Murucin Kan Dutse
Chapter 100 of 146
watan Azumi saura yan kwanaki a lokacin sai kuma ba hankalin maigidan wuri daya don da gani akwai abinda yasa a gaban shi.
Ni dai ban tsananta wa kaina sai nasan may yake ciki ba ina dai kokarin wurin ganin na sauke duk wani nauyin da ya dace ai mashi.
Wani abinda na lura dashi kuma shine duk dare sai mun kwanta za, a kira shi da waya zai dauki lokaci yana waya.
Lokacin ne na fara shan jinin jikina da gane cewa da mace yake waya sai na nemi walwala a tare dani na rasa amma duk da hakan bani nuna komai a fili na bar abin a raina kawai.
Ana azumi saura kwana ukku lokaci duk kwanan shi shidda da dawowa yace zai koma kano a gobe banyi mamaki ba ko zaton wani abu tunda nasan cewa gida ne can kuma akwai iyali.
Sai da ya shirya yafito yana waya naga shirin wucewa yakeyi nace daddy sai ya juyo yana kallo na naji yace da wanda yake wayan minti biyu ya kashe ya kara juyowa inda nakke yace dani umm,humm ?
Na dan kwantar da murya nace daddy dama naga kafin ka dawo za a tashi da azumi shine nace baka sai muna abin taron azumin ba.
Yace ban fahince ki ba may kike nufi da hakan nace wai da nace kayan shan ruwa kodon yaran nan ko ?
Yace Rahama yaushe kika fara wanan halin har ni zakice wai ban sayo maku wani abu ba ko may kike nufi da wanan maganan naki ?
Ko kin taba min magana akan na sayo maku abu a gidan nan bani ke sayowa ba in naga dacewan hakan ?
A sanyaye nace don Allah daddy kayi hakkuri nayii kuskure dama don naga wancan karon ka dan jiima baka dawo bane yasa nai magana yanzu din.
Yace o,wo yai min wani irin kallon sama da kasa kamar wanda ke hake dani dama yana jirace na tanka mai.
Nace Allah ya tsare aje lafiya adawo lafiya yace amin kamar a hasale ya juya ya wuce abin shi batare da ko juyowa ba again.
Mamaki ya kamani nakai zaune a kujeran dake kusa dani ban san abinda yasa daddy yanzu magana ba magana ba sai ya hauni da masifa sosai.
Aisha ce takawo min Haidar da ke kuka na karbe shi sai ga baba ya biyo su ya kwanta a jikina nan na sauke ajiyan zuciya na gyara ina fitar da nono nabawa yaron.
Ina shayar da yaeon ina tunane ga baba da ke tsaye rabin jikin shi kwance a jikina ya damay ni da tabe tabe a fuskana.
Nace a sanyaye don haushi nakeji a raina bari mana baba yaton bai bari ba nakai mai duka akai abinda bana yi duka sai dai inwa yaro fada.
Take yaton ya fara kuka sai kuma yabani tausayi bashi ya bata min rai ba na fashe haushin uban shi a kan shi.
Na jawo shi da hannu daya ina lalashin shi har na samu yai shiru Aisha taji kukan shi ta fito tana tambayan may ya samay shi kuma ?
Nace baijin magana ne na dan duke shi shine kikaji ya bare baki haka yana damun mutane da kukan banzan shi.
Nan dai taja yaron suka fice suka barni ina tune a zaune sai naga ni may ma yakaini yi mai magana bayan nasan yadda muke a yanzu dashi.
Sai zuwa sha biyu har lokacin banajin dadin yadda muka rabu ya tafi dani a hasale sai na yanke shawaran kiran shi na bashi hakkuri.
Kira daya biyu ga hudu ya daga yace cikin muryan shi mai nuna har yanzu baya jin dadin ranshi da fadin.
Yaya akayi kuma na dake nace ba komai sannu da hanya kawai dama zan maka sai kuma na baka hakkuri bisa ga saba makan danayi da zu a yafe min don Allah nayi kuskure na sani.
Yace is ok sai anjima ssi ya kashe wayan kit bin wayan nayi da kallon mamaki may naiwa daddy ne haka nake tambayan kaina ?
Abinda ban sani ba ashe bani kadai ke fuskantar wanan halin ba kowan mu ya rasa gane kan shi tun zuwan shi gidan su hindatu abubuwa suka jagule baki daya a kan shi.
Wanan zuwan da yayi yazo a tsayar da maganan komawan ta gidan shi har ya iso gida baida walwala ba isa gidan shi ba sai da yaje gidan su hindatu ya zube tsaraban da ya sawo masu a hanya.
Ya samu iyayyen shi da zance sai dai hajiya ta nuna bata yarda ba taso abar hindatu a hakkura hakana a hakkura kawai.
Amma yadda daddy ya dage sai hankalin su ya tashi Alhaji yai gyaran muryan yace kinga ayi hakkuri tunda shike da abin shi don haka barshi ya gyara auren shi a zauna lafiya.
Dole hajiyan ta hakkura sai dai bataso hakan ba Alhaji ya tura manya aje a gyara zancen sai ga masu zuwa sun dawo da sabuwar magana kuma.
Wai iyayyen hindatu da ita kanta sunce in har zai amincr idan ta koma ya maida ita Abuja da zama ita ma ta amince da zata dawo.
Nan hajiya ta hau fada tace sam ba zai yuyu ba anan ma gaban kowa yaya aka kare da ita balle ta bisu can inda babu idon kowa sai su yasu yasun su.
Amma daddy na zuwa yace may zai hana ya amince da nan da can ai duk gidan shine shike da iko akan komai don haka ai wanan ba matsala bane ai.
Hajiya tace yanzu da hankalinka Alhaji karami kake wanan magan kafa san halin yarinyar nan sarai bawai ta canza bane .
Yace kai hajiya ita hindatu wani haline da ita kawai ni keda gidana ai zan san yadda zanyi indon wanan ne ai ba wani matsala akan shi.
Tace a, a fa yar mutane dake can zaune kalau cikin rufin asirinta kada taje ta tayarwa yar mutane da hankali kuma ?
Hajiya ita da Rahama din ai duk ni aje su ko may zai kawo wani fitina kuma yanzu tunda kowa yasan kowa dama .
Hajiya bata dai gane komai ba don ya dage daya amince da atafi din shi ba matsalar komai ga yin hakan tace to shike nan ai may daki shiyasan inda ruwa ke mai yoyo.
An mayar da aure ko su anty dake garin basu da labari sai ji da sukayi ga bakin shi yake fada masu batace dashi kalla ba don ta fahinci irin rawan kafan da yake duk aanan lokaci ta san kuma ruwa baya tsami banza ai.
Bayan kwana biyar sai gashi ya dawo lokacin Azumi nada kwana biyu da dauka bai nuna min komai ba mun tare shi cikin mutunci.
Sai bayan an sha ruwa yana zaune da yaran suna hira na shigo falon bayan na idar da sallah nai mashi sannu da shan ruwa na juya zan wuce yace dani gobe ina son duk wani kayan daki a fitar sai za a saka sabo ne .
Na juyo da mamaki don naga kayan ai basu komai ba amma kuma sai na share don kada na daukowa kaina magana nace Allah ya kaimu kawai.
Sun gama ya sallami yaran yai shirin kwanci sai dana fahinci cewa yadan dade da shigewa na shirya naje dakin.
Na mulke jikina da ture masu kamshi don kawar da karnin nonon da nake shayarwa a lokacin.
Har na shiga na kwanta yana waya bai gama ba har barci ya dauke ni ya gama bai tayardani ba sai da muka tashi don yin sahur.
Washegari tin safe muka tashi da aikin kwashe kayan da ya umurce mu dayi bamu jima da kwashewa baaka fara shigo da wasu iri dirka dirkan kujeru masu kyau da girma.
Ma aikata suka gyara komai sai dai dakina da dayan dakin dake facin din na ihisan komai nashi iri daya ne da nawa kala ne kawai aka banbanta masu sai biyu zuwa uku suka gama lokacin ina kitchen mun fara hada abin buda baki ko.
Munyi mamakin ganin hakan amma naja bakina nai shiru ban tsaya magana ba don jin ko yaya hakan din.
Sai dare sosai ya dawo har yaran sun shige ko dakun nan su don azumi ne kowa ya gaji ba wani dogon hira.
Ko ni har na shige na kashe wutan falon ya dawo gidan jin motsin dawiwan shi yasa na fito ya na zaune yana cin abincin da ya samu an jera mai na buda baki.
Nai mai sannu da zuwa ina kokarin juyawa naji ya kira sunana na dakatar da tafiyan dana fara yi tare da juyowa gare shi.
Yace zoki samu wuri ki zauna ina son nayi magana dake ne samun wuri nayi na zauna sai dai ba gaf dashi ba.
Yace Rahama ina son yin wani magana dake ne sai dai ina fatan zaki fahince duk da nasan ba wani bakon abu bane sosai a gare ki.
Gabana ne ya soma harbawa don ban san wani magana bane wanan wanda ba bako na bane haka ?
Maganan da zanyi bawai ya sabawa sharia bane ko da wata manufa zanyi sai dai daurowan hakan .
Na tattara natsuwana ina sauraren abinda zai fada min din a yadda yake maganan shi mai kama da roko kuma da gadara yasa nasan akwai wata a kasa.
Jin nayi shiru yasa ya dago kai ya dan kalle ni yace dani kina jina kuwa nace inaji kai nake saurare ai .
Yadda nai magana yasa yasan a shirye nake ke nan da inji abinda zai fada din a lokacin.
Ba wani magana bane sai dai kiyi hakkuri a yadda na tsara zaman mu a baya yanzu an samu akasin hakan don Hindatu zata dawo nan garin ku zauna tare.
Dam dam naji gabana ya fadi shike nan ni nawa ya samay ni inko hakane gara kawai na barsu na koma kano komai ya fanjama fanjan.
Kinji abinda na fada aiki nace kwarai kuwa ai wanan ba matsala bane don gidan ka ne danan da can sai dai ni zan barku na koma kano na zauna tunda dama na gama abinda ya kawo ni garin ina ga zaifi maku dadi hakan ma don ku sakata ku wala ba sai na tsaya a tsakanin ku ba.
Yace aiko kina nan bazaki hanamu sakata ba kamar yadda itama bazata hanaki sakata ba din.
Don haka gara na koma inda na saba yafi min zama a cikin ku mu kadai dagani sai ku a garin mutane.
Yace wanan kuma maganan ki ne kin dai ji tsarin danayi yanzu a gidana nace naji don haka zuwa jibi zata iso don mun mai da auren mu da ita.
Nace ai naga alaman an maida aure tunda take son zuwa takurawa wacce ka sayo ba auro ta kayi ba kamar kowa dama dani tafita yanzu kuma ta dawo dani a ranta.
Yace wanan kuma tunanen ki ne hakan ni dau gidana ne kuma yadda nake so zan tsara kowa na da hakki a gare ni .
Idan zaki fahince ni ki kwantar da hankali don babu abinda zai faru tunda ita ba bakuwar ki bace.
Ni dai na fada maki abinda ake ciki in zakiyi hakkuri ku zauna lafiya dan ba wanda ya kawo wani a cikin ku nina kawo kowan ku kowa kuma da halin shi zan zauna dashi.
Na mike nace wanan sai kuma a yaudari wata ba ni ba Allah ya baku zaman lafiya dama tare na samay ku ai koda na shigo don haka kunfi kusa.
May ya kawo zancen yaudara anan dukkan ku ai mata nane babu wacce zan tsaya yaudara daga cikin ku.
Banyi tsamanin jin haka daga gareki ba a yadda na tsamoki da farko daga cikin ku na kawo ki nan don yanzu nace wata zata zo ku zauna shine zai zama matsala.
Na juyo tare da tsayawa nace tun farko ai saida na baka shawaran yin haka amma kace dani ba tsarin ka ba ke nan haka kaga dama.
Sai yanzu din ta kullo ni arai zata zo tace zata shiga min rayuwa ban sa akai ba balle a kar min .
Kuma kafin ma ta taso ni na isa gida ko sai tayi da wata amma badai Rahama ba dai kan.
Inda nasan wanan shirin kake kwana da kwanaki aida baka bata lokacin ka ba gurin shiri da kafada min tuni da angama ai.
Na juya na wuce zuwa dakina ban kara tsayawa sauraren shi ba ina shiga nafara hada kayana dake cikin wardrobe.
Tsab nagama shirins tunda dare na rufo kofana tare da hayewa gado wurin yara na da Aisha dake kwance gefen su.
Barci ya kaurace min a idona sai faman tunane nakeyi don na tabbatar da wanj manufa hindatu ta zabi biyoni Abuja wanan karon wanda manufan bai wuce kalman daukan fansa ba akaina.
Tunda dama tana cewa a dalilin shegen dana akai mata saki don haka sai ta rama abinda nai mata koda zata tafi tsirara ne.
Abubuwan da daddy ke min duk kwana kin na dama nasha jinin jikina da akwai wata akasa gashi kuwa yau naji da kunnuwa na.
Kai namiji sai a barshi kawai idan ya tashi munafuncin shi sai dabara da wayo ya bace mashi wai yau daddy ne da bakin shi yake ce min da hindatu zamu zauna gidan nan.
Matar da bata maida fitina bakin komai ba aida in zauna da ita gara nakoma can in ma dafani anty zatayi yafi da hindatu ta shigo min da balai gida.
Wai ma sai bayan da ya gama komai shine yanzu ya mayar dani sakarai yazo fada min abinda ta zaba don ta dawo mai.
Ba wani dadi naji ba koda nike ni kadai din balle ace an karo min sabon fitina akaina.
Ni wanan rayuwan auren da may yai kamane wai kullun sabon fitina da kanana kanan rashin fahinta ke zo muna.
Ni dai arabu yafi min komai sauki da wanan zaman danger da muke da kishiyoyi wi da mijin ma haka wi.
Da yake barci barawo ne sai da yai dabaran satana cikin wanan halin da nake ciki da asuba ranan shi da kan shi ya tashe ni inta dasu Aisha suyi sahur acikin waya.
Ban fito don sahur ba dama ni ban damu da yin sahur din ba kullun balle yau da raina yake a bace.
Ruwan sanyi kawai nake da bukatan sha na koma na kwanta nafito falin din in dauki ruwa a kitchen nan nagan shi zaune yana shan tea suna sahur shida Nasir don yaron akwai shi da kokarin Ibada sosai.
Ban ko kalli inda suke ba na wuce zuwa kitchen kai tsaye sai Nasir din ke cewa dani kin tashi mummy nace eh Nasir ba tare da na tsaya ba na wuce abina uban yabini da kallo kawai.
Ganin yaron ya bini da kallo yasa yai murmushi yace yau mummy ka fushi take kyale ta yaron yace but why daddy yace wa yaron nothing cikin daga kafadan shi.
Sai can yace wai bata son dawowan maman Ihisan nan gari haba daddy a gidan nan wanan matar zata dawo ta zauba da mu haba haba gidan zai zama badadi ke nan daddy .
Wani tsawa ya dakawa yaron yana fada dashi Nasir har yaushe kasan irin wanan magana ina ruwanka da harka.
Yaron ya ja bakin shi yai shiru haka ya mike ya bar uban zaune a falo ya bi bayan yaron da kallon mamaki da takaici.
Kafin karfe bakwai na shirya tsab na shirya yaran nawa kuma tare da Aisha da Atika sai helen da nake tunanen yadda zanyi da ita don dole na sallamay ta koma gida.
Muryana da Aisha ya tsinkayo daga dakin shi lokacin da nake cewa da ita kuyi sauri ku shirya bana son muyi tafiyan rana don kun san azumi ne ga helen ta dage da kukan ta wai sai ta bini a fadawa wacce ta kawo min ita tare zamu tafi.
Ban fi minti biyar ba da shiga ya shigo dakin da sallaman shi ya bi kayana dake a tsakiyan dakin cikin troler dina da kallo.
Ya juyo inda nake yana murmushi yana cewa wai ke da gaske tafiya zakiyi ne kike nufi Rahama don dan wanan magana ?
Ban juyo na kalle shi ba sai takarduna da nake cusawa a wani jakkana ganin ban juyo ba yace dani ki zauna muyi magana ban jiyo ba still sai ya karaso inda nake a tsaye din ya kamo hannuwa na duka biyo na dago idanuwa da suke cike da bacin rai na sauke a kan shi.
Ganin yanayi na yasa ya fahinci a cike nake da bacin rai tun daren jiya sai yaji baiji dadin yadda a lokaci daya na sauya ba akan may zan sawa kaina damuwa dayawa haka don kawai wata zata zo mu zauna a tare.
Amma a fili sai cewa yayi Rahama kin bani mamaki wallahi ban taba tsanmanin wanan matakin ba a gare ki don kawai wata zata zo shine abin bata rai gareki alhalin kin san dama bake kadai bane gareni.
Kiyi hakkuri ki kwantar da hankalin ki yanzu ai in kin wuce sai tace tsoron ta kike yi har kin gudu ko kina kishi da zuwan nata nan.
Na dago idanuwa na na sauke akan shi akamar zanyi magana sai na zare hannaye na daga gare shi a raina nace kai namiji dai bai da tunane shi yanzu har ya matan irin rikicin dake tsakanin mu da ita ne a baya inda bamu haduwa wuri daya ba ai fitina ba.
Balle yau ace wai har shi da kan shi zaiyi sha, awan tara mu a gida daya irin wanan wani irin gululun bakin ciki ya tokare min zuciya na naji ko ganin shi bana son yi a idona tare da dana sanin zama dashi.
Zama nayi idanuwa na suka fara fitar da hawaye n takaici zama yayi a kusa dani ya kamoni zuwa jikin shi na fisge da karfi nace kada ka soma ka tabani wallahi na gaji da yaudara irin naka.
Baka kauna ba ka sona zaman dole kake dani na sani ba