Showing 240001 words to 243000 words out of 452169 words

Chapter 81 - Mayrah Complete By Khaleesat Haydar

sanin aikin likitanci kike nufi kenan?" Without thinking twice tace "Na fi sa composure a aikin, may be because i don't shout and Nag" Dr Khalil na dariya yace "To sai anjima, zan kira ki" Tace "Ohk" MD ya dinga kallon wayar hannunsa, ita kuwa ganin Dr Khalil bai katse ba sai ta katse kiran, MD ya ajiye masa wayar kan Table a takaice yace "Call her back tayi providing International passport dinta gobe" Dr Khalil yace "Aa kai da kace... MD ya katse sa yace "Instruction din da Ceo ta bani kenan, don haka kayi abinda nace maka" Yana kai wa nan ya fita daga office din, dariya kawai khalil yake don har cikin ransa yaji dadin maganganun da Mayraah tayi a kan kunnensa, shi kansa jiya da
Dr Balogun ke basa labari yay mamaki, MD da ko jUSI cOmmon AsInmatic attacK aa ya sameta jiya ya kasa tabuka komai ya dawo kamar learner, to in ba rami me ya kawo rami, daukar wayar yayi ya sake kiran Mayraah bayan ta daga yace "Kina da international passport?" Ta dan yi shiru, sai kuma tace "Eh" Yace "In za ki shigo gobe sai ki taho da shi" Da mamaki tace "Why?" Yace "Ceo ce ta ce a sanar maki haka" Mayraah was a bit confused, ta ma rasa tunanin da zata yi, to me za ayi da passport din nata, sallama Dr Khalil yayi ya katse wayar. Washegari da taje asibiti har rana MD bai shigo ba, tun da safe ta kai ma Dr Khalil passport din nata, wajen karfe biyu suka shiga theatre za su yi wani aiki da Dr Balogun da Dr Khalil, tana kokarin saka nose mask before putting on her sterilized hand gloves kamar ance ta juya suka yi ido hudu da MD, dauke kai tayi don bata ma san ya shigo ba and she felt unhappy after realizing tare da shi za ay aikin, yawanci aikinta a Operation theatre bai wuce ta dinga mika Sterilized Instruments ba sai kuma suture, MD zata dinga mika ma Instruments din kamar wancan ranan, tana mika masa abinda ya bukata na farko suka hada ido sai kawai ya fadi daga hannunsa, wata nurse ta dauko wani Sterilized Instrument din da sauri ta kawo masa, sau hudu suna haka da shi, it is either idan zai maido mata sai ya fadi a hannunsa, ko kuma idan ta mika masa zai amsa sai a samu matsala, ita dai she is calm, Dr Khalil ya dawo inda Mayraah take yayi kasa da murya yace "May be u are tired, just go, nurse Sadeeya will continue..." Ta dan kallesa a ranta tace ko dai MD dink is tired, duk fa sun ga shi ke contaminating Instruments din not her, daga hannunsa suke faduwa ba nata ba, juyawa tayi ta bar wajen, karfe shidda saura driver dinta ya zo ya mayar da ita gida. Ranan friday da yamma Maheer ya iso daga kano via flight, Mayraah was so happy seeing him don ita da driver ne ma suka je airport tarbo su, yana gama gaisawa da Ammi ta kai sa wani daki dake parlor da damuwa tace "Yaya naga ka rame, what's happening?" Yace "Aiki mana, kema nan da kwana kadan zaki ga kin rame ba dai kin fara aikin ba" Mayraah bata yarda ba, ta dinga insisting ya gaya mata what the problem is, Haseenah dai tafi minti ashirin zaune ita kadai a parlorn, Ammi da ke kitchen tana karasa girkin da take ta fito Parlon ganinta ita kadai ta nufi dakin da Mayraah ta kai Maheer, Ammi kanta wasn't happy with how she saw Maheer, tana kallonsu tace
"Ka tashi ga chalet din can a bude yake, kun bar ta ita kadai parlor, ya kamata taje ta huta ita ma, Mimi zata kai maku abincin yanzu" Shi gaba daya ya ma mance da wata Haseenah, bayan some minutes ya mike ya fita a dakin. Bayan minti sha biyar Mayraah ta kai masu abincin Chalet, Yana bedroom Haseenah kuma na zaune parlon ta bi ta da ido har ta ajiye abincin sannan ta fita... Ammi na zaune parlonta da Maheer sai Usman dake danna wayarsa, da damuwa tace "Gaskiya ni dai hankalina bai kwanta ba kwata kwata, yaushe ma ta fara aikin ta samu full experience har matar zata ce xa aje conference da ita England? Ina manyan likitoci da Nurses din asibitin, aa gaskiya bazata ba" Maheer ya sauke ajiyar zuciya yace
"Kai ya ka gani Barrister?" Sai a sannan Usman ya daga kai ya kallesu yace "It's weird gaskiya, daga fara aiki ko sati biyu bata yi ba a kawo maganar fita waje, irin wannan tafiyar ai da experienced staffs ake zuwa" Maheer yace "Haka ne, nima kuma nayi mamaki" Ammi da hankalinta ya tashi tace "Ni gaskiya aikin ma sai a bari, kuma fa matar ba musulma bace, gwara a samar mata a wani waie kawai ta hakura da wannan" Murmushi kawai Maheer yayi, Ammi tace "Abbanku da na dawowa yau zan gaya masa, aikin ya fita kai na gaba daya wallahi" Mikewa Usman yayi ya fita daga parlon, Ammi ma ta mike tace "Kasan zan yi bakuwa bari in je in ga ko me aikin ta gama abinda na sa ta" Yace "Ohk" Ammi na fita parlon Maheer ya mike ya tafi dakin Mayraah. Kusan karfe uku Hajiya Maimuna mahaiftyar Haseenah ta iso gidan, tun da ta shigo hankalin Haseenah ya ki kwanciya, kawai dai tana zaune parlorn ne tana yaken karfin hali, Ammi ta tarbeta sosai suka gaisa da fara'a, Mayraah ta kawo mata abincin da aka mata, Hajiya Maimuna tace "Kawai na ce ko a gurguje ne in zo in ga gida kafin in koma kano, gida kam Alhamdulillah yayi kyau Allah ya sanya alkhairi, Allah ya sa rai aka yi ma" Ammi tace "Ni da na zata kwana za ki yi Hajiya?" Hajiya Maimuna tace "Ai daga gidan nan airport zan tafi, biki muka shigo tun ran juma'a wallahi, to nayi niyyar zuwa jiya asabar sai Allah bai yi ba sai yanzu" Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace "Toh amma ai za ki ci abinci Hajiya" Hajiya Maimuna tace "Wallahi na ci abinci kafin in fito, Alhamdulillah" Ammi tace "Da kika kirani dazu da safe har nake tunanin in kin zo akwai maganganun da za mu yi Hajiya" Sosai gaban Haseenah yayi mugun faduwa jin abinda Ammi tace, Mayraah dai na zaune parion ita ma, Hajiya Maimuna tace "Flight din na dare ne Hajiya, ko yanzu za mu iya maganar, Allah dai ya sa lafiya" Ammi ta dan yi murmushi, sai kuma tace
"To gaskiya ba lafiya ba Hajiya" Hajiya Maimuna tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ina ji Hajiya" Haseenah ta mike zata bar parlon, Ammi tace
"Aa ki dawo ki zauna Haseenah" Sunkuyar da kai tayi ta koma ta zauna, Nan Ammi ta fara yi ma Hajiya Maimuna bayanin duk abinda ke faruwa bata boye mata komai ba, Daga karshe Ammi tace "Nasan kin san was maganganun nan was kuma ba lallai ki sani ba... To kin ji abinda ake ciki Hajiya" Hajiya Maimuna da ta kasa dago kanta sai zufa take bayan few seconds, tace "Amma baki kyauta min ba Hajiya, wallahi baki kyauta min ba, yanzu duk abubuwan nan su far babu wanda ya sanar min, na kwanaki ma da tayi dambe da kawarta Badiyyah banda ta kira kannena suka je suka yi rashin mutuncin da suka yi babu yawuna wallahi ban sani ba Hajiya, ban san komai ba, yanzu ni Haseenah zata tona ma asiri ta kunyata ni a idon duniya duk zatona tana zaune lafiya gidan mijinta?" Sai kuma ta fashe da kuka ta mike tace "To wallahi Allah ya isa tsakanina dake Haseenah, kin cuceni don sai ace tarbiyar da na maki kenan, bayan Allah a gani nayi iya bakin kokarina ganin na maki tarbiyyar da ya kamata dai dai gwargwado" a fusace ta rufeta da marita ko ina tana zaginta, Ammi ta rikota da sauri tace
"Aa Hajiya ba sai kin doketa ba, don Allah kiyi hakuri….." Hajiya Maimuna na huci tace "Wallahi dama in ta kashe auren ta nemi gidan wata uwar ba ni ba, kar ta kuskura ta nufo inda nake, da dadi ha dadi haka navi hakuri a aidan ubanta.

73
Abba dake zaune parlon Ammi ya ajiye drink din hannunsa yana kallonta yace "Saboda ance za aje kasar waje da ita sai kice ta ajiye aiki Madam? Ai kamar this is a privilege for her, i see nothing wrong don asibiti ya zabe ta cikin wa enda za su je England conference...." A hankali Ammi tace "Gaskiya ni dai hankalina bai kwanta ba, of all the staffs in the hospital why her? Yaushe ta fara aikin har za a zabeta?" Abba ya kalli Maheer dake parlon yana kallonsu yace "Can you hear ur mother?" Murmushi yayi yace "Kuma conference din nasan bazai wuce kwana biyu zuwa uku ba fa Ammi" Ammi tace "Ko ma kwana daya ne ni dai kawai hankalina bai kwanta ba" Abba yace "Toh tunda haka ne sai Usman ya bi su England din, hope yanzu hankalinki ya kwanta?" Maheer ya juya yana kallon Abba, Ammi ma dai tayi shiru tana kallonsa, mikewa Abba yayi yace "Let me get some rest" Daga haka ya fita daga Parlon zuwa part dinsa, Ammi na kallon Maheer tace "Is there anyway da za a sanar ma asibitin a cire sunanta daga masu tafiyar pls? Wani Usman ne zai bi ta kanta in ma yaje England din, harkan gabansa kawai zai yi ya juyo ranan da yaji ance za su dawo" Maheer yace "Kawai Ki bari ta je Ammi, kamar yanda Abba ya fada it's a privilege, don ba kowa ne zai samu hakan ba, may be ita me asibitin ta yaba da nutsuwarta ne sannan taga yanda take aiki, ko kin manta daughter din taki da first class ta fita? Did you know what that means? Kar kiji komai ana samun haka sosai, beside ba da ita kadai bane ai za aje dole da akwai staffs da aka zaba, it's something we should be happy about" Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace "Toh shikenan tunda ka ce haka" Mayraah na dakinta da daddare bayan tayi shirin bacci Ammi ta shigo da sallama, zaunawa Ammi tayi gefen gadon tana kallonta tace "Ya ciwon kan?" Mayraah tace "Yayi sauki tun dazu Ammi" Sai kuma ta marairaice tace "Stress din aikin nan ne fa Ammi, kullum da sassafe mutum zai fita bazai dawo ba sai 6:30, and every day the hospital is always busy with patients, ko lokacin hutu fa mutum bashi da" Ammi tace "A haka nan zaki saba daughter" Mayraah ta girgiza kai tace "Gashi kusan 5 weeks har yanzu ban saba ba, meaning bazan iya sabawa ba" Ammi tayi murmushi don kusan kullum sai tayi complain din zuwa aikin nan, Ammi tace "Toh yanxu yaushe ne tafiyar ta ku? You said ur Visa is ready" Mayraah tace
"Nima ban sani ba, but naji kamar Dr Khalil yace next week" Ammi tace "To Allah ya kai mu, abincin da kika girka ma yayan naki ya kare ne?" Mayraah tace "Za ki ci ne Ammi?" Ammi tace "In zan samu ba" Murmushi Mayraah tayi tace "Akwai sauran kadan, bari in debo maki" Sauka tayi daga kan gadon ta fita daga dakin Ammi ta bi ta da ido, magana take son mata amma ta rasa ta inda zata tara, can ta sauke ajiyar zuciya still thinking of where to start from, Mayraah na sauka kasa taga Maheer parlon yana kallo, tun da ya dawo Abuja daga kano yau kusan 4 weeks kenan bacci ne kawai ke kai sa chalet shi ma wajen karfe dayan dare wani lokacin, yana dawowa aiki main building yake nutowa, komai a dakinsa da ke nan main building din yake yi, duk aka yi girki mai aikin Ammi ke kai ma Haseenah Chalet, wani Iken ta kan shigo babba parlon gidan wataran ma kwata kwata bata shigowa tana can chalet ita kadai, Mayraah na kallonsa tace
"Yaya ka sha shayin?" Yace "Na sha" Kitchen ta nufa ta zubo ma Ammi sauran abincin da ta dafa ma
Maneer dazu sannan ta dawo parlon, yace "Yaushe kika fara cin abinci haka Mimi?" Dariya tayi tace
"Ammi fa zan kai ma" Yace "Better" Murmushi tayi ta koma sama ta kai ma Ammi abincin, Ammi na amsa kawai ta mike don ta rasa ta inda zata fara mata maganar da ya kawo ta dakin, ta sa a rai zata bari in sun dawo daga England kawai. Yau tun da Mayraah ta tashi take dakinta a kwance bata fito ba, breakfast ma har Bedroom Ammi ta sa me aiki ta kai mata, it was a Friday kuma yau ne ranan tatiyar tasu zuwa Uk amma evening Flight, jin ana knocking kofarta ta kalli agogo dake nuna karfe uku na rana ta sauka daga kan gadon ta bude kofar, Maheer ne tsaye bakin kofar yana sanye da farin Gezna, daga sama har kasa take kallonsa, sai kuma tayi murmushi ta jingina da kofar a hankali tace "Good afternoon" Yace "Afternoon Mimi" Ta langwabar da kai tace "Kayi kyau kamar wani sabon ango, nasan yau mata suna ta kallon ka a hanya ko" Ya dan buda ido yace "Ango kuma" Tana murmushi tace "I am serious u look gorgeous" Bai kulata ba yace "Duk efizyn zaki je England ne yau ya sa kika ki fitowa parlor mu ganki?" Tayi dariya tace
"Yaya wallahi kamar a fasa tafiyar da ni, i wish kawai za ace banda ni, i am so tense" Yace "Why?" kamar zata yi kuka tace "Kawai haka nan, i don't understand why i am tense" Ya sauke idonsa kasa yace "Sauko mu yi Lunch" a hankali tace "Ohk" Daga haka ya juya ya sauka kasa, ita kuma ta juya ta koma dakin zata dauko hular ta, suna zaune parlon su biyu kadai, eating from the same plate Haseenah ta shigo parlon, kamar hadin baki suka mata kallo daya suka dauke kai a tare, kitchen ta nufa ta je ajiye warmer din da za a sa mata abincin dare, tana fitowa bata ko kallesu ba ta fita daga parlon, Mayraah na gama cin abincin ta dinga ma Maheer hira a parlon tana basa labarin irin cases da take gani a asibiti, wanda kawai sauraronta yake a ransa kuma yana tunanin may be ta mance shi ma likita ne, a haka Ammi ta sauka downstairs ta samesu, ta kalli agogo tace "Ke ba karfe biyar bane Flight dinku kike nan zaune?" Sai da gaban Mayraah ya fadi don ita ko son a tuna mata da tafiyar nan bata yi, Maheer yace "Mimi that's true ki je ki shirya da wuri, gwara ki jirasu da ace sun jiraki" A hankali ta mike ta wuce sama, bandaki ta shiga tayi wanka ta dauro alwala ta fito, bayan ta idar da sallahn asr Ammi ta shigo dakin, tana kallonta tace "Kin sa kayan naki cikin akwati ne?" Girgiza kai tayi, Ammi tace "Ke dai komai kin fi son sai kinyi cikin kurarren lokaci, ance maki flight karfe biyar ya kamata ace kuna airport ma yanzu" Usman ne yayi knocking kofar dakin sannan ya bude, yana kallon Mayraah yace "Ina kika ajiye wayarki ake ta kiranki?" Ta dan buda ido da sauri ta nufi karkashin pillow da ta ajiye wayar dazu, miss calls din Dr Khalil ta gani har uku, ta kalli Usman dake mata wani kallo, Ammi ta fiddo mata wani abaya ta ajiye gefen gado tace "Gashi nan ki saka" Usman yace
"Kin bar su tun dazu a waje suna jiranki" Daga haka ya juya ya bar bakin kofar, Ammi ta bude baki tana kallon Mayraah da ta kasa tabuka komai, da kanta ta fara hada mata few clothes dinta da duk wani abu da zata bukata a akwati, bayan barin Usman wajen sai ga Maheer, a bakin kofa shi ma ya tsaya yace "Mimi they are waiting for u outside kiyi sauri...." Kayanta ta dauka ta fara sa wa, Ammi ta gama hada mata komanta a akwati, Maheer na kallon Ammi yace
"Akwai sanyi sosai Uk, she shouldn't forget her jacket" Ammi ta kalli Mayraah tace "Rigunan sanyinki suna dakina kije ki dubo da sauri" Mayraah na fita daga dakin Maheer ya bi bayanta yace "Do not forget ur sanitary stuffs, hopefully har ki dawo kila...." Mayraah ta buda ido don har ta manta, sai bayan kusan minti goma Maheer ya sauka downstairs da akwatinta tana biye da shi a baya, Ammi ta rakasu har compound tana mata Allah ya tsare hanya, kana ganin Ammi kasan babu yanda ta ya ne da tafiyar Mayraah, suna fita kofar gida Mayraah ta ga mota anyi parking, Dr Khalil ya bude masu booth Maheer ya ajiye akwatin, tana kallon Maheer tace "Yaya gobe Ya Usman din zai je can?" Maheer ya gyada mata kai yace "In sha Allah" A hankali ta bude back seat ta shiga don ko ba a gaya mata ba taga alamar da mutum a front seat din, Dr Khalil suka yi sallama da Maheer sannan ya koma cikin motar, Mayraah ta daga ma yayan nata hannu kamar zata yi kuka, Dr Khalil yayi reverse suka bar anguwan. Tana daga kai suka hada ido da MD ta madubi, sauke idonta tayi murya can kasa tace "Good evening" ya ji ko bai ji ba oho, don bata ji ya amsa mata ba, Dr Khalil yace "Ina kika ajiye wayarki, kin kuma san karte nawa ne flight din naku" Tace "Shiryawa nake ne" Dr Khalil ya girgiza kai yace "Ku dai mata komai sai kun saka African time a ciki...." Mayraah dai ta ci gaba da danna wayarta bata ce masa komai ba, MD na kallon Khalil yace "Plss ka bi route din da za mu yi sauri, it's easy to miss a flight.." Dr Khalil yace "In sha Allah baza ayi missing Flight din ba we will get there in time" Suna isa airport MD ya sauka, Dr Khalil ma ya sauka daga motar ya fiddo hand luggage din MD wanda jacket dinsa ne kadai a

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login