Showing 210001 words to 213000 words out of 452169 words
Chapter 71 - Mayrah Complete By Khaleesat Haydar
ta rungumesa ba ta fashe da kuka, murya can kasa as if bai yarda ita bace yace "Mimi??" Haseenah tayi saurin dauke kai bayan ta saki wayarta dake hannunta ba tare da tasan ma tayi hakan ba, juyawa Usman yayi bayan ya dauke kai ya fita daga parlon, Ammi ta kasa motsawa daga stairs din da take tsaye, hawaye na zuba idon Mayraah ta rufe fuska a kirjinsa tayi karfin halin cewa "I missed you so much yaya" as if whispering yace "Why did u leave just like that Mimi?" Ido hudu tayi da Ammi dake tsaye hawaye a fuskarta ta kasa saukowa downstairs din, Mayraah ta sauke idonta kasa... Zame jikinta tayi daga na Maheer ta daga kai tana kallonsa kamar yanda shi ma yake kallonta babu ko kiftawa, he is just hoping this is not one of his everyday dreams, har sannan hawaye bai daina sauka idon Mayraah ba, kawai tayi gathering courage ta tafi wajen Ammi, Ammi na ganin haka ta fashe da kuka sosai, Mayraah ta rungumeta cikin rawan murya tace "Don Allah kiyi hakuri Ammi, ban san yanda zan yi ba ne..." Haseenah bata san sanda ta fita daga Parlon ba tare da ta amshi irish din da take jira ba ta koma Chalet. Mama Ladi da ta fito daga bangaren Ammi cike da masifa tana cewa "Haka kawai ba dangin iya ba na baba wannan wahala haka, o'o wallahi bazan iya ba don nayi ma kaina fada na daina shiga abinda bai shafeni, ga daki can an bar mata ban san me yasa take biyo mu nan tayi ta mana kazanta tana cutata ba...." Komawa baya Mama Ladi tayi da sauri tana gwalo ido bayan ta hango Mayraah tace "Wacece wannan kuma?" Sai a sannan Mayraah ta sake Ammi ita ma tana kallonta, Mama Ladi ta rike haɓa tana gyada kai tace "Ba shakka!! to ina iyayen naki da suka jefa ki a kwata kina jaririya? Inji dai tare ku ka dawo da su?" Mayraah ta sunkuyar da kanta, Mama Ladi tace "Amma wallahi ke kam da ba don kada Ammi ta kullaceni ba sai ince butulu ce ke me manta alkhairi, haka kawai kika kama hanya kika shiga duniya kika bar mata da hawan jini mu kuma kika bar mu da rashin isasshen bacci kullum cikin tunaninki da alhinin bacewarki, Sannan yanzu ba kunya ba tsoron Allah galau galau kin kwashi kafafuwa kin dawo ke kadai, ni fa duk tunanina tare ai za ku dawo da iyayen naki tunda baki da mutunci kiri kiri kin nuna ai babu abinda kika hada damu, duk abinda muke maki kika rufa ido kika ci mana mutunci, haka nayi kwana biyu a asibiti wajenki ko runtsawa ban yi ba ga yunwa, amma baki gani ba sai da kika zalunce mu kika daga mana hankali, Mamuda ya dawo kamar wani zautattce wani lokacin takalmi wari wari yake sa wa ya fita, duk caji opis din kano babu wanda bai tafi ya kai cigiyarki ba, mu dai Allah ya isa rashin cin abinci da wadatattcen bacci da kika janyo mana" Tuni Ammi ta kama hannun Mayraah suka bar wajen, Mama Ladi ta bi bayansu still. Tun da Mayraah ta shigo parlon Ammi take kallon Badiyyah dake kwance kasa tayi wani bakikirin kamar bata taɓa haske a rayuwarta ba ga wasu uban kuraje da suka cika mata fuska, Mayraah ta zauna kan kujera don Ammi da take son tambaya ko Badiyyar bata da lafiya ne tuni ta fita daga parlon, kasa daurewa Mayraah tayi tana kallon Mama Ladi tace "Mama bata da lafiya ne?" Mama Ladi tace "Wa? Wai Badiyyah? Ai Badiyyah cikin shege tayi in baki labari Mera, cikin shege dai da kika sani" Tsabar shock Mayraah bata san sanda ta mike tsaye ba, Mama Ladi tace "Aa koma ki zauna ba wani batun rikicewa don kema bamu san daga inda kike ba yanzu haka" Mayraah ta dinga kallon Mama Ladi babu ko kiftawa, Mama Ladi na kakkabe kujeran da taga Badiyyah ta zauna dazu tace "Hajja dai in gaya maki ta sallama ma duniya Badiyyah tace ko sunanta aka kira mata bata yafe ba, ta mata Allah ya isa yafi cikin kwando, ko ido suka hada sai ki ga Hajjan ta fara tari kamar zata shide yanzu haka zancen da nake maki Hajja tana can gidan Yahanasu a kaduna, sai kin ga gidan ko kiwon kare baza ayi a gidan nan ba don sai cuta ta kama karen ya mutu a banza, ni dai tun da na rakata ko minti sha biyar banyi cikin ɗan kuturun gidan ba na gudu gidan Mariya tunda dai abinda ya faru ba wai ya shafeni bane kawai zumunci nake dubawa, banda ma na kai zuciya nesa ai da sai dai ki dawo ki ga na canza wani pamilyn, don wannan pamilyn namu dai ba pamilyn nuna ma duniya bane, pamilyn mu ya zama barbadadden pamilyn, Badiyyah ta lalata mana Pamily kawai sai dai muce Allah ya isa, gidan Mariya da na gudu in samu sauki can kuma yanda kika san kasuwar kurmi tunda babban gida ne uwar mijin da uban mijin duk suna ciki da bataliyarsu, wannan karen ya shigo, wancan dokin ya fita haka dai abun ba tsari, ke in takaice maki washegari da asuba nasa aka kaini tasha na hau mota na dawo kano inda na fi wayo, to shine sabida rashin tsoron Allah aka makala ma baiwar Allah Ammi Badiyyar take ta fama yanzu haka, banda ma Mamudan mutumin kirki ne ina zai yarda wannan annobar ta zauna masa gida ta lalata masa tarbiyyar yaransa maza, ai da muna da yan uwa a kauye kyan Badiyyah kawai a turata can har sai ta haihu ta zauna tayi renon shegen a can, to bamu da kowa a kauye, Mamudan ma fa da farko kin amincewa yayi yace a fitar masa da ita daga gidansa, to kin dai san Abban naku da shegen tausayi ga kuma tausayin matarsa da yake, a haka dai daga karshe yace a kyaleta ta zauna amma ko nan da gate baya son ta je kada yan anguwa su sa shi a bakin duniya suce ga me cikin shege a gidansa, kiri kiri Mariya taki tafiya da ita aka bar Ammi da wahala, Allah dai ya isa kawai" Mayraah sai kallon Badiyyah da hawaye ke sauka idonta kawai take, kullum sai tayi kuka kamar ranta zai fita a gidan saboda Mama Ladi, da kyar ma in Mama Ladi bata daura mata depression ba saboda bad mouth dinta, Mama Ladi tace "Don haka kike baya baya da ita, mu ma duk baya baya muke da ita gaskiya, mu a zamaninmu idan mutum yayi cikin shege ma rataye kansa kawai yake ya mutu, ko kuma ya gudu ya bar garin sai bayan shekara hamsin, to ita kinga ai taki yin ko daya" Bude kofar parlon aka yi Ammi ta shigo da breakfast ta kawo ma Mayraah, ko bata bude baki tace komai ba kasan tana cikin farin ciki mara misaltuwa, she looks so happy wanda duk wanda yasanta yasan rabonta da wannan farin cikin an kwana biyu, Usman really took she and Maheer unaware don duk abinda yake yi bai gaya masu ba, Mama Ladi ta bi ta da kallo har ta ajiye tray din hannunta tana kallon Mayraah tace "Taho ki karya daughter" Mama Ladi ta rike haɓa tace "Yanzu tun safe in tashi ko ruwan shayi da ke da shegiyar sabuwar me aikinki baku bani ba sai wannan mata da bamu san daga inda take ba zaki kawo ma tray guda na kumallo jikinki na ɓari? Ni da na kwana gidan baki ban komai ba sai warce bata kwana ba?" Ko kallon Mama Ladi Ammi bata yi ba sai ma daukan tray din da tayi ta wuce dakinta da shi tace "Taho Mimi" Mayraah da duk jikinta yayi sanyi da halin da Badiyyah ke ciki ta share hawayen idonta ta bi bayan Ammi tana tafiya a hankali zuwa bedroom dinta. Ammi da kanta ta hada mata shayin ta debar mata komai sannan ta koma ta zauna tana kallonta, Mayraah ta daga kai tace "Ammi Abba fa?" A hankali Ammi tace "Na kirasa yana hanya" Mayraah ta dau shayin da Ammi ta hada mata ta fara sha, Ammi ta mike ta fita daga dakin zata je kai ma Mama Ladi nata breakfast din, Ammi na fita babu dadewa Maheer ya shigo dakin, Mayraah ta daga kai tana kallonsa har ya iso inda take ya duka yana kallonta, ta sauke idonta tace "In hada maka shayin kai ma?" Ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yace "Ki rage min kawai" Tace "Sai mu sha tare..." Zaunawa yayi saman darduman yana facing dinta, bayan ta kurbi shayin hannunta ta mika masa, ya amsa ya kai baki, ita kuma ta fara cin irish din da Ammi ta zuba mata da ketchup da kwai, Ya ajiye cup din shayin bayan ya sha a hankali yace "Me yasa kika tafi Mimi?" Bata yarda ta dago kai ta kallesa ba cikin sanyin murya tace "That's bygone yayana" Ya gyada mata kai kawai still looking at her, bayan few seconds tace "Baza ka ci irish din ba?" Dauka yayi ya fara ci, ta dau cup din shayin ta sha kadan ta ajiye, daga kai tayi suka hada ido, yace "I missed you Mimi" Ta ɗan yi murmushi tace "I missed you more" A haka Ammi ta shigo dakin ta samesu, Ammi na kallonsa tace "Ba ga can naku an kai maku ba?" Mayraah ta kalleta tace "Ammi ni ce nace ya ci" Shi dai murmushi kawai yayi, Ammi ta zauna gefen gado still looking at them.
Mayraah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
*Ina Mai farin cikin gabatar maku da garin Sabaya gangariya Mai dadin gaske Wanda zata cikomaku da da ramar ku jikin ku yayi gwanin sha'awa, ina uwar gida a
Amarya zawarawa yanmata Kai jama'a wannan lafiyayyar sabayar ta maman Khadijah har maigidan ma da yaran gida duk zasu iya Shanta batada wata matsala dan neman Karin bayani zaku iya tuntubar mamann Khadijah Kai tsaye ta number waya ko WhatsApp*
63
Mayraah na gama yin breakfast ta shiga yin wanka bandakin Ammi, Maheer kuma ya fita da tray din da suka yi breakfast din downstairs zuwa kitchen, ko da ta fito wanka ta tarar Ammi ta dauko mata kaya daga dakinta ta ajiye mata gefen gado, bayan ta shafa mai ta shirya ta fito parlor, har a sannan Badiyyah na parlon Ammi a kwance ita kadai, Mayraah na tafiya a hankali ta karasa kusa da ita ta durkusa tana kallonta tace "Ya jikin?" Kai kawai Badiyyah ta gyada mata, Mayraah tayi shiru tana kallonta hawaye na taruwa idonta, abubuwan da suka faru a baya ne da dalilin faruwansu kawai ke yawo mata a zuciya, da sauri ta goge idonta trying to shun away the thoughts off her mind, cikin sanyin murya tace "Kin yi breakfast ai ko?" Nan ma Badiyyah ta gyada mata kai tana kallonta, wani tausayinta Mayraah ta dinga ji har cikin ranta, she can't just imagine Badiyyah da ta sani ce wannan, a whole Badiyyah, Ammi ce ta shigo parlon, Mayraah ta juya tana kallonta, tana tsaye bakin kofar tace "Fito ki je wajen Abbanki Mimi, he is around" Mayraah ta mike tana goge wasu hawayen dake taruwa idonta ta nufi Ammi, a tare suka sauka downstairs, Mayraah na hada ido da Abba dake zaune kan kujera ya mike tsaye yana kallonta, sosai jikinta yayi sanyi ta sunkuyar da kanta and for the first time she felt guilty akan abinda ta aikata, for the first time ta ji bata kyauta abinda tayi ba, nan da nan hawaye ya cika idonta ta nufesa da sauri ta rungumesa sosai ta fashe da kuka tace "I am sorry Abba, don Allah kayi hakuri, i don't know what came over me, i was...." Kasa ci gaba tayi tana kuka sosai, Abba yayi patting din bayanta a hankali bai ce komai, tayi kukanta me isarta sannan ta durkusa nan gabansa cikin rawan murya tace "Don Allah ka yafe min Abba" Har a sannan ta kasa hada ido da shi, Abba ya zauna kan kujera a karo na farko yayi magana yace "It's okay Daughter.... I am glad you are back home hale and hearty, that was our prayer and hope, Alhamdulillah" Ganin yanda take kuka ya shafa kanta yace "Nace ya isa haka my dear" Ta gyada masa kai tana goge hawayen dake sauko mata, gefensa ya nuna mata ta dawo ta zauna ta daura kanta a jikinsa, sai a sannan ta lura da mutanen dake zaune parlon, Mama Ladi ce dake ta taɓe baki tana hararanta sai Hajiya Amina dake ta kallon Mayraah tana murmushi, matar looks so happy da dawowar Mayraah, Mayraah ta kalli Abba ya gyada mata kai yace "Go and greet her" Mikewa tayi ta ɗan kalli direction din dining da ta hango Usman a zaune shi ma yana kallonta, ta karasa har gaban Hajiya Amina ta durkusa gabanta ta gaisheta, Hajiya Amina ta dago ta sitting her down by her side ta jawota jikinta tana amsa gaisuwar ta da fara'a, Ammi dai na tsaye stairs taki karasowa cikin parlon all her attention na kan Mayraah, Mama Ladi da take ganin abinda ake bai shafeta ba ta mike tana kallon Ammi tace "Ke har yanzu fa shegiyar me aikinki bata kawo ma bakuwar nan abinci ba, ko kafura ce mai aikin da bata san ance baƙon ka annabinka ba" Ammi bata tanka Mama Ladi ba, don dauke kai ma tayi, Hajiya Amina na murmushi tana kallon Mama Ladi tace "Ayya Mama nace mun yi breakfast kafin mu fito" Mama Ladi tace "Aa ko farfesun ne bari inje in debo maki da burodi mu bamu gaji rowa ba a pamilyn mu" Daga haka ta wuce kitchen da sauri, Ammi ta juya ta wuce sama Abba ya bi ta da kallo, Mayraah na son tashi daga kusa da Hajiya Amina ta bi Ammi amma sai ta kasa, gaba daya she is not comfortable sitting down with her, mikewa Abba yayi ya wuce sama. Sai kusan karfe sha biyu Hajiya Amina da Abba suka bar gidan har sannan kuma Ammi bata sauko kasa ba, sai upstairs Hajiya Amina ta tafi tayi mata sallama a part dinta, Mama Ladi kuwa babu wanda zai ce ba wajenta Hajiya Amina ta zo ba don babu labarin karaye da bata ba Hajiya Amina ba, saboda ita ne ma har Hajiya Aminar ta iya kai wa karfe sha biyu a gidan, tunda ita kadai ce downstairs sai Usman dake aiki da laptop dinsa a dining area. Mayraah ta shiga dakin Ammi bayan tafiyar Hajiya Amina ganinta kwance har a sannan ta zauna gefenta tana kallonta tace "Ammi ko dai baki da lafiya ne?" Ammi ta sakar mata murmushi tace "Aa kawai hutawa nake Daughter" Mayraah tace "Toh ba abinda za a kawo maki?" Ammi tace "Aa... i am okay" Shiru Mayraah tayi, tun dazu take zaune dakin da Badiyyah take kwance bayan Ammi tace ma Badiyyar ta koma can za a gyara mata part dinta, ita dai ta rasa wani irin tausayin Badiyyah take har cikin ranta, sai Mama Ladi ce ta zo ta kirata taje suyi sallama da Hajiya Amina tana mata mitar meye hadinta da Badiyyar zata ne ta makale mata kowa na baya baya da ita salon ta shafa mata wani cutar, ita dai Mayraah bata ce mata komai ba, bayan tafiyar Hajiya Amina ne ta hauro sama ta shigo part din Ammi, mikewa Mayraah tayi after some minutes, Ammi na kallonta a hankali tace "Anjima idan na tashi ki zo in gyara maki gashin ki" Mayraah tace "Toh Ammi" Fita tayi daga dakin ta koma dakin da Badiyyah take, Badiyyah na kallonta da kyar tace "Baƙin sun tafi? Ina son in je parlor na gaji da nan din" Mayraah tace "Eh sun tafi" Ita kanta Badiyyah yau ta ɗan samu sukuni tunda ba ayi neglecting dinta as always ba, yau gashi har ruwan wanka sai da Mayraah ta tara mata ta samu tayi wanka, hatta Ammi bata bi ta kanta a gidan iyaka ta ajiye mata abinci in ta ga dama ta ci, wanka ma idan ta ga dama taje ta tara ruwa tayi, sai kuma Maheer da ta saka yake bata medication shi ma yana ajiye mata magani yake fita, Mama Ladi kuwa sai dai bata kyallara ido ta ganta ba, munanan kalamu sai wanda ta manta ne bata sakar mata, hakan kuma ke sa Badiyyar kuka sosai taji kamar ta mutu ta huta kawai, yau kuwa tun da Mayraah ta dawo take by her side even if she is not saying anything to her, Mayraah tace "Sun tafi, za ki iya saukowa, ba kowa a parlon" Da kyar ta lallaba suka koma downstairs ta kwanta nan tsakar carpet, sabuwar mai aikin gidan ce ta kira Mayraah da ladabi tace "Hajiya ta hanata saukowa ta kwanta nan saboda baƙi masu shigowa fa" a hankali Mayraah tace "Ba jimawa zata yi a nan ba" Suna cikin magana Haseenah ta leko Parlon don tabbatar da Mama Ladi bata ciki kafin ta shigo, tana ganin bata parlon ta shigo zata kitchen ta debi abincin rana, dama yanzu ko gas bata kunnawa sai an girka a nan ta faki idon mama Ladi ta shigo ta diba tunda ba wai kanta ya gama healing bane ita ma har yanzu jinya take, tana kyallara ido taga Badiyyah ta fara wakar habaici tana taunar cingam wai wata tayi cikin shege don ta ci ragon suna.... Can kuma ta hango Mayraah wani matsiyacin kallo ta mata ta shige kitchen bata fasa wakar da take ma Badiyyah ba, Mayraah dai ta bi ta da kallo, ita dai Badiyyah dama ko kallon direction dinta bata yi ba don duk haduwar da za su yi da Haseenah a gidan wakar da take mata kenan, to tana fama da kanta ina taga ta kulata. Washegari wajen karfe goma na safe Mayraah ta tashi daga baccin da take, har ta mance rabon da tayi bacci peacefully kuma me tsayi