Mayrah

Chapter 94 of 152

da yawa yau" Mikewa Mayraah tayi suka koma cikin asibitin tare da Aunty Mariya, a haka dai har Mayraah suka yi kwanaki bakwai tare da Aunty Mariya a asibitin, all this while MD gaba daya attention dinsa da curiosity na kan Genetic testing din da Ceo ta basa ayi, ya rasa dalilin kaguwan da yayi result din ya fito, sai kirga kwanakin yake, a washegarin ranan kuma Abba ya bukaci ayi discharging dinsu a gaya masa bill in dai babu sauran matsala don kowa yaga Mayraah yasan ta samu lafiya sosai, Bayan azahar Dr Khalil na kallon MD dake zaune kan office chair dinsa bayan ya sanar masa bukatan Abba yace "Amma kai ya ka ga? Ni dai a ganina ya kamata ayi discharging dinsu" MD yayi shiru, shi kansa yasan Mayraah ta samu sauki yanzu, kuma tunda case din nata a hannunsa yake shi ya kamata yayi discharging dinta amma yaki yin hakan beside ita ma Ceo bata ce yayi hakan ba don kullum sai ta kirasa ta tambayi jikinta asibitin ne dai taki shigowa, Dr Khalil yace "Wai tunanin me kake ne sir? Ko baka gaji da ganinta bane har yanzu?" Da murmushi ya kare maganar, Shi dai MD bai tankasa ba, can yace "Ban gane ban gaji da ganinta ba, let me call Ceo first...." Da mamaki Dr Khalil yace "Ceo kuma? Ita da bata kasar, beside naga ba a taɓa sanar mata ba idan za a sallami patient?" MD yace "Tana kasar nan, beside file din a hannunta yake not me...." Dr Khalil yace "Really, naga yau sati daya bata shigo ba, na zata ta koma ne wallahi....." MD yace "Bata da lafiya ne, but she is better now" Dr Khalil yace "Allah ya bata lafiya" MD ya dau wayarsa yayi dialing number Ceo yana fara ring ta daga, bayan ya gaisheta ya sanar mata dalilin kiran, Ceo tayi shiru, bayan few seconds tace "Zaka iya discharging dinsu, as for bill da ya tambaya kuma, tell him basu da bill" a hankali yace "Ohk Ma'am" Tace "Yaushe result din nan zai fito Aliyu?" Yace "Zuwa anjima in sha Allah" cikin sanyin murya tace "No bill for them" Yace "Ohk Ma'am" Mikewa yayi ya nufi kofa Dr Khalil ya bi bayansa. Tun da Mayraah taji an sallamesu take farin ciki don gaba daya ta kagu su bar asibitin ta koma gida, shi dai Usman bai gane dalilin da zai sa MD yace babu maganar bill everything is free ba, Aunty Mariya na kallonsa tace "Aa fa barrister, ni a ganina saboda staff dinsu ce shi yasa suka ce babu zancen Bill" Usman yace "Gaba daya yaushe ta fara aikin har ta zama staff dinsu? Kinsan yau kwananta nawa a asibitin nan kuwa? ko ICU kinsan nawa ake biya a rana daya balle wannan asibitin me tsada, kuma tayi kusan sati daya a ICU, hatta drugs da alluran da aka dinga mata kwanaki masu tsada ne, ga kuma abincin da ake bata sau uku a rana, so i don't understand dalilin da zai sa yace babu Bill" Mayraah dai sai kallon Usman take, Aunty Mariya tace "Mu dai koma menene Allah ya saka masu da alkhairi barrister, kuma don Allah kar ma ka gaya ma Ammi don nasan sai ta kara juye batun nan, amma nafi tunanin kawai don ta fara aiki ne tare da su yasa suka yi duk wannan abun a kyauta, yanzu dai an sallami Maheer din ne?" Da sauri Mayraah ta juya tana kallon Aunty Mariya babu ko kiftawa, lkci daya ta sauka daga saman gadon da take tace "Aunty ba shi da lafiya ne?" Usman dai kallonta kawai yake, Aunty Mariya ta ɗan zare ido don ta mance a gabanta tayi tambayar, nan da nan ta kirkiro murmushi tace "Jiya ya dawo bashi da lafiya shine ya je ganin likita, amma da sauki ai" Mayraah dai ta dinga kallonta babu ko kiftawa, Can ta juya ta kalli Usman da damuwa tace "Ya Usman dama Yaya bashi da lafiya shi ne aka ki gaya min?" Usman yace "Ya samu lafiya yanzu, idan mun je gida za ki gani" Aunty Mariya ta kama hannunta suka fita daga ward din Usman ya bi bayansu, kamar yanda MD ke avoiding eye contacts da Mayraah for the past one week now, ita ma hakan take a wajenta, don tun da ta gane shine yayan Musharraf wanda back then Musharraf ya sha bata labarinsa amma kuma yace mata yana canada ta ma rasa gane ko kunyan abubuwan da ta dinga masa a baya take, ko kuma dana sanin abinda tayi masa take, wani zuciyar sai yace mata ai ita bata taɓa masa komai ba shine ma yayi ta mata walakanci, but all the same ko don saboda Musharraf ta dau alwashin dole zata ce masa yayi hakuri abubuwan da suka faru a baya amma dai ba yanzu ba tukun, suna fitowa Reception tare da Aunty Mariya kawai ta hada ido da shi, sosai gabanta ya fadi ta sunkuyar da kanta da sauri, Aunty Mariya na kallonsa da murmushi fuskarta tace "Toh Dr mu zamu tafi gida, Allah Ubangiji ya saka da alkhairi, don Allah ayi ma sauran likitocin ma godiya" Ya sauke idonsa yace "Ameen, Allah ya tsare" Kallo daya yayi ma Usman ya juya ya tafi sama, su kuma suka fita daga asibitin, Mayraah na shiga gida bayan ta rungume Ammi dake kitchen tana masu girki don Aunty Mariya ta kirata ta sanar mata an sallamesu, tambayar farko da ta fara yi ma Ammi bayan ta saketa shine "Ammi ina Yaya?" Ammi ta ɗan yi murmushin karfin hali tace "Anjima zai dawo, mu je kiyi wanka" Da damuwa Mayraah tace "Aa Ammi dama ashe bashi da lafiya ne kika ce min ya tafi kasar waje, don Allah ki gaya min inda yake" Ammi ta kama hannunta tace "Kin ga, in dai yaya ne ai dole zaki gansa tunda gida daya za ku kwana, yanzu mu je ki yi wanka ki ci abinci kafin la'asar yayi" Daga haka Ammi ta ja ta suka fita daga kitchen din zuwa sama. Tun da MD ya ga result din DNA test da Ceo ta sa ayi for the past one week ya shiga wani irin rudani da confusion, gaba daya tunaninsa ya kwance, don result din na fitowa kasa hakuri yayi har sai da duba duk da yasan bai kamata ya duba ba, kasa zaune yayi ya kasa tsaye a office dinsa, gashi ko awa daya ba ayi da su Mayraah suka tafi gida ba, does it mean matar nan da ya gani kwance saman gado ita ce mahaifiyar Mayraah? But how? Meye relationship din matar nan da Ceo? Da kansa fa ya debi jinin matar, sannan ya debi na Mayraah, how comes Genetic test din came out Positive, bai san sanda ya dau wayarsa ya kira Ceo da sauri ba, yana fara ring ta daga, ya koma ya zauna cike da confusion yace "Ma result din ya fito yanzu" Shiru Ceo tayi kamar bazata ce komai ba, sai kuma a hankali tace "Nasan ka duba Aliyu, me ka gani?" Cike da confusion yace "Ma'am it came out Positive" Cikin rawan murya Ceo tace "To ita ce mahaifiyarta" MD ya mike tsaye yace "But how Ma? Are you in anyway related to the Woman?" Ceo tayi karfin halin cewa "It's a very long story Aliyu" sai kuma ta fashe da kukan da take ta kokarin dannewa, MD da zuciyarsa ke bugawa yace "To mahaifinta fa?" Nan ma Ceo tayi shiru kamar bazata ce komai ba, sai kuma tayi murmushin takaici cikin rawan murya tace "Yana nan Aliyu, da kuma zan ambaci sunansa kai kanka zaka san sa, don he is well known amma yafi shekara bakwai rabonsa da Nigeria, time to time mu kan hadu da shi a UK" MD ya koma ya zauna ya ma rasa abinda zai ce mata, da kyar daga karshe ya iya cewa "Yanzu taya za a gabatar ma foster parent dinta wannan issue din?" Shiru tayi kamar bazata ce komai ba tana murmushin takaici, sai kuma a hankali tace "I will give them the time, day, date, month and year din da suka ganta, da kuma dai dai inda suka ganta din, da kuma yanayin da suka ganta" zuwa yanzu she was trying so hard to control her self kar ta fashe da kuka sosai, MD ya kara shiga wani confusion din, ya mike tsaye yace "Amma ta yaya kika san duk wannan Ma? Dama kinsan sanda aka yi deserting dinta ne da kuma inda aka yi deserting dinta?" Hawaye ne kawai ke sauka idonta ta kasa ce masa komai, bayan wasu seconds tayi gathering courage tace "I said it's a long story Aliyu, i will get back to you" Daga haka ta katse wayar yanda zata yi kukan dake cin ta sosai.

Mayraah is 500 via 3276052019 Fcmb Hauwa bello jidda

Ur evidence via 07087865788




*_TAHO KI GANI_*👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽

_shin kinsan da zaman wannan kuwa?,ko kina can kina bulayin neman inda zaki samu ingantattun kayan mata da SUPPLEMENT masu inganci cikin musulmin farashi?_

*Turqashi,ga biyan buqata ga sauqi*!

*ZAHRA DANGE* 👉🏽 _face behind LADY APHRODISIAC AND MORE_

*dealer in all kind of supplement and herbal aphrodisiacs kayan mata*
*Kayan mu will make you last on bed and permanently end the pain and embarrassment of weak eraction and premature ejaculation*


*Muna hadin bridal package*
*postnatal combination of natural herb's and supplement*

*Akwai hadin uwar gida mai da tsuhuwa yarinya*

*Akwai hadi na infection (sanyi herbs)*

*Akwai Zuma Mai saukar DA niima nan take tare da dandano Na mussaman*

*Muna kalolin gumbar Kamar gumbar madara, gumbar Aya, gumbar ridi, gumbar kasko, yar kicihi, Alhaji ba nan kake ba d.s*

*Akwai kalolin tsimi kamar Dan la'asar, tabaje, tsimin yar gata d.s*

*Muna DA kalolin gari nasha kamar sa buzu kuwa, sinadarin aya, abin sirri ne, emergency, rakumi DA akala, runbun dadi, kinfi Amarya d.s.*

*Muna special kaza, danbu,ciccibi, Yan shila,zuciya d.s*

*Akwai Na matsi different types DA sabulu na tsalki.*

*TA BANGAREN SUPPLEMENT*

*muna da na gyaran skin da kuma herbal aphrodisiacs supplement*

*Akwaisu Juliet eve, royal jelly, ultimate maca, suprodine, frozen detox, frozen collegen, majakani,amirna, khusus, dara,cantik ayu, pesona d.s*

*We have capsules, pills, chocolate, and different coffee that will make you sweet, firm, tight, young, beautiful and healthy.*

*Akwai different oils both siyan d'aya ko sari*

*Muna nan a garin SOKOTO sannan muna tura kaya ko ina a fadin duniya yaje maka cikin aminci IN SHA ALLAH*🌐

*_ZAKU IYA TUNTUBARTA KAI TSAYE TA WANNAN NUMBER WAYAR_*

07034400732

*_SIYAN NA GARI MAI DA KUDI GIDA_*👌🏽👌🏽👌🏽

86
Ammi ta ajiye abincin da ta kawo ma Mayraah har bedroom dinta da farfesun hanta tana kallonta tace "Ko zaki sha shayi?" Mayraah ta girgiza kai tace "A'a abincin ya isa Ammi" Ammi ta nufi kofa, Mayraah dai ta bi ta da kallo har ta fita ta kullo mata kofar, a hankali ta rufe abincin ta matsar gefe daya sannan ta mike ta dau hularta ta saka ta nufi kofar dakin ta bude a hankali tana leka corridor, sai da ta daina hango Ammi sannan ta fito ta kulle kofar dakinta ta sauka downstairs, dakin Maheer ta tafi ta kwankwasa kofar gently sannan ta murda handle din ta bude kofar, a tare suka juya shi da Usman suna kallon kofar, ta ɗan wara ido ta karasa ciki da sauri tana kallon Maheer da damuwa ta durkusa gabansa tace "Yaya baka san na dawo ba ne?" Sai kuma ta kalli Cannula din hannunsa kafin tace komai yace "Yanzu drip din ya kare zan yi sallah sai in je inyi welcoming dinki Mimi" Ta mike tana kallonsa cike da damuwa tace "Me ya sameka yaya? Since when were u sick?" a hankali yace "Naji sauki ai, Alhamdulillah" Ta kai hannu forehead dinsa gently taji temperature dinsa is normal, cikin sanyin murya tace "Allah ya sauwake yaya" Ya sauke idonsa yace "Ameen Mimi, ya naki jikin?" Tace "Ai naji sauki tuntuni" Ta kalli abincin dake kasa cikin warmer, ta durkusa ta bude tace "In zuba maka abincin?" Yace "Lokacin sallah yayi ai, sallah zan yi first" Zaunawa tayi saman carpet din tace "Ohk i will wait, idan kayi sai in zuba maka" Murmushi yayi yace "Ke baza kiyi sallan bane?" Sai a sannan ta daga kai ta kalli Usman dake kallonsu, sai taki cewa komai kawai ta sunkuyar da kanta ta tallabi chin dinta tana murmushi, shi dai Usman wayarsa kawai yake dannawa, Mikewa tayi tace "Idan an idar da sallah zan dawo Yaya" Yace "Ohk" Usman ya dau wayar Aunty Mariya ya mika mata yace "Ki kai ma Aunty wayarta" Amsan wayar tayi sannan ta fita daga dakin, Usman na kallon Maheer yace "Za ka iya zuwa masallacin ne?" Maheer yace "Let's pray here" Mayraah na komawa daki ta debi abincin da Ammi ta kawo mata dakin, a hankali take cin abincin, lkci daya jikinta yayi sanyi bayan ta tuna incident din da ya sa tayi kusan sati uku a asibiti, duk son ta da abincin sai ta kasa cin da yawa don nan da nan ya fita ranta, daga karshe ta rufe kawai ta mike a hankali ta koma saman gado ta kwanta incident din na dawo mata a kai vividly, bayan minti ashirin taji an bude kofar dakin, juyawa tayi da sauri taga Usman tsaye bakin kofar dakin ta mike zaune kafin tace komai yace "Ya idar da sallahn, ki je ki zuba masa abincin" Ta sauko daga saman gadon tace "Toh" Sai kuma da sauri tace "Yaya kai ka ci abincin?" Yace "Sai anjima" Daga haka ya bar bakin kofar ta fita zuwa dakin Maheer, yana zaune saman darduma ta samesa da counter a hannunsa, ta kulle kofa ta karaso ta durkusa kusa da shi tace "Ka gama yaya?" Yace "Na gama" kallonsa ta dinga yi ganin yanda ya rame, da damuwa tace "Yaya for how long were u sick?" Da fingers dinsa ya nuna mata alamar 2 days, bata sake cewa komai ba ta bude warmer din, same food ne da wanda ta ci dazu a dakinta, ta debar masa ta sa cokali sannan ta koma gefe ta zauna tana kallonsa, sauke idonsa yayi ya dau spoon din ya fara cin abincin a hankali, bayan few minutes yayi breaking silence din dakin yace "I heard MD yayan Musharraf ne ko...." Mayraah ta wara ido tace "Yaya i was very very shock, it was the least thing I expected yaya.... Kuma fa basa kama, kawai dai suna da same thick eye brow with fingers, apart from that i see no resemblance, or may be their noses look alike also, sannan yanayin halinsu ma iri daya wallahi, at times fa idan MD din yayi wani abu sai Musharraf ya fado min, attitude dinsu is almost same, just that Musharraf baya ba irrelevant issues relevant kamar MD, ashe shi MD da Maminsu yake kama, yaya that very day kawai sai nake ganin abun kamar a mafarki wallahi, what a coincidence...." Murmushi kawai Maheer yake yana cin abincin gabansa yana sauraronta, don kanta tayi shiru, ya daga kai ya kalleta yace "Kamar dama kina jiran wannan tambayar ki fara amayar da abinda ke ranki?" Mayraah tayi er dariya tace "Wallahi na rasa da wanda zanyi labarin, i was so shock and confused at the same time, sai nayi regretting abubuwan da na dinga masa a asibitin" a hankali ta karasa maganar, Maheer na kallonta yace "Wasu abubuwa kika dinga yi masa?" Mayraah ta ɗan langwabar da kai tace "Ko da yake shine ai ya janyo duk abinda nayi masa" Maheer yace "Gaya min abinda kika masa" Zata yi magana aka bude kofar dakin, duk suka daga kai, Ammi ce tsaye bakin kofar dakin, mamakin abincin da Maheer yake ci tayi, don for the pass 5 days sai dai ya sha tea kadan ko kuma ya sha fruits amma ba dai abinci ba, ko da ta tilasta sa ya ci abincin to cokali biyu zai yi da kyar, yanzu kuma taga ya ci da ɗan yawa, Mayraah zata mike Ammi tace "Yi zaman ki, ke kin ci abincin ne?" Mayraah ta gyada mata kai tace "Na ci" Rufe kofar Ammi tayi ta bar wajen, Maheer ya kalli wayarsa dake vibrate ya dauka yana kallon screen din, can ya kalli Mayraah yace "Shi yake kirana" Mayraah ta buda ido sosai tace "MD din?" Maheer ya gyada mata kai sannan yayi picking call din ya kai kunne tare da sallama, gaisawa suka yi sannan Maheer yayi shiru yana sauraron sa, can yace "Ohk zuwa yaushe kenan?" Daga karshe dai Maheer yace "Alright, ba damuwa" Katse wayar yayi, Mayraah dai sai kallonsa take eagerly taji abinda MD yace masa, bayan ya ajiye wayar da sauri tace "Yaya me yace maka?" Maheer ya ja hancinta yace "Cewa yayi akwai sauran drip uku da za a saka maki a asibitin da kuma allurai 5, wai a maido ki yanzu" Mayraah bata san sanda ta hade rai ba tace "Aa ko ba drip ba, sai dai ya sa ma kansa, ni dai kowa yasan na warke" Dariya Maheer yayi, tana ganin haka ta marairaice tace "Pls be serious mana yaya, nasan ba haka yace maka ba, don Allah ka gaya min me yace maka?" Maheer ya ajiye spoon din hannunsa a hankali yace "Cewa yayi zai zo gida mu hadu, he wants to discuss an issue with me" Mayraah dai tayi shiru tana kallonsa a ranta kuwa sai nanata issue din take, bude kofa aka yi duk suka juya, Usman ya shigo ya ajiye ma Mayraah leda a kusa da ita yace "Wash the fruits for him" Ta bude ledan tana lekan ciki sai kuma ta kallesa tace "Yaya ni fa?" Yace "Au zaki sha ko?" Ta wani turo baki tana kallonsa, yayi murmushi yace "It's for the both of you" Ta washe baki tace "Toh mun gode yaya" Tare suka fita dakin da shi, ita ta wuce kitchen zata wanko fruits din shi kuma ya haura sama.
Bayan isha Maheer ya fito parlor bayan MD ya kirasa ya sanar masa

Download complete TXT · Novel page