Mayrah

Chapter 98 of 152

dai ko" Mama Ladi tace "To Allah ya tsare" Ammi tace "Ameen" Kofa ta nufa Mama Ladi tace "Kin dai ji Badiyyah na can ranga ranga asibiti rai a hannun Allah wai ta zame wajen shiga bandakin Yahanasu, kinsan bandakin gidan Yahanasu ko na kasuwa albarka, ga uban gansa kuka, har wani yauki yauki bandakin yake wllh, abun dai ba arziki ko dake duk kun sani ai, ita fa Yahanasu tun muna yan mata take kazanta gashi ya bi ta har tsufa, ko ruwa baka iya sha in ka shiga gidanta sai in kai ma kazamin ne" Ammi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, yaushe hakan ya faru?" Aunty Mariya ta numfasa tace "Da asuba aka kirani, ashe tun jiya da daddare abun ya faru" Ammi tace "Amma jikin da sauki dai ko?" Mama Ladi tace "Wuyarta ace mana tayi ɓari, kilan ma da gangan ta zame, ko da yake cikin shege ai kowa yasan naci ne da shi, ba wani zancen barewa" Ammi na kallon Aunty Mariya tace "Wa ke tare da ita a asibiti?" Aunty Mariya tace "Wai babbar jikar Yahanasu, sun kira Hajja tace masu ai ita bata garin ma, Yahanasun ma taki bin su asibitin, dole haka ni nayi masu transfer dazun nan wai za a kara mata jini, sannan she is unconscious, wannan ne ma yasa nake son in koma kadunan yau" Ammi tayi shiru ta ma rasa me zata ce, can ta sauke ajiyar zuciya tace "Shikenan, in sha Allahu zan karasa asibitin in mun je kadunan" Aunty Mariya tace "Toh Allah Ubangiji ya kai ku lafiya, wai har su Maheer?" Ammi tace "Eh har su" daga haka ta fita daga dakin. Ammi na kallon Abba bayan ya gama shiryawa, cikin sanyin murya tace "Yallabai ga wani suggestion da ya zo raina yanzun nan" Abba ya juya yana kallonta yace "Na me fa?" A hankali tace "Ni a nawa tunanin Yallabai why not mu bar Mayraah kawai ba sai mun je da ita kadunan nan ba, wallahi bana son abinda zai sake daga mata hankali duk da dai naga tun jiya bata saka damuwa a ranta ba, yau ma naga da walwalarta ta tashi ba wani damuwa, to kar mu je kadunan nan kuma ta samu heartbreak din da ya fi na jiya, i don't want my daughter to be hurt" Abba ya ɗan yi shiru yana kallonta, bayan wasu dakikai yace "Kar ki damu, in sha Allah abinda kike tsoro bazai faru ba, tun da kin ji me asibitin tace mutumin na ta bibiyanta a kasar waje yana tambayarta ita uwar Mayraah din, so wannan ne nima ya bani karfin gwiwan aje da ita, in sha Allah babu abinda zai faru sai alkhairi, we will go with her" Ammi sai da taji wani rass jin kalman da Abba ya fada wai Uwar Mayraah, sunan da ita ke ta bearing for 22 years now, a hankali Ammi ta sauke idonta tace "Toh shikenan" Abba yace "Hope duk sun gama shiryawa?" Kallonta Abba ya dinga yi jin bata ce komai ba, kuma bata ma san yayi mata magana ba, Abba yayi kasa da murya yace "To meye kuma damuwar? Gaya min menene kuma" Ta ɗan yi yake, sai kuma a hankali tace "And yallabai, sai jiya cikin dare abubuwan da suka faru suka dinga dawo min zuciyata, yallabai gaban wan Musharraf din nan fa aka yi duk wannan maganar? Wallahi da abun nan ya fado min cikin dare kasa bacci nayi, bai kamata ayi komai a gabansa ba, mun yi babban kuskure, kuma wannan kamar kara tona ma kanmu da ita Mayraan asiri muka yi, shi ma ai ba haka ake ba, family issue ne wannan da sai ya fita ya bamu waje, amma yana zaune duk ta bada wannan mummunan labarin shi ma yana ji" Abba ya sauke ajiyar zuciya yace "Maheer da Usman sun min wannan maganar tun jiya, but ya muka iya? tunda kika ga tayi duk maganan nan a gabansa kinsan ta yarda da shi ne sosai and suna da kusanci da kyakkyawan alaka da shi, kin ga bayan da muka hau sama zuwa dakin ita wannan matar ai bata fara magana ba sai da tace nurse din ta fita, so she trust him definitely" Ammi ta bata rai tace "Duk da haka dai, yayan fa tsohon saurayin Mayraan ne, yanzu idan ya kwashi duk wannan labarin mara dadin fada ya je ya gaya masu fa? Ni dai wallahi hankalina yayi mugun tashi da abun nan ya fado min cikin dare" Abba yace "In ma yaje ya gaya masu ba abu bane da zai dame mu, it's left for them, don ba mu da wani business da su har a tashi duniya, don su ne musabbabin rugujewan farin cikin Mayraah" A sanyaye Ammi tace "Haka ne Yallabai, lokaci na wucewa kuma airport da nisa daga nan" Abba yace "Ki duba ko sun gama shiryawa" Kofa Ammi ta nufa ta fita daga dakin. Usman ne zai yi driving din na su zuwa airport, Mayraah dake sanye da hijab har kasa tana kallon Maheer tace "Yaya to wa zai dawo da motar" Maheer ya bude mata back seat kafin su Ammi da Abba su karaso yace "Zai bar motar a airport" Mayraah tace "Amma dai biya ake ko?" Yayi murmushi yace "What did u expect" Murmushin tayi ita ma ta shiga motar, Usman dai yana zaune driver seat, Maheer ya zaga ya bude ma Abba front seat don yasan can zai ce zai zauna, karfe takwas da few minutes suka bar gidan heading to the airport. Ko da suka isa airport suka tarar Ceo har ta iso tare da Aaria sai nurse dinta duk suna zaune a lounge, Ceo ta mike tsaye suka gaisa da Abba da Ammi, sannan ta amsa gaisuwar su Maheer, Aaria dai sai kallon Mayraah take, Mayraah ta sukunyar da kanta, bayan ta gaida Ceo ta karasa gunta tana tafiya a hankali, zaunawa tayi tana kallonta ta gaisheta cikin sanyin murya, Aaria bata fasa kallonta ba kuma ta kasa amsa gaisuwar da take mata, Mayraah ta sunkuyar da kanta zuciyarta na bugawa, bayan few seconds Aaria ta sauke idonta kasa, nan da nan hawaye ya fara sauko mata, Ceo ta koma gefenta ta zauna ta jawota jikinta speaking calmly tace "Common My love, where is the promise u made to me" Aaria ta daura kanta saman shoulder din yayarta hawaye na sauka idonta, ita dai Mayraah bata iya ta dago kanta ba, Ammi dai sai kallonsu take, ashe kyan Mayraah ba komai bane a inda kyan uwarta yake, cause her mother is really beautiful, babu wanda zai bata shekarunta ko kuma yace ta haifi kamar Mayraah, A haka suka yi boarding jirgi, shi dai Maheer yayi mamakin da bai ga MD ba don ya zata da shi za su je kadunan, but daga shi har Usman a ransu sun ga hakan ya fi.
Karfe tara da rabi suka sauka airport din garin kaduna, motoci uku na airport din suna jiransu, nan da nan mood din Ammi ya canza bayan taga MD ya sauka daga cikin daya daga motocin, daga Maheer har Usman ma basu ji dadin ganinsa ba, a haka suka karasa har gun motocin, bayan duk ya gaishesu Ceo tace "Ya me jikin? Is she better?" Yayi murmushi yace "He is better Ma'am" Tace "To Allah ya basa lafiya" Cikin ladabi yace "Ameen, ni zan dau taxi in koma gida, idan kun gama za ku taho airport sai ki min waya Ma....." Sosai hankalin Ammi ya kwanta jin abinda MD yace, duk da dai aikin gama ya gama don me ya rage da bai sani ba kuma, Ceo tace "Where are you headed now?" Yace "Malali..." Ceo tace "Ohk to ba damuwa, zan kira ka if we are done"
Bayan sun iso unguwar Malali, su Abba suka ga motarsu Ceo dake gaban nasu sun yi parking a gefen hanya, hakan yasa nasu drivern ma yayi parking, sauka drivern motarsu Ceo yayi ya nufi gun wasu matasa dake tsaye bakin hanya, daga yanda suke communicating zaka fahimci tambayarsu direction din gidan da za su yake su kuma suna masa kwatancen, bai jima tsaye yana magana da su ba ya koma ya shiga mota, Wani hadadden layi suka shiga bayan sun kara tafiyar wasu mintuna, nan ma sai da drivern su Ceo ya sauka yayi tambaya aka sake basa direction, tun da suka baro Abuja sai yanzu Mayraah ta dinga jin zuciyarta na bugawa sosai, kwantar da kanta tayi jikin Ammi da ta rungumeta ta lumshe ido, dai dai gate din wani gida me girman gaske wanda aka yi ma gini irin na zamani suka ga driver din su Ceo yayi parking bayan sun wuce wasu yan sanda kafin su shigo unguwan, motarsu Mayraah ma yayi parking a bayan nasu Ceo, sai da Ceo ta sauko tare da Aaria da nurse dinta sannan Abba ma suka sauka, da kyar Mayraah ta iya saukowa daga motar Ammi na rike da hannunta, her heart is just beating so fast, bayan motocin su akwai wasu tsadaddun motoci biyu a kofar gidan ko wanne kuma da soja daya tsaye jikin motar, Ceo ta nufi babban gate din gidan su Abba na biye da ita a baya, Securities din na kallonsu babu yabo babu fallasa da turanci suka shiga tambayarsu wa suke nema kuma daga ina suke taho, wasu dattawan maza biyu ne cikin shiga ta alfarma suka bude gate din gidan suka fito, security daya ya kulle gate din, gaisawa suka yi da Abba da su Ceo a mutunce, har Abba ya gane daya daga cikinsu don he is a wealthy business man that is well known, kallon securities din bakin gate din daya daga dattawan yayi cikin harshen turanci yake masa magana a ɗan fusace yace "Duk wanda za ku ga ya zo a wannan lokacin to zuwa yayi ya duba mai gidan, so ku barsu su shiga ba sai kun tsaya dogon surutu ba" Da ladabi securities din suka ce "Yes sir" bude masu gate din suka yi duk suka shiga ciki, Ceo dake rike da hannun Aaria tana kallon daya daga securities din tace "Ina ne direction din shiga entrance na gidan?" Nuna mata yayi da ladabi, tana kallon Nurse din dake tare da su ta nuna mata wani waje da aka yi a compound din domin shan iska tace "Farida zaki iya jiranmu a can" Da ladabi Faridar tace "Toh Ma" Daga haka ta tafi can ta zauna, parlor na farko su Ceo suka shiga wanda babu kowa a ciki, hakan yasa ta karasa har second parlor din kanta tsaye su Abba na biye da ita a baya, shi dai Maheer har mamakin courage da confidence dinta yake kuma da alama sam bata da tsoro, Ammi dai gabanta sai faduwa yake kar mai gidan ya masu tijara ko ya koresu, suna shiga second parlor din wata mata da bazata wuce 43 ba ta fito daga wani bangare, tsaye tayi tana kallonsu at the same time tana masu sannu da zuwa, lokaci daya ta buda ido sosai bayan sun hada ido da Aaria, da sauri ta karasa har inda suke tsaye da mamaki tace "Maryam??" Ammi da tayi stiff a inda ta tsaya sai kallon matar take bata ko kiftawa....

Mayraah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788

90
Juyawan da wannan matar da ta kira sunan Aaria zata
yi suka yi ido hudu da Ammi dake ta kallonta da wani expression gabanta na faduwa, Matar ma ta dinga
kallon Ammi ba ta ko kiftawa alamar tana son tuno inda ta taba saninta ita ma, duk da haka dai fuskarta
da fara'a take nuna masu kuieru tana welcoming
dinsu tace "Bismillahn ku ga kujera...." Ammi ta sauke
idonta, hannunta rike da na Mayraah ta karasa
kujeran suka zauna tunani iri iri na yawo a ranta, gaba
daya she is just confused, Abba ma duk suka karasa
can cikin parlon suka zauna kan kujera, Ceo na rike da kanwarta ta zauna tare da ita a gefenta, Dai dai
nan wata dattijuwar mata ta shigo parlon zata raka
wasu bakinta biyu, tana ganinsu Abba duk da bata
san ko mutum daya a cikinsu ba tayi welcoming dinsu
da fara'a, after seeing off her visitors ta dawo parlon
ta zauna tana murmushi idonta da attention dinta duk
na kan Mayraah tace "Sai dai har yanzu ban wayi
kowa a cikin ku ba wallahi" Tana fadin haka ta kalli
matar dake tsaye tun shigowarsu Abba parlon tace
"Aunty Sadiva a kawo masu ruwa mana ko"' Matar da ta kira da Aunty Sadiya ta juya ta bar parlon don duk
iya kokarinta na ganin ta tuno inda ta taba sanin
Ammi ta kasa tunowa, tunanin da take ta yi kenan a
tsaye amma ta kasa tuna Ammi, Ceo na kallon
dattijuwar nan da ta kasa dauke idonta kan Mayraah
calmly tace "Wajen Mai gidan mu ka zo idan babu
damuwa pls Hajiya" Matar na murmushi tace "Oh...
Allah sarki, to ku karaso parlon nasa ai vana ciki" Tana
fadin haka ta mike, ta nufi wani parlon suka bi
bayanta gaba daya, wannan din ma wani babban ne that is well furnished, tayi masuiso ha A duk suna biye da ita a baya, bayan duk sun shigo ta kulle kofar, tsaye Abba da Ammi da su Maheer suka yi ba tare da sun karasa can cikin parlon ba basa ko kiftawar kirki suna bin duk occupant din parlon da kallo, wani Dattijo ne kishingide a saman lallausan carpet ga fruits iri iri a gabansa, daga gefensa kuma
Musharraf ne zaune sai MD da shi ma yake zaune kasan carpet din kusa da Mamin sa, daga daya side din wannan dattion kuma wani mutumi ne da bazai haura shekaru 48 ba, MD ne ya fara mikewa da sauri tsabar yanda ya rikice yana kallon su Abba da Ceo, sai kuma Musharraf da shi ma ya mike yana kallonsu da mugun mamaki, sannan wannan mutumi da yake late forty's dinsa shi ma ya mike tsaye da sauri cikin wani irin yanayi yana kallon Aaria yace "Maryam?" Ita dai Aaria kallonsa kawai take bata ko kiftawa, MD ya ji kafafuwansa sun kasa ci gaba da daukarsa a hankali ya durkusa kan knees dinsa yana repeating Innalillahi wa inna ilaihi raji'un a zuciyarsa, Mami was dumbfounded sai bin su Abba gaba daya take da kallo, shi ko Dattijon nan da yayi saurin daidaita zamansa in ya kalli su Abba, sai kuma ya kalli Ceo, sannan ya kalli su Maheer, haka nan dai ya dinga bin su da kallo kana ganinsa kasan shi ma dai ya shiga rudani a wannan lokacin, Matarsa da ta kawo su parlon sai bin kowa take da kallo with confusion, infact everybody in that parlor was more than confused, Ceo ta kama hannun Mayraah dake ta kallon su Musharraf da wars da idanuwanta kamar za su fito don mamaki, ita Ammi tsabar kidimewa haka ta bude baki hangangan tana kallonsu, Ceo na Mayraah ta tafi har gaban wannan mutu' A Cane tsaye ya kasa daina kallon Aaria, tana nuna masa Mayraah babu yabo babu fallasa tace
"Abdallah!! Your Child" Tana fadin haka ta juya ta koma inda su Abba ke save ita ma ta tsava tana kallon Abdallah wanda ke ta kallon Mayraah da ta sunkuvar da kanta hawave a sauka idonta kamar an bude pampo, Mikewa tsaye dattijan yayi yana ma Ceo wani kallo yana huci kafin yace komai matarsa warce ita ce mahaifiyar Abdallan ta dakatar da shi, cike da takaici tace "Kar ka ce mata komai, kar ma ka fara Alhaji, fuskar yarinyar nan kawai zaka kalla and it says it all" Juyawa Dattijon yayi ya sake kallon Mayraah, zuwa sannan ne Aunty Sadiya ta shigo parlon tana kallon Ammi wanting to know their mission a gidan Babban vavansu don sai vanzu ta tuna a inda ta taba saninta wato ranan da suka je kai lefen Mayraah da kuma sanda suka je amsowa, Hajiya Ramatu ta fashe da matsanancin kukan takaici a parlon tana girgiza kai, Ceo ta juya tana kallon Abba hawaye cike idonta tana nuna masa Abdallah, Calmly tace "Alhaji wannan mutumi da kake gani shine yay assaulting Kanwata many years ago, putting her in a family way, a sanadin haka har ta samu 'ya mace out of wedlock...." Sai kuma ta nuna masa Dattiion wanda aka fi sani da Hon Alhaji Kabir Saminu tana murmushin takaici hawaye na sauka idonta tace "Wanna kuma shine mahaifinsa wato kakan Mayraah wanda ya sa aka kulleni gidan yari na wata bakwai" Da sauri Abdallah ya karasa gun Aaria da wani expression yana zare ido bakinsa na rawa yace "Did you hide anything from ur sister afterward Maryam??" Wani kallo Ceo ta jefa masa strictly tace "Kar ka kuskura ka firgita min kanwa Malam, stay back" Abdallah ya koma gun mahaifiyarsa cikin kidimewa ya durkusa gabanta vace
"Mommy duk fa kun san abinda ya faru 22 years ago, babu abinda baku sani ba don Allah ku ce wani abu"
Mahaifiyarsa dai sai goge hawayen dake ta sauko mata take tana girgiza kai ta kasa cewa komai tsabar takaici da zafin da zuciyarta ke mata, Mami kam rike kanta da yayi mata nauyi tayi tana nanata Innalillahi wa inna ilaihi raji'un a zuciyarta, in dai abinda ya faru ne a wancan lokacin ai duk kowa a family ya sani ba boyayyen abu bane, zuwa sannan Aunty Sadiya kafafuwanta sun kasa daukarta sai bin kowa na parlon take da ido abu ne wanda ya zo masu dukkansu a ba zata, durkushewa Musharraf yayi a nan kasan parlon zuciyarsa na wani irin bugawa, Tuni Hon Alhaji Kabir ya mike kasan tsadadden carpet da yake zaune ya koma kan kujera ya zauna da kyar ya jinginar da kansa jikin kujeran ya dafe gefen kirjinsa, mikewa matarsa tayi da sauri ta nufesa ta zauna kusa da shi cikin rawan murya tace "Baka da lafiya Alhaji, pls let's take everything easy, we should take everything bit by bit, kar kay stressing kanka, ka kwantar da hankalin

Download complete TXT · Novel page