Showing 438001 words to 441000 words out of 452169 words

Chapter 147 - Mayrah Complete By Khaleesat Haydar

ta fita taji abinda za su ce, duk suka daga kai suna kallonta Mama Ladi tace "Toh ma in ba rashin nutsuwa irin naku ba ai da kun zauna kun nutsu za ku ga dacewar hakan, to babu me gaya maku gaskiya banda ni, ita Hajja ko watse taron suna ba ayi ba ta tattara ta tafi, ban san menene tsakaninta da Mamuda ba banda haka ai yanzu an dena wnn sukurtakan kauyancin, yanzu yarinyar nan Mera surkarki ce ko kin ki ko kin so, kuma tana da dangin ubanta kaca kaca a duk Najeriya, sannan ga uwarta ma a raye, hakuri za ki yi ki ajiye batun ke kika riketa tun tana tsumma ki dena bake bake kan lamarinta, tunda aka watse taron suna lafiya bayan kwana biyu ko ni da Mashir din sai mu kai masu ita kaduna har bayan arba'in, amma bakya riketa a nan kice tayi jego ba, tayi laulayi a gidanki tayi jego a gidanki bayan ga dangin ubanta na kusa ai abun ya zama son kai, suma ai za su so ta kusanto su, banda ma kun aurar da ita da wuri ai da yanzu duk ta saba da yan uwanta, pamilyn ubanta fa pamily ne babba ba irin namu kirgaggu ba, ita Mariya ba haihuwa ta taɓa ba balle tasan yanda ake yi ta dinga nusar dake" Ammi tace "To shikenan Mama, idan Abban nasu ya shigo zan sanar masa" Mama Ladi tace "To ya dai fi, wani abun ya kamata ki zauna ki nutsu ki san abinda ya kamata ba sai ana nusar da ke ba, ga dai jikoki an fara ajiye maki, ni ba ma sai naje ba ko Mariya sai su kai ta da Mashir din don ban cika son gantali ba gaskiya yanzu" Daga haka ta nufi kofa, har ta fita sai ta kuma dawowa tace "Wai ni ita Eemani yaushe zata dawo ne, abu kusan wata daya fa yau, tun da suka kyallara ido suka ga dayar ta samu daukaka gata can a Canada da lafiyayyen mijinta shine suke kokarin shige ma yaran kuma yanzu, har da wani bugo waya a turo Eemani za su yi biki a pamily, kun ga kenan sun ga yaran za su daukaka a duniya bari su lallaba su shige jikinsu, ta yanda in Ihisaani ta haihu sai ace za a biya ma daya a cikinsu tikitin jirgi yaje wajenta, to uban kuturu ma yayi kadan balle na makaho, Allah ne sanadin auren Ihisani da Mendi ni ce sanadi, don ba uban wani ya cusa min ita ba, banda kokari na yaushe Mendi zai wani lura da ita? don haka me zuwa Canada in Ihisani ta haihu a bayana yake wallahi" Daga Ammi har Aunty Mariya kallon Mama Ladi suke, Aunty Mariya na murmushi tace "Amma mu ai haka muke so Mama, ko ba komai za su nuna su su ce dangin ubansu ne, su kuma suce 'ya yansu ne, mu kam haka muka fi so don duk inda za aje a dawo sune dai gatansu, kuma da da matsala in dai Eeman ce tuni zata dawo" Mama Ladi tace "Ki iya bakin ki Mariya, Mamuda ne gatansu sai ni, sai Ammi" Mama Ladi bata jira cewar Aunty Mariya ba ta fice daga parlon, Aunty Mariya ta kalli Ammi, after some seconds Ammi tace "In sha Allahu zuwa Jibi sai ku kai ta kadunan, tun da kinga mahaifiyarta ma na nan kuma tace min za su yi sati hudu nan gaba kafin su koma" Aunty Mariya tace "Toh Allah ya kai mu jibin" Ammi tace "Ameen" Sosai Mayraah taji dadi har ranta bayan Ammi ta sanar mata zata je kaduna gobe, Aunty Mariya ce ta hada mata kayanta da na baby, da duk wani abu da zata bukata... Ammi na zaune dakin Mama Ladi dake ta linke kayan da Bilkisu ta wanke mata, Mama Ladi na girgiza kai tace "Inaaaa, sam bazan iya gantali ba gaskiya, naga dai ita ma Mariyan ai ba yarinya bace, ko kuma ki yi ma kawarki lauya magana, don dai yini daya ta temaka taje ta mika maki Mera gun dangin ubanta ta dawo ai bazata ce a'a ba tunda ba miji gareta ba, sai su je da Mariyan da Mashir" Ammi tace "Toh amma me yasa baza ki ba Mama Ladi" Mama Ladi tace "Bazan fa je ba, ni ba er iska bace, ko wani tsohuwa na killace gu daya banda Ladi, an maida ni gantalalliyar karfi da yaji bana nan bana can" Linke kayan karshe ta saka a akwatinta ta fita ta bar Ammi a dakin. Wajen karfe tara na dare Maheer ya shigo dakin da Mayraah take tare da Babynta, ya gaida Aunty Mariya dake zaune dakin ta amsa tace "Duk yau shiru baka shigo ba Dr" yana ɗan murmushi yace "Eh na ɗan yi busy ne Aunty" Aunty Mariya ta mike ta fita daga dakin, Mayraah dai kallon Maheer kawai take, ya sakar mata murmushi ya karasa inda take yace "Hello mai jego...." Ya kamo hannunta yace "How are you wife?" Kwace hannunta tayi tace "Shi ne baka zo da safe ba ko..." Zaunawa yayi yana facing dinta yace "I'm so tired Mimi, kuma kin ga naje aiki" Tace "Ohk" Ya kalli Babyn dake bacci ya daukosa ya gyara masa hularsa yana kallonsa, kamar yanda Mayraah ke kallonsa, yana daga kai suka hada ido ya ja hancinta yace "Why are you staring at me that way?" Tayi murmushi tace "Why are you staring at my Baby that way too" Yana murmushi yace "Gaskiya kam Babynki" Tace "Do you have a nickname for him?" Yana kallonta yace "Ke dai da kika sa masa suna za ki nemo nickname, i tot Musharaff din ma zaki dinga kiransa ae" Mayraah dai kallonsa kawai take, ya dau wayarsa dake ringing, Mayraah na kallon screen din taga Abba ke kiransa, ya kwantar da Babyn hannunsa yace "Abba na jirana dear, zan je parlonsa in samesa.." Daga haka ya mike ya fita daga parlon. Washegari Sunday da safe Mama Ladi da Aunty Mariya suka tafi raka Mayraah da babynta kaduna, Maheer ne yayi driving dinsu har can, Hajiya Ramatu tayi farin ciki da zuwansu duk da Ammi ta sanar mata tun kan su taso, dakin dake kusa da na Hajiya Ramatu aka gyara ma Mayraah da Babynta, bayan Azahar Maheer ya kai Aunty Mariya gidanta yayi dropping dinta sannan ya dawo daukan Mama Ladi su koma Abuja, da mamaki Hajiya Ramatu ke kallon Mama Ladi da ta sakale tsadadden jakarta ta gyara yafin mayafinta tace "Dama baza ki kwana biyu ba Hajiya Ladi?" Mama Ladi na girgiza kai tace "Aa tafiya zan yi Hajiya, Mamuda ne ma yayi min magana naji nauyinsa shine nace to bari in rakota, banda haka ai har yanzu gajiyar suna bai gama bin lafiya ba, yanzu haka duk kasusuwa na nukurkusa suke" Hajiya Ramatu tace "To amma ki tsaya ku gaisa da Alhaji sun kusa gida yanzu haka daga airport, yau ya dawo kasar" Mama Ladi zata yi magana sai ga Alhaji Saminu ya shigo parlon da sallama, nan suka gaisa da Mama Ladi, sai ga Maheer ya shigo har parlon don gaida Alhaji Saminu duk da sun hadu a waje, Alhaji Saminu ya amsa da fara'a sosai, Hajiya Ramatu tace "Za su koma Abujan ne" Alhaji Saminu yace "Duk a yau din, toh maa sha Allah, Allah ya tsare hanya...." Hannu ya saka a aljihunsa ya ciro bandir din dubu daddaya ya ba Hajiya Ramatu yace "A ba Hajiya ta sha ruwa a hanya" Ya sake saka hannu a aljihu ya ciro wani bandir din ya mika ma Maheer yace "Ka kara mai" Maheer dai yayi kasa da kai, Alhaji Saminu yace "Amsa mana, fetur nace ka kara a hanya" Maheer ya amshi kudin yana masa godiya, sai da Mama Ladi tayi kame kamenta sannan ta amsa kudin da Hajiya Ramatu ke hada ta da Allah ta amsa, Mama Ladi tace "To Allah Ubangiji ya sa a fi haka" A haka suka bar gidan da Maheer, sai da suka dau hanya Mama Ladi ta ciro rafan kudin a jakarta ta fara kirgawa, shi dai Maheer kallonta yake ta madubi yana driving, ta gama kirga kudin ta mayar cikin jaka tace "Dama nasan dubu dari ce, daga haka kyautarsa ke farawa bai bada kasa da haka, toh shi dai ya sani, ni dai ba saboda Allah na kai masa jikarsa ba" Murmushi kawai Maheer yake bai ce mata komai ba. Days went by, Then weeks, sosai Mayraah ta samu kula gidan kakanninta, tayi jego cikin gata da tarairaya, just 5 weeks da tayi tana jego a gidan tayi wani kyau ta murmure ta dawo kamar ba ita ba, Shi kansa babynta da suke kira Aryaan yayi wayo kamar ɗan wata biyu, duk bayan kwana biyu Mom dinta ke zuwa gidan da twins dinta, a can Abuja kuwa kusan kullum Ammi ke kiran Mayraah to check on her and the Baby, haka ma Abba da kan kirata time to time, a sati hudun nan sau biyu Maheer ya zo kadunan to check on her and Aryaan, kuma siyayya sosai yake masu idan zai je, sai da suka cika 6 weeks Aunty Halima ta dage ma Mayraah da gyaran ciki da waje don Hajiya Ramatu tace next week zata koma dakinta don har ta wuce 40 days, duk wani abu da ya kamata sai da aka ma Mayraah na gyara, ana gobe Mayraah zata koma Abuja Mom dinta da Dad suka koma US, Washegari Sunday Aunty Halima da Cousin sis dinsu suka raka Mayraah Abuja, tun ana saura kwana biyu su maida ta aka sanar ma Ammi. Bayan tafiyar su Aunty Halima don ko awa daya basu yi gidan ba suka juya don drivern Alhaji Saminu ne ya kawosu, Ammi da Mama Ladi na zaune parlorn downstairs, Ammi na rike da Aryaan dake ta mata dariya kamar ya san ta, duk inda Mayraah tayi idon Mama Ladi na kanta, yanzun ma da ido ta bi ta har ta nufi kitchen zata je dauko ruwan babynta, Mama Ladi ta kalli Ammi ta rike haɓa tace "Ke kiji yarinya ta zama mace, kamar dai ba Mera figaggiya ba, iko sai Allah, mata ta cicciko abunta tayi bul bul sai juya mana baya take, kana ganinta kasan dadi kan dadi akayi ta loda mata gidan kakannin nata, shi kan sa yaron dubesa tabarakallah ya zama bukeke, gaskiya nononta me kyau ne" Mama Ladi ta kyabe baki ta mike ganin Ammi ba tanka ta zata yi ba ta wuce sama, dakin Eeman ta tafi ta sameta kwance idonta a rufe, Mama Ladi tace "Kin hakura da kukan kenan, to tsoro nake kar in tofa nawa cibi ya zama ƙari" Juyawa tayi ta fita ta kullo mata dakin tayi kasa da murya tana tafiya tana cewa "To ina dadi er uwarta na Canada ita ace tana Najeriya, ba sai a rabu da ita ba, har dae ita ma Allah ya bayyana mata wani dake rayuwa ƙasar waje tunda ba mummuna bace ita har ta ma so tafi er uwar kyau, kawai ana nema ayi ma yarinya dole, ni dai ba ruwana...." Bayan Isha Maheer ya zo gidan, yana zaune parlon Ammi bayan ya gaishesu ita da Mama Ladi, Ammi ta kira Mayraah dake dakinta, Mayraah ta fito ganin Maheer ta gaishesa ya amsa, Ammi tace "Dare yayi ki daukosa ku tafi gida" Mayraah tayi shiru tana kallon Ammi don ta zata a gidan za su kwana, Mama Ladi tace "Jiya Balki da Eemani suka je suka kalkale maki gidan suka goge ko ina suka wanke maki bandakunan gidan, har zanin gado sun shimfida maki a daki, babu abinda zaki yi idan kun je" Juyawa Mayraah tayi a hankali ta koma dakin Ammi ta dauko Aryaan dake bacci ta fito, Bilkisu ce ta kai masu kayansu booth din motar Maheer, Ammi na kallon Mayraah tace "Baya tashin dare ai ko?" Mayraah ta gyada mata kai tace "Baya tashi" Mama Ladi tace "To sun dai koya maki yanda zaki masa wanka dai ko, kar ki je ki halaka ɗan mutane da sabulu" Ammi ta kalli Mama Ladi tace "Sai kace ba nurse ba Mama" Mama Ladi tace "Atoh, gwara dai mu ji tun wuri" Ammi ta kalli Mayraah tace "Ko baza ki iya masa wanka ba?" Mayraah na murmushi a hankali tace "Zan iya" Mama Ladi tace "To gwara dai haka" karfe tara suka bar gidan bayan Mama Ladi da Bilkisu sun raka su har bakin mota. Suna isa gida Mayraah ta tafi dakinta ta sake kakkaba bed spread din kan gado ta kwantar da Babynta dake bacci, sannan ta cire hijab dinta ta linke ta fita daga dakin, zaune ta tarda Maheer a parlor tace "Baka shigo da kayan ba?" Yace "I will bring them in tomorrow, ko da abinda zaki bukata a cikin kayan ne in shigo da su ynxu?" Ta girgiza masa kai, yace "Ohk... Bacci babynki yake?" Tace "Ban gane Babyna ba? Kai ba naka bane?" Yace "Aa wannan naki nr wife since you named him, our next baby will be mine cause i will be the one to name him" Yana murmushi ya kare maganar, ita dai kallonsa kawai take don she didn't fine what he was saying funny, ya mike ya kamo hannunta still smiling ya dawo da ita kan kujeran da yake zaune ya zaunar da ita shima ya zauna yace "C'mon Baby gal, ko ni baza a bani privilege din naming next baby ba?" Tace "Wannan ma kai ne kace ka bar min naming din ai, bani nace ka bar min ba, i never tot zaka ce i should name the baby" Ya mata side hug yace "Haka ne Sweetheart, i pray our next baby should be a beautiful girl just like you" At the mention of giving birth to another Baby sai da Mayraah taji zuciyarta ya tsinke, a hankali tace "Ni nace maka zan kara haihuwa ne?" Murmushi yayi yace "Za ki kara mana wife, amma ba yanzu ba don nima ban mance wahalan da kika sha ba baby, kin sha wahala sosai, shi sa na baki zabin sunan babyn, but our next baby which i pray should be a girl zanyi naming dinta after Haseenah in sha Allah" Mayraah bata san sanda ta daga kai tana kallonsa ba babu ko kiftawa, yayi kasa da murya yace "Kinsan a rayuwar nan komin lalacewan mutum zaka ga definitely yana da good side dinsa, so wani lokacin idan na tuna good side din Haseenah i just feel...." Shiru yayi bai ci gaba ba, Mayraah dai kallonsa take still not blinking, ya sauke wani bayanannen ajiyar zuciya a hankali yace "Just that her bad side over shadowed the good side of her, bazan mance wani abu daya da Haeeenah ta min na kyautatawa ba, akwai wani lokaci....." Shiru ya kuma yi kamar me nazari, sai kuma ya girgiza kai yace "Ko da yake, let just leave this discussion for another day" Mayraah ta mike daga kusa da shi ta koma baya tana kallonsa tace "You are looking into my face kake gaya min zaka yi naming yarinyar da ban ma kai ga haifa ba with Haseenah? Are you for real?" Maheer yayi kasa da murya with surprise written all over his face yace "Wait Mimi... Is there anything wrong with that? Do you actually find this not okay?" Nan da nan hawaye ya cika idon Mayraah, tana girgiza kai muryarta na rawa tace "I know why you are saying all this, amma tsakanin ka da Allah Yaya why did you have to pretend u are okay with my decision concerning the naming of this baby? Why do u have to pretend plsss" Maheer ya mike yana kallonta yayi murmushi yace "So that to please you Mimi, dole in so abinda Mimina ke so, But kinsan wani abu?" Mayraah ta dinga kallonsa with shock all over her face, A hankali yace "Ita mace in dai namiji ya taɓa rungumar ta, ko yayi kissing dinta, ohk... Stuffs like that dai, to baya taɓa fita completely daga ranta ko shekara nawa zata yi a duniya, those memories will be ringing in her brain once in a while...." Da kyar Mayraah ta iya bude baki tace "Ban gane ba yaya" Yace "Look into my eyes and tell me baku taɓa rungumar juna da shi ba Mimi, tell me bai taɓa tabaki ba sanda ku ke dating, infact har bayan kun rabu a sanda kike zuwa office ki samesa daga gidana, that not being enough har gidansa kin sha bin sa...." Mayraah taji kafafuwanta sun kasa daukanta ta dinga kallonsa kamar ranan ta fara ganinsa, Yace "Ina ga kin manta sanda kika dawo gidana wataran Hijab dinki na kamshin turarensa, sbda guilty conscience ban ce maki komai ba kika maza kika yi soaking hijab din a bandaki, ko kin manta?"

Mayraah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence via 07087865788

141
Mayraah ta dinga kallon Maheer with shock ta kasa ce masa komai hawaye na sauka idonta, sosai kanta yayi mata nauyi ta dinga jin kamar parlon na juya mata tsabar yanda maganganunsa suka daketa, Maheer ya juya yana backing dinta calmly yace "And i am sorry to tell u that, ni ba sunan tsohon saurayinki na saka ma yarona ba Mimi, i named my son after your father, though ban san ko ke kin sanar ma su Ammi da yan kaduna sunan Ex dinki aka sa ma babyn ba, and still ke zaki iya bari a ranki cewar sunan da kika zaba aka sa ma yaronki cause u are entitle to ur thinking, but reverse is the case in my own thinking.... i never named my son after ur Ex, ke dai ki ci gaba da kallon yaron as ur Ex namesake, ni kuma zan ci gaba da kallonsa as ur dad's name sake.. na sa a raina that you are taking me for granted because i am just an alternative to you Mimi, I wasn't ur choice and i will never be ur choice, kawai dai kinyi biyayya ne

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login