Showing 213001 words to 216000 words out of 452169 words

Chapter 72 - Mayrah Complete By Khaleesat Haydar

haka, wanka tayi ta shirya sannan ta gyara ma Ammi dakinta ta fito parlor, Maheer ta gani zaune parlon shi kadai, ta karasa kusa da shi ta zauna kasa tace "Yaya ina kwana?" Yana kallonta yace "How was ur night?" Tace "Alhamdulillah" Yace "Kan ya daina ciwo?" Ta ɗan buda ido sannan ta cire dankwalin kanta don gashinta suka zubo kasa tace "Ya daina" Tun jiya da Ammi tayi mata kitson kalaba take complain din ciwon kai don ta dade bata yi kitso ba, hakan ma yasa ta kwanta da wuri jiya da daddare, yanzu kuma da ta tashi taji babu ciwon, yana kallon kitson nata yace "Yayi kyau" Murmushi tayi tace "Thank you, yaya result dinmu fa?" Sai bayan da tayi tambayar gabanta ya fadi sosai she can't imagine her spilling, ya ɗan yi shiru yana kallonta, nan da nan hawaye ya cika idonta, yanzu gaba daya hawaye baya mata wahala nan da nan take hawaye, cikin rawan murya tace "I had issues ko?" Yace "Nasan tsohon saurayinki ya gaya maki ai" Har sannan gabanta na faduwa tace "Wallahi yaya A'a, babu ta inda zai yi accessing dina ya gaya min" Yace "Ai na zata kin ga result din naki tuntuni" Ta girgiza masa kai tayi narai narai da ido, yace "To bari in nuna maki, but...." Hankali tashe tace "But what yaya??" Yace "Promise me u will be calm ko me zaki gani, kuma ki gode Allah" Wasu hawayen ne suka taru idonta, yace "Toh shikenan" Da sauri ta goge idonta tace "I will be calm plss" Yace "Good, dawo nan" Mikewa tayi ta koma gefensa da ya nuna mata ta zauna sai tsuru tsuru take da ido, ya shiga WhatsApp dinsa ya nemo chat dinsa da Hamidah da ta turo masa result din, Mayraah da duk jikinta ke bari don bata san me zata gani ba ta rufe fuskarta da kujera, ya dubo result din da Hamidah ta turo masa sannan yace "Here...." Ƙin dagowa tayi tace "Kawai ka gaya min plss" Yace "Toh shikenan bari in ajiye wayar" Dagowa tayi da sauri ta amshi wayar cikin dakiya tana kallon screen din, wani kara tayi ganin pass, ta maida dubanta da sauri gun CGPA dinta kawai taga da first class dinta ta fita, ai bata san sanda ta rungumesa ba cike da farin ciki, ya ɗan buda ido yace "Ke... baki da hankali ne" She was soo happy ta zamo kasa tace "Alhamdulillah" Sai kuma tayi sujud shukr, yace "To abinda ya kamata kiyi kenan kike shirme" Mayraah ta dade bata yi farin cikin da tayi a moment din nan ba, amma fa can kasar zuciyarta tunanin ta yanda za ace ta fita da first class take, ita fa tasan abinda tayi a exams din, how comes Kuma ta fito da first class dinta still, but all the same she is soo Happy, mikewa tayi ta dawo gefen Maheer ta zauna tace "Yaya how about sis Badiyyah's result?" Yace "She was expelled" Jikin Mayraah yayi sanyi tayi shiru tana kallon sa, shi ma kallonta yake, can ta sunkuyar da kanta, yayi kasa da murya yace "Je ki amso breakfast dinki" Mikewa tayi ta fita daga parlon ya bi ta da kallo. Bayan 4 days da dawowan Mayraah tana kwance dakin Ammi da rana wayarta ya fara vibrate, dubawa tayi taga Dr Khalil ne ke kiranta tunda ta dawo sau daya ya kirata sai yanzu kuma, dagawa tayi ta kai kunne tayi masa sallama, bayan ya amsa ta gaishesa, yace "Ya kike ya gida?" Tace "Alhamdulillah, ya Ashnaah da Ashfah" Yace "They are fine, kin koma gida kin mance mutane ko" Murmushi tayi tace "Aa ni ban manta ka ba...." Yace "Gashi nan ko hello babu" Tace "Ai bana son in kiraka ne saboda mom twins" Yace "I understand Mayraah, ya Umminki?" Tace "She is fine Alhamdulillah" Yace "Ranan ai Barrister ya hadani da ita mun gaisa" Tace "Da gaske??" Shiru Dr Khalil yayi saboda bude office dinsa da aka yi, ganin wanda ya shigo yace "I will call u back" Daga haka ya katse wayar ya ajiye, Files din hannunsa yayi dropping masa kan table yace "I will be flying to Adamawa later, attend to this files and submit them to me before evening" Dr Khalil yace "Ohk sir, zaka je wajensu Mama kenan" Bai ce masa komai ba yana duba wani textbook dake kan table dinsa, Shi dai Dr Khalil kallonsa kawai yake, after checking the textbook ya daga kai ya kalli Dr Khalil yace "At last ka hakura ka samar mata aikin a wani asibitin kenan, but i was surprise da naga baka yi resigning ka bi ta can ba" Dr Khalil yayi kamar bai gane maganar da yake ba yace "Wa kenan?" MD na kallonsa yace "Ka fi ni sani" Dr Khalil ya fashe da dariya yace "Wait!!! Are you trying to ask for her whereabout in disguise?" MD ya hade rai kafin yace komai Dr Khalil yayi saurin cewa "She is being sick, very sick, ko picking call bata yi.... Kuma as our boss ya kamata kai da any other Dr or Nurse including me mu je mu dubata, she is seriously sick, an tafi da ita kano gun iyayenta...." Juyawa MD yayi ya fita daga office din, Dr Khalil ya bi sa da kallo yana murmushi. Bayan magrib Mayraah ta sauko downstairs ta shiga kitchen don dafa ma Ammi shayin da ta saba yi mata, bayan ta daura tea din ta zuba duk kayan kamshin da zata saka aka bude kofar kitchen din ta juya da sauri, ya shigo kitchen din suna hada ido tace "Ina yini" Bai sake kallonta ba yace "Lafiya lau" Rabonta da ganinsa tun jiya da safe, plate ya dauka zai debi abinci ta bi sa da kallo jin yanda yake wani kamshi tace "Yaya Maleeha fa?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Wacece haka?" Ta wara ido tace "Ita Maleehar ce baka sani ba?" Yace "Tuna min dai" Dariya ta fara yi sosai, ya juya yana kallonta tayi dariyar me isarta tayi shiru, still shi dai kallonta yake, tace "Kilan ma daga wajenta kake yanzu haka yanda naji kana kamshi shine kake min pretending" Yace "Haba" Ta kara kyalkyala dariya tace "I am sure" Yace "Aa sai dai ki rakani mu je yanzu" Da sauri tace "To don Allah mu je, bari inyi sauri in gama yi ma Ammi shayi sai in kai mata kafin nan ka gama cin abincin sai mu tafi" Yana kallonta ya mayar da abincin da ya fara diba a warmer yace "Sai mun dawo zan ci" Ta ɗan buda ido tace "Toh kaci ko kadan ne mana" Girgiza mata kai yayi without saying anything, tace "Toh bari in baka shayin Ammi kadan ka sha" Daga haka ta maida hankalinta kan shayin da take, shi dai yana tsaye yana kallonta, cikin few minutes ta gama dafa shayin ta dauko karamin tea cup da saucer dinsa ta fara zuba masa, sannan ta nufesa tana kallonsa kamar yanda shi ma yake kallonta, mika masa tayi a hankali tace "Here" taga bai amsa ba kuma kallonta yake, tace "Yaya" Sai da ta sake kiransa yayi saurin mika hannu ya karba, tace "Why are u absentminded? Tunanin me kake yi" Bai sake kallonta ba yace "Nothing, idan kin gama ina jiranki" Daga haka ya fita daga kitchen din ta bi sa da kallo, wani mug ta dauka ta zuba ma Ammi shayin bayan ta kashe gas din ta goge wajen ta fita daga kitchen din, tana ajiye ma Ammi shayin tace "Ammi gashi na gama" a hankali Ammi tace "Allah maki albarka" Mayraah tayi murmushi ta mike tace "Ammi zan raka ya Usman wajen wata frnd dinsa yanzu" Ammi ta kalli agogo tace "Frnd kuma?" Dariya tayi tace "Eh" Ammi tace "Toh sai kun dawo amma plss kar ku jima dare yayi" Hijab Mayraah ta shiga dakin Ammi ta dauka, sai da ta fara shafa turare a jikinta, har ta mance rabon da tayi amfani da wannan special turaren nata tun kafin a fasa aurenta ta daina amfani da turaren sai yau kuma da ta daukosa cikin kayanta, bayan ta gama shafa turaren ta dau Hijab dinta ta saka sannan ta fita tayi ma Ammi sallama, sai da ta fara shiga dakin da Badiyyah take ta sameta tana bacci, abincin da ta kawo mata ma kadan ta samu ta ci, Mayraah ta rufe sauran sannan ta fita downstairs, zaune ta tadda Usman a parlon yana jiranta ga tea cup din da ta zuba masa shayi ya sha rabi ya ajiye sauran, tana kallon sauran shayin a hankali tace "Yaya bai maka dadi bane?" Yana kallonta yace "Yayi" Tace "To naga baka shanye ba" Yace "Ya isa" Karasawa tayi ta duka gabansa ta dau sauran shayin ta wuce kitchen ya bi ta da kallo, Mayraah na shiga kitchen din ta shanye sauran shayin ta wanke cup din da sauce ta ajiye inda sauran suke sannan ta fito, tana kallonsa tace "Yaya mu je" Mikewa yayi ya nufi kofa ta bi bayansa. Suna fita compound din bayan sun bar anguwan taji yace "Kar ki sake saka turaren da kika saka yanzu" Mayraah ta juya tana kallonsa da mamaki, can tace "Saboda me yaya?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Kar ki sake kawai nace" shiru tayi bata ce komai ba, bata ce masa komai ba, ita dai tana ta zuba ido ta ga ta inda za su billo gidansu Maleeha tunda ta san gidan kuma taga sun wuce hanyar gidan, bayan sun yi nisa sosai da anguwan ta kasa daurewa ta juya tana kallonsa tace "Yaya sun tashi ne daga gidansu?" Yace "Ehh" Tace "Ayya, i was wondering naga mun wuce unguwan tun dazu" Ya juya ya kalleta yace "Kin taɓa zuwa ne?" Ta zaro ido tace "Gaya min fa tayi" Yace "Ohk" after almost 30mins ride ta gansu a wani anguwa na masu shegen kudi, ta dinga bin manyan gidajen da kallo har taga yayi horn bakin wani gate mai gadi na lekowa ya gansa ya buda gate din ya shiga yayi parking yana kashe motar ya sauka, Mayraah ma ta sauka ya kulle motarsa, ganin ya nufi entrance din gidan da sauri tace "Yaya ba kiranta zaka yi ba tukun" Yace "Na kirata ai" Bin bayansa tayi har suka iso kofar shiga cikin gidan, Mayraah was shock ganin Hajiya Amina ta bude masu kofa, da fara'a take masu sannu da zuwa, Mayraah dai ta sunkuyar da kanta, da tasan nan Ya Usman zai kawota da babu abinda zai sa ta biyo sa, haka nan dai ta zauna kan kujera ta gaisheta, Hajiya Amina ta amsa da murmushi tana tambayarta Ammi Mayraah bata dago kanta ba tace "Tana nan lafiya" Hajiya Amina ta kalli Usman tace "Kwana biyu shiru baka billo ba Barrister" Sai kuma da sauri tace "Au na tuna Yallabai yace min kaje kaduna, to ya aikin?" Yace "Alhamdulillah" mikewa yayi yace "Zan shiga masallaci inyi sallah" Tace "Toh shkkn" Daga haka ya fita parlor zai tafi masallacin dake jikin gidan daga gefe wanda Abba ya gina, Hajiya Amina na kallon Mayraah tace "Mu je Abban naki na sama a parlor ki gaishesa" Mayraah ta mike har a sannan fuskarta babu wani walwala ta bi bayanta zuwa upstairs, Abba yayi farin cikin kawo Mayraah da Usman yayi, dama yana ta son ce ma Ammi a kawota gidan ko yini ne tayi amma ya bar ma zuciyarsa don bai san yanda Ammi zata dau batun ba, liyafar abincin da Hajiya Amina ta ajiye masa ya zuba masu tare da Mayraah, Hajiya Amina tace "Je ki ga ko yayan naki ya dawo masallaci ya zo ya ci abinci" Mikewa Mayraah tayi ta fita daga dakin ta sauka downstairs, Zaunawa tayi kan kujera ganin Usman bai shigo ba, bayan some minutes sai ga shi ya shigo parlon, ta tashi tana kallonsa tace "Yaya wai kaje sama inji Abba, pls yaya kana gama cin abincin ka maida ni gida plsss don Allah" Sosai ta marairaice masa don har ga Allah gida kawai take son ta ganta, Yace "Nan din ba gida bane?" Ta wani hade rai tace "Ni dai pls mu tafi gida" Sama ya wuce ta bi bayansa har zuwa parlon Abba, kusan duk bayan kwana biyu sai Usman ya zo gidan sai in baya gari, Maheer ne dai tun ranan da Abba ya kirasa ya zo bai sake bin hanyar gidan ba har yau, Da kyar Mayraah ke cin abincin da Abba ya zuba masu, Hajiya Amina na zaune parlon tana kallon TV, har daga karshe Mayraah ta mike tace ta koshi, Hajiya Amina tace "To mu je kiyi sallan isha" Babu yanda Mayraah ta iya haka ta mike ta bi bayanta suka fita parlon zuwa part dinta, bayan tafiyarsu with few minutes Usman ya ajiye spoon din hannunsa, Abba yace "Are you satisfied" Usman bai yarda ya kallesa ba, kansa na kasa yace "Sure... dama Abba akwai maganar da nake son zan yi maka" Abba na kallonsa yace "Ohk, i am all ears barrister" Ganin yayi shiru kamar me tunanin ta inda zai fara maganar Abba yace "Ina jin ka Usman, tell me what is it" Usman ya daga kai a hankali ya kalli Abba.....

Mayraah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa bello jidda

Ur evidence via 07087865788

*Ina Mai farin cikin gabatar maku da garin Sabaya gangariya Mai dadin gaske Wanda zata cikomaku da da ramar ku jikin ku yayi gwanin sha'awa* *Ina uwar gida da Amarya zawarawa yanmata Kai jama'aaaa wannan lafiyayyar sabayar ta mamn Khadijah har maigidan ma da yaran gida duk zasu iya Shanta batada wata matsala dan neman Karin bayani zaku iya tuntubar mamann Khadijah Kai tsaye ta number waya ko WhatsApp*
07037777442

64
Shiru Abba yayi yana ta kallon Usman, can ya ɗan yi murmushi yace "Did you say this to anybody? I mean did u discuss it to anyone?" Usman ya girgiza masa kai without looking at him, Abba ya sauke ajiyar zuciya, bayan few seconds yace "Not even her?" Usman yace "Eh" Abba na gyada kai yace "Gaskiya nayi farin ciki da wannan batun Usman, i am so happy about it, and this is what i wished for few months back, but...." Usman ya daga kai ya kalli Abba, calmly Abba yace "I want u to let ur intentions be known to her before anything...." Usman ya girgiza kai da sauri yace "Abba kawai ba sae nayi hakan ba, kawai dai..." Sai kuma yayi shiru, Abba yace "You have to Usman, kwanaki i wasn't willing to give her an alternative cause tunanina hakan kadae ne mafita gare mu da ita baki daya, and i understand you too then da kayi declining... But yanzu i don't think i will do anything without her consent, say ur mind to her, go on a courtship with her...." Kallon Abba kawai yake baya ko kifta ido, Abba jinjina masa kai giving him assurance yace "Ko nan da sati daya ne in dai da consent dinta you gat my back son" Usman bai iya yace komai ba ya sauke kansa, Abba dai sae kallonsa yake, bude kofar parlon aka yi Mayraah ta shigo da sallama, Abba ne kawai ke kallonta, Usman kam bai daga kai ba, har ta karaso ta zauna gefensa tana kallonsa tace "Yaya na gama mu tafi gida" Abba yace "Nan din ba gida bane?" Ta kallesa ta ɗan yi murmushin karfin hali tace "Abba ae ban ce ma Ammi zamu kwana ba shi yasa" Abba ya gyada kai yace "Toh in kin ce mata sai ki zo kiyi weekend a nan din" Mayraah dai bata ce komai ba ta mike tana kallon Usman tace "Yaya Ammi fa tace kar dare yayi sosai" Sai a sannan ya daga kai ya kalleta yace "To ba yanzu zan tafi ba" Ta marairaice tana kallonsa, mikewa Abba yayi yace "Naga ko karfe tara bai karasa ba ai Mimi, so there is still time, bari inje inyi sallah" Fita yayi daga parlon, Mayraah ta zauna kusa da shi kamar zata yi kuka tace "Yaya pls kaga dai Ammi bata san za mu zo nan ba ko, kuma ce min kayi wajen Maleeha fa za mu je, ni dai ka tashi mu tafi gida don Allah" jin yayi shiru ta ɓata fuska tace "Ka ji mana yaya" Sai a sannan ya juya ya kalleta yace "Nan din daji ne?" Ta turo baki ta koma ta jingina jikin kujera tana kallonsa fuskarta a daure, har bayan minti sha biyar bai ce mata ba, ita ma bata ce masa ba a parlon, lkci lkci take turo baki duk yana lura da ita, can ya mike tsaye, tana ganin haka ita ma ta tashi, ya kalleta yace "Ke a nan fa za ki kwana" Ko rufe baki bai yi ba tace "Wallahi bazan kwana ba" Tana fadin haka ta nufi kofa yace "Kar ki fita" Dawowa tayi tana kallonsa kiris ya rage ta fashe da kuka, ya koma ya zauna kan kujera, a hankali yace "Now tell me, me yasa baza ki kwana nan ba?" Ta zauna kasa daga gefensa tace "Kawai wajen Ammi zan tafi" Jin bai ce komai ba ta daga kai suka hada ido, tace "Pls mu tafi yaya" Hajiya Amina ce ta shigo parlon tana kallon sauran abincin da ba a taɓa ba tace "Ka ci abincin kuwa barrister?" Yace "Eh na ci, za mu tafi ne" Hajiya Amina tace "Ina ce ai a nan Mayraah zata kwana" Usman yace "Bata zo da shirin kwana ba" Hajiya Amina tace "Toh shikenan, ko weekend ne sai ta zo" Mayraah ta sauke wani ajiyar zuciyar relieve sanda taga sun bar gidan. Sai da suka yi nisa sosai ta kallesa tace "Yaya baza mu siya ma Ammi Apples da watermelon ba?" Yace "Ok za ki siya mata?" Tayi er dariya tace "I am not together with my Atm?" Ya ɗan kalleta yace "Nawa za a ara maki?" Ta langwabar da kai tace "Like 10k" Yace "Ohk" gun da ake siyar da fruits yayi parking ta juya ta kallesa tana jiran ya bata

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login