Showing 186001 words to 189000 words out of 452169 words

Chapter 63 - Mayrah Complete By Khaleesat Haydar

yasan halin da take ciki a inda take" Mami tace "Musharraf ita 'ya mace komin rintsi ban ga dalilin da zata bar gidansu ba ko ince gidan da ta taso, bata da wani hujjan da zata ce ta bar gida, ni fa tunda yarinyar nan ta iya tsallaka kafa tayi tafiyarta har aka zo ana zargin ka akayi arresting dinka naji ta fita a raina bazan boye maka ba, who knows the life she's living now tunda ta gwammaci ta shiga duniya tayi rayuwarta..." Musharraf da yaji haushin furucin Mami har ransa yace "Mami kika san wani pressure yasa ta tafi? She is so young for all this that is happening to her, she can't think straight, so ake yarinyar ta kamu da depression, she is just 22 fa Mami" Mami tace "Ni dai in za ma ka cire ta a rai ka ci gaba da harkokin gaban ka is better u do so, don babu aure tsakanin ka da wannan yarinyar just put that in mind, in kuma har ka mance abinda guardian dinta suka mana a police station sai in ji, it's simple idan har zaman kasar ma baka so to ka tafi Canada ka samu Daddy...." Musharraf ya katse ta yace "Waye Daddy? Mami pls ki daina hadani da gayen nan, i have no business with him" Mami tace "Shi ɗan uwan naka zan daina hadaka da?" Musharraf ya sauka daga kan gadon yace "Ɗan uwana that is happy with what i am going through, he is happy with my downfall, ko sau daya bai taɓa kirana duk wannan abubuwan dake faruwa ba" Mami tace "To saboda me zai kiraka, kai kiransa kake Musharraf?" Bai sake sauraronta ba ya fice daga dakin. Maheer na zaune parlon Ammi yayi kasa da murya yace "Ammi yau za a sallami Haseenah daga asibiti, so Abba insisted in kawota gidan nan har ta karasa samun sauki" Hajja da ke zaune parlon hannunta rike da carbi ta dago da sauri tana kallonsa jin abinda yace, Aunty Mariya ma da ta zo jiya da mai gidanta da ya zo yi ma Hajja jaje ta kalli Maheer da mamaki, Hajja tace "Wani gidan? Wai ci gaba da zama da matsiyaciyar nan zaka yi kake nufi Maheer? Ko dai baka da kai ne? Ita Hasinar kake mararin dawowa da ita har zaka kawota gidan nan?" Ammi dai bata ce komai ba, Hajja ta kalleta ta hade rai tace "Ya kika yi shiru Ammi? Kema kin goyi bayan ta dawo ya zauna da er matsiyatan kenan tunda har kika yi shiru" Ammi ta kalli Hajja ta sauke ajiyar zuciya tace "Hajja ba daga ni bane, nima na so nuna ma Alhajin hakan amma yace lallai Maheer bazai rabu da ita ba saboda ɗan matsalar nan da aka samu, shi yasa kawai na hakura na ja bakina nayi shiru" Hajja na gyada kai tace "Eh lallai, dole kice ɗan matsala tunda ba ke aka kai Caji opis ba aka ci ma mutunci aka walakanta ba ko shi Mamudan, ae ni aka taɓa dama ba ku ba, karshen biyayyar da kike ma Mamuda naga sakayya ya maki da kishiya ai, ke uwar yan bin miji, wato baza ki iya nuna masa ke baki yarda ba an ci mutuncin uwarki shine kika yi shiru kika kyale hukuncin da ya yanke, to ba komai ai rayuwa ce" ita dai Ammi kanta na kasa, mikewa Hajja tayi tana kallon Aunty Mariya tace "Ni ai sai in bar gidan, dama banda lalura da damuwar da yayi min yawa ban san halin da yarinyar mutane ke ciki ba ga dangin ubanta sai zarya suke mana me zai zaunar da ni a gidan surki har zuwa yau, ai an san ba halina bane wannan, ki tashi mu je Mariya dama zuwanki kawai nake jira kuma jiyan baku iso da wuri ba" a hankali Ammi tace "Aa kiyi hakuri Hajja yanxu haka fa Alhajin suna hanya da Badiyyar mun yi waya da shi yace an gama komai in Allah ya yarda yau zata dawo gida an rufe case din" Ko rufe baki Ammi bata yi ba Badiyyah ta shigo parlon, Hajja ta saki salati ta fashe da kuka ta tafi da gudu ta rungumeta tana kiran sunanta, Ammi dai sai kallon Badiyyah take ganin yanda ta rame tayi bakikirin kamar ba ita ba, ita kanta Aunty Mariya sake baki tayi tana kallon Badiyyah, Hajja na kallonta daga sama har kasa cikin kuka tace "Sannu Badiyyah, sannu, Allah Ubangiji ya saka maki wannan abu da aka maki, Allah ya saka maki" Aunty Mariya tace "Allah ya saka mata fa kika ce Hajja? Yarinyar da ta dauke wayar mutane me tsada ne zaki dinga yi ma wannan addu'ar? Maganar da sai da na kai zuciyata nesa na iya sanar ma mai gidana saboda kunya, kuma ke nan har kullatata kika yi ban zo ba, sata fa Hajja? Gaskiya wannan ba karamin abun kunya Badiyyah ta ja mana ba ta ja ma kanta, me ta rasa da zata jefa kanta cikin wannan mummunan hali na satan kayan mutane?" A mugun fusace Hajja ta juyo zata yi magana sai ga Abba ya shigo da sallama, Hajja ta koma ta zauna tayi kasa da kai don dama da hijab dinta a jiki, Abba ya zauna ya gaida Hajja, Hajja ta amsa tana masa sannu da kokari, Aunty Mariya ta gaida Abba ya amsa, sannan yana kallon Badiyyah on a serious note yace "Ke bude kunnuwanki ki saurareni" Badiyya dake rakube jikin Hajja ta daga kai tana kallonsa yace "Kin ga sati dayan nan da kika yi hannun hukuma? To ya kamata ya zame maki darasi a rayuwarki, in har baki yi hankali ba a sati dayan nan to ko baza ki taɓa yi ba, da girmanki da hankalinki ban ga dalilin da zaki dau wayar mutane da sunan sata ba, me kika rasa da har kika ji sha'awar yin sata Badiyyah?" Hajja tayi kasa da murya tace "Mamuda kilan dai akasi aka samu, amma ni nasan halin Badiyyah wallahi sata ba halinta bane bata taɓa daukar min ko kwandala ba tun da ta taso" Tana fadin haka Badiyyah ta fashe da matsanancin kuka tace "Abba kawata ce fa ta bani ajiyar wayar ban san sato shi tayi ba" Abba ya daka mata tsawa yace "Wato bakin ki bazai mutu ba, da aka ce ki fadi inda kawar take kin fada a gaban yan sandan? Maganar banza maganar hofi, ke kika saci wayar ba kawarki ba" Aunty Mariya tace "Ai mara kunya ce, sam bata da kunya, don in har tana da kunya ma bazata bude baki tayi magana ba a nan, kuma dama duk inda makaryaci munafuki yake za a samesa da daukar abinda ba nasa ba, to kanki kika ja ma abun kunya wallahi ba mu ba, sannan ga record dinki na sata can wajen yan sanda" Hajja dai ta kalli Aunty Mariya ta gefen ido bata ce komai ba, Abba ya mike kawai ya fita daga parlon don shi case din ma kunya kawai ya basa kawai babu yanda ya iya ne yayi involving manyan mutane masu ganin girmansa, ace wai er kanwar matarsa ce tayi satar waya, satar ma a hotel kawai dai bai son bude zancen ne gaba daya sai dai yayi da Ammi but he is highly disappointed don a hotel Badiyyah tayi satar wayar, ga Maheer da Usman suka ki shiga case din suka bar sa shi kadai yana ta fama for one week, Aunty Mariya na ganin fitar Abba kafin Hajja ta samu damar ce mata komai ita ma ta mike ta fice daga parlon zuciyarta na tafarfasa, Hajja na kallon Badiyyah ta mike ta dagota tace "Tashi mu je gida kiyi wanka in samar maki abinda za ki ci, ba komai rayuwa ce, wanda bai zo ba ma jiransa yake" Ammi dai sai kallonsu take cike da takaici wai er late sister dinta ce haka, yanzu da Rukayyah na da rai Badiyyah ai bazata zama haka ba, Allah ya gani tayi bakin kokarin ganin ta ba Badiyyah tarbiyar da ta ba nata 'ya yan, tarbiyar da ta ba Mayraah ta so yi ma Badiyyah amma Hajja tayi ta intruding saboda son duniya da ta dauka ta dora ma Badiyyah don maraici, haka yasa Badiyyah ta daina tsoron kowa ta daina ganin kowa da gashi tunda tasan Hajja zata tsaya mata, ko kallon banza su Maheer suka ma Badiyyah sai Hajja ta ɓata rai, wani lokacin har Ammi hakan ke shafa don sai ta fita harkanta na sati da satittika duk don kan Badiyyah, wannan dalili yasa Badiyyah na cewa tana son Musharraf Ammi tace a hakura a bar mata tunda ita tasan wacece Hajjar, amma at the end duk da hakan bata fita ba, ta dalilin Badiyyah yau gashi babu Mayraah, tunanin hakan yasa hawaye ya kawo idon Ammi, shi dai Maheer ido kawai yake bin su da shi, Hajja na kallon Badiyyah tace "Baki da lafiya ne, naga kina layi? Ko dukanki suka yi a can?" Badiyyah ta marairaice tace "Jiri nake gani, kuma...." Da sauri ta rufe baki tana tsaye inda take kamar wata er yarinya ta fara kwararo amai Hajja ta gigice tana rike da ita tana salati, Ammi ta taso ta nufo su, Maheer dai sai kallonta yake babu ko kiftawa. Mayraah na zaune ita da Hafsat wajen karfe tara da rabi sauran nurses din na ta harkar gabansu attending to patients da suka zo allura, Hafsat tace "Ko energy drink ne ki amso Ilham don kar ki zama weak anjima, naga jinin naki ya ɗan sauka kadan da na duba, kuma akwai operation har biyar yau..." Mayraah tace "Ai ba da ni za a shiga theatre din ba..." Bata rufe baki ba Dr khalil ya shigo Reception din daga meeting room, tun safe da suka shiga meeting sai yanzu suka fito, MD ma ya shigo reception din ya wuce Dr Khalil dake gaisawa da patients, a takaice ya amsa gaisuwar nurses din zai wuce sai kuma ya juya kallon Mayraah, keenly yace "Hey, i didn't see u in any of the 2 meeting, are you a staff in here?" Nan duk nurses din suka maida hankalinsu kan Mayraah, wasu farin ciki fal cikinsu suna jiran jin me zata ce, Dr Khalil ya karaso yana kallon MD yace "Wannan satin ta fara aiki, kuma...." MD ya daga masa hannu yace "She should speak for her self pls" Yana fadin haka ya maida dubansa kan Mayraah a takaice yace "Madam me ya hanaki shiga meeting?" Mayraah ta nuna masa Dr Khalil a takaice ita ma tace "He have said it all" Ba MD ba, hatta Khalil was shock at her reply, Duk nurses din ma suka saki baki suna kallonta da mugun mamaki, Khalil ya dafa shoulder din MD yayi kasa da murya yace "I spoke to you about...." MD ya dakatar da shi yace "Meet me in my office" Daga haka ya wuce sama kamar zai tashi, Mayraah dai ko a jikinta don ko daga kai ta kallesa bata sake yi ba, Dr Khalil ya juya ya bi bayan MD din, Hafsat ta dawo gefen Mayraah tana zaro ido tayi kasa da murya tace "Ke Ilham why did u speak to him that way? Baya son raini fa? He is our boss Ilham" Mayraah ta kalleta tace "How did i speak to him, tambayata fa yayi kuma an riga an basa amsan tambayar da yayi min and he is still repeating the question" Wata nurse na hararanta tace "Kina wasa da aikin ki kenan yarinya, ko baki san shine MD din duk asibitin nan gaba daya ba, ke haka aka koya maki tarbiya a gidanku, kina ganin ya fara maki magana za ki mike tsaye da sauri ba wai ki zauna kina basa amsa ba cikin isa da gadara, who are you? Ke kamar kanki na hayaki daga fara aiki last week ko, to ina me tabbatar maki idan baki yi hankali ba yau shine karshen aikinki a asibiti nan ba dai MD kika ma rashin kunya ba, kin zata su Dr Hamid da Dr Balogun ne masu fasa maki kai wai kin iya aiki ko, to MD no go area ne, da kyar idan bazai yi firing dinki yau ba" Wata nurse din ta amshe tace "Ki kyale ta mana, yara duk sun je private University sun karbi Degree sun zo nan suna raina mana hankali suna maida mu bamu san me muke ba, to wa zata nuna ma iya aiki in ba karya ba" Mayraah dai bata ko kallesu ba balle ta basu amsa, infact kamar ma ba da ita suke ba, kai ita fa ba dole sai ta bar asibitin ta kama gabanta bata son isa da izza ga nurses ma sai raina mata hankali suke, abeg she can't, Can dai ta kalli Hafsat warce da alama duk jikinta yayi sanyi don a kaf asibitin hatta likitocin kaffa kaffa suke da MD har ma fararen fatan, Mayraah ta kalleta as if whispering tace "Wai shine me asibitin ne wannan jaraba haka?" Hafsat tace "Aa, but he is in charge of everything" Mayraah tace "To su waye masu asibitin?" Hafsat tace "Ceo din ba musulmai bane kamar ma ba yan kasar nan bane, but MD is the Managing Director cause he is good at what he does, kowa shi ya sani" Hafsat ta marairaice tace "Ni tsorona kar yace zai yi firing dinki kin ga ko tanka ki bai yi ba ya wuce sama yace Dr Khalil ya bi sa" Mayraah ta kyabe baki ta dauke kanta tana wasa da farcenta, iyaka ta koma Suleja abun ta tayi ta bacci ba shikenan ba. Dr Khalil ya zauna kan kujera bayan ya gama sauraron MD yayi kasa da murya yace "Look Dr, yarinyar bata san ka bane, and satin ta daya kenan da fara aiki a nan, pls pls consider..." MD ya dakatar da shi sounding so pissed off yace "Plss I don't want to see her in this hospital nace maka Khalil, bana son in sake sauka downstairs for any reason in ganta a asibitin nan seriously, banda kai waye kaga yake kawo health worker just like that inyi employing din sa ba tare da an bin proper procedure for the employment ba, ban ga CV ba, babu interview babu komai, infact ita ban ma kai ga ce maka komai kan employment din nata da ka min magana ba kawai ka sa ta fara xuwa aiki without my consent har ka bata uniform Dr, sannan yanzu from all indications naga rude workers ka fara kawo mana asibitin, so she should leave immediately pls, bamu da vacancy" Dr Khalil ya sauke ajiyar zuciya yace "Kai matsalata da kai saurin hawa, ka ma ki tsayawa ka saurareni" MD ya mike ya buga table dinsa yana kallonsa da kyau yace "Bazan saurareka ba Khalil, she have to leave this hospital immediately ko in kira security yanzu su fidda ta" Murmushi khalil yayi yace "Kasan er wacece?" MD ya koma ya zauna calmly as if counting his words yace "I don't care" Khalil ya mike yace "Kayi hakuri ka bata second chance pls, ni kaina nasan bata kyauta ba but she seriously needs this job, nasan kai me hakuri ne don Allah ka janye batun bazata sake aiki ba, idan ya so i can tell her idan ta tafi yau she should stay back home har sai ka bata employment din fully kafin tayi resuming" MD ya mike yace "She should stay back home, i am not employing her at all, i mean my words" Dr Khalil ya juya ya fita daga office din ya sauka floor din da office dinsa yake, yana zaune office ya kira downstairs yace a turo masa Mayraah, ba a dau lokaci ba ta shigo office din nasa tana kallonsa, sai da ya mata izinin zama sannan ta zauna, a hankali yace "Ilham me yasa kika yi ma MD magana rudely?" Mayraah tace "Did my words sound rude? Ni wallahi ban sani ba" Kallonta kawai yake, ta sunkuyar da kanta, bayan few seconds Khalil ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya yace "Yanzu ki tashi ki je office dinsa ki basa hakuri politely, and be careful with ur words pls Ilham, speak to him politely kice yayi hakuri kinyi kuskure baxa ki sake ba, talk to him remorsefully" Mayraah ta zaro ido tace "Office dinsa kuma?" Khalil yace "You have to Ilham, office dinsa na last floor"


Mayraah is 500 via 3276052019 Fcmb Hauwa bello jidda



Ur evidence via 07087865788



INA MATA MASU AJI, BA ‘YAN RAKIYAR MATA NAKE NEMA BA. SHIN KINA DA LABARIN COMPANY DINNAN NA APHRODISIAC MA’ANA KAYAN MATA WATO *HONEYDROPS* DA KE GARIN *SOKOTO* SUNA DA INGANTATTUN KAYA DA BA SU DA NA BIYU WANDA SUKE DAWO MIKI DA MARTABARKI TA MACE KI DAWO TAMKAR BUDURWA ‘YAR SWEET 16, SUNA DA ZAFAFAN KAYA DA SUKA HA’DA DA *INFECTION FLUSHERS, BREAST FIRMING AND ENLARGEMENT PRODUCTS, HIPS AND BUTTS PRODUCTS, DIFFERENT TYPES OF WETNERS, VARIETIES OF SWEETENERS, VIRGINITY BACK PRODUCTS WATO TIGHTENERS *(MA’ANA AKWAI KALOLIN KAYAN QARIN NI’IMA, QARIN DADI, QARIN DANDANO DA KUMA MATSI NA BAN MAMAKI), SANNAN KAYANMU NA DA HADIN SINADARAN DA KE SAKA MALLAKA DA SOYAYYA A ZUCIYAR MIJI*

KAYANMU SUN HA’DA

*INFECTION FLUSHER*
*ORIGINAL SABAYA*
*ECHOES OF FOREVER*
*MOWA’S SECRET*
*HER ROYAL HIGHNESS*
*ETERNAL FLAME*
*SUGAR QUEEN* DA SAURANSU. KI HANZARTA SAVING LAMBATA KI KUMA YI MIN MAGANA DON SIYE KO SARI KO KUMA KASANCEWA CIKIN MASU SA’AR SAMUN KAYANMU A KYAUTA YAYIN DA MUKA YI GIVEAWAY. ZA A IYA TUNTUBARMU A LAMBOBI KAMAR HAKA 08167888934 KO KUMA 07026039714. KO A SHIGA LINK DOMIN MAGANA DA MU KAI TSAYE wa.me/+23481678888934

*MUNA MARABA DA KU, MUNA GARIN SOKOTO MUNA AIKE KOWANI GARI KOWACCE QASA CIKIN AMINCI*

55
Mikewa mayraah tayi ta fita daga office din dr khalil bayan ya bata direction din zuwa office din md, jingina tayi da bango tana tunanin yanda zata fara zuwa office din nasa, in taje sai tace masa me? bayan few seconds ta fara tafiya zuwa last floor walking slowly, with direction din dr khalil ta isa har door din office din

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login