Showing 207001 words to 210000 words out of 452169 words
Chapter 70 - Mayrah Complete By Khaleesat Haydar
mu je station din yanzu, kawai tambayoyi za su maki...." Ta fashe da kuka sosai tace "Toh ba sai mutum yayi laifi ba ake kai sa station, ni me nayi? Don Allah kar ka boye min ka gaya min" Yace "Nace maki it's not something serious Mayraah, yanxu haka daga station din nake, kawai suna daukan statement dinki zan dawo da ke gida, kar ki wani daga hankalinki" Cikin kuka tace "Statement of what? What wrong have i committed?" Yace "Na fa ce ki kwantar da hankalinki, i am with you, yanzu ba daga Abuja nake ba saboda ke?" Share idonta tayi tana kallonsa, yace "Dauko wayarki mu tafi lokaci na wucewa" A hankali ta juya ta koma cikin gidan, wayarta ta dauko da handbag dinta ta fito, a cikin motarsa ta samesa yana jiranta, bayan ta kulle gidan ta tafi ta bude front seat ta shiga motar, kana ganinta kasan duk jikinta yayi sanyi sosai kuma a tsorace take, bayan sun bar layin ya kwantar da murya yace "Pls calm down Mayraah, kema kinsan bazan bari ayi harming dinki ba, beside i told u it's not something serious, u need not to worry kar ki je jininki yayi kasa" Ta fashe da kuka tace "But i want to know what i did, ina son sanin menene ya sa suka zo za su tafi da ni, wani laifin nayi? I know kasani tunda kaje station din, definitely u are aware, you are just hiding it from me, don girman Allah ka gaya min menene ko zan samu relieve" Dr Khalil ya ɗan kalleta, sai kuma yace "Ohk bazan boye maki ba, kinsan me ke faruwa?" Ta girgiza masa kai da sauri zuciyarta na bugawa, ya ɗan yi shiru sai yace "Kinsan ko wani society or rather community, da irin ka'idarsu ko kuma ince da irin way of life dinsu, da yanda suka ba al'adarsu da addinin su muhimmanci, right??" Shiru tayi tana kallonsa waiting for him to go straight to the point, ya sauke ajiyar zuciya yace "To kin dai ga garin nan da kike ciki yawanci majority dinsu musulmai ne, sannan akwai Hausawa babu laifi, so the community are against gidan da kika kama kina zaune ke kadai kina zaman kanki don suna da yara kuma suna duba tarbiyar yaransu suna tsoron kada yaransu suyi tunanin hakan abu ne me kyau mace ta kama babban gida irin wannan tayi zamanta, sannan sunce ke kince kina karatu amma sun gano ba karatu kike ma a garin Abujan ba, iyaka idan kinje kinyi abinda za ki yi a Abuja sai ki dawo nan ki bude gida ki shiga bayan kwana biyu ki sake komawa cikin Abuja, sannan a complain dinsu sun ce akwai saurayin da ma yake zuwa ya sameki a nan din" Sake baki Mayraah tayi tana kallonsa har zuwa sanda ya dasa aya, she was so shock and speechless, yace "To ban san ko bayan zuwan da nayi last week ko akwai wani wanda ke zuwa wajenki ba" Mayraah bata san sanda ta fashe da kuka ba tace "Allah ya saka min, wallahi bazan yafe masu ba, tunda na dawo nan babu wanda ya taɓa zuwa wajena sai kai, bazan taɓa yafe wannan kazafin da suka min ba" Dr Khalil ya langwabar da kansa yace "Kinga abinda nake gaya maki ai ko, mutuncin ya mace gaban iyayenta, in ko ba gaban iyayenta ba to gidan mijinta, in dai a arewa ne duk inda za ki je to wallahi kallon da za a maki kenan baza ki taɓa canza su daga maki kallon nan ba, a takaice gani suke sharholiyarki kike shigowa kiyi a Abuja sai ki dawo nan Suleja ki fakee, let me tell u something.... kiwon mutane ake yanzu ba fa dabba ba, duk footstep dinki a kan idon mutane yake" Mayraah dai ta kasa cewa komai sai kukan bakin ciki da takaici take, har suka iso garin Abuja ta kasa daina kukan da take har ya ma daina lallashinta, wani station taga sun zo, bayan yayi parking a waje yana kallonta yace "Kiyi hakuri in sha Allah komai ya zo karshe daga yau, wipe off ur tears and trust me I will be by ur side" A hankali ta goge idonta tana kallonsa cikin rawan murya tace "Toh yanzu me zan ce masu idan mun shiga?" Yace "Kar ki damu, na riga na masu bayanin komai, iyaka Statement dinki za a dauka, shikenan" Daga haka ya sauka daga motar ita ma ta sauka har lkcn hawaye ya ki tsaya mata, she felt so hurt da irin kallon da mutane suke mata, ga Ahmad, Zainab, and now sulejan da take, calmly yace "Na fa ce ki daina wannan kukan" Ta gyada masa kai da kyar tana kara goge idonta, ya nufi cikin station din tana biye da shi a baya. Dr Khalil ya gaisa da yan sandan cikin station din yace "Za mu iya shiga office din Dpo din?" Police officern yace "Ehh suna ciki har yanzu, You can go in...." Ya kalli Mayraah dake tsaye gefensa kamar warce tayi ma sarki karya gaba daya a tsorace take don bata taɓa shigowa police station ba, calmly yace "Mu je" Bin bayansa tayi har xuwa office din Dpo din, ya bude kofar ya fara shiga da sallama sannan ita ma ta shiga gabanta na faduwa sosai, makalewa tayi jikin kofar tana kallon wanda ke zaune kan Sofa a office din babu ko kiftawa, can ta juya a hankali ta kalli Dr khalil kamar idanuwanta za su fito, Dpo ya daure fuska yace "Kee, shigo ki kulle ma mutane office" Ji tayi kamar ta zura a guje, ta dai kulle kofar da kyar ta sunkuyar da kai, amma ta kasa karasawa ciki don gaba daya tayi shock a wajen, tuni Dr Khalil ya tafi ya zauna kan kujera, Dpo ya bata thumbs up yana gyada kai cikin jinjina yace "The runaway girl!!" Kasa daga kai tayi, cikin daga murya yace "Ya sunanki?" Da kyar ta daga kai ta kallesa cikin karfin hali tace "Mayraah" Yace "Mayraah the runaway girl.... to nemi kujera ki zauna" Ta saci kallon wanda ke zaune kan sofa din, ai tana ganin irin kallon da yake mata tayi saurin dauke kai kamar munafuka ta tafi ta zauna kan kujera ta takure waje daya, shi dae Khalil murmushi kawai yake, Dpo yace "Kin san wannan da yake zaune?" Sunkuyar da kai tayi, ya mata tsawa yace "Ke..." Cikin rawan murya tace "Yayana ne" Yace "Ya sunansa?" saboda tsoron kar ya sake mata wani tsawan cikin rawan murya tace "Ya Usman" Dpo yace "Yau kwananki nawa da barin gida?" Ta fashe da kuka ta kasa cewa komai, yace "Ba kuka nace ki min ba malama, warce ta iya tsallakawa ta bar gida ai zuciyarta ya kekashe kenan babu wani batun kuka, kwananki nawa yau da barin gida?" Cikin rawan murya tace "Kamar 3 weeks" Yace "Kuma baki da intention din komawa anytime soon ko?" Daga kai tayi tana kallonsa hawaye na sauka idonta, Dpo din yayi shiru, sai kuma ya nuna mata kujeran dake gaban table dinsa yace "Dawo nan ki zauna" Mikewa tayi tana kuka ta tafi ta zauna kan kujeran, yace "Mayraah" Ta daga kai ta kallesa hawaye na sauka idonta, yace "Abinda kika yi kin kyauta kenan? Saboda wasu unforseen circumstances sun faru that doesn't mean it is the end of life my dear, what if hannun mutanen banza kika fada? Did you know the type of era we are in now? Kinsan irin munanan cases da muke dealing da kullum a wajen nan? me yasa za ki zabi kawai ki bar gida saboda an samu matsala? pls nan gaba ko wani kika ga zai yi abun nan da kika yi ki basa shawaran kar yayi ba shi da amfani, ita dama rayuwa kowa da ƙaddararsa taki a haka ta zo sai kiyi hakuri ki zama me imani ki amshesa hannu bibbiyu, ko da wasa karki sake tunanin wannan shine solution dinki ke macece, leaving home is never a solution, ke baki tunanin halin da iyayenki da yan uwanki za su shiga saboda abin nan da kika aikata? Ko ke ba musulma bace? Don duk musulmi an san sa da tawakalli ne" Ita dai kanta na kasa hawaye sai sauka idonta yake, yace "Yanzu kin san ta yanda aka bi ki har Suleja?" Ta girgiza masa kai, ya dauko wani kwali ya ajiye mata a gabanta, kallon kwalin ta dinga yi sai kuma ta saci kallon Usman dake kallonta tayi saurin dauke kai, Dpo yace "Ko da wasa next time do not try this nonsense again pls" Sai kuma ya kalli Dr Khalil yace "Kai kuma Allah ya saka maka da alkhairi for all ur effort, ni yanzu zan fita, za ku iya tafi Allah ya tsare gaba....." Har suka fito daga office din Dpo Mayraah bata yarda ta kalli Usman ba, sai makalewa kusa da Dr Khalil take, bayan sun fita daga police station din, Dr Khalil na kallon Usman yace "Ina kuka nufa yanzu, don naga it's almost magrib" Ita dai Mayraah na can gefe tsaye gabanta sai faduwa yake, ta saci kallon Usman yafi a kirga, Usman yace "Ba komai, na saba driving din dare, i will drive to kaduna in sha Allah" Dr Khalil yace "Toh ba damuwa, idan ka isa kadunan sai mu yi waya" Usman yace "To in sha Allah, thank you so much Dr" Dr Khalil yayi murmushi yace "You are welcome" Daga haka Dr Khalil ya koma gun Mayraah yace "Ki je ku tafi..." Ko rufe baki bai yi ba Mayraah ta fashe da kuka tace "Wallahi ni dai tsoronsa nake ji, na shiga uku" Dr Khalil ya buda ido yace "Saboda me?" Cikin kuka tace "Zai iya marina na sani, dama yaya Maheer ne" Dr Khalil yayi murmushi yace "Haba dai, ba abinda zai maki" Cikin kuka tace "Wallahi zai iya, me yasa ba Yaya Maheer bane ya zo" Juyawa Dr Khalil yayi ya kalli Usman da ya rungume hannu yana tsaye jikin mota fuskarsa babu yabo babu fallasa, komawa yayi wajensa yana ɗan murmushi yace "Barrister don Allah ayi mata hakuri, tace tsoro take ji zaka bugeta" Usman ya girgiza kai yace "Not at all.... Ka tambayeta ko na taɓa dukanta, she is waisting our time, muna da tafiya a gaba" Dr Khalil yace "To plss ayi hakuri barrister" Sai da Dr Khalil yayi da gaske da Mayraah sannan ta tafi ta shiga motar Usman, amma tana shiga sai ta wani tsuke fuska tana makale da handbag dinta, Usman ya kara yi ma Dr Khalil sallama sannan ya bude driver seat ya shiga ya tada motar, Dr Khalil ma ya nufi motarsa, har suka hau kan hanya bai ce mata ba ita ma bata ce masa ba.
Mayraah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa bello jidda
Ur evidence via 07087865788
*Ina Mai farin cikin gabatar maku da garin Sabaya gangariya Mai dadin gaske Wanda zata ciko maku da ramar ku jikin ku yayi gwanin sha'awa, Ina uwar gida a Amarya zawarawa yanmata Kai jama'a wannan lafiyayyar sabayar ta* *mamn Khadijah har maigidan ma da yaran gida duk zasu iya Shanta batada wata matsala dan neman Karin bayani zaku iya tuntubar mamann Khadijah Kai tsaye ta number waya ko WhatsApp* 07037777442
62
Mayraah na ganin sun kusa Suleja ta kallesa a karo na farko tana fidgeting fingers dinta a hankali tace "Don Allah yaya zan iya dauko jakana?" Ganin bai ce mata komai ba driving dinsa kawai yake, ta kauda kai bata sake cewa komai ba. A hankali Mayraah ta bude idonta daga baccin da ya dauketa ta gansu a cikin garin kaduna, gyara zama tayi da sauru ta tana kallonsa don ya maida mata kujeran baya yanda zata zama comfortable sanda take baccin, shi dai driving dinsa kawai yake pretending kamar bai ma san ta tashi ba, tun daga Abuja har zuwa yanzu da suke kaduna yaki ce mata komai, duk da almost half of the journey ma bacci take, wani hotel taga sun shiga bayan yayi parking ya bude motar ya sauka, babu bata lokaci ita ma ta sauko tana kallonsa ya kulle motarsa ya nufi cikin hotel din, ta wani tura baki ta bi bayansa, executive room ya biya masu, bayan ya amshi makullin dakin suka bar reception din, ita dai bin sa kawai take a baya har zuwa dakin, har cikin ranta take wishing dama Maheer ne, babban parlor ne da bedroom suka yi lodge in... Bayan ya ajiye wayoyinsa da car key ya cire agogonsa ya ajiye kan kujeran parlon Mayraah dai sai bin sa take da kallo tana turo baki, sai a sannan ya daga kai ya kalleta, ta sunkuyar da kai da sauri kamar munafuka, sai kuma ta ga ya nufi kofa har ya fita ya kulle kofar, a hankali ta karasa ta bude kofar bedroom din ta shiga ciki, bayan ta ajiye handbag dinta da wayarta ta koma parlon, sabulun da hotel din suka basu ta dauka ta shiga bandaki tayi wanka sannan dauro alwala ta fito ta koma daki, bayan ta idar da sallah ta rage Ac din dakin ta kwanta duk da yunwan da take ji don ko abincin rana bata ci ba, tana ta kwance taji an bude kofar dakin, kin juyowa tayi sai ma kulle ido da tayi da sauri don bata san me zai ce mata ba, sai taji yace "Fito ki dauki abinci" tana jin haka ta bude ido ta turo baki duk da ba ganinta yake ba sai kuma ta mike zaune tana murza ido tana kallonsa, juyawa yayi ya bar bakin kofar, ta sauka daga kan gado ta bi bayansa, Kallon ledan abincin dake kan table din gabansa tayi, sae taki karasawa ta dauka don ita fa bata yarda da wannan shirun da yayi mata ba, can ganin bai ce mata komai ba a hankali tace "Toh ni don Allah ka ajiye min kasa in dauka" Sae a sannan ya daga kai ya kalleta, tayi narai narai da ido ita ma tana kallonsa, gani take kawai planning din yanda zai wanka mata mari yake, tashi taga yayi ya bar wajen ya koma 3 seater ya zauna, tana tafiya a hankali ta tafi ta dau ledan ta koma daki tana satan kallonsa, shi kuma ya bi ta da kallo. Washegari da asuba Mayraah ta idar da sallah bayan ta gama azkar dinta har ta koma ta kwanta taji yayi knocking kofar dakin, ta mike zauna tana kallon kofar har ya bude, zamowa kasa tayi daga kan gadon murya can kasa tace "Ina kwana yaya" yace "Ban sani ba... dauko stuffs dinki mu tafi" Ta ɗan buda ido tace "Bazan yi wanka ba" Kallon da taga ya mata ya sa ta tashi da sauri ta dau handbag dinta da waya, ya juya ya bar bakin kofar ta bi bayansa tana duba wayarta dake nuna karfe shidda da rabi, check out suka yi daga hotel din bayan ya basu makullin dakin, ta bude front seat din motarsa ta shiga, bayan some minutes of warming up the car suka fita daga hotel din ya kama hanyar kano. Karfe tara suka shigo garin kano, Mayraah na ganin sun kusa gida haka kawai jikinta yayi sanyi, lokaci daya taji ta rasa sukuni, she don't know how everybody will accept her back, bata san ko Ammi will still welcome her back home ba, tunanin hakan yasa hawaye ya cika idonta ba tare da ta sani ba don kawai ji tayi yana sauka fuskarta, rufe fuskarta tayi da hijab dinta tana shessheka, Usman ya kalleta yana ci gaba da tukinsa yace "Ohk in maida ki Abujan kenan?" Cikin kuka tace "Aa" Yace "To me ya faru?" Ta fashe da wani sabon kukan tace "Ban san ko Ammi..." Kasa ci gaba tayi saboda kuka, Usman yayi kasa da murya yace "Ammi missed you, since you left she is not fine" Mayraah ta daga kai ta kallesa hawaye na sauka idonta, bai sake ce mata komai ba har suka shigo anguwan, yana horn bakin gate mai gadi ya bude gate din da sauri, ya shiga ciki yayi parking a garage, Bayan ya kashe motar ya juya ya kalli Mayraah da ta fada duniyar tunani, yace "I hope u will never repeat such mistake again" Ta juya a hankali ta kallesa sai kuma ta gyada kai, a hankali yace "Abba was there for you, i was there for u, so was Doctor but u decided to follow ur heart that lead you astray" Cikin rawan murya tace "I am sorry" bude motar yayi ya sauka, amma ta kasa bude motar ta fito duk jikinta yayi sanyi wasu sabbin hawayen na zuba idonta, zagayowa yayi ya bude mata kofar yana kallonta, sunkuyar da kai tayi ta sauka ya nuna mata entrance din gidan yace "Mu je" Babu musu ta fara tafiya tana share hawayenta gabanta na faduwa, tsoro take kada Ammi taki ce mata komai, she don't think zuciyarta zai iya daukan hakan, yana biye da ita a baya har suka iso entrance din shiga parlor, ta kasa bude kofar ta juya ta kallesa har sai da ya karasa gabanta ya bude kofar bai shiga ba ya juya yana kallonta, muryarta na rawa tace "I am afraid" Yace "U need not to be, everyone misses u badly" Ta gyada masa kai tana goge idonta, yace "Shiga..." Ba musu ta wucesa ta shiga parlon ya bi ta da kallo, Mayraah na shiga parlon tayi ido hudu da Haseenah dake tsaye kofar kitchen tana jiran sabon mai aikin Ammi ta bata irish din da taji tana soyawa wai ita bazata iya girki ba, Sake baki Haseenah tayi tana kallonta, Mayraah ta dauke idonta ta kalli direction din stairs jin kamar ana saukowa, Maheer ne ke saukowa tare da Ammi yana ce mata "Gaskiya Ammi i am only doing this because of you, but it's stressful for me, menene yasa baza a sa ta a mota ita ma ta tafi kadunan ba...." Ido hudu yayi da Mayraah dake kallonsa babu ko kiftawa, ai bata san sanda ta nufesa da gudu