo gida" Mayraah tace "Ban gane nace zan dawo gida ba, kai komai sai ka wani cire kanka ka bar mutum a ciki, me yasa baza ka ce mata kawai zan koma gida ba without involving me?" Shiru Maheer yayi, don abu kadan ke provoking dinta yanzun nan sai ta dandankara ma mutum magana, sai da tayi shiru don kanta yace "Toh kiyi hakuri Mimi, in ta dawo zan ce mata zan tafi da ke gida" Mayraah dai bata ce masa komai ba tana cin shinkafar dake kafanta, Yace "Let me take my bath i will call u back later" Tace "Aa zan yi bacci kafin nan" a hankali yace "Ohk" Tace "Kawai ni dai gobe ka siyo min kayan shayi ka kawo na gaji da maganarta a gidan nan" Maheer yace "Ohk i will dear, zan maki shopping gobe in sha Allah" Tace "Allah ya kai mu" Yace "Ameen" Tace "Sai da safe" Yace "Har mun gama wayar Baby?" Tace "Bacci na fara ji" Yace "Ohk My love, sleep tight, don't forget ki ajiye abinci kusa dake ba sai kin sauka downstairs ba later cikin dare" Tace "Ohk..." Sallama ya kara mata sannan ya katse wayar, Ita da Ihsaan ne kawai a part din Ammi, Eeman na can da Mama Ladi. Eemaan na kitchen tana ta kokarin dafa ma ita da Mami Ladi irin shayin da taga Ihsaan na yi ma Ammi, tafi minti ashirin a kitchen din da ta fara dafa shayin in ta ɗanɗana sai taji yayi daci sosai, ta rasa me take sa wa yake sa shi ɗacin nan, daukan na hudun tayi zata zubar kenan aka bude kofar kitchen din, da sauri ta juya bayan sun hada ido, ta ajiye shayin hannunta ta kashe gas din ya kulle kofar kitchen din ya nufo ta. Ya tsaya dai dai kusa da ita yace "Have i turn to a ghost that you are running away from?" Ƙin dago kanta tayi, yace "Eeman" Ta wani kallesa da manyan idonta, sai kuma ta juya masa baya ta fashe da kuka ba hawaye, jawota yayi kusa da shi yace "To gaya min me na maki?" Bude kofar kitchen din aka yi ya saketa da sauri amma tuni Mama Ladi ta shigo, yi tayi kamar bata gansu ba tace "Usuman awa guda kenan yarinyar nan tace zata dafa mana irin shayin da ake yi ma Ammi, na ji shirun yayi yawa nace to Allah ya sa ba fasa tukunyar tayi ba" Usman bai yarda su hada ido da Mama Ladi ba don sarai yasan ta gansu, ya nufi inda Eeman ta ajiye shayin ya dau cokali ya debi shayin ya kai baki yaji daci kamar ta saka shuwaka, Mama Ladi tace "To bari in dauko kopi in zuba nawa bazan tsaya iskanci ba" Usman ya juya ya ɗan yi murmushi bai dai ce komai ba, Mama Ladi ta dauko cup da cokali ita ma sai da ta fara debo shayin ta kai baki sai kuma ta juya ta kalli Eeman, bayan ta hadiye da kyar tace "Tirr, yanzu uwar meye wannan kika dafa Eemani? Ke yanzu ba a wani abun arziki dake, babu abinda kika iya sai kawo tsegumi, ga er uwarki nan sai tayi girkin mudu biyu lafiya lau, komanta tsaf tsaf cikin nutsuwa gwanin ban sha'awa, aa gaskiya Ammi na da aiki a gabanta don babu shegen namijin da zai zauna dake a haka ki sa masa hawan jini wataran ya nakada maki shegen duka ya koro mana ke mu kuma saboda ƙin Allah muce bai kyauta ba bayan duk mun san halinki, haka dazu da safe nayi da na sanin ce maki ki gyara min daki, to yanzu kina nufin zubda wnn tsadadden shayin za ayi ko me? Ba fa sato kudi Mamuda yake ba, Bamu gama ji da barnatar mana da abinci da Mera ke yi a gidan nan ba kema gashi zaki barnatar da tsadadden shayi, da na sani Ihisani nasa bakina alekum wllhi, dama kar in ga kafarki a dakina na gaji dake kuma haka" Mama Ladi na kai wa nan ta fice daga kitchen din, Usman dai sai kallon Eeman da ta sunkuyar da kai yake, yayi kasa da murya yace "Yaushe za ki iya abun arziki a rayuwar ki Eeman? Just common tea ma baki iya dafawa ba" Ta wani turo baki zata fita daga kitchen din ya rikota ta fashe masa da kuka sosai, lallashinta ya shiga yi yana kallon fuskarta a hankali yace "Kyale Mama Ladi, ita ma tana kamar ki ba abinda ta iya sai hawa bishiya da debo ma mutane masaran da suka shuka a gonarsu" Eeman ta kyalkyale da dariya hawaye na zuba idonta tace "Ta yaya ka sani Yaya?" Usman na murmushi ya goge idonta yace "Yayarta Hajja ke bamu labari, in masu gonan suka biyota gida Hajja ta basu hakuri ta mayar masu da masaran su, ita kuma ta nakada mata duka" Ganin yanda Eeman ke babbaka dariya ya wani hade rai yace "Kee" Ta hadiye dariyar ta marairaice tace "To ba kai ne ka ban dariya ba" Yace "Yanzu ki tafasa min just ordinary water, sai ki saka

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login