Murucin Kan Dutse

Chapter 101 of 146

yau ba don gashi yau ka nuna afili da kan ka ka dauko min tashin hankali har dakina gara na koma gida inda akasan darajana da kima ta.
Yace kamar yaya na dauko maki fitina har dakinki a kanki zata zauna idan tazo ko may kike tunane haka da zuwan ta din ina kowa da halin shi zai zauna.
Nace haba daddy kabarni don Allah na yi abinda zai fisheni kadai riga da ka zabi wacce kake da muradi a kanta ba sai ku sha zaman ku ba.
Bina yayi da kallo ganin na mike na ci gaba da shiri na ya dan dade a tsaye yana kallona sai ya juya ya fita har nagama shirina komai da yake nawa na dauka.
Waya na ke ringing na dauka a zatona ko Faiza ce da naiwa magana ta samo min mota sai naga bakuwar nomba ce na dauka da sallama a bakina.
Ina mamakin waye kuma ke kirana da safe hakane wai ban dai kai karshen tunane na ba naji muryan namiji yana karba min sallaman nawa.
Mun gaisa dashi ya kira sunana yace Rahama nasan baki gane mai magana ba ko nace eh hakanane.
Yace to yayan ki Bashir ne abokin mijin ki nace au yaya kaine ya kwana biyu ya iyalin ka yace suna lafiya sai nai shiru.
Can yace Rahama yaya akayi haka kuma daga jin hindatu zata shigo wurin ku ku zauna sai kuma ki rikicewa abokin nawa keda ake yabo kuma Rahama zaki bari har wata hindu can ta bayar dake.
Rahama duk fa wani hannkurin da kike a gidan nan kowa dake tare da ku ya sani don Allah daga yau ki dauri ki zama MARUCIN KAN DUTSE A GIDAN MIJIN KI FITAR KI SAI AN DAURE.
Nasiha sosai yai min masu ratsa jiki har yake ce min duk abinda na gani don Allah na daure na bar komai ga Allah yace dama haka take bukata a gareki ai .
Wanda yayi kaka abu don kaji haushi ka sani shine kuma har zaka bari ya fahinci ka raza da shirin shi don Allah narokeki da ki daure ki zauna dakin ki yi hakkuri yanzu idan kikai fushi kika tafi dariya za ai maki wallahi kin dai san halin ku na mata da tsegumi ba banza Hindatu ta bar mijin ku ba nina sani don ni ke ganin abinda akeyi.
Wanan kuma ba komai bane don kece zaki shawo hankalin komai da zata so aiwatar wa don kara gurbata mashi da rayuwan shi.
Shiru nayi ina sauraren shi sai hawayen da ke zubo min yace don Allah Rahama kiyi hakkuri don tafiyan ki ya tayar da hankalin mijin ku sosai wallahi shi da kan shi ya kirani yake fada min halin da kuke ciki tun jiya daya fada maki.
Shi hakkuri wuta gare shi amna a karshe dadin shi yawa gare shi idan ka daure don haka ki janye wanan maganan tafiya don Allah Rahama.
Cikin muryan kuka nace da ka barni na basu wuri yaya bashir tunda banda amfani a gare shi.
Wa ya fada maki Rahama keko keda amfani a garshi shima ya sani ai don ko sha anin Saade idan da baki hakkuri ai da ba a kai haka ba ko.
Muna gama waya da bashir sai kuma ga mama Laraba ta kirani nace itama an kai karan nawa wurinta ke nan shike nan ni nawa ya samay ni dada.
Mun gaisa ta shiga lalashina ta na bani magana fada sosai tai min tare da lurar dani illar abinda nake son yi din takuma kara fahintar dani yadda zan zauna da hindatun idan tazo tunda na riga na san halin ta nai mata godiya na share hawaye na dole in zauna kada na zamo wacce bata jin maganan manyan ta.
Aisha na kira don ta dauki yaron da ya gama shan nono take cewa dani an fasa tafiyan ne anty nace da ita eh kawai ta dauki yaton tace anty kiyi hakkuri don Allah koma may ye Allah nagani ai.
Ban fito ba shima bai shigo ba da rana nafito inda zamu hada abin buda baki tare da yaran muna kitchen din naji dawowan shi ban damu da naje gaida shi ba yadda nake matukar jin zafin shi ranan.
Shima dakin shi ya shige bai damu da yazo inda muke ba don bats kan mu yakeyi ba ma a lokacin dawowan matar shi nan yake ta faman shiryawa kawai a ganina.
Ina aiki ina tunanen yadda zan zauna dasu mutumin ma da ya ajeka ba wai ya damu da damuwar ka bane a yadda nasan hindatu zanga rayuwa kala kala a wurin ta sai dai ya zama wajibi nima dole na fito da nawa gwanin ta don nuna mata jiya ba yau bane fa.
Mun gama komai na shirya mai inda zai yi buda bakin shi na shige daki nsi wanka na shirya ina jiran lokacin sgan ruwa yayi sai tunane nake gobe iwar haka muguwar bakuwar mu ta iso gidan ko nace a fili ubangiji Allah ya haushe ni kan duk wani kulli da zatazo min dashi a gidan nan.
Sai da na idar da sallah na dan sha tea kawai a dakina don shi nake iya sha a lokacin don raina ba dadi har lokacin a haka na wuni a gidan dashi.
Nafito a cikin kwalliya na yana zaune yana waya yana hango fitowa na ya katse wayan da yakeyi din cikin nuna rashin damuwa na isa inda yake zaune na gaidashi da shan ruwa shima ya amsa min a sake.
Na juya zan wuce sai naji yace dani ina kuma zaki baki ban abinci ba juyowa nayi ina dan kallon shi kawai.
Nace zan koma daki ne naga ai komai na aje a gurin ba sai na tsaya ba yace wa kike son ya zuba min to ?
Kamar nace ya jira matar shi tazo ta zuba mai mana saidai nai shiru kada ya gane kishin nawa yakai haka da yawa.
Sai dai nace dashi naga kamar baka tashi ci bane yanzu kana waya kada na takura maku ne ai.
Yace waya kikaga inayi yanzu zo ki zuba min naci yunwa nakeji dama banci komai ba bayan ruwan da nasha dazun.
Ban musa ba na juya nakoma na fara hada mai abinda zai ci din a cikin plate.
Ya jawo zuwa gaban shi ya fara ci sai na dan so mikewa yace ina kuma zaki kin san dai ba haka kika saba yi min ba ko.
Ban musa ba na samu wuri na zauna a gefe ina amfani da wayan dake a hannu na sai cin abincin shi yake hankalin shi a kwance.
Ya gama yake cewa hada min ruwa na watsa ko zanji jikina ya dan sake min ban motsa don banda nayir tashi a lokacin sai da ya kara fafin bakiji bane sai na mike kawai ba tare da nai magana ba na wuce , uwa dakin.
Na shiga dakin ke na sai ga wayan anty ya shigo min ina hada ruwan wankan muke waya mun gaisa take tambayana ashe kuma Hindatu a wurin ku zats zauna wanan karon ?
Nai murmushi nace haka yace anty tace to akai zuciya nesa dai don kin san halinta ba bakuwar ki bace kikuma kula sosai don kin san makircin ta.
Kagin nai magana sai gashi ya shigo dakin lokavin har na gama hada msi komai da zaiyi amfani dashi a bandaki din.
Nace da anty tayi hakkuri zan kira nan da minti goma sai na kashe wayan na juyo zan fita daga dakin sai naji yai caraf ya rike ni ta bayan shi tare da juyo ni ina fuskantar shi.
Yai murmushi yace ke naga alamar ki idan na biye maki gaba zamuci gaba dayi har bakuwar taki ta samay mu a haka cikin wanan halin.
Mutum ance yayi hakkuri ba sai ya hakkura ba ya barwa Allah alamarin sa anfi son mutum ya dinga hakkuri da duk abinda yazo mai na kaddara.
Na dago idanuwa da suka rine zanyi magana yace ya isa haka please bana son jin wani magana akan zancen nan abar komai ya wuce please.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NE, , , , ,

78
Washegari Ina tsaye a kitchen ina duba kayan amfanin mu sai naga komai akwai sai kaayan miya da muke amfani dashi fresh ne ya dan kare.
Na dan kai lokaci a tsaye ina nazari abinda zamuyi anjima na shan ruwa ina nan a tsaye ne sai ga Aisha ta samay ni a kitchen din.
Tace tun jiya nake tunanen kayan miyan bazasu ishe mu ba yau sai dai idan na za ai miya ba sabo nace ai yazama dole Aisha tunda yaran sin fi son mai miya nagani.
Motsi mukaji na alaman an bude kofan gidaan an shigo cikin gidan sai dai bamuji sallama ba kuma.
Aisha ce ta fita ta gani don yaran suna makaranta a lokacin heleen kuma ta na baya tana wankin kayan ta.
Sai gata ta dawo tana cewa dani Anty maman Ihisan ce fa da wata bakuwa suka shigo naji gabana ya fadi ras nace innalillahi wa inna alaihin rajiun a cikin zuciya na na karasa da Allahuma ajirni fi musibuti wa, akalilli hairan min ha.
Take naji natsuwa yazo min a lokaci daya na daure na fito daga kitchen din daidai lokacin da yai daidai da shigowan maigidan shima.
Fuskan shi asake yake fadin ashe har kun iso ko tace wallahi ko kasan sammako mukayi don mu iso da wuri dama.
Sannu da zuwa nake mata amma sai tai kamar batajini ba tai wani sharewa na juya wurin shi ina mashi sannu da dawowa ya amsa min hankalin shi na kan su.
Na juya zan wuce naji yace ina kuma zaki Rahama ga baki anyi na waiwayo ina kallon su kafin nai magana naji tace bakuwa dai nikan aiba bakuwa bace a gidan nan.
Murmushi nayi kawai na sa kai zan wuce yace ina tambayan ki zaki wuce kuma mana ?
Sallah zan shiga nayi lokaci ya gabato na bashi amsa da hakan na fara tafiya abina batare da na tsaya ba yace idan kin idar da sallah ki samay ni a falo na shige abina ina jin suna dararakun su nace lokacin ki ne mata.
Alwalan na shiga na dauro na fito na shimfida abin sallah nafara gabatar da Nafila sai na kawo azahar nayi ban tashi ba na zauna ina rokon ubangijina da yai min kariya akan hindatu dama ko wani mai kina.
Can bayan wani dan lokaci naji muryan shi yana kiran sunana daga kofa sai dana dan dauki lokaci na fito falon ya zaune itama din tana zaune a gefen shi bakuwar ina tsanmani tana daki ne.
Na iso wurin naji yace kin shiga kin zauna kuma bayan na fada maki idan kin idar ina jiranki a falo nace ai gani yanzu na idar da sallah dama.
Na samu wuri na zauna a daya daga cikin kujeran dake falon ban dago kai na kalli gurin da suke a zaune ba kamar zata shige mai jiki.
Ya dan juyo yana kallona nai kamar banga yanayi ba don ba zan ba da fuskan da zata zo min da zafi ba don nasan a shirye ta tako garin da ganin yadda take wani fisge fisge.
Hindatu tace dear ya sauke ajiyan zuciya ya dan waigo inda nake yace Rahama nace naam daddy yace magana nake son yi daku tun yanzu kafin yaran nan su dawo daga school.
Ai muna jin ka tace dashi yace ba wai na hada ku nan bane don aita min rigima ko tashin hankali ba a gida na kawo kowan ku nan ne don mu zauna tare mu tsira tare bana son jin fitina ko hayani daga kowan ku a gidan nan in ba haka ba ran mai shi zai baci.
Sai kuma zancen yara yarana kun san bana son banbamci kowa ya rike min su kamar duk ku kuka haife su da cikin ku.
Ina ga sauran bayani kan kwana wanan ya rage a tsakanin ku kuka san yadda zaku raba abin ku dai.
Sai tace ai wanan ba matsala inkaji fitina dama an dauko shine kowa ai yasan halin kowa a cikin mu banga abinda za, a tsaya kuma fadi ba yanzu.
Kwana kuma yadda muke a baya can gida haka zamuyi ko yanzu two two days kowa yayi ya fita ba shike nan ba.
Na juya nace shike nan zan iya tafiya kagama ko yace shike nan abinda zan fadi dama bana son jin komai a gidan nan .
Na mike na barsu zaune tun kan na shige naga takai kwance a jikin shi yace a, a baki da hankaline hindatu Azumi fa mukeyi.
A raina nace duk abinda kika zo dashi dai gida kika zo don yanzu ba Rahaman da bace wanan da kike fadawa son ran ki.
Juyowa nayi na kira Aisha tazo daki ta samay ni dama tunda naji cewa zata dawo nan nasa suka dawo dakin dake kusa danawa hannun mu daya dasu.
Ta shigo tana dauke da Haidar daya tashi daga barci nace kai har ka falka ke nan wanan barcin dai baikai ko ina ba.
Ta zauna nace da ita dama ina son kara ja maki kunne ne akan zaman matar nan damu na dai fada maki har helen don babu ruwan ku da harkan ta.
Tace anty na sani kuma Atika ma naja mata kunne tun jiya har helen din yanzu ma na fadawa helen din tazo.
Nace shike nan ba wani abu bane dama tace abinci fa nace yadda
naga wanan matar tazo Aisha bari muga gudin ta tukun don kada muyi tace kuma waya samu.
Bata fita ba nan ta zauna abinta muna hira helen ma ta shigo tace dani anty naga dare ya fara abinci fa sai dai naga wanan matar a kitchen tana bude bude nace yi zaman ki mu gani.
Can muka fara jin kamahin girki na tashi a gidan sai da nai sallah la, asar na fito daga daki na samay ta tafito daga kitchen din nake cewa ashekina ciki bata ko kalli inda nake ba tace eh kawai ta shige.
Na koma daki abina ban jima da shiga ba yaran suka shigo gida sai ga su sun samu bakuwa a gidan Ihisan kan da murnan ta ta fada a jikin uwarta.
Tace wa yaran ku halan kunyi bakin ciki da ganina ne naga kunyi wani cirko cirko kuna kallona kamar kun ga bakuwa.
Jinior baiko bi ta ianta bw sai cewa yake ina little mum din mu take helen da ta kwaso shayi ta daka mata tsawa tace ke yar aiki kizo ki kwashi kayan nan ki wanke.
Sai yarinyar tace anty bata bari na wanke masu kaya ita ke wankewa ko Aisha tace to ni ba antyn bace maza zoki kwashe su.
Kamar nasan sunayi sai gani na fito daga daki naga helen tana wanke kayan abincin namu nace da ita helen yaya haka bana hanaki ba ashe ?
Tace wanan bakuwar anty ce tace na wanke mata na fada mata tace sai na wanke kafin in magana sai najita daga baya na tana fadin eh nice nan nasa ta wanke muna su.
Nace amma ni bani bari ta wanke muna kayan ibadan mu don ba musulma bace ko kin manta watan azumi muke watan ibada ne.
Na manta kin san bani azumi ne sai yanzu danaji daga bakin ki dai na tuna kallon mamaki nai mata kawai nace helen bar kayan na wanke su shige dakin ki.
Sai cewa tayi dama nasan akwai tsiya akan yaran nan dake don dama naji komai gamay dasu to ki sani duk wace tazo cin arzikin mu ba zan barta ba.
Sai lokacin na juyo nace da ita wasu ko wasu kan ai kina ganin su dole ki barsu inda kika gansu din.
Tace haka kika ce ko nace kwarai kuwa ai kema kina da ya da ar aiki sai ki saka su don ban saka naki ba.
Na wuce abina na barta a tsaye ta fara haushin ta data saba don ba yau ne farkon ganin ta ba a gare ni nasan ta nasan halin ta tun a baya.
Ina shiga daki sai ga Nasir da Jinior Nasir ke cewa dani little mum wai may wanan matar tazo yine a gidan nan yaushe ne kuma zata koma ta barmu please da zuwan ta tafara wa mutane fada a gida haka.

********* ********* *********
An sha ruwa kowa yana dakin shi gidan ya koma shiru ranan daga hindatu sai daddy ne a zaune a falon ga abinci dafa duka data dafa ya saka a gaban shi tun cibi daya daya diba ya hade shi da kyat bai sake iya kara na biyu ba.
Don yaji da kaurin kuna dake tashi ga abincin ga ba magi ko mai naiji ba wai shi may azumi zai yi buda baki dashi.
Sai faman surutu take zuba mai yana dai amsawa da kyat da eh a, a don biye mata kada ranta ya baci.
Na fito daga dakina dauke da Haidar na samay su zaune a hakan na gayar dashi da shan ruwa ya amsa da fara,ar shi yanawa haidar wasa.
Ban saukr yaron ba na juya abina na wuce zuwa kitchen don Nasir ne ya fito dani nai mashi abinda zaici ba zai iya cin wanan abincin ba.
Miya na hada dole a cikin daren nan na zuba shinkafa a rice cooker na dafa masu shine yaran gaba daya sukaci suka kwanta niko na sha tea kawai.
Washegari abinci ne tule an barta dashi a kitchen ta fara fada da masifa don taga tunkuyar da naiwa yaran abinci da shi.
Ta kwasa fuu taje ta fadawa maigidan harda zancen helen da yadda mukayi a jiya din sai da ta fada mai komai.
Ina jiran yai min magana sai banji yayi ba haka ta zubar da abinci mai yawa tunda ba almajiri ko wani mabukacin da zata iya ba anan.
Yau da

Download complete TXT · Novel page