Showing 219001 words to 222000 words out of 452169 words
Chapter 74 - Mayrah Complete By Khaleesat Haydar
saw his call" Usman yace "Ohk send him the address" Tace "Ai ban sani ba to, gashi kayi masa sending..."
" Tana fadin haka ta
mika masa wayarta, amsan wayar yayi ya rubuta address din gidan ya bata tayi sending ma Dr Khalil, sai ga kiransa ya shigo wayarta ta daga yace "Ohk expect us in 30mins time" Tace "To Allah ya kai mu" katse wayar tayi ta ajiye tana kallon Usman dake kallonta yace "Kije ki gaya mata za ki yi baki" Mayraah tayi shiru, sai ga Hajiya Amina ta shigo parlon da abinci ta debo masa, ya kalleta yace "Na fa ci abinci a gida" Tace "Ko kadan ne ka ci" Mayraah dai ta mike zata wuce sama don taje tayi wanka Hajiya Amina tace "Kema naga ba ki wani son cin abinci, dawo sai ku ci tare" Mayraah ta kalli Usman da Usman da
ya kalleta shi ma, Hajiya Amina ta ajiye
masu tuwo da vegetable soup tace "Taho
ku ci Hajiya" Mayraah tayi murmushin
karfin hali kawai ta koma ta zauna, Hajiya
Amina tayi wucewar ta sama, tuwon
Mayraah ta fara ci ba tare da ta jira sa
ba, bayan few minutes ya sakko kasa
shi ma ya dau spoon ya fara cin tuwon,
tana kallonsa tace "Is it sweet?" Yace
"'Wa yayi?" Ta langwabar da kai tace "Ni mana" Yace "Bari in gama tukun sae
inji ko yayi" Dariya tayi ta ci gaba da cin tuwon ta, bata wani ci da yawa ba ta tashi ta bar masa ta wuce sama, sai da ta fara zuwa dakin Hajiya Amina ta sanar
mata da zuwansu Dr Khalil sannan ta
koma dakinta tayi wanka ta shirya, jikin windown dakin ta tsaya tana viewing din
unguwan that's beautiful, sai abun yake
mata kamar ta taba zuwa anguwan nan,
ko ma dai ba shi ba ita dai tasan ta zo
area kamar haka, Lokaci daya Musharraf fado mata, ta zaro ido gabanta na
faduwa, kamar unguwan da ta taba zuwa
ta samesa fa, tana cikin wannan tunanin
wayarta dake kan gado yayi vibrate ta
juya ta dauko wayar ta daga ganin Dr
Khalil ne, yayi mata sallama yace "To, ga mu a house number din" A hankali
tace "Ohk" Katse wayar tayi ta dau veil
dinta ta fita, bata tadda Usman a parlor
ba, hakan ya bata mamaki, sai ta koma
sama ta gaya ma Hajiya Amina bakin
sun iso, Hajiya Amina tace "Ba sai kin fita
ba bari zan kira mai gadi ya bude masu
gate din kawai" Mayraah tace "To, yaya
ya tafi ne?" Hajiya Amina tace "Eh dama
Daura zai tafi, kuma ya wuce" Mayraah
tayi shiru, sai kuma tace "Bai ce min zai
tafi ba" Hajiya Amina tace "Ai na zata
kun yi sallama" Mayraah bata sake cewa
komai ba Hajiya Amina ta kira mai gadi
tace ya bude ma baki gate, Mayraah
ta juya ta fita daga dakin. Bayan some mintues ta sauka Downstairs don bude masu kofa, tana bude kofar taga Dr Khalil, murmushi tayi masa tace "Sannu da zuwa Baban twins" har cikin parlon tayi masa iso bayan sun gaisa ta kawo masa ruwa da lemo, yace "Ya jikin?" Tace
"Naji sauki, kace har da su Dr Hamid" yace "Ohh su mota za su bi zuwa kd sannan su dau train, sun wuce tun dazu, nima hakan na so yi but it's not possible" Mayraah tace "Allah sarki" Hajiya Amina ta shigo parlon suka gaisa da khalil da fara'a sannan ta koma sama, Dr Khalil yace "Ita ce Ammin?" Murmushi kawai Mayraah tayi, yace "I spoke to ur brother, the Barrister, about ur work.... he said he will get back to me idan yayi magana da Abbanku, that was today in the morning so ban san ya za su yi ba, ina dae jiran kiransa" Mayraah tayi shiru tana kallonsa, yace "So duk yanda Abbanku yace haka za ayi, i hope za su bar ki kiyi aikin, in future za ki ji dadin hakan, no matter how wealthy ur parents are yana da kyau ace kai ma kana da source of naka income din" Mayraah tayi murmushin karfin hali bayan ta tuna she is just an abandoned orphan warce ko gadon wa enda take ma kallon iyayenta bata da shi, tunanin hakan ba karamin distablizing dinta yayi ba a lokacin, Dr Khalil yace "I think zan zo in tafi airport kar in yi missing flight..." A hankali tace "Baka sha ruwan ba ai" yace
"am okay, i just ate" tace "Toh shikenan" ya mike yace "Kiyi ma Ammi sallama pls" tace "In sha Allah" rakasa tayi bakin kofar parlon, yace "Baza ki rakani har waje ba kenan" tayi murmushi tace "Zan raka ka" A tare suka nufi gate din gidan suka fita har kofar gida, ya kalli Mayraah yace "Mu je ku gaisa da wani Dr, kin dai san sa... tace "Ohk" karasawa gun motar tayi Dr Khalil ya bude kujera me zaman banza, turus Mayraah tayi tana kallon wanda ke zaune, shi ma tunda ya kalleta sau daya ya dauke idonsa yana ci gaba da kallon abinda yake yi a waya ya wani keeping serious face, ta kalli Dr Khalil da yayi mata alama da she should greet him, hakan yasa a takaice tace "Good day" ko jira ya amsa bata yi ba ta bar wajen, bata san shi ma bayi da niyyar amsawa ba, tana kallon Dr khalil tace "To Dr Allah ya tsare, a gaida min twins" Dr Khalil ya girgiza kai yana kara jinjina halinta, ta sakar masa murmushi tayi wucewarta cikin gida, Ta madubi MD ya bi ta da kallo har ta shige gidan, sae kuma ya kalli Dr Khalil yace "Wanna fitsararriyar yarinyar kake dagewa in shiga cikin gidan in duba ko? Does she even look like someone that is sick at all? Wallahi idan na maka
Allah ya isa batamin lokaci da kayi sai Allah ya kama ka, what nonsense, yanzu meye amfanin nan din da ka kawo mu?" Dr Khalil ya kasa rike dariyarsa don daga
Mayraahn har MD din ba karamin dariya suka basa ba, Dr Khalil ya zagaya ya shiga driver seat, MD yace "Allah bazan yafe maka ba, haka kawai kayi forcing dina mun zo nan yarinya ta fito ta min rashin kunya? Do you have any grudges against me Khalil?" Dr Khalil na danne dariyarsa yace "Oga boss i never forced u, kai da kace zaka Yola meye na biyo mu kano program din da kafi karfin attending, da ba sae ka tafi yolan ba kawai, sai dai in sharri zaka min sir, kuma fa ta ce maka good day" a fusace MD yace "Da na buge mata baki zata san good day, ni sa'anta ne da zata ce min good day, do i look like her mate ko an gaya mata Ina harka da yara, wannan fa bata wuce 16 years ba idan aka duba real date of birth dinta" Dr Khalil ya tada motar suka bar layin, MD ya gyara zama yace "Nonsense, saboda suna common Miller road shine take tunanin kowa sa'anta ne?" Dr Khalil yace "Yanzu dai ba Ghetto ka ganta ba balle ka samu abun fade" MD yace "Muna komawa Abuja zan yi erazing data din da ka bani, she should come for interview...
Dr Khalil dai murmushi kawai yake yana driving dinsa, can dai yace "Kai fa Dr ko manyan likitoci ba harkansu kake shiga ba, sabgar gabanka kawai kake baka da lokacin su balle wanna yarinyar da kace shekaranta 16, naga ita dai ta samu time dinka sosai"
66
Ranan Lahadi karfe sha daya Mayraah ta gama shiryawa ta rufe karamin jakarta, sannan ta dau wayarta ta kira Maheer, yana fara ring ya daga, yace "Mimi" Tace "Ina kwana yaya" Yace "Lafiya lau, how was ur night" Tace "Alhmdlh, dama ce maka zan yi na shirya" Yace "But ai sai da yamma Mimi" Ta ɓata fuska tace "Don Allah yaya ka zo ka tafi da ni gida, yau fa Abba yace, it doesn't matter ko da safe ne ko da yamma" Yace "Toh kin ga ina wajen aiki yanzu, after work sai in biyo in dauke ki, be patient please" Ji tayi kamar ta fashe da kuka, yace "Are you there?" da kyar tace "Na ji" Daga haka ta katse wayarta tana turo baki, bude kofar aka yi ta juya, Hajiya Amina ta shigo tace "Mu je ki rakani gidan makotanmu in masu gaisuwa, they lost their daughter 4 days ago" Mayraah tace "Toh" Mikewa tayi ta ciro Hijab dinta ta saka sannan ta bi Hajiya Amina suka fita, gidan dake kusa da na Abba suka shiga, Bayan Hajiya Amina tayi masu gaisuwa ta gabatar masu da kanta a matsayin neighbor dinsu don tun zuwanta anguwan ba gidan wanda ta shiga, godiya suka mata sosai, Ita dai Mayraah na zaune, bayan ɗan lokaci Hajiya Amina tace "Toh bari mu koma, Allah ya gafarta mata, ya bada hakurin rashi" Suka mata godiya sosai sannan ta fita parlon da Mayraah, suna fita gate din gidan Mayraah ta dinga kallon motar dake tafiya duk da ya wuce gidan da suka fito, Hajiya Amina tace "Kinsan wanda ke cikin motar ne irin wannan kallo haka" Mayraah ta girgiza kai da sauri tace "Aa" Daga haka ta bi ta suka shiga cikin gida, tana komawa dakinta ta dau wayarta, dialing number dinsa tayi da ainahin sim da take using yanzu, har ya katse bai daga ba, ta sake kira sai ya daga, shiru tayi, yana jin haka yace "Mayraah" Ta sauke idonta kasa a hankali tace "Good morning Sir" Yace "Me yasa kika daina kunna line din da kika kirani da shi kwanaki, pls me yasa kike min haka Mayraah, is it because i care? Is it because i love you" Nan da nan jikin Mayraah yayi sanyi jin yanda yake maganar, a hankali yace "Mayraah" Cike da karfin hali tace "Ina ji... naga ka fito gida yanzu, ina za ka?" Musharraf ya kalli inda yayi parking a anguwan, everywhere was so silent balle ace ta ji hayaniyar mota or so, yace "Did u just guess?" Tayi murmushi tace "I saw you.... But in my dream" cikin sanyin murya yace "Mayraah my life isn't the same again ever since you left me, ban san haka so yake ba i wouldn't have started wllh, ni ban gujeki ba duk situation din da ya faru ke kika gujeni, da na sani da na ci gaba da zamana ban fara relationship ba, i had no luck in relationship kuma tsakanina da Allah na so ki ba da wani nufi ba, i resigned lecturing few weeks back, lecturing caused me all what i am going through now, i regret it, assuming a asibiti nake aiki may be sau daya zan ganki ki tafi shikenan ba lallai ki sake dawowa in ganki ba, amma as a lecturer, seeing you everyday made me fell in love with you without me realizing that, i never bargained for all this Mayraah, i am still yet to recover fully from the death of my father and only sister, then all of a sudden you...." Kasa ci gaba yayi, nan da nan hawaye ya cika idon Mayraah jikinta yayi sanyi sosai ta kasa ce masa komai, ya katse wayar kawai, ta fashe da kuka, har ranta tasan she still loves Musharraf but su Abba baza su bari ta auresa ba, likewise his parent baza su bari ya aureta ba, kwanciya tayi tana kukan tausayin kanta. Wajen karfe hudu Maheer ya kirata, ta daga wayar tayi shiru, yace "Can i come over now?" A hankali tace "Yaya can i leave it tomorrow pls" Da mamaki yace "Why tomorrow?" Ta mike zaune tana dafe kanta dake mata ciwo tace "Kawai naji ina son in bari sai gobe da safe, ban san me yasa ba" Maheer yace "But are you okay?" Ta gyada masa kai tace "Ehh but deep down i want to leave tomorrow instead of today" Yace "Ohk then, zan gaya ma Ammi" Da sauri tace "How will you tell her?" Yace "Don't worry Mimi, zan ce mata ban baro asibiti da wuri ba" Tace "Yauwa yaya" Yace "Bacci kika yi ne?" Tace "Yanzu na tashi" Yace "Ohk, to bari in yi sallah it's almost time" Tace "Toh sai Anjima" Daga haka ya katse wayar ita ma ta mike ta shiga bandaki. Tana idar da sallah ta sake dialing number Musharraf, yana ta ring har ta fidda ran zai daga sai gashi ya daga, a hankali tace "When are you coming back?" Yace "To where?" Tace "Gidanka" Yace "I am home ae" tace "Naga ka fita dazu around 11:30" ya ɗan yi shiru, sai kuma yace "How?" Tace "In ur white car, u were on either black or navy Blue polo" Musharraf that was very surprise yace "Wait! How did you know?" Tayi murmushi cikin sanyin murya tace "That shows i am with you now and always" Musharraf yayi shiru, can yace "I believe kin zo anguwan ne" Tace "Not at all" Yayi kasa murya yace "Pls Mayraah, for the sake of the love i have for you tell me where are you now? Ina kika tafi" Tace "Ina Miller road" Musharraf yace "Miller road? I don't understand" Tace "Yea" Yace "Wajen wa?" Tace "My aunt" Yace "But i am not too far from Miller, just few streets away" A hankali tace "I know" A bit confused yace "But which of ur aunt?" Tace "Baka san ta ba" Musharraf yace "Don Allah in da gaske kike send me the house address, don Allah ba don ni ba, don't play with my feelings Mayraah" Ta ɗan yi murmushi tace "I will send u the address" Daga haka ta katse wayar ta masa fowarding address da ta tura ma Dr Khalil jiya, tana tura masa ya kirata yace "Don girman Allah da gaske kike Mayraah" Tace "Toh shikenan" Yace "Ohk, ok i am on my way now, right away" Daga haka taji ya kashe wayar, nan gabanta ya fara faduwa, to wa zata ce ma Hajiya Amina zai zo, what if yana zuwa Maheer ko Usman suka zo fa, ko kuma Abba ya dawo, ya zata yi? wannan tunanin yasa taji hankalinta ya tashi sosai, tasan babu wani nisa daga gidansa zuwa nan, ta mike da sauri ta tafi ta samu Hajiya Amina, Hajiya Amina tace "What will u be making for dinner?" Mayraah tace "Akwai sauran abincin Aunty" Hajiya Amina tace "Toh shikenan" Sunkuyar da kai Mayraah tayi tace "Dama Aunty wani coursemate dina ne..." Sai kuma tayi shiru, Hajiya Amina tace "Feel free" Mayraah tace "Yana nan anguwan ne, zai zo mu gaisa" Hajiya Amina tace "It's okay, sai ki shigo da shi parlor ku gaisa ba komai" Mayraah ta girgiza kai da sauri tace "Aa za mu zauna a compound" Hajiya Amina tace "Toh shikenan" Mayraah har ta juya sai kuma ta sake dawowa tace "Aunty ai Abba bazai dawo ba yau ko?" Hajiya Amina tayi murmushi tace "Bazai dawo ba, kar ki damu" Mayraah ta juya ta fita daga parlon, tana komawa dakinta taga miss calls din Musharraf har 4, Hijab ta sa ta sauka downstairs, tana isa gate bayan mai gadi ya bude mata ta gansa tsaye jikin motarsa, kallonta yake babu ko kiftawa kamar yanda ita ma take kallonsa, she just can't explain how she felt seeing him at the same time sai taga ya rame, kana ganinsa kasan ba shi da rest of mind, tayi karfin halin cewa "Ka shigo" Ya nufota har sannan yana kallonta, ta juya ta koma cikin gidan, wajen shan iska ta tafi yana biye da ita ta zauna, shi ma ya zauna yana facing dinta, a sanyaye tace "Good evening sir" kasa amsawa yayi ya dafe kansa, ta sauke idonta tana goge hawayen da ya fara taruwa da yatsunta, cikin rawan murya tace "Kayi hakuri, this our destiny" Yace "What is our destiny Mayraah?" Ta daga kai ta kallesa tace "Allah bai rubuta za mu yi aure yanzu ba" Yace "Sai yaushe?" Tayi karfin halin cewa "May be years to come, in dai da rabon za mu yi aure babu wani abu da zai hana hakan amma a yanzu kam ban ga alaman za mu yi ba" Yana gyada kai yace "Sai yanzu na sake tabbatar da baki so na Mayraah, i now believe ni ne kawai nake son ki, ni ne kawai nake bata lokacina" Ta fashe da kuka tace "Saboda me zaka ce haka? Iyayenka baza su yarda ka aureni ba, nima iyayena baza su yarda in aureka ba bayan duk abubuwan nan da suka faru a dalilin wedding dinmu that never occurred, and ah baya da nake tunanin zan iya bin ka mu tafi mu yi aurenmu a wani waje may be ban zauna nayi tunani da kyau bane a kan hakan, i get to understand that it's the biggest mistake da ni da kai za mu yi making idan mun yi hakan, aure babu albarkan iyayenmu bazai mana lasting ba, daga karshe duk za mu zo muna da na sani ne, but keep in mind sir, you still remain my first love, a kanka na fara soyayya akan ka nasan menene so ina alfahari da hakan, sannan kayi min so na tsakani da Allah, kayi min so na aure, kuma har gobe bazan taɓa daina sonka ba sai ma sonka ya karu a zuciyata, kawai mu jira lokaci Sir, ina ji a jikina we are meant for each other kuma za mu yi aure amma ba yanzu ba, may be sai a gaba ta yanda bamu yi zato ba, but for now let act just like frnds mu ci gaba da zumuncinmu da communication don mu samu sauki a ranmu...." Ya ɗan yi murmushi ya mike, a hankali yana kallonta yace "Thank you Mayraah" kallonsa kawai take ganin yanda idonsa ya kada, ya juya ya nufi gate, mikewa tayi da sauri tace "Sir..." Ko waiwayowa bai yi ba har ya isa gate din ya bude ya fita, wasu hawaye ne suka dinga sauka idonta ta koma ta zauna ta hade kanta da table tana kuka a hankali..... Ammi na zaune parlon Abba tana xuba masa abinci bayan magrib, bayan ya kunna TV yace "Mayraan bata dawo ba yau ne?" Ammi tace "Maheer din yace bai baro asibiti da wuri ba