Showing 237001 words to 240000 words out of 452169 words

Chapter 80 - Mayrah Complete By Khaleesat Haydar

zaune tana kallon TV ta kalleta tace "Ko dai mu bari zuwa gobe ko da daddare ne in kin dawo aiki mu je daughter?" Mayraah ta zauna gefenta tace "Aa Ammi mu je yau pis kin ga fa na riga nayi girkin, nasan goben a gajiye zan dawo" Ammi tace "Toh shikenan, mu je kawai..." Mikewa tayi ta shiga daki ta dauko gyalenta da jaka, sannan suka sauko downstairs, sai da Mayraah ta tara shiga kitchen ta dau warmer din two da miyar ganyen da tayi ta kai mota, driver na compound yana jiran fitowarsu, Mayraah ta sanar masa inda zai kai su sannan ta bude ma Ammi back seat ta jira har ta karaso ta shiga ta kulle motar sannan ta tafi front seat ta zauna, tafiyar kusan minti talatin da biyar suka yi suka iso gidan, Drivern yayi parking bakin gate, Mayraan ta sauka ta dauko warmers din biyu, Ammi ma ta sauko daga motar ta sanar masa jiransu zai yi sannan suka shiga cikin gidan, Karime ce ta bude masu kofar parlon tana ganin Mayraah ta rungumeta cike da farin cikin ganinta tace "Sannunku da zuwa...
Ku shigo" Mayraah na murmushi suka shiga parlon da Ammi, ta ajiye warmers din hannunta, bayan Karime sun gaisa da Ammi ta mike tace "Bari in yi ma Hajiyar magana tana daki" Ba a dau lokaci ba sai ga ta tare da Ummi, shigowa parlon Ummi tayi da fara'arta tana masu sannu da zuwa, Mayraah ta koma kusa da inda Ummi ta zauna ta gaisheta, Ummi ta amsa da fara'a tace "Kwana biyu ko leko mu kin ki yi Ilham, shine ranan Khalil ke ce min ai mamanki sun dawo Abujan ma gaba daya, ina jin ko kwana biyar ba ayi ba da ya gaya min haka" Mayraah na murmushi tace "Ai naje kano nayi sati biyu ne shi yasa Ummi" Ummi tace
"Maa sha Allah, Maman taki ce wannan ko" Ammi dai murmushi kawai take, Mayraah ta gyada kai tace "Ita ce" Suka kara gaisawa da Ammi, Ammi ta mata godiyan rikon Mayraah da tayi, Ummi tace "Kai haba babu komai, ai yi ma kai ne" Mayraah tace "Inna na daki?" Ummi tace "Tana ciki, ku shiga ku gaisa" Mayraah tace "Nayi mata girki ne" Ummi tace "Ai ko kin kyauta wallahi, Allah maki albarka" Mayraah ta mike tana kallon Ammi tace "Ammi mu je ku gaisa da Inna" Mikewa Ammi tayi ta bi bayan Mayraah zuwa dakin inna, karime ta dau warmers din ta bi su a baya zata kai dakin, Sosai inna tayi farin cikin ganin Mayraah bayan sun gaisa da Ammi tace "Kai amma wannan er taki er albarka ce warce bata mance alkhairi, na dade ban ga yarinya me hankali kamar ta ba, ki ji fa har da girki ta min abun sha'awa, yaushe ma na samu haka a gidan nan, doya ce fa yanka hudu suka hadani da shi dazu kamar a fursin wallahi" Ammi dai murmushi kawai take tana kallon Inna, su da suka yi niyyar barin gidan da wuri sai da inna ta ja Ammi da zance, su ne har kusan karfe shidda a gidan, Ummi ma tuni ta shigo dakin Inna ta zauna suna hiran gaba daya, magana daya biyu sai innan ta Gwale Ummi, Ummi dai ko bin ta kanta bata yi, a haka dal Ammi ta samu suka lallaba suka bar gidan inna na cewa tana nan zuwa zata sa Khalil ya kai ta, bayan sun kama hanya Mayraah na kallon Ammi tace "Kamar Mama Ladi ko Ammi" Dariya Ammi tayi tace "Wannan ai ta so ta fi mama Ladi, gaskiya Ummin na hakuri da ita..." Mayraah tace "Ai kam Ummi ba ruwanta bata biyeta" Washegari ko da Mayraah taje alki su Khalil basu dawo Lagos ba wai sai Tuesday, hankalinta kwance tayi aikinta a asibitin babu wanda ya takura ta, a ranta ta dinga fatan da ma kar su dawo da MD din nan, a rikesa a branch dinsu na can Lagos din ace an masa transfer. Da daddare Mayraah na shirin kwanciya kiran Maheer ya shigo wayarta, dauka tayl ta zauna geten gado sannan ta daga, bayan sun gaisa, a hankali tace "Was it successful yaya?" Yace "Nop Mimi, wai sai nan da wata uku" Lokaci daya jikin Mayraah yayi sanyi, for kusan 4 days yake ta kokarin ganin ya samu transfer din zuwa Abuja, har Abba sai da yayi intervening a issue din, duk hope dinta yau idan ya kirata zai ce an maidosa Abuja, jin bata ce komai ba yayi kasa da murya yace "Kin yi shiru" a hankali tace "To me zan ce?" Yayi murmushi yace "Ki ce min congratulations" Ta buda ido tace "Wai anyi Transferring dinka?" Yace "Yes Mimi" Ba karamin farin ciki Mayraah tayi ba, har sallan dare sai da tayi a yan kwanakin nan duk don ya samu transfer din sai gashi kuma ya samu, yace "But Abba ne fa yasan yanda ya bi aka yi Transterring dina, it won't have been possible idan ba don shi ba" Mayraah tace "Maa sha Allah, congratulations yayana i am so happy with this news, yanzu yaushe zaka yi resuming aiki a nan?" Yace "Sai monday next week, but in sha Allah zuwa friday zan dawo Abujan" Tace "Toh Allah ya kai mu yayana" Tana son tambayarsa ko da Haseenahn za su taho amma dai tayi shiru bata yi tambayar ba, yace
"Bari in kira Ammi in gaya mata, i told u first before her" Mayraah na murmushi tace "To yaya, bye" Maheer na kiran Ammi bayan ita ma tayi farin ciki tace
"To yanzu ya za kayi da yarinyar nan?" Yace "Kawai ta tafi gidansu" Ammi tace "Aa babu wannan zancen Maheer, babu yanda muka iya haka zaka taho da ita nan, the chalet here is almost 2 times bigger than the one u are inside now, hakuri za kayi ku taho tare" Maheer yayi shiru don bai yi expecting Ammi zata ce haka ba, Cikin kwantar da murya tace "I understand you dear, amma kayi hakuri na dan lokaci ne, bazan taba goyon bayan ka ci gaba da zama da Haseenah ba yanzun ma kai ma kasan akwai dalili ne" Shi dai bai ce komai ba, don gaba daya mood dinsa har ya baci.
Ranan Wednesday Mayraah na shiga asibiti da safe bayan ta dubo wata patient a wani ward tana dawowa reception sai ga Dr Khalil ya shigo, tana hango wanda suka shigo tare kawai tayi saurin juya masu baya pretending bata gansu ba, da haka ta nufi wani ward da sauri ta shige ciki kamar zata je dubo wani patient, duk MD na kallonta, nurse din wajen ta gaishesu da ladabi, har MD din ya fara tafiya toward step sai kuma ya dawo ya cire glasses dinsa yana kallon nurse din da kyau yace "Anyi cleaning office dina yau?" Nurse din ta mike da ladabi tace "Yes sir, ai kullum sai cleaner din ya yi cleaning office din sannan ya maida ma secretary spare key... He does that every day ko baka nan" Yace "Fine, i need my library shelf carefully dusted and cleaned to my satisfaction today, Da muka shigo ai kamar ba ke kadai bace a nan" Ta gyada kai da sauri tace "Eh ni da nurse Ilham ce, amma ta shiga ward 3 zata dubo patient" Yace "Good, look for her ki gaya mata abinda nace don ita zata yi aikin ba wani ba, or you just tell her to meet me in my office immediately" Nurse din tace "Okay sir" shi dai Dr Khalil na tsaye yana kallon MD da mamaki, Nurse din ta tafi da sauri inda Mayraah ta shiga don kai mata sakon MD, Dr Khalil ya bi bayan
MD da ya nufi step yace "Dama nurse ta taba maka gyaran office Dr? We have more than enough cleaners in here" MD yace "Za a fara yau, kai baka ga duk ka sa yarinyar nan ta gama raina mu ba, wato tafi karfin ta tsaya ta gaishemu shine zata shige ward, to zata yi gyaran every nook and cranny na office dina yau kuwa, next time ma idan tayi repeating haka abinda zan yi mata kenan, silly girl" murmushi kawai
Dr Khalil yake yana biye da shi a baya. Mayraah ta dinga kallon nurse din da ta kawo mata sakon MD tace "In same sa a office kuma? Allura fa zan ma patient din nan idan ta gama cin abinci" Nurse din tace "| will handle that, kawai ki tafi ya ce yana jiran ki" Mayraah ta fita daga ward din ta tabe baki ta wuce sama, jiya da baya nan asibitin so conducive wallahi.
Knocking din office din nasa tayi tana hade rai, har sai da ta kwankwasa sau uku sannan taji yace a shigo, ta bude kofar ta shiga, gaban table dinsa ta tafi ta tsaya bata bari ta kallesa ba tace "Good morning sir" Bai amsa gaisuwar ba ya nuna mata direction da shelf din Libraryn nasa yake yace "Take out all those textbooks and articles, dust and clean, finish with that first...." Mayraah ta dinga kallonsa taki cewa komai, ya daga kai ya kalleta yace "What are you still waiting for?" Juyawa tayi ta nufi shelf din da ya nuna mata tuskarta a daure, ya bi ta da ido, tana isa nan ta fara sauke textbooks din daya bayan daya tana ajiyesu kasa, sai da ta sauke many of the textbooks ta fara jin kamar dust a hancinta, still dai ta ci gaba da fiddo su, tana ajiye na hannunta taji tari ya taho mata, da sauri ta rufe hancinta da hannunta, kamar tayi triggering tarin soda kuran dake hannun nata, ta durkusa nan kasa da sauri within few seconds she began gasping for breath, bai san sanda ya karasa inda take ba ya duka gabanta ya dago kanta da sauri yana kallonta yace "Are you Asthmatic?" Sai kuma ya janyeta daga wajen textbooks din ya zaunar da ita kan office chair dinsa trying to help her with first aid, amma numfashinta sai kokarin daukewa yake, Ikci daya duk ya daburce a wajen kamar bai taba zama likita ba a rayuwarsa, gashi dai bayan pills da injections har inhaler akwai a show glass din magunguna dake office din but he was just lost ya kasa yi mata komai, dai dai nan Dr Balogun ya shigo office din, da sauri ya nufosu lkci daya kuma yake tambayar me ya sameta, yana fahimtar Asthma ne ya fara mata abinda ya kamata a wajen, cikin kankanin lokaci ya dauko pills a show glass ya bude ya dau bottle water dake kan table ya bata, with his help ta hadiyi pill din, they were there for almost 15 mins yana kokarin calming dinta har ta fara sauke numfashi a hankali, MD was just standing like a quack Dr a wajen with no help, Dr Balogun ya dinga mata sannu, bayan some minutes yace "Are you okay now?" Ta daga idanuwanta da suka kada, duk da azaban da kirjinta ke mata ta gyada masa kai, yace "Ok now duk ward din da kika ga babu kowa a nan sama kije ki kwanta, get some rest" Tayi karfin halin mikewa tsaye Dr Balogun ya bata hanya yana mata sannu, tana tara tafiya ta ji kanta na juya mata tayi baya zata fadi, kafin ta kai kasa MD yayi saurin riketa, Dr Balogun yace
"Her Bp is low" kwantar da ita MD yayi kan examination bed dake office din nasa, Dr Balogun na kallonsa yace "Akwai coffee powder ayi making mata coffee ta sha?" MD ya dauko Tea cup dinsa yana wankewa sau daya ya kalli cikin cup din keenly, kafin yayi attempting sake komawa ya wanke Dr Balogun ya amshi cup din yace "I will do it..." Cikin mintuna kadan yayi making coffee a cup din ya mika masa yace "I have a patient in my office... I will be back idan na sallamesa yanzu" MD ya amshi Coffee din ya juya yana kallon Mayraah da idonta ke a rufe, Dr Balogun ya fita daga office din da sauri don dama tambaya ya shigo yayi masa....

72
Mayraah na sauka second floor ta had da Dr
Khalil ya fito office dinsa da was files, yana ganinta ya nufo ta da sauri yace "How are you feeling now?" Ta gyada masa kai a hankali tace
"Alhamdulillah, i am better now" yace "Ina za ki je?" Tace "Driver yana jirana a waje" Yace "Did he ask you to go home?" Ta gyada masa kai, yace "Alright, Allah ya kara lafiya" Tace "Ameen, Nagode" Downstairs suka sauka a tare, ta tafi ta dauka handbag dinta tayi ma Nurse Hafsat sallama sannan ta bar asibitin, tana isa gida
Ammi dake parlonta suna waya da Aunty Mariya ta kalli agogo sannan tayi ma Aunty Mariya sallama ta mike tana kallonta da mamaki tace
"Naga kin dawo da wuri" Mayraah ta kalli agogo dake nuna karfe biyu tace "Bana jin dadi ne"
Ammi ta nufeta da sauri tana taba iikinta tace
"Subhanallah, me ya sameki? Since when?"
Mayraah tace "I had an attack daxu da safe"
Ammi ta zaunar da ita kan kujera da damuwa tace
"Garin yaya ?" Mavraah ta sauke ajivar zuciva tace "Ina jin wajen kamar akwai kura ne, ni kuma ban sani ba, amma ai naji sauki yanzu, an bani magani na sha after sometime na dawo normal shine har nayi bacci" Ammi tace "Toh Allah ya sauwake, but duk in kika ga wajen da zai iya accommodating dust ki dinga saka nose mask Mimi, ki daina fita babu shi kin ji?" Mayraah tace "In sha Allah Ammi" Ammi tace "Bari in kawo maki abinci, kin yi sallah?" Ta gyada kai tace "Nayi" Ammi ta mike ta fita daga parlon zata je kawo mata abinci, Mayraah ta jinginar da kanta da kujera, bayan wani lokaci wayar Ammi ya fara ring,
Mayraah ta mike tana kallon wayar gain wanda ke kiranta ta karasa inda wayar yake ta dauka sannan tayi picking ta kai kunne, sallama yay ta amsa, a hankali tace "Good afternoon" Daga daya bangaren yace "Are you okay?" Murmushi tayi tace "Me yasa ka tambaya?" Yace "I sense that from ur voice, baki da lafiya ne?" Tace "Asthma dina ne ya tashi a asibiti" Yace "Subhanallah, how did that happen?" Tace "I am very fine now, naji sauki sosai, yaya hope dai ka gama shiryawa?
Kasan friday din ya kusa fa" Yace "Sure, Allah ya kai mu lafiya" Tace "Ameen" Yace "Kin sha magani amma?" Tace "Eh an ban a asibiti" Yace "Toh Allah kai mu lafiya" Tace "Ameen" Yace "Kin sha magani amma?" Tace "Eh an ban a asibiti" Yace "Toh Allah ya sauke, be careful pls Mimi always go around with ur nose mask to avoid such issues" Tace
"To yaya" Yace "Ammi fa?" Tace "Taje kitchen"
Yace "Ohk, i will call her back later, go and get some rest Mimi" a hankali tace "Bye" Washegari Wednesday Dr Khalil na office dinsa bayan fitar wata patient MD ya shigo, Dr Khalil ya daga kai yana kallonsa har ya karaso ya zauna vace "I just finish speaking with Ceo, tana son zata yi magana da yarinyar nan, kaga daga common Asthmatic attack jiya shine tayi taking advantage taki zuwa aikin yau, who does that pls, idan nayi magana kace i am not being considerate... Dr Khalil vace "Sai kace mata bata da lafiya mana..." MD yace "To dama idan ba haka ba me kake son in ce mata, imagine ceo fa, yarinyar da common workshop a lagos bata kai a fara zuwa da ita ba shine take tambayar ko tana da international passport, for what? ni ban ma san yanda zan mata bayani cewar ba a bisa ka'ida aka dauketa aiki a asibitin nan ba, idan ba ayi hankali ba fa sai ceo tace da ita za aje conference din nan" Dr Khalil yace "Nan din ba bakin ciki zaka mata sir?
Tun da kaga haka ceo din is gradually becoming fond of her, jininta ya hadu da ita ne, kai ne har yanzu ka ki kwantar da hankali ka lura how lovely the pretty girl is ba" MD yace "And how will dat add any impact to my life? That is not my problem Khalil, yanzu cewa tayi a kira ta a tambayeta ko tana da international passport, and i should feed her back immediately" Kallonsa kawai Dr Khalil yake, MD yace "So now after some minutes i will call and tell her tace bata da international passport.." Dr Khalil ya jawo wayarsa yayi dialing number yana fara ring ya sa a handsfree, ba a dau lokaci ba aka daga, murya can kasa tayi sallama, her voice was so cool and calm, MD ya masa wani kallo ya mike amma sai bai fita ba, Dr Khalil ya amsa gaisuwar da tayi masa yace
"Ya jikin?" Tace "Alhamdulillah" Yace "Me yasa baki zo aikin yau ba" Ta dan yi shiru, sai kuma a hankali tace "I am still recovering, kuma ni bana son a dinga min masifa anyhow" Dariya ta ba Dr Khalil, MD ko ya gyada kai bayan ya ji me tace, Dr Khalil yace "To wa ke maki masifa Mayraah?" Tace "MDn ku mana, he is always finding fault where there is none, ko gajiya baya yi da fada, energy da yake sakawa a fada da ma a field dinsa yake sakawa da ya fi, kuma gwara ni ranan allura ne kawai na dan zama confuse da zan ma yarinya, shi kuwa a whole asthmatic patient a gabansa babu abinda ya iya yi, just going up and down like a student, i nearly thought him to be quack wallahi, ko ni da nake nurse bazan yi haka ba..." Dr Khalil ya cire wayar a handsfree da sauri laughing out loud, kallon wayar MD ya dinga yi babu ko kiftawa, yana ganin Dr Khalil ya cire a handsfree ya fizge ya mayar handsfree din, Mayraah tace "It's not funny fa, na dade ina mamaki da na dawo gida jiya, ko level 4 student a medicine bazai yi abinda yayi ba" Dr Khalil yace
"To ai shikenan. a takaice dai kin fi sa

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login