Showing 432001 words to 435000 words out of 452169 words
Chapter 145 - Mayrah Complete By Khaleesat Haydar
madara da Milo, banda sugar, kin ji abinda nace?" Eeman na kallonsa tace "Na ji" Sau biyu yana repeating din kansa kafin ya juya ya fita daga kitchen din ya koma parlor ya zauna. 15 mins later Eeman na tsaye parlor da mop a hannunta ta gama goge shayin da ya fadi kasa garin kawo masa, takalmi ne a kafarta duk da ta share pieces din mug din da ya tarwatse a kasa kafin ta goge wajen, tana ta kallon Usman dake danna wayarsa, shi kam ko kallon inda take bai yi ba, a hankali tace "Yaya in hado maka wani shayin?" Wani kallo ya jefa mata, tayi shiru ta sunkuyar da kai, juyawa tayi ta maida mop din hannunta inda sauran suke sannan ta dawo parlon zata wuce sama, yace "Kee" Ta juya ta kallesa, Ledan dake dinning table ya nuna mata, tana tafiya a hankali ta dauko ledan har biyu ko wanne da gasasshen kaza a ciki, zata nufosa yace "Kar ki zo min nan, ki kai ma Mimi daya...." Kamar munafuka tace "Dayan nawa ne?" Hararanta yayi, ta sunkuyar da kanta ta wuce sama tana ɗan murmushi, sai da ta ajiye ledan nata kazan a daki sannan ta kai ma Mayraah nata, ta dawo dakin kenan ta bude kazar ta aka bude kofa, Tuni Eeman ta matsar da ledan zuwa daya side din gado ta kwanta ta lumshe ido kamar me bacci, Mama Ladi ta shigo dakin tana cewa "Eemani nace yau baza ki kwana dakina ba ne, ina ta jiranki tun dazu" Eeman taki bude ido, Mama Ladi sai bin dakin take da kallo jin kamshin kaza, Eeman ta mike zaune tana murza ido Mama Ladi tace "Har na gaji da jiran ki naga shiru baki shigo ba shine nace bari dai in duba ko lafiya" Kallon Ledan kazan Mama Ladi da ta zagayo zuwa daya side din gadon ta tsaya tana yi tace "Wannan fa?" Eeman ta ɗan yatsine fuska tace "Ya Usman ne ya kawo min ni bana so, maida masa zanyi" Mama Ladi tace "Ji banza, ki maida masa a saboda me" zaunawa Mama Ladi tayi ta jawo ledan, Eeman na washe baki ta dau cinyan kaza daya ta fara ci tace "Dama karya nake ba maidawa zan yi ba fa" Mama Ladi ta dau tsoka daya tana gyara zama ta kai baki tace "Atohh dai, ko uwaka ubanka kake da mutum don ya baka kaza ai baka ki amsa ba tunda ba rokonsa kayi ba, kin ma ciri tuta don ban taɓa ganin ya siya ma ko uwarsa kaza ba sai ke, da gani sulhu yake nema, kar ki kuskura ki sake masa fuska har sai ya sake siya maki wani kazar" Tas suka cinye kazar da Mama Ladi, Mama Ladi ta mike tana gwaguyen ƙashin kazan hannunta tace "Bari in dauko mana lemo me sanyi a firiji" Tana fita ko minti biyar ba ayi ba sai gata ta dawo ba lemun, ta jefar da sauran kazan hannunta ta zauna tana kallon kafarta cikin tashin hankali tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, wani shege tsinanne ya fasa kwalba na taka ya shige min kafa" Eeman ta fashe da wani mahaukacin dariya har da kwanciya tana kyakyatawa.
Washegari Saturday karfe goma Maheer ya shigo gidan, Ihsaan da ta gama sharan gidan gaba daya tayi mopping tana goge gogen kayan kallon ta juya tana kallonsa ta gaishesa, ya amsa yace "Sannu da aiki" Tayi murmushi ta ci gaba da abinda take, ya karaso ya zauna parlon yace "Mimi bacci take ko?" Ihsaan tace "Ehh bata tashi ba" Mama Ladi ce ta fito daga kitchen, ganin Maheer tace "Aa, yaushe ka shigo Mashir" Gaisheta yayi ta amsa ta zauna tace "Kai, wallahi Mendi yayi dacen mace, kafin mu tashi bacci fa yarinyar nan har ta mana kumallo, gashi ta gyara ko ina fes ta share sai kamshi ke tashi a gidan, kasan Balki tare suka tafi da Ammi za a ajiyeta garinsu wai uwarta ba lafiya, ina gaya maka Eemani na can cikin bargo, wallahi mijinta ya banu ya lalace kyau a bari sai tayi shekara talatin kafin a aurar da ita don banga zata yi hankali shekaru biyar kusa ba" Maheer dai danna wayarsa kawai yake yana murmushi, Mama Ladi tace "Gwara Mera za mu ce ba ita kadai bace shi sa take baccin asara yanzu, bata tabuka mana komai a gidan nan sai ci da bacci, tunda dai kafin tayi aure duk mun san tana da hazaka bata da son jiki shi sa abun bai dame mu ba, amma lamarin Eemani na ban tsoro, wllh Ammi na da aiki ja a gabanta, da za aji ta nawa ma kar Balki ta dawo gidan nan, Eemani ta amshi duk aikin Balki" Maheer was just pressing his phone bai ce komai ba, Ihsaan kuma tana ta goge gogenta ita ma, sai ga Usman ya shigo parlon, sai da ya fara gaida Maheer sannan ya kalli Ihsaan, gaishesa tayi ya amsa, Mama Ladi dama tun asuba da ta sauko hada shayin farko suka hadu ya gaisheta, yana kallon Ihsaan yace "Ba na hanaki aiki a gidan nan ba Ihsaan? Ina Eeman din" Mama Ladi tayi karaf tace "Bata tashi ba wallahi, tana can cikin bargo" Usman na kallon Ihsaan yace "Je ki taso ta" Ihsaan ta ajiye towel din hannunta ta wuce sama, Mama Ladi ta zauna tace "Ai dai aure Ihsanin zata yi ta bar ta, zan ga a wani gida zata dinga bacci har karfe goma, dama Balki an sallameta ba sai ta dawo mana ba" Tare Ihsaan da Eeman dake kumbure kumbure suka sauko kasa, taki yarda ta hada ido da kowa tana murza ido, Maheer na kallonta yace "Je booth din motata ki shigo da kayan ciki" Sai a sannan ta daga kai ta kalli Maheer ta gaishesa ya amsa sannan ta nufi kofa ta fita, Mama Ladi sai kallon Usman dake mata mugun kallo take tana ɗan murmushi tace "Kyau wataran ka tsutsula mata belet dinka, in ko baka yi haka ba bazata taɓa shiga taitayinta ba a gidan nan, kaga da haka er uwarta take sai muce ai an sangartasu ne dama, kai dai kawai ka bar yaro me son jiki, tsaf zai kunyata ka a idon duniya, to ga dai Eemani shimfidar gado ma bata iya ba" Eeman ta dinga shigo da shopping din da Maheer yayi a safiyar, Mama Ladi dai ba bakin magana, sai satan kallon kayan take, nan ta fara zargin to ko de Eeman ta fada ma Mera abubuwan da ta dinga fada ne jiya, sai da Eeman ta shigo da duk kayan, Maheer yace "Weldone" Ta ɗan yi murmushi zata wuce sama Usman ya mata wani tsawa, juyowa tayi kamar zata yi kuka tana kallonsa, yace "Put this at the back of ur brain, ke zaki yi girkin rana sannan kiyi na dare" Da sauri Mama Ladi ta mike tana girgiza hannu tace "Aa Usuman, gaskiya a'a, kar ma a fara, ba fa iya cin girkinta muke ba a gidan nan, so kake mu wuni da yunwa mu kwana da yunwa, ina laifin kace Ihsani ta yi mana namu girkin, ita Eemanin sai ta girka wanda kai da ita za ku ci, aa wallahi babu me tilasta mana mu ci girkin Eemani a gidan nan, kar ma a fara" Mama Ladi na kai wa nan ta wuce sama, Usman na kallon Eeman da har taji dadi a ranta yace "Ke zaki yi both Lunch and Dinner" Ta fashe da kuka tace "Ammi ce fa tace Ihsaan ta dinga girki ni in dinga sharara da goge goge" Tuni Usman ya fita daga parlon, Maheer dai murmushi kawai yake yana danna wayarsa, Ihsaan kuma ta ci gaba da abinda take, Eeman ta zauna bakin stairs tayi tagumi tana rusa kuka. Ammi na dawowa daga kano da kwana biyu Mayraah ta sa Maheer ya gaya mata zata koma gida, Ammi na zaune parlonta bayan magrib sai kallon Mama Ladi dake ta bayani take, Mama Ladi tace "Aa ba zancen ki dinga kallo na haka ba Ammi, wallahi in aka kuskura aka kai lefen yarinyar nan katsina kwashe mata kaya tsinannun dangin uban za su yi, mutanen da duk mun san ba tsoron Allah garesu ba, da wani idon za mu kalli pamilyn Alhaji Saminu in suka ga an kwashe kayan da suka kai?" Ammi tace "To ya kike so ayi Mama, can din ya kamata akai lefen don ta ko ina sun fi mu iko da yarinyar nan, in ma sun kwashe mata kaya su da Allah, kuma ai dangin MD din sun san inda suka kai lefe da kike cewa da wani idon za mu kallesu" Mama Ladi tayi tagumi tace "Ni dai na shiga uku ni Ladi, komai ace sun fi mu iko da yara, ta ina suka fi mu ikon nan ne wai tukun? shegun da suka kasa rike marayun yaran kuma ayi ta cewa sun fi mu iko" Maheer dake parlon yayi dariya shi dai bai ce komai ba, Mama Ladi ta juya ta kallesa tace "Kai kaji wani shashashan batu Mashir, mutanen da ba tsoron Allah garesu ba ayi ta wani mutunta su ana cewa sun fi mu iko da yara, ni dai wallahi basu fi ni iko da yan biyun nan ba" Maheer yace "To kawai abinda ya kamata ki shirya ki je katsinan a amshi lefen dake kawai Mama" Mama Ladi ta gyara zama tace "Haka kuma ya kamata ayi fa, ai dama ya kamata ace mutum daya yaje daga nan tunda wajenmu yaran nan suke, to a ina za ayi daurin aure da taron biki?" Ammi tace "Can katsina za ayi daurin auren, su yi taron su muyi namu a nan" Mama Ladi tace "Kuma mu dai ke da amarya a nan, yaushe naji Mamuda na cewa zata je katsinan?" Ammi tace "Cewa suka yi ba sai ta zo ba da ya sanar masu, wai sun ce hanya ba kyau" Mama Ladi ta saki salati tace "Ɗan abinda za su mata na aure fa suke gudu, yo Allah na tuba ko ni bazan mata kayan daki ba balle Mamuda, kai amma gaskiya ban taɓa ganin tsinannun mutane irin dangin uban yaran nan, wato basu da niyyar mata komai, to ni dai na hakura ma da zuwa amsan lefen, kada inje su bar ni da yunwa ni ba kowa gareni a katsina ba in shiga uku" Ammi tayi dariyar da bata yi niyya ba Maheer na taya ta, Mama Ladi ta mike ta nufi kofa tana cewa "Shi kuma Usuman ko budurwar gano mugayen halayyansa da yake ta boye mata tayi ne tace ta fasa auren, to ni dai har yau ban ji an sake zancen kai kudi ba, to dama ko alhakin Eemani ai ya isa yasa asirinsa ya tonu gun budurwar tasa, mutumi duk ya bi ya takura er mutane kullum sai ta zubda hawaye a gidan nan, in an bi ta a sannu in dai aiki ne ai duk zata iya wataran ba sai an dinga matsa mata ba, dama masu suna Hajara Allah na tuba ai duk an san halinsu ne wnn, sam basu da kwanturol" Maheer ya daga kai da sauri yana kallon Mama Ladi, ita dai Ammi murmushi kawai tayi, Mama Ladi dai ta fice ta bar masu parlon, bayan fitar Mama Ladi Ammi ta kalli Maheer don dazu taga yana ta kame kame yana son mata magana sai kuma Mama Ladi ta shigo, Ammi tace "Ko gida za ku koma tare da Mimin ne?" Ya daga kai ya kalli Ammi, yayi kasa da murya yace "Cewa tayi in maki magana zata koma gida saboda Mama Ladi" Ammi tayi murmushi don duk kwanan Drama suke da Mama Ladi don ma Mayraahn bata wani tanka ta, Ammi tace "Toh shikenan, yau din za ku tafi?" Yace "Eh" Ammi tace "To kayi mata magana ta fito ku tafi tana cikin daki" Mikewa yayi ya shiga dakin Ammi, Mayraah ta mike zaune tana kallonsa, ya mata murmushi yace "Nayi ma Ammi magana" A hankali Mayraah tace "Ka ce mata za mu tafi da Ihsaan?" Ya zauna gefenta yace "Aa ban gaya mata ba, ke dai ki gaya mata" Tare suka fito parlon, Mayraah ta zauna tana kallon Ammi a hankali tace "Ammi don Allah za mu je da Ihsaan" Ammi tace "Gyaran jiki za a fara yi mata ai Mimi, ko ku je da Eeman" Da sauri Mayraah tace "Aa Ammi" Ammi tayi dariya tace "Wai ya ake min kakkabi da 'ya ta ne" Mayraah ta marairaice tace "Ammi ai ko daga can za a dinga zuwa yi mata gyaran jikin" Ammi tayi murmushi tace "To ai ko ta bi ku ba dadewa fa zata yi ba Mimi, ko a samar maku me aiki?" Mayraah ta girgiza kai tace "Aa" Ammi tace "Toh shikenan, kiyi mata magana ta shirya sai ku tafi" Murmushi Mayraah tayi ta mike ta fita daga parlon don sanar ma Ihsaan ta hada kayanta, Mama Ladi ce ta shigo parlon Ammi da sauri tace "Ammi ke kika ce Ihsaani ta hada kaya ta bi Mera?" Ammi tace "Eh" Mama Ladi tace "To a gaskiya ki buga ma Balki waya duk inda take ma ta dawo, ubanwa zai dinga mana girki a gidan nan, ba dai Eemani ba dai ko? Yarinyar da ko shayi bata iya dafawa ba, shinkafan nan ɗan banza in ta dafa sai ya caɓe, To wallahi Buga ma Balki waya ta dawo babu me iyawa da girkin Eemani a gidan nan in dai ba zaman yunwa ake son mu fara a gidan Mamuda ba" Ammi dai bata ce ma Mama Ladi komai ba har ta fita daga parlon, a haka Mayraah suka bar gidan tare da Ihsaan....
Tun da Mayraah ta koma gidanta da Ihsaan ta lura gaba daya bata da walwala ko abincin kirki bata ci, tun ma daga gidan Ammi Mayraah ta lura da hakan, amma yanzu hakan yafi worst, it's just 2 weeks away from her wedding, ranan da daddare bayan Maheer yayi bacci Mayraah ta zame jikinta daga nasa ta sauka daga kan gadon ta dau hijab dinta ta saka a kan kayan baccin jikinta sannan ta nufi kofa ta bude a hankali ta fita, dakin da Ihsaan take ta tafi, zaune ta ganta saman gado ta hade kanta da gwiwa, tana jin an bude kofa ta dago kanta da sauri tana goge idonta, Mayraah ta karasa har kan gadon ta zauna tana kallonta, Ihsaan dai ta kasa kallonta, Mayraah tayi kasa da murya tace "Few days back na tambayeki meke damunki kika ce min ba komai Ihsaan, ko kina son komawa gidan Ammi ne?" Ihsaan ta girgiza kai hawaye na sauka idonta, Mayraah ta kamo hannunta tace "Then tell me what ur problem is, kwana biyu na lura kun dena waya da MD ko?" Ihsaan ta fashe mata da kuka, Mayraah tace "Did u have issue with him?" Girgiza mata kai Ihsaan tayi hawaye na sauka idonta, Mayraah tace "To me yasa ku ka dena waya?" Cikin rawan murya tace "Na kashe wayan" Mayraah ta jawota jikinta tana patting bayanta cikin kwantar da murya tace "Tell me what the problem is Ihsaan, take me as your big sis, in kuma baza ki gaya min ba gobe sai in sa Yaya ya kai mu gidan Ammi sai ki gaya mata ita" Ihsaan ta girgiza mata kai da sauri, Mayraah tace "Then tell me what is it" hawaye na sauka idonta a hankali tace "Ni tsoro nake ji" Mayraah tayi shiru jin abinda tace, can tayi murmushi ta dago kanta tace "Tsoron MD din?" Ihsaan ta fashe mata da sabon kuka ta gyada mata kai, sosai ta ba Mayraah dariya amma ta dake bata yi ba, ta rungumeta tana patting din bayanta tana murmushi, gaba daya ta ma rasa me zata ce mata.
Mayraah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
139
Maheer ya bude kofar ward din a hankali ya shiga ciki ya kulle, yana tafiya slowly ya nufi inda take kwance bayan ta bude idonta dake rufe tana kallonsa, dukawa yayi ya kamo hannunta yana kallon idonta da suka kumbura, gently ya goge mata hawayen da ya gangaro gefen idonta ya hada goshinsa da nata, yayi kasa da murya yace "Weldone Wife, may Allah S.W.T bless you" Ita dai kallonsa kawai take har sannan hawaye na bin gefen idonta, ya lumshe ido yayi kissing dinta, yace "Hope you are fine?" Da kyar ta gyada masa kai har sannan hawaye bai dena bin gefen idonta ba, ya sake kissing dinta yana share mata hawayen idonta yace "Billah i love you so much Mayraah, thank you for making me a father, today is one of my happiest day in life, Allah ya maki albarka wife" Mikewa yayi ta dalilin bude kofa da aka yi, wata nurse ta shigo ward din ta karaso har inda suke, Maheer ya amshi babyn hannunta yana kallon fuskar babyn, Nurse din ta kalli Mayraah da murmushi fuskarta tace "Congratulations Madam, Allah ubangiji ya raya, Allah ya baki lafiyar shayarwa" Daga haka ta juya ta fita daga ward din, Maheer ya duka ya dora ma Mayraah babyn a jikinta ta sauke idonta tana kallon kyakkyawan Babyn dake ta mutsu mutsu da baki, ganin taki rungume babyn yayi kasa da murya yace "Common Mimi, hold ur bundle of joy, let him feel ur warmth" Rungume Babyn tayi a jikinta ta lumshe ido wasu hawayen suka zubo idonta, shi dai kallonta kawai yake yana murmushi, bude ward din aka sake yi Mama Ladi ta shigo Ammi na biye da ita a baya rike da basket na kayan shayi da flask da cup, Mama Ladi ta saki salati tace "Kai jama'a... yanzu salon ma'aikatan asibitin su yi mata kallon bata da kowa yasa ka kawota asibiti tun jiya tana nakuda ita kadai baka sanar mana ba Mashir? Yaushe zaka fara yin abu irin na magidanta ne fisabilillahi gashi har an haifa maka yara uku biyu suna lahira, kai kanka kasan nas nas da gulman jaraba kamar don su aka halitto gulma, yanzu haka nasan duk asibitin