Mayrah
Chapter 93 of 152
dai ko kallonsa bata yi ba hawaye na sauka idonta, Abba da ransa yayi mugun baci yace "Zan maida ita asibitin kuma wallahi bana son ganin kafarta a can, gwara ke Mariya ki je ki ci gaba da jinyarta" Ammi ta mike tace "Wallahi bazaka maida min yarinya asibitin matar nan ba, ai asibitoci kala kala ne a Abuja kuma masu kyau, wanda ma suka fi wancan kyau, me yasa baza a canza wani asibitin ba..." Ko kallonta Abba bai yi ba ya shige dakin Aunty Mariya ta bi bayansa, Usman ya kama hannun Ammi da ke kuka suka fita parlorn ya maidata wani parlor yayi kasa da murya yace "Ammi bai kamata ki fito da ita asibitin ba, har yanzu fa ba wai samun sauki tayi ba kuma kema kin sani..." Katse sa tayi tana kuka tace "Me yasa baza ku fahimce ni ba ne wai Usman??" Usman ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yace "Na fahimce ki Ammi, birth certificate dinta da ta bukata ka'idar asibitinsu ne za ayi photocopy a saka cikin file din patient, kinsan ko wani asibiti da rules din su, so baki tsaya kin fahimci dalilin tambayar certificate din da tayi ba kika yi saurin yanke hukunci" Ammi dai bata fasa kukan da take ba, Usman ya dinga kokarin kwantar mata da hankali. Aunty Mariya na rike da Mayraah suka sauka downstairs Abba na biye da su a baya, gaba daya jikin Aunty Mariya yayi mugun sanyi, bata san sanda Abba ya dawo mafadaci haka ba cikin kankanin lokaci, da da ne a yanda ta san sa uffan bazai ce ma Ammi ba sai dai kawai ya maida Mayraah asibiti, amma yanzu sam ba haka ba, ya daina mata uzuri kwata kwata, Mayraah na rungume jikin Aunty Mariya har suka isa asibitin a motar Abba, zuwa sannan kam gaba daya jikinta ya rikice don sai sarkewa numfashinta yake, hakan ya sa aka shiga Emergency da ita. Duk yanda Ammi ta so zata koma asibitin bayan tafiyar su Aunty Mariya Usman bai yarda ya bar ta ta koma ba ganin yanda ran Abbansu ya baci, cikin kwantar da murya yace "Ammi pls ki bari gobe da safe sai ki je tunda tare suka koma da Aunty Mariya kuma kinsan zata kula da ita sosai, don Allah kiyi hakuri ki bari gobe, nima yanzu bazan koma ba, idan ya so gobe da sassafe sai mu je" a haka dai ya dinga kwantar mata da hankali har ta hakura da komawa asibitin amma ba can cikin ranta ba, su Hajja da Mama Ladi suna can dakin visitors basu ma san me ke faruwa ba a gidan. Karfe sha biyu saura aka cire ma Mayraah oxygen da aka sa mata bayan numfashinta ya dawo dai dai, MD da Dr Hamid ne tsaye Emergency ward din watching her closely, MD ya karasa kusa da ita ganin kamar magana take son yi, dukawa yayi yana kallonta bai dai ce komai ba, da kyar tace "Ina son zan sha ruwa pls" Yayi shiru bai ce komai ba kuma bai fasa kallonta ba, hakan yasa ta dauke kanta tana kallon direction din Dr Hamid kilan shi zai taimaketa, shi ma da yaga magana take son masa ya isa kusa da ita ya duka yace "Ya aka yi?" Murya can kasa tace "Dr ruwa nake son zan sha" Calmly Dr Hamid yace "Za ki sha zuwa anjima, be patient" Ta marairaice tace "I'm very thirsty" Yace "I know, za ki sha anjima kadan" Daga haka ya juya ya fita ward din, Abba dake bakin Emergency din a zaune tun dazu ya mike yana kallon Dr Hamid, Dr Hamid yace "Numfashinta is stable yanzu, zuwa karfe daya za a maida ta ward" Abba ya sauke ajiyar zuciya yace "Toh
Alhamdulillah" Barin wajen Dr Hamid yayi.... Mayraah ta kara kallon MD kamar zata yi kuka tace "Don Allah ku bar ni in sha ko kadan ne" Shiru yayi da farko, sai kuma yace "Zan baki anjima" Hawaye ya cika idonta tace "To ka kira min yayana nasan shi zai bani" Ya kafeta da ido, a hankali yace "Wani yayan naki?" Tace "Ya Maheer" a hankali yace "Ohk..." Juyawa yayi ya fita daga ward din, bayan wani lokaci ya dawo rike da disposable cup karami da ya debi ruwa kadan cikin Dispenser din dake reception, tana ganin ruwan zata mike zaune amma ta kasa don duk jikinta is weak, ya ajiye karamin cup din, helping her to seat on the bed gently, sannan ya dau ruwan da kansa ya bata very little a ciki, zai mayar ya ajiye a hankali tace "Kadan fa na sha" Sake bata sip daya yayi dai dai nan Dr Balogun ya shigo, da mamaki yake kallonsa da ruwan hannunsa, MD yayi saurin ajiye sauran ruwan sai kuma ya fita ya bar ward din, Dr Balogun yayi disposing ruwan da cup immediately, Aunty Mariya dai na zaune reception tayi tagumi kamar ance ta juya taga Ammi kamar an jefota, mikewa tayi da mamaki ta nufeta da sauri tace "Ammi? Meyasa kika taho cikin daren nan" Ammi da idonta ya kumbura don kuka cikin rawan murya tace "Bazan iya bacci ba Mariya" Aunty Mariya ta kasa ce mata komai, a ranta kuwa fata take Allah yasa kada Abba ya sake wani fadan in ya ganta, can ta kama hannunta suka tafi suka zauna tana kallonta tace "Kin shiga kin duba Maheer?" Ammi na share idonta tace "Ina? Me ya samesa?" Aunty Mariya tace "Ai yana gidan, yana dakinsa baya jin dadi" A hankali Ammi tace "Ai ban sani ba" Aunty Mariya tace "Da ku ka dawo dazu bacci yake ne, saboda shi ne ma nake zaune parlor sai ga ku kun shigo" Ammi dai tayi shiru bata ce komai ba. MD na komawa office dinsa ya tadda Musharraf zaune yana duba wani littafi to distract him daga damuwar halin da Mayraah take ciki, tun da ya fito daga Emergency da aka shigar da Mayraah ya dawo office din yayansa ya zauna, kallo daya Musharraf yayi masa ya maida idonsa kan littafin hannunsa, MD ya ajiye stethoscope dinsa ya zauna kan sofa din office din without looking at Musharraf yayi kasa da murya yace "Now tell me, are you still interested in getting married to her" Musharraf ya daga kai ya kallesa, sai kuma ya ajiye book din hannunsa yace "Who?" MD ya jinginar da kansa da kujera yayi kasa da murya yace "The Girl" Musharraf ya sauke idonsa yace "Why the question?" MD ya kallesa yace "I will make sure...." Shiru yayi ta dalilin wayarsa dake vibrate, ya dauka yana kallon screen din, ganin Ceo ce ke kiransa ya daga ya kai kunne, bata taɓa spending din night a asibitin ba a iya saninsa sai gashi yau har karfe sha biyu da rabi na dare bata tafi gida ba, bayan yaji abinda tace a wayar a hankali yace "Ohk Ma'am" Daga haka ya mike ya nufi kofa Musharraf ya bi sa da kallo har ya fita. MD na isa office dinta ya sameta zaune kan 3 sitter ta lulluba da karamin duvet kamar me jin sanyi tana jiransa, tun da ya shigo yake kallonta ganin yanayinta ya dawo kamar mara lafiya, da ladabi yace "Are you really okay Ma'am, is anything the matter?" Kujera ta nuna masa alamar ya zauna without looking at him, ba musu ya zauna yana kallonta, bayan few seconds ta sauke idonta kasa cikin sanyin murya tace "Tambaya nake son maka Aliyu" Yace "Ohk Ma ina ji" Calmly tace "What did you know about Mary Ann" Ya sauke idonsa kasa, ya ma rasa ko mamakin tambayar nata yayi ko akasin haka, duk da ya jima yana mamakin dalilin da yasa ta sake haka da Mayraah har aka je da ita UK kuma ta sauketa gidanta bayan yasan tana da trust issues, wanda a duk ma'aikatan asibitin nata shi kadai yasan gidanta both UK, Abuja, and Lagos, bayan few seconds ya dago kansa yace "Ma'am ni ban santa ba, ban taɓa ganinta ba sai a asibitin nan, sai dai a yau i was also shock bayan da naga Mamina da Younger brother dina sun zo dubata all the way from kano, and i get to know that fiancee din brother na ce ita da na ce maki an fasa aurensu kwanaki" Ceo dai kallonsa kawai take, can tace "Brother din ka kuma?" MD ya sauke ido a hankali yace "Nima sai yau na sani" Ceo na kara wrapping din duvet din jikinta tace "Ko zan iya sanin me yasa aka fasa auren?" MD ya ɗan yi shiru, a ransa yaji bai kamata ya tona ma Mayraah asiri ba, this is supposed to be her secret in this hospital, yana jin ko Dr Khalil bai san wacece ita ba from the look of things, and bai kamata ya ce ma Ceo ai ita din ba a san asalinta ba, CEO ta dafa shoulder dinsa a hankali tace "Akwai wani abu da zaka boye min ne Aliyu? Talk to me kar ka ji komai" MD ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya, ya san dai ko ya gaya ma Ceo wacece Mayraah yanda yaga take jinta a ranta ba raguwa zai yi ba, lumshe ido yayi ya bude bayan ya gama nazarin yanda zai sanar ma Ceo wacece Mayraah ba tare da yayi tarnishing image dinta ba, Murya can kasa yace "Uncles dina sun gano foster parent kawai gareta...." CEO dake ta kallonsa babu ko kiftawa ta sauke idonta ta dalilin hawayen da ya ciko mata, shi dai MD kallonta kawai yake, ta jawo tissue kan table din gabanta tana goge hawayen da yaki tsaya mata, MD yayi karfin halin cewa "Are you alright Ma?" Da kyar tana ci gaba da goge hawayen dake ta zuba idonta cikin breaking voice tace "Kasan me Aliyu?" Ya girgiza kai yana kallonta, cike da karfin hali tace "Ina son za mu je gidana yanzu, i want to show you something" Yace "Ok Ma'am" Mikewa tayi ta wuce Bedroom dinta ya bi ta da kallo, wondering why she is crying tun dazu, he is just confuse at this point, ba a dau lokaci ba ta fito sanye da kayanta, ko wayoyinta da jaka bata dauka ba ta nufi kofa, ya bi bayanta suka fita daga office din.
*Nagode da kulawarku*
Mayraah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa bello jidda
Ur evidence via 07087865788
*Ina iyaye, yayye da Anties din yaran suke ne If you're looking for an exclusive Baby clothing boutique then visit us at Kids Collection & Fabrics
Shop No BB3, Palm Height Plaza. Opposite Padofec Estate, VON / Trade more road Abuja Nigeria.
Muna da Kayan yara masu kyau da inganchi directly from Bangladesh, Turkey and Dubai
Kuma masu sauqin kudi da rahusa very unique & affordable. Muna delivering zuwa ko wace jaha a kowane Lokaci
For more beautiful pictures and videos check our whatsApp https://wa.me/2348035943474 or Instagram page @kids_collection_nfabrics
https://www.instagram.com/kids_collection_nfabrics?igsh=YzljYTk1ODg3Zg==
For enquiries and order
Contact 08035943474
You'll never regret buying from us.*
85
Personal Driver din Ceo yayi parking a babban parking space din dake cikin gidanta, ta bude back seat ta sauka MD ma ya sakko daga front seat yana kallonta, entrance din shiga mansion din nata ta nufa yana biye da ita a baya, babu kowa a babban parlon gidan ta wuce upstairs, MD ya zauna a parlon ya bi ta da kallo har ta haura sama, bayan dan lokaci daya daga ma'aikatan ta da ya sani a gidan ta sauko kasa ta gaishesa da ladabi sannan tace "Sir tace ka sameta upstairs" MD ya mike tayi leading dinsa zuwa wani babban parlor a sama, nan ma dai babu kowa ciki ya zauna, zuwa yanzu shi kansa ya kagu ya ji dalilin kawosa gidanta da tayi by this time, yayi sensing akwai wani abu me muhimmanci da yasa ta kawosa gidan and he is eager to know what that is, bayan kusan minti goma sai ga ta ta shigo parlon tana kallonsa a hankali tace "Come in Aliyu" Mikewa yayi ya bi bayanta suka bi wani corridor me fadi sannan ta bude daya daga kofofi hudu dake wajen ta shiga yana biye da ita a baya, babban daki ne sosai that is well furnished, babu abinda babu a cikin dakin, kwance saman gadon wata kyakkyawar mace ce da bazata haura shekara 42 ba cikin babban duvet, tsaye a dakin wata registered nurse ce sai maid biyu, Ceo ta karasa kusa da ita ta zauna tana shafa dogon gashinta a hankali tace "Meet Dr Aliyu" Kallonsa kawai matar take babu ko kiftawa, MD ya dan kirkiri murmushi yace "Good Morning ma'am" ta dai kafesa da ido, Ceo ta sauke idonta kasa, bayan few seconds ta kwantar da ita a hankali tana kallonta, Maid din dake tsaye ta karasa da sauri ta gyara mata duvet din da pillow, Ceo na kallon nurse din dakin tace "Ya aka yi bata yi bacci ba har yanzu?" Da ladabi nurse din tace "Farkawa tayi Ma" Ceo ta sauke idonta tace "Sorry i interrupted ur sleep, pls get me a Syringe and Needle" Nurse din ta juya ta bude wani kofa ta shiga ciki, ba a dau lokaci ba ta dawo rike da shi, Ceo na kallon MD tace "Come over Aliyu" Ya karasa kusa da gadon, shi ta sa ya debi jinin, matar was calm har ya gama diban jinin, bayan few minutes Ceo tayi pecking forehead dinta sannan ta kwantar da ita, Daga haka ta mike ta nufi kofa tana fita MD ya bi bayanta, tsaye ya sameta a parlor ta fada duniyar tunani, ya sunkuyar da kansa don shi dai at this point he is confuse at what she is up to, ga jinin dake cikin karamin roba inside a ziploc da ke hannunta, to wace mata ce wannan da ta sa ya debi jininta don shi dai duk zuwansa gidan bai san da ita ba, bai kuma taɓa ganinta ba duk da har upstairs ya kan kai ma Ceo sako, ya dai san ma'aikatan gidan kaf dinsu amma banda wannan mata dake kwance wanda ga dukkan alamu she is not even stable, kallon Ceo ya sake yi ya ga ta dan yi murmushi tana goge hawayen da ke taruwa idonta without looking at him tace "We are going back to the hospital now Aliyu" Ya gyada kai yace "Ohk Ma" Shi ya fara nufar kofa cike da mamaki ya fita daga parlon sannan ta bi bayansa tana tafiya a hankali, karfe biyu da rabi suka isa asibitin, Dr Balogun da shigowarsa reception kenan ya karasa yana ma Ceo sannu da zuwa, Ba tare da ta kallesa ba tace "An maida Mary Ann ward ne ko har yanzu tana da Emergency?" Da ladabi yace "An maida ta ward ma, ai numfashin nata is stable yanxu" Tace "Wani ward din take?" Gaya mata yayi ta nufi ward din MD na biye da ita, Aunty Mariya ce zaune ita kadai a ciki sai Mayraah da ta samu bacci, Aunty Mariya tayi ma Ceo din sannu da shigowa ta koma gefe, Ceo ta amsa idonta na kan Mayraah sai kuma ta kalli MD, calmly tace "Get a Syringe and Needle" MD ya juya ya fita ward din wondering abinda zata yi da shi, bayan few minutes sai ga shi ya dawo, Ceo tace "Take her blood sample" MD was stunned jin instruction din da ta basa, haka nan dai ya debi jinin Mayraah sannan suka fita daga ward din Aunty Mariya dai ta bi su da ido, MD ya raka Ceo har office dinta, bayan ta zauna ta basa sample din da ta sa ya diba a gidanta, a hankali tace "Genetic testing for the both samples nake so Asap" Mamaki ne ya cika MD ya dinga kallonta, har mamakin ya kasa boyuwa a fuskarsa, genetic testing kuma? To me hakan ke nufi? What is her aim nayi genetic test for the both samples, ya dai yi karfin halin amsan samples din yana kallonta, can ya juya ya nufi kofa ta bi sa da kallo idonta cike da wasu sabbin hawayen.
Washegari da safe bayan Ceo ta shiga ward din da Mayraah take ta dubata ta fito, har bakin motar ta MD ya rakata da laptop dinta, bayan ta shiga bayan motar ya mika mata laptop din ganin yanayinta yace "Ma'am u need rest" Ta gyada masa kai a hankali tace "Sure, pls ku kula da ita yanda ya kamata" Yace "We will do that Ma" kulle mata motar yayi daga haka ya juya ya koma asibitin, a reception ya tadda Musharraf ya fito daga ward din da Mayraah take, MD na kallonsa ganin zai fita yace "Ina zaka?" Musharraf yace "Airport, my flight is in 30mins time" MD yace "Why did u book without telling me?" Musharraf yace "Mami ai ta gaya maka yau zan koma kano" MD yace "Allah ya tsare" Daga nan ya wuce sama, Musharraf kuma ya fita daga reception din. Daga wannan ranan Ceo bata sake shigowa asibitin ba, a kwana hudu Mayraah ta samu sauki sosai har tana iya cin abinci, all through this 4 days Aunty Mariya ce tare da ita a asibitin sai Usman da Ammi dake zuwa dubata kullum, don Abba ya hana Ammi kwana asibitin. Yau da yamma suna haraban asibitin da Aunty Mariya bayan sun yi strolling kamar yanda likitocin suka ce ta dinga yi duk yamma, Mayraah ta kalli Aunty Mariya da damuwa tace "Aunty wai me yaya yaje yi a kasar waje ne har yanzu bai dawo ba?" Aunty Mariya tace "Wani aiki ne ya kai sa mana, amma nasan ya kusa dawowa in sha Allah" Mayraah dai tayi shiru tana nazarin abinda Aunty Mariya tace, can dai ta sake kallon Aunty Mariya tace "Shine zai tafi bayan yasan bani da lafiya?" Aunty Mariya tayi dariya tace "Gaskiya kam, don kamata yayi ya ajiye masu aikin ya zauna kusa da kanwarsa har sai ta samu lafiya" Murmushi Mayraah tayi bata sake cewa komai ba, Aunty Mariya tace "Ta shi mu shiga ciki ai kinyi strolling din