Showing 435001 words to 438000 words out of 452169 words
Chapter 146 - Mayrah Complete By Khaleesat Haydar
ya dauka an kawota tun jiya da safe gashi har yau da maraice ba a ga kowa nata a tare da ita ba, wannan tozarci har ina Mashir" Shi dai Maheer bai ma kalleta ba balle ta sa ran zai tanka ta, Tuni Ammi ta karasa kusa da gadon da Mayraah take ta duka tana kallonta da babyn kusa da ita, she couldn't hide the joy on her face, tana girgiza kai trying not to shed tears amma hakan bai yiwu ba don sai da hawayen ya zuba idonta tace "Sannu Mimi, sannu daughter..." Mayraah ta ɗan yi murmushi kawai tana kallonta, Ammi ta dau Babyn jikinta tana kallo babu ko kiftawa, he was soo cute kamar ɗan larabawa jazir da shi, shi din ma dai yanayi yake da Maheer, Mama Ladi tayi maza ta amshesa jaririn daga hannun Ammi tace "Allahuuu Akbarrr, Allah mun gode maka da wannan ni'imar da ka mana, mace ce ko namiji?" Maheer yace "Namiji" Mama Ladi tace "Iko sai Allah, wannan balarabe kuma daga ina ni Ladidi, dama jarirai na da mikakken hanci? Iko sai Allah, ku ga ɗa kamar ɗan larabawan gaske, gashi sai da ya riƙa yayi bul bul a ciki aka haifosa tabarakallah maa sha Allah, kuma da kanta ta haifosa, Lalle Mera jaruma ce, ga dai rabin fuskar na uwar, rabi kuma sak na uban" Sai da Maheer ya kalleta, sai kace wani alien wai rabin fuska na uwa rabi kuma na uba, wannan wace irin mata ce, Ammi dai ta duka kusa da Mayraah ta kamo hannunta tana mata sannu, Duk ƙara da kawaici irin na Maheer haka ya nufi inda Ammi ta ajiye basket din da ta shigo da, ya bude flask din zai fara hada ma Mayraah shayi, Ammi na ganin haka ta mike amshi cup din a hannunsa, tsabar farin ciki da murna ta mance da batun kayan shayin, tana hada ma Mayraah shayin tayi masa barka, yayi kasa da kai yace "Ameen" Mama Ladi dai sai kallon jaririn take tsabar kyau kamar shi ya halitto kansa, anya ta taɓa ganin jariri me kyau haka ma kuwa, can tace "Ashe dai kwanaki jagwal aka haifo mana muke ta rawan jiki kamar tarwada, Ga dai jariri kamar daga tsatson larabawa ni ko sai kallonsa nake kamar na samu hoto, to uwa kyau uba kyau, kakanninsu ta wajen uwa da uba su ma kyau kamar su suka yo kansa, kunga kuwa ai dole a haiho balarabe, Allah sarki Badiyyah mijin dai na can kamar gwaggwon biri, ko me zata haifo" Sai da Ammi tayi stiff jin abinda Mama Ladi tace, can dai jiki a sanyaye ta gama hada ma Mayraah shayin yana tiriri ta mika mata, Mayraah ta amsa a hankali, Maheer ya fita daga ward din ganin Abba na kiransa yasan ya karaso asibitin ne.
Bayan isha Ammi ta kamo hannun Mayraah ta sauko daga kan gado a hankali ta saka takalmanta, Ammi ta mika mata hijab din da zata saka don an sallamesu, Abba ya nufi kofar ward din yana rungume da jaririn ya fita looking so happy, the happiness he felt holding Maheer as a new born was exactly how he is feeling today holding Maheer's son, tun da suka shigo dazu tare da Usman har aka yi discharging Mayraah suna nan asibitin, Maheer ya dau basket din kayan shayi zai fita Mama Ladi tace "Ai kyau ace duk inda mutum zai je kar ya kuskura ya bar abun magana ko abun kunya, don wannan abun magana ne Mashir ya bar ma Mera a asibitin nan, tana fara nakuda zai kawota asibiti sai yayi sauri ya bugo min waya, in ma bai bugo min ba ya bugo ma uwarsa ya sanar mata mu bar duk abinda muke mu gudo asibitin, amma sam Mashir bai yi haka ba, ya kawo er mutane kawai ita kadai tun jiya da rana har yau da maraice" Usman dake kallonta don tayi maganar nan yafi sau biyar tun shigowansa ward din da Abba, zata ci gaba da magana ya katse ta yace "To wai ko an kira an gaya maki me za ki zo kiyi a asibitin banda labari kamar yanda kike yi yanzu Mama? ai ba ko wani asibiti bane suke yarda ai masu gayya a zo a cika masu waje da surutu, ba asibitin gwamnati bane nan din, sannan duk wani me kula da ita naga ai a bayan mijinta yake, da ba don nan yake aiki ba ma baza a bari ki shigo ba...." Ammi dai gyara ma Mayraah Hijab dinta kawai take, Usman ya mike ya bi bayan Maheer ya fice daga ward din, Mama Ladi da ta kasa tashi daga kan kujeran da take zaune ta kalli Ammi a hankali tace "Kin ga dai ban yi da yaron nan Usuman ba amma babu abinda ya mance bai gaya min ba a nan" Sai kuma ta fara matsar kwalla tana gogewa da gyalenta tace "Yau da dashi nake abun bazai min ciwo ba, shi Mashir din bai da baki ne? Da yake yaron arziki ne yaron kirki me ladabi da biyayya da girmama manya kinga ai tun dazu da nake ta mitata bai tanka ni ba tsabar yanda ya koshi da tarbiya, me nayi ma Usuman ya zage ni haka? Daga dai na nuna bakin cikina ba a kira mu mun zo asibiti mu taya Mera da addu'a ba tana nakuda" Ammi ta kalleta tace "Don Allah ki taso mu tafi Mama kiyi hakuri ki rabu da Usman..." Mikewa Mama Ladi tayi tana share hawaye ta bi su suka fita daga ward din.
Gata kam babu irin wanda Mayraah bata gani ba ta ko wani Angle, washegarin ranan da ta haihu Grandma dinta ta kamo hanyar Abuja, Aunty Mariya ma haka, she felt soo love ta ko ina, ranan da Grandma dinta ta iso tana zaune daki da yamma Ummin Zainab na shirya Baby bayan ta gama masa wanka Bilkisu ta shigo dakin da sallama tana rike da wayar Maheer ta mika mata tace "Wai gashi za ayi maki magana Maman Baby" Mayraah ta amshi wayar tana duba screen din, bude ido tayi ganin video call ne, sai kuma ta sunkuyar da kanta tana murmushi, muryar Ihsaan taji tana cewa "Aunty Mimi Congratulations" Mayraah ta daga ido tana kallon Screen din wayar hannunta, taga Ihsaan a bayan kujeran da MD ke zaune tana waving mata hannu tana murmushi, sosai tayi wani kyau ta cicciko kamar ba ita ba, Mayraah na murmushi tace "Hi Ihsaan ya kike" Ihsaan na murmushin ita ma tace "Lafiya lau Aunty, ya baby?" Mayraah ta haska mata babyn don Ummin Zainab ta gama shirya sa ta kwantar da shi, Ihsaan tace "Waow, he is so cute Aunty, plss peck him on the lips for me" Ita dai Mayraah murmushi kawai take, kuma ko da wasa taki yarda ta hada ido da MD dake kallonta yana murmushi, mikewa yayi ya bar kusa da Ihsaan da ta cika masa kunne lamenting how handsome the baby was, yana kallon Mayraah yace "Congratulations matar Yaya" Mayraah ta ɗan kallesa ta rufe ido da hannunta still smiling, yace "Hope you are doing fine?" Ta zame hannunta ta gyada masa kai a hankali tace "Alhamdulillah, how is Canada?" Yace "Cool Mimi, in sha Allah in few days time za mu shigo Nigeria" Mayraah tace "Toh Allah ya kai mu" Yayi er dariya yace "Sai ga Mimi da Babyn Yaya... Mimi gave birth to Lil Maheer" Mayraah ta wani turo baki tana masa wani kallo, yana dariya yace "Bye Dear, take good care of ur self, Allah ya kara lafiyar shayarwa" A hankali tace "Ameen Nagode sosai, Allah ya dawo da ku lafiya" Daga haka suka yi sallama ta ajiye wayar, Mayraah ta juya ta kalli little Baby dinta dake bacci, har ranta take jin babyn, ko gajiya da kallonsa bata yi, ganin su biyu ne kawai a dakin ta duka giving him a kiss on his soft cheek, bude kofar dakin aka yi ta mike zaune da sauri, Maheer ne ya shigo dakin, tun safe rabon da ta gansa, ta dinga kallonsa har ya karaso cikin dakin, ya isa har gabanta ya duka, kissing her forehead yace "How are you wife?" Ta gyada masa kai tana murmushi tace "I'm fine...." Ya duka ya dau babyn yana kallonsa, sai kuma ya kalleta yace "I'm still yet to figure out wanda babyn ke kama da" Mayraah ta nuna masa kanta, Yana murmushi ya zauna kan kujera yana facing dinta, tun dazu yake son magana da ita amma sbda mutane bai samu daman hakan ba, a hankali yace "Na baki zabin sunan babyn, wani suna kike son ayi masa huduba da?" Mayraah tayi shiru tana kallonsa, lkci daya wasu memory suka dinga dawo mata, after some seconds ta sunkuyar da kanta, cikin sanyin murya tace "Are.... you, okay with Musharraf?" Maheer ya dinga kallonta, bata iya ta hada ido da shi ba, after a while yayi kasa da murya yace "Why not Mimi, in har haka kike so, so be it in sha Allah" Ta daga kai ta kallesa, hawaye ya gani idonta, ya mike ya dawo inda take ya kwantar da Babyn hannunsa sannan ya zauna kusa da ita da damuwa yace "Is there any other thing apart from this Wife?" Ta girgiza masa kai, yayi mata side hug yana goge mata hawayen idonta a hankali. Ana saura kwana biyu suna Mom din Mayraah da Dad dinta suka iso Nigeria da 1 year old twins siblings dinta, that same day Hajja da Yahanasu suka shigo daga Kaduna, sannan Omar ma ya sauka garin Abuja. Bayan magrib Mayraah na zaune tana cin tuwon da aka yi mata da assorted vegetable soup, Mama Ladi kuma na zaune ta daura kafa daya kan daya ga jariri tana gasa masa cibiya da wutan garwashin dake gabanta, gaba daya Mayraah ta kasa concentrating kan abincin da take ci don duk hankalinta na kan abinda Mama Ladi ke yi ma Babynta, gashi attention dinta sam baya ma kan abinda take labari kawai take ba matar abokin Abba da ta zo barka kai sai ka rantse ta taɓa sanin matar, su uku kadai ne a dakin, aka bude kofa, Mayraah ta daga kai tana kallon warce ta shigo, Mama Ladi ta ajiye towel din hannunta ta matsar da garwashin gabanta tace "Wacece wannan kuma ta afko mana cikin daki?" Sai a sannan Mayraah ta gane Badiyyah ce ta shigo, don kwata kwata bata ganeta ba da farko, salati Mama Ladi ta saki bayan ita ma ta gano ta, Badiyyah ta karaso cikin dakin ta zauna kan carpet tana gaida Mama Ladi, Mama Ladi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, Badiyyah?" Badiyya na murmushi tace "Ina wuni Mama" Mama Ladi ta ɗan saci kallon matar abokin Abba, sai kuma tace "Lafiya lau" Mama Ladi bata sake cewa komai ba daga haka, Badiyyah na kallon Mayraah tace "Barka Mayraah, Allah Ubangiji ya raya Baby" Mayraah da duk jikinta yayi sanyi, a hankali tace "Sannu da zuwa sis Badiyyah" Badiyyah na kallon saman gadon tace "Ina Babyn?" Mama Ladi ta mika mata jaririn hannunta, Badiyyah ta amshi yaron tana kallonsa tana murmushi, mikewa Matar abokin Abba tayi tace "Bari in koma can daya parlon Mama" Mama Ladi tace "Toh shikenan, su Ammin ma ai suna can tun dazu" Matar na fita Mama Ladi ta sake kallon Badiyyah da sauri ta gwalo ido tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Badiyyah baki da lafiya ne? Meye haka ya sameki?" Murmushi kawai Badiyyah take tace "Lafiyata lau Mama" Ammi ce ta shigo dakin don ita ma tunda taga Badiyyah hankalinta ya tashi sosai, sai ga Usman ya shigo shi ma he was so shock at how he saw Badiyyah don shi ma bai ganeta ba da ta shigo at first, Ammi ta karaso ciki tana kallon Badiyyah ta zauna gefen gado tace "Baki da lafiya ne Badiyyah?" Badiyyah ta sauke idonta bata ce komai ba, bayan few seconds ta dago kanta, sai ga hawaye na sauka idonta, shi dai Usman na tsaye bai ma karaso inda suke ba, Mama Ladi ta fashe da kuka tace "Yanzu shikenan don kaddarar rayuwa ta fada ma yarinyar nan sai duk a hadu a gujeta babu wanda ya damu da yasan halin da take ciki a gidan miji, babu me zuwa inda take duk an watsar da lamarinta? marigayiyar uwarta fa er uwar ku ce uwa daya uba daya, shkkn don bata da rai sai er ta ta tagayyara?" Ammi dai ta kasa cewa komai, sosai jikinta yayi sanyi, Badiyyah ta share hawayen dake ta zuba idonta, Mama Ladi na kallonta tace "Matansa nawa mijin naki ne wai?" A hankali Badiyyah tace "Yace min daya, ashe su biyu ne, kwanan nan kuma ya kara wani auren" Mama Ladi tace "Kunji gwaggwon birin banza ko? Ke a ina ma kika samo mummunan halitta irin wannan Badiyyah, anya ma musulmi ne?" Wasu hawayen suka zubo idon Badiyyah a hankali tace "Ashe tsibbu yake bai gaya min ba, ce min yayi Malamin addini ne shi ashe ba haka bane" Mama Ladi tace "Kun ji shege ko, Malamin addinin kafurci yake nufi, ni dama tunda na gansa lkcn bikin na sha jinin jikina da shi, mutum kamar wanda baya alwala kafafuwansa duk wasu lafiyayyun kanta duk sun lalace kamar na kafirin dake zuwa gona, kuma shine har yanzu kike zaune da shi ki ci uban me da shi?" Ta fashe da kuka tace "Yace bazai taɓa saki na ba, gashi matansa gallaza min suke, duk ni ke komai a gidan, har duka sun taɓa yi min kuma ya goyi bayansu, ga girki da itacen da nake yi kullum safe, rana da dare, kullum sai nayi surfe, sannan ga su da manyan yara duk sun raina ni, har karuwa suke ce min, kayan da aka min duk sun sace bani da komai a daki yanzu, dama yace bazan haihu ba don yaransa ashirin da shidda, magani yayi ta ban ina sha har na wata daya daga baya yace min aikin yayi, bazan haihu ba...." Mama Ladi ta daura hannu biyu a ka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, shikenan ya cuce ki ya lalata maki mahaifa, yanzu Badiyyah gidan na ubanki ne da baza ki gudo ki bar masu ba? Shkkn ya cuceki" Badiyyah na kuka a hankali tace "Ko nace zan gudu sai inji bazan iya fita daga gidan ba Mama, na sha hada kayana amma sai in kasa fita, kawai sai dai in mayar cikin sif" Mama Ladi tace "Yau nake ganin abinda ya isheni ni Ladi, dama har yanzu akwai sauran tsinannu a duniya? kafe ki fa yayi a gidan da tsafi ta yanda baza ki ji sha'awar fita ba, to garin yaya ya bari kika taho nan yanzu?" Badiyyah tace "Tun da aka yi haihuwan na sanar masa yace bazan je ba, ina ta rokonsa nace kwana biyu kawai zan yi, shine yace sai dai in san yanda zanyi don bai da kudin motar da zai bani, da ya ce haka sai na siyar da akwatuna na shine na samu kudin motar, ya kuma ce kwana daya kawai zanyi" Mama Ladi tace "Zai ci kaza kazan sa kuwa, sai dai ya saka uwarsa a dakin naki amma wallahi baza ki koma gidan nan ba, yo ba gwara gidan gyaran hali ba, kaji min shege arne, mu dau yarinya fara kal mu basa ya maido mana da duna? To wallahi baza ki koma ba, ai kin gama wannan kadararren auren yau, kotu kawai za mu maka Bokan, ai kyan mutumin nan Hasinu" Ita dai Badiyyah hawaye kawai take, Usman ya juya ya fita daga dakin, Ammi was speechless, sosai jikinta yayi sanyi, haka Mayraah da ta kasa cin abincin gabanta.....
Ranan suna da yamma Mayraah ta gama canza kayanta for the countless time, daurewa kawai take don zuwa lkcn ta gaji sosai, sanye take cikin wani tsadadden lace tana tsaye gaban madubi, mai make up ta gama daura mata dankwalinta, sosai tayi kyau kamar wata sabuwar amarya, Maheer ya shigo dakin don Aunty Mariya ya tambaya inda take ta gaya masa, kallonsa kawai Mayraah take kamar yanda shi ma yake kallonta, tun safe bata sake ganinsa ba sai yanzu, Mai make up din ta fita ta bar masu dakin, ya karasa har inda take tsaye ya rungumeta sosai, ta kwantar da kanta kirjinsa ta lumshe ido tana shakan daddadan kamshinsa, juyata yayi leaning his head on her shoulder yana kallonta ta madubi a hankali yace "You look cute Maman Baby" Ta madubin take kallonsa, ya sauke idonsa a hankali yace "Za ku gaisa da wani frnd dina, meet me outside" Tace "Ohk dear" Sai da ya fita dakin sannan ta dau gyalenta ta bi bayansa, har a lkcn gidan cike yake da jama'a, kaf family din dad dinta babu wanda bai zo sunan nan ba, tun safe Mami da matar Musharraf da Ihsaan suka zo gidan, a safiyar ranan Ihsaan suka sauka Nigeria da MD, A haka Mayraah ta fito compound duk ana bin ta da kallo, duban inda zata ga Maheer take a compound din, ta gansa tsaye tare da Umar ta nufe su, Maheer dake jingine jikin wata mota ya dinga kallonta har ta iso inda suke tana ɗan murmushi, tahowa yayi dab da ita ya kamo hannunta a hankali ya saka mata makullin hannunsa yana kallon kwayar idonta yayi kasa da murya yace "Just a little token for you soulmate, thanks for making me a Dad" Umar dai murmushi kawai yake yana kallonsu, Mayraah was speechless and stunned at the same time, it was something she never saw coming, ta juya ta kalli tsadadden dalleliyar sabuwar motar dake parking space, bata san sanda ta rungumesa ba, nan da nan hawaye ya kawo idonta, dai dai nan Musharraf da MD suka shigo compound din.
Mayraah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
140
Aunty Mariya ta daga kai tana kallon Ammi bayan Mama Ladi ta fita tace "Kuma gaskiya Mama ke fada Ammi...." Kawai ganin Mama Ladi suka yi ta shigo parlon, ashe makalewa tayi bayan