Showing 216001 words to 219000 words out of 452169 words

Chapter 73 - Mayrah Complete By Khaleesat Haydar

kudin taje ta siyo, bude motar yayi ya sauka ta bi sa da kallo, bayan wasu mintuna ya dawo ya ajiye mata ledan kan kafarta yace "15k, sai ki biya yaushe?" Dariya tayi tace "Muna isa gida" Yace "Alright" Suna isa gida bayan yayi parking ta bude motar ta sauka ta jira shi ma ya sauka, bayan ya rufe motar ya jingina jiki folding his arms yace "Mun iso gida" Bata san sanda ta fashe da dariya ba tace "Yaya ko ciki fa bamu shiga ba" Yace "Toh" Daga haka ya nufi cikin gidan, ta bi bayansa tana murmushi, suna shiga parlor Maheer kadai ne zaune yana danna wayarsa, sau daya Usman ya kallesa ya wuce sama, Mayraah na ganin Maheer ta nufi kujeran da yake ta zauna kasa ta ajiye ledan hannunta tana kallonsa tace "Ina yini yaya" Yace "Ina ku ka je?" Ta buda ido tace "Yaya ce min fa yayi wajen budurwarsa zai je shine ya kai ni Miller road, ashe wajen Abba zai je" Maheer ya maida dubansa kan waya yace "Ohk" Tace "Yaya ka ara min 15k cash pls" ya kalleta yace "Me za ki yi da 15k?" Tana murmushi tace "Just borrow me pls" Yace "Sai ki maida yaushe" Dariya ne ya taho mata tace "Gobe da safe" Yace "Ohk, mu je in baki" yana fadin haka ya mike, tashi tayi ita ma ganin ya nufi kofar fita tace "Aa yaya zan jira a nan ka kawo min pls" Ya juya yana kallonta yace "Why?" Shiru tayi bata ce komai ba, ya karasa kusa da ita, still looking at her yace "Why?" Ta sauke ajiyar zuciya tace "I am not going there because of ur wife" Yace "Do not call her my wife again Mimi, Haseenah is not my wife" Ita dai bata ce komai ba, yace "Mu je" a hankali ta fara tafiya tana biye da shi a baya, sai da suka iso chalet din tace "Amma bazan shiga ba, i will wait outside Yaya" Tana fadin haka ta tsaya dai dai stairs din chalet din, shi ma bai yi forcing dinta ta shiga ba, yana bude kofa Haseenah dake zaune kan kujera tana waya ta katse wayar tana goge hawayen idonta tana kallonsa, ko kallonta bai yi ba ya bar kofar a bude ya wuce daki, kamshin turaren da ta dinga ji na shigowa parlon ya sa ta mike ta taho bakin kofa don jikinta ya bata da mutum a wajen, tana ganin Mayraah bata bari sun hada ido ba ta koma inda take ta zauna, ba a dau lokaci ba Maheer ya fito da cash din a hannu, ya mika ma Mayraah ta amsa tace "Thank you Yaya" Shi dai bai ce mata komai ba yana kallonta, ta juya ta sauka daga chalet din ta koma main building din gidan da sauri, ledan fruits din ta dauko sai da ta fara zuwa dakin Usman tayi knocking ya bude kofar ganinta ya koma ciki ya zauna, ta bi bayansa tana murmushi tace "Ga kudin" Amsa yayi ya ajiye gefensa, ta juya ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita. Washegari Mayraah na idar da sallan asuba bayan ta gama azkar ta shiga dakin da Badiyyah take, zaune ta sameta kasa, Mayraah ta zauna tana kallonta tace "Ya jikin?" Badiyyah ta gyada mata kai, Mayraah tace "In kawo maki kunun ko shayi" Badiyyah tace "Ko wanne" Mikewa Mayraah tayi ta fita, Bangaren Ammi ta fara tafiya don ta gaisheta, tana shiga ta tadda Mama Ladi na minshari kan darduman da tayi sallah, dakin Ammi ta karasa tayi sallama, Ammi ta amsa mata, ta shiga dakin... Maheer na zaune gefen Ammi, ita kuma tana zaune kan darduma, Mayraah ta duka kusa da Ammi ta gaisheta, Ammi tace "Kin tashi lafiya" Mayraah tace "Alhmdlh" Kallon Maheer dake kallonta tayi tace "Ina kwana yaya" Yace "Lafiya lau" Mikewa tayi tace "Zan dawo Ammi" Daga haka ta nufi kofa Ammi ta bi ta da kallo har ta fita, sai kuma ta kalli Maheer a hankali tace "We will continue later Maheer" Bai bari sun hada ido ba yace "Ohk" daga haka ya mike ya fita daga dakin. The next day friday Mayraah na dakin Badiyyah da yamma Mama Ladi ta shigo, Mama Ladi tayi tagumi daga tsayen da take tace "Naga abinda ya isheni ni Ladiyo, Wato ke dai Mera baza ki ji shawaran da nake baki ba ko? Baki da aiki sai makale ma wannan mata kamar almajira, nace ki fita hanyarta kiyi ta kanki kin ki, me yasa kike cusa kanki a abinda bai shafeki bane? yarinyar da kowa yasan ba sonki take ba tun asali, yarinyar da saboda ita kiri kiri aka fasa aurenki da ɗan matsiyatan can, ko ke baki lura alhakinki ke bin ta ba? Ko wani me ciki za ki ganta fes fes gwanin sha'awa amma Badiyyah kamar sabuwar almajirar kana rod dake garin kaduna, ke ko don kar kije ki shaƙi wata cutar baza ki kama kanki daga zuwa inda Badiyyah take ba? To ni dai ba ruwana Mamuda na kiranki, yana can parlon Ammi yace ki je" Daga haka Mama Ladi ta fice daga dakin tana toshe hanci, Mayraah ta kalli Badiyyah da hawaye ya cika idonta, kasa ce mata komai tayi amma har cikin ranta bata son abinda Mama Ladi ke yi ma Badiyyah a gidan, abun yayi yawa, mikewa tayi ta fita daga dakin ta tafi bangaren Ammi, Abba na zaune parlorn Ammi, Ammi kuma na ta harkan gabanta, Mayraah ta zauna ta gaida Abba, Abba ya amsa yace "Anjima Usman zai kai ki can gidan Hajiya Amina kiyi weekend, mai aikinta bata nan" Sai a sannan Ammi ta juya ta kalli Abba, Mayraah dai ta kasa cewa komai tana kallon Abba, Abba yace "Sai ki dau kayan da za ki tafi da su" Ammi na kallon Abba cikin karfin hali tace "Mamuda kawai fitowa za kayi kace min kana son ta koma gidan matarka, ba sai ka yi wani corner corner ba, just go straight to the point" Mayraah ta sunkuyar da kanta lokaci daya har hawaye ya kawo idonta, Abba na kallon Mayraah yace "Tashi ki tafi kiyi abinda nace maki" Mayraah ta mike ta juya ta nufi kowa hawayen dake makale idonta ya zubo fuskarta ta fita daga parlon, sai a sannan Ammi ta fashe da kuka ta nufi dakinta, Abba ya bi ta da kallo, sai kuma ya tashi ya bi bayanta, kuka sosai ya sameta tana yi, ya zauna gefen gado yace "Kin ga, babu ta yanda za ayi kice zan raba ki da Mayraah, Mayraah is staying there for just 2 days ta dawo nan..." Cikin kuka Ammi ta katse sa tace "To ban amince ba Mamuda, kuma bazan taɓa amincewa ba, babu inda Mayraah za ta je ai ba wani ɗan iskan ya rainan min ita har zuwa yau ba, ba wani ya sha min wahalanta ba, ba wani ya...." Kasa ci gaba tayi tana kuka sosai zuciyarta na mata zafi tace "Mamuda kar ka sa inji ina dana sanin aurenka, abinda ban taɓa yi ba sai yanzu da aurenmu ya doshi shekaru arba'in, wahalan da na ci a gidanka da irin sadaukarwa ta da abinda zaka biya ni kenan? Is this what i deserve Mamuda? Is this how to pay me? Ko me zan maka na cancanci haka? Me yasa zaka yi saurin mance halacci na gareka? After all my sacrifice yanzu wata from no where zata zo ta fi ni ƙima da mutunci a idonka, wata ce zata zo tayi reaping where she never sowed, ban taɓa zaton haka daga gareka ba Mamuda, kuma a duk zaman mu in dai na cuceka...." Kasa ci gaba tayi tana kuka sosai ta mike ta bar masa dakin kawai, ya sake tashi ya bi ta parlor. Mayraah na dakinta bayan ta ci kukanta Abba ya kwankwasa kofar ya bude, mikewa tayi daga zaunen da take tana kallonsa, Abba yace "Dauko kayanki" Yana fadin haka ya bar bakin kofar, jikin Mayraah yayi sanyi sosai, fitowa tayi daga dakin ta tafi bangaren Ammi, a bedroom dinta ta sameta, Mayraah ta karasa kusa da ita ta zauna ta ma rasa abinda zata ce, Ammi tayi karfin halin cewa "Ki je kiyi yanda Abbanki yace Mayraah" Mayraah ta fashe da kuka tace "Ammi ni bana son in je gidan" Ammi tace "Ran sunday za ki dawo in sha Allah, in ma ba a dawo dake ba zan sa Maheer yaje ya dauko ki, be a good girl kije ki dau kayanki kala biyu" Kuka kawai Mayraah take, Ammi tace "Tashi ki je my dear" Mikewa tayi tana goge hawayen idonta ta tafi ta dau kayan nata kala biyu a karamin jakanta, tana dawowa bangaren Ammi ta tadda Abba a parlon, hakan ya sa ta juya ta fita ta sauka downstairs kawai, bayan kusan minti sha biyar Abba ya sauko yace "Je ki mata sallama ki zo mu tafi, i don't want go miss my flight" A hankali Mayraah ta mike ta wuce sama zuwa part din Ammi, a parlor ta sameta still a zaune, Mayraah ta zauna kasa tana kallonta cikin sanyin murya tace "Ammi don Allah kiyi hakuri..." Sai kuma ta fashe da kuka, Ammi ta dafa kanta tace "Kar ki damu daughter, u are not to be blame, ba komai, ranan lahadi Maheer zai je ya dauko ki" Mayraah ta gyada mata kai hawaye na sauka idonta, Ammi tace "Tashi ki je, idan yayi dropping dinki airport zai wuce" Mayraah ta mike tana goge hawayenta ta nufi kofa Ammi ta bi ta da kallo tana kokarin ganin hawayen da ya taru idonta bai zubo mata ba, Sai da Mayraah ta fara shiga dakin da Badiyyah take, ta duka gabanta tace "Zan je Miller road" Da sauri Badiyyah ta mike zaune ganin jakar hannunta cike da karfin hali tace "Yaushe za ki dawo?" Tana fadin haka hawaye ya cika idonta, Mayraah ta kwantar da murya tace "On Sunday in sha Allah, ba dadewa zan yi ba" Kai kawai Badiyyah ta gyada mata hawaye na sauka idonta, Mayraah ta mike ta fita daga dakin duk jikinta yayi sanyi. Suna isa gidan a waje Abba yayi parking suka shiga ciki, Hajiya Amina tayi farin cikin ganin Mayraah sosai, ganin yanda ta makale bakin kofa tace karaso ciki mana, sai a sannan ta karasa ciki ta xauna, sallama kawai Abba yayi ma Hajiya Amina, tayi amsa addu'an Allah ya tsare ta rakasa har compound ita dai Mayraah na zaune kan kujera makale da jakarta, sabon drivern da Abba ya dauka a gidan shi yayi driving dinsa zuwa airport, Hajiya Amina ta dawo parlor tana kallon Mayraah tace "Tashi mu je ki ga dakin ki" Mikewa Mayraah tayi ta bi bayanta suka tafi sama, Hajiya Amina ta bude mata dakin tace "This is ur room" Mayraah ta dinga kallon dakin ganin tsadaddun furnitures din ciki kamar dakin amarya, sauke kanta tayi kasa ta karasa cikin dakin. Bayan isha Mayraah na daki tana kokarin dialing number Dr Khalil saboda miss calls dinsa da ta gani Hajiya Amina ta shigo, hakan yasa ta fasa kiran, zaunawa gefen gadon Hajiya Amina tayi tana kallonta tace "Abincin ya isheki?" Mayraah ta gyada mata kai tace "Na koshi" Hajiya Amina tace "To maa sha Allah, ya kika baro su Amminku?" Mayraah tace "Lafiya lau, tana gaisheki" Hajiya Amina tace "Ina amsawa, chatting kike ne" Mayraah ta girgiza mata kai tace "Aa" Hajiya Amina tayi murmushi tace "To yanzu waye surkin namu ne?" Mayraah ta ɗan kalleta sai kuma ta sunkuyar da kai, Hajiya Amina na murmushi tace "Feel free to talk to me dear, i am also ur mother" Mayraah ta ɗan kirkiri murmushi da kyar tace "Aa ba kowa" Hajiya Amina tace "Are you sure?" Mayraah ta gyada mata kai, Hajiya Amina tayi shiru tana kallonta, can a hankali tace "Ni kuma kin san wa nake maki sha'awa Mayraah?" Mayraah ta daga kai ta kalleta ba tare da ta shirya yin hakan ba, Hajiya Amina tayi kasa da murya tace "Yayanki" Mayraah dai ta dinga kallonta tana imagining wani yayan take nufi har ranta bata kawo su Maheer ba fa tunda ita dai tasan ba aure tsakaninsu a mentality dinta, Hajiya Amina tace "Kin ga ya san halinki, ya san wacece ke, kema kuma kin san halinsa kilan har littafi sai ki iya rubutawa akan halayyarsa, you 2 will make a perfect couple Mayraah, beside he is a calm and gentleman" Mayraah ta sunkuyar da kai feeling uncomfortable with the conversation, har cikin ranta bata san wani yayan take nufi ba fa ita, Hajiya Amina tace "Kin dai ga abinda ya faru akan aurenki kwanaki, so hakan kadai shine rufin asirinmu gaba daya" Hajiya Amina ta kalli wayar hannunta dake ring ta mike tace "Bari in amsa waya" Daga haka ta nufi kofar Mayraah ta bi ta da kallo har ta fita...

65
Wajen karfe goma Mayraah na kwance sai juye juye take, har a lokacin maganganun Hajiya Amina sun kasa fita daga ranta, tayi kokarin gano wani yayan nata take nufi amma taki bari zuciyarta ya kai tunanin ta kan brothers dinta she just believe ba su bane and she is sure of that, wayarta ne ya fara vibrate, ta jawo a hankali tana kallon me kiran, Dr Khalil ta gani da kamar bazata daga ba sai kuma tayi picking ta kai kunne, gaisawa suka yi yace "Ina kika shiga yau baki picking call? A hankali tace "Bana jin dadi ne" Yace "Subhanallah, what's wrong with you?" Tace "Kawai kamar zazzabi ne" Yace "Allah ya sauke" Tace
"Ameen thank you" Yace "Dama za mu shigo kano gobe, kinga if it's okay we can come over mu duba ki kafin mu koma Abuja" Mayraah tayi shiru, can tace "Kai da wa?" Yace "Dr Balogun da Hamid, mun shigo wani program ne" Mayraah tace "Toh shikenan Allah ya kai mu" Yace "Ameen, Allah ya kara lafiya" Tace "Ameen Nagode sosai' Yace "Kinsan Ceo din ma ta koma tun last week but nan da few days zata shigo saboda workshop da za ayi" Mayraah tace "Ohk, Allah ya kai mu" Yace "Ameen, till tomorrow, in mun shigo kafin zan kira ki in sha Allah" Tace "To a gaida min twins" Yace "Za su ji" Daga haka ya katse wayar, mikewa zaune tayi tana tunanin yanda zata samu gobe ta koma gida wajen Ammi in ma Dr Khalil za su zo gwara suje can din su sameta a gidansu, don ita dai tasan nan ba gidansu bane, wayarta ta sake daukowa tayi dialing number Maheer, yana fara ringing ya daga a hankali tace "Yaya" Yace "Mimi" tace "Good evening" Yace
"So u still have my digit" Tayi murmushi kamar yana ganinta, yace "To ya aka yi?" Tace "Yaya plss i want to come back home tomorrow" Yace "Da gobe da jibi duk daya ne Mimi, just be patient, or is there any problem?" Ta girgiza kai tace
'I am not comfortable" shiru yayi, sae kuma yace "Kiyi hakuri ki bari har jibin sae ki dawo gida kar Abba yayi fushi" Bata sake cewa komai ba, yace "Are you there?" Cikin sanyin murya tace "Na ji" yace "Good gal" Tace "Zan kwanta" Yace
"Ohk sleep tight, kin ci abinci?" Ta gyada masa kai vace "To sai da safe" katse wayar tayi ta ajiye ta rufe ido. Washegari da yamma Mayraah na kitchen tana girkin da Hajiya Amina ta sa tayi masu, tuwo ne da vegetable soup tace tayi,
Mayraah har ta mance rabon da tayi girki, bata fito kitchen din ba sae kusan karfe biyar bayan ta gama komai, zaune taga Usman parlor, ta dan buda ido tace "Lah yaya yaushe ka zo?" Ya kalleta sannan ya ci gaba da danna wayarsa yace "Now" tace "Ina yini" yace "Lafiya lau" Tace "Ya Ammi fa?" Yace "She's fine" tace "In kawo maka tuwon na gama" Yace "Na ci abinci " tace "Ohk" karasowa cikin parlon tayi tana kallonsa ta zauna gefensa tayi murmushi tace "You look cute" ya daga kai ya kalleta yace "Really" ta gyada masa kai still looking at him, yace "Ke ma"ta zaro ido tace "Nima me?" Yace "Abinda kika ce min" ta kyalkyale da dariya tace
"Ae ka fi ni kyau, shi yasa Maleeha take ji da kai" shi dai kallonta kawai yake, sai kuma ya kamo hannunta calmly yace "Ke kuma kin fi Maleehar kyau ai" Mayraah tayi shiru jin abinda yace, lokaci daya ya saketa ya ciro wayarsa zai fara dannawa, tayi kasa da murya tace "Yaya don Allah in zaka tafi zan iya bin ka?" Yace "Abba yace sai gobe" Hajiya Amina ce ta sakko downstairs ganin Usman tace "Yaushe ka shigo barrister?" Yace "Yanzu" mikewa Mayraah tayi Hajiya Amina tace "Har kin gama girkin kenan?" Mayraah ta gyada mata kai tace "Na gama" Hajiya Amina tace "To Sannu da aiki" Mayraah ta dan yi murmushi ta wuce sama Usman ya bi ta da ido, Hajiya Amina ta karaso ta zauna tana kallonsa tace "Ya gidan?" Yace
"Alhamdulillah" Mayraah na shiga daki ta dau wayarta taga kiran Dr Khalil har uku an hour ago, zaro ido tayi don ta mance yace mata za su zo yau, kiransa ta fara yi, yana fara ring ya daga yace "Bacci kike ne?" Tace "Aa ina kasa ne, ina yini?" Yace
"Lafiya lau, ya jiki?" Tace "Alhamdulillah naji sauki" yace "Ba don an daga flight dinmu ba ae kilan da yanxu muna Abuja, sae 8pm Flight din, so now.... ina ne anguwan naku?" Ta dan yi shiru sae kuma tace " will call you back in few minutes time" yace "Ohk then" katse wayar tayi ta sauka downstairs, gun Usman ta nufa don
Hajiya Amina ta shiga kitchen, ta zauna kasa daga gefensa tana kallonsa tace
"Yaya wannan Dr din nan ne za su zo nan wai sun shigo kano wani program, can they?" Usman yace "It's okay... Mun yi waya da shi ae daxu na tambayesa ko zai karaso yace min babu time saboda flight dinsu 3pm ne" Mayraah tace "Eh yace min an daga flight din sai dare, i just

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login